A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????????????????

Kaga Bari na ajjeka anan Idan kaga najima ban fito ba Dan Allah kar Ka tafi, ko kuma kake lekowa ta kofar tunda a bude take, gaji? Don Allah fah,

Mus’ab yace’ taya Zan tafi na barka anan ai hakan bazai iyuba ma, kasan nasan halimu,

Yawwwa fav I love you,
Yafada Yana rungume Shi, shima rungumota Shi yayi yace’ I love you too twinny prove them Zaka iya Ka Basu mamaki, Kaji ko?

Gaban Shi faduwa yake kuma yasan fav din yasani kawai be masa magana bane, jinjina masa kai kawai yayi sannan mus’ab ya fita ya samu gaba da gidan kadan ya zauna ganin Dan abin Zama haka,ya juyawa gidan Baya kamar ba anan yake ba, shikuma yayi horn, aka bude masa,ya sai yazo saitin Mai gadin ya Mika masa hannun suka gaisa,

yace’ am Dan Allah kuwa Sameera tana ciki?

Mai gadin yace’ ehh tana nan,

Yace’ to Dan Allah Dan min sallama da ita bari na gyara parking,

Sannan ya shigo shikuma ya rufe gate din sannan ya wuce cikin gidan, bema wani Gama Shigar da motar ba kawai juyowa yayi da motar daidai idan zai fita kawai ya fice basai Yana Kwane Kwane ba,be wani jima ba Mai gadin yazo yace’ tana zuwa,

Shikaidai yasan yarda zuciyar Shi take bugawa Ashe de da beji komai ba Yana ganin su a lokacin Yana ganin ta fito ya kulle Ido ya rufe, ya dauko wayar sa Yana kallan hotanta dake wallpapern Shi a fili ya furta I sacrifice for u,kome za’a min Zan jure sabida ke, I love you My naughty girl, lovely sis ever,

Sameera kuwa tunanin Wanda ya kirata tayi, kofar a bude hakan yasa ta nufi wurin kofar data gani a bude,duk wani takunta da zuciyar Shi take
Takawa bugunta karuwa yake,

Tana zuwa tace’……..

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

  36

Da Asuba bayan sunyi sallah suka koma suka kwanta, ya kwashe duk yarda sukayi da Alhaji Munir ya fada Mata,

yace’ yanzu na rasa mafita,bansan ya zamuyi ba,

Shiru tayi tana sauraran sa kafin ta dago,
tace’ ya kake gani idan aka ninka masa kudin orphanage din, idan yaga zunzurotun kudi zai yarda,

Yace’ kina ganin hakan zaiyi kuwa?

Tace’ sosai ma,Abu na farko da zakuyi ba bakar fata zaku sa ba, a Kira Wanda yake Felix Wanda yake Kula da companyn Paris kaga komai zai zo da sauki, tunda yasan Abban mu, kuma shin Abban idan yaga farin fata kuma yaga kudi da gudu zai yarda,

Yace’ yarda kika ce hakan za’ayi,

Tace’ idan kun dau shawara ba? Amma a ganinka ba kuwa wani business din yake zuwa ba? Wanda Baya so a sani? Yake fakewa da zuwa company?

Shiru yayi Yana jiya maganar ta,
yace’ banyi tunanin wannan ba,

Tace’ yanzu kayi,

Tace’ companyn Abuja shine next target, Dina,

Yace’ mezakiyi?

Kawai kudai ku dai ku zauna ku zuba ido, ku kula da komai,
Tace’ Amma a Naga 40 million muka ansa taya Ka sai company nan?

Yace’ ina ruwanki, kawai ki zuba ido kiyi kallo, ki Kula da aikin da kikeyi,

Murmushi tayi tace’ time will tell,am sorry,

Shima murmushi yayi,kawai ya rungumeta,

Tace’ Bana Jin ya bar mana wannan companyn, dole zaiyi wani Abu akai,

Yace’ kamar ya?

Tace’ kamar yarda da na fada ma,dole Yana Shirya wani Abu,

Shiru yayi yana tuno abinda ta fada masa Yana hadawa wuri guda, ya ilahi,

Da safe tana bacci ya Shirya zai fita, Baya so ya fita ya barta Amma ta Zama dole ya fita tsab ya Shirya abinsa har yazo bakin kofa sai kuma ya juyo ya ganta kamar ya kamar ya dawo yakeji sai dai idan ya tuna aikin da zaiyi sai kawai yasa Kai ya fice Yana tunanin ta, key din ya Bari a jikin kofa, yarda zata gani sannan ya fice, wurin mota ya kalla anan ya tuna su Mas’ud girgiza Kai kawai yayi ya fita, ya kulle Mata kofar gate din,ya fara takawa a kasa gashi unguwar shiru babu kowa a Layin duk Yan makaranta sun tafi Baya gahaka kuma Layin su duk wayanci Amareni da sabbin zuwa a Layin su, tafiya yake har ya karyo kwanar da zai sada Shi da babban titi Yana tafiyar sa, mota ya gani tayi parking a gaban Shi ya dago,yaga waye, su yusseer ne kallo Daya masu ya gane su,

Yusuf yace’ Ka shigo mu tafi,
Murmushi yayi zaiyi magana yaseer ya fito ya koma baya, shigowa yayi suka tafi,

Yusuf yace’ ina zaka je?

Yace’ kunga ku ajjeni ma a bakin hanya don wurina da nisa kuma school zakuje Kar ku makara,

Yaseer yace’ ai lecturer bazai zoba shiyasa ma yau bamu fito da wuri ba,

Yusuf yace’ ina ne?

Yace’ Ida kasan Tsohon M&M to nan,

Shiru yusuf yayi, yaseer ne yabada amsa da yasani,

Yaseer yace’ yanzu ai ya koma Ummu,

Ummu tace’ ehh sabida sunana akasa shiyasa Abubuwan su suke da dadi, ba?

Yaseer yace’ kaga shirme, wayace maki haka ne to?

Yusuf yace’ kawai dantaji ance Ummu,

Tace’ bawani nan sunana ne, Ummusalma Ummu nan gani nan Bari,
Tace’ daman ma Baku dawo ba da bakina ya huta da masifa,

Dakwa har yanzu kina nan a rame ai, kamar a hure ki hantsala,

Rama bata Hana mutuwa,

A tare suka ce first time in history,

Banza tayi dasu bata tanka ba, sai kuma can, tace’ laaaa mu gaidar dashi ba,
Yaya ina kwana,

Shi dariya ma suke bashi,kawai de yayi shiru, da lafiya kawai ya amsa Mata, sude shiru sukayi Basu gaida dashi ba tunda sun san sun Zama abokai,

Lokacin suka karaso wurin, godiya ya masu zai fita,
Yusuf yace’ Dan Allah nace ko kasan Wanda ya siya companyn nan?

Murmushi ya masa Mai kyau yace’da damuwa ne?

Yusuf yace’ a,a bakomai kawai de ina San sani ne Dan Allah,

Binaif yace’ nine, da matsala?

Yusuf yace’ innocent you? Besan a fili ya furta ba,

Binaif yace’ lafiya kuwa?

Yusuf yace’ ah bakomai inasan numbern Ka Dan Allah,

Beyi musu ba ya ansa wayarsa ya saka masa ya Kara masu godiya ya fita.

????????????????????????????????

‘ya’yan Hajiya ne dukan su suka zo kwansu da kwarkwartar su tamkar yaune ake bikin kowa kaga ni Yana cikin farin cikin zuwa gida, sukan zo akai akai sai dai ba dukansu suke faruwa irin na yau ba wasu sun haihu wasu kuma har yanzu Allah be Basu ba wasu kuma Daya haka de suka zo, babbar su wacce ta girme su,

tace’ Hajiya ya kamata muje muga mu ga matar Binaif,

Mebinta itama ta girmeshi,
tace’ wallahi kuwa hakan ya kamata,

Hajiya idan kunje sai ma ku kwana Dan ku muzguna Mata daman ‘yar kauye ce,

Saima tace’ nidai babu inda zani, bazani gidan ‘yar kauye ba,

Wata daga cikin su, tace’ Haba Anty Mariya da Anty zakiyya ba wallahi ba yi bane hakan Yakamata Ku San fa yanzu kun girma kuma kuna da yaran da zaku aurar nan gaba gaskiya hakan beda riba Sam wallahi,

Anty Mariya tace’ ke Dan gidanku kema yanzu kin girma ko? Har zaki ke fada min magana haka?

Tace’ Ai gaskiya ce na fada,ko Baki da ‘ya ai kinda kannai baza kiso ayi masu haka ba,

Anty Mariya tace’ ikon Allah yau ni Mariya Hudaya take fadawa magana haka, Kauwar kauwata cab,kefa kauwata ce ta wurin hudu fah imagine,

Anty zakiyya tace’ Ai kina da akusa Dani take sai mangareta marar kunya,

Hajiya tace’ kunga ya isa haka kedaman tun kina karamar ki kike kawo musu cikas idan bazaki ba ki zauna a idan ba lalle ba dole, sude dukan su zasuje harda yara ma kuwa manyan yaran ne kawai baza’aje da su ba kima ji dawai atoh bana San shashanci banza Dana hofi,

Hudaya shiru tayi batayi magana ba,

Anty tace’ Ai ni lamarin Hudaya wallahi Yana Bani mamaki Sam sai kace Bani na haifeta ba,
Zarah’u tace’ ahh mu ai zuwa dole ne wannan muje muci uwar ‘ya wallahi ko ya kukace,

Khadija tace’ wanna hakkun ne wajibine kafin ma yarinya tazo ta rena mu gwara take Baya Baya idan anzo abin dangi a to,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button