A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dawowar Rukayya gidan yasa na dena aiki ita take yi idan kuwa zanyi to tare zamuyi shakuwa Mai karfi ce ta Shiga tsakanin mu harta kai da bama maganar da Hausa sai da fulatanci babu abinda take so irin taga na haifi abin dake cikin na ga wata irin son yayan ta da take yi haka shima Yana san ta wannan abin yasa aka hadawa Rukayya tarkon sata Hajiya kuma ce ta hada wannan abun ba kowa ba hakan ya mugun bata min rai kuma nasan Hadi ne tun daga nan ya dena Kula ta sosai duk wani Abu Idan aka nema aka Rasa sai a zo dakin da take kwana za’a same shi tun yana Mata magana har yazo ya dena ko ta gaishe Shi Baya ansawa bata taba fada ba ta rike abin tsakanin nida ita har ciki na yayi girma yazo watan haihuwa muna zaune kullum da irin abin da ake fada masa muna cikin damuwa sannan ni kuma Bana iya fada masa sabida wannan zurfin cikin nawa da beda amfani ko kadan.
Kwatsam wata Rana da daddare suka zo lokacin har na fara bacci dayake ba a daki na yake ba ranar suka tashe ni ita da kawar ta Hafsa tace zabi biyu zasu bani na farko idan na haifi yaran nan zan tafi na barshi su zasu Kula dani za’a nemi ni a rasa na biyu kuma idan na haife Shi ban tafi ba zasu yi ajalin abinda na Haifa sannan kuma suyi ajalin Alhaji sannan kuma suce nice nayi wannan abun. Nasan zasu aikata hakan yasa na yanke hukunci tafiya na barshi a ranar da na haife shi ina fito wa da ga asibitin aka dauke ni aka kaini can wani gida Ido na a rufe aka ajje ni gidan gidan kasa ne daki daya ne sai ban daki ba kitchen ma ko baranda babu ga zafi gidan a haka nayi rayuwa ta gidan ya kwarabe musamman da damuna amma sai dai suzo suyi faci facin sa da kasa suyi gaba duk wata suna aiko min da kayan abinci sai dai kadan ne Baya isa na wata dayan sai dai na can cana haka Ida ana ruwa babu inda zanyi girki sai dai nayi daki na sha wahala ni kadai tun ina damuwa har nazo na dena hatta ruwa shima na wata ake kawo min har na wanka da komai da komai fita kuwa kulluma a kulle nake sannan suka ce bani ba fita duk ranar da na fita to nayi ajalin yaro na da hannu na”.

Anan ta tsaya ta goge hawayen ta.
tace, “gashi yanzu bansan wanne hali rukayya take ciki ba bansan ko ta shirya da yayan ta Mai son ta ba bansani ba ko yaran ta nawa? Allah sarki Rukayya she did a lot to me, Iyaye na kuma nasani Suma zasu ji haushi na sosai bansan ya zanyi ba ga yaya na”.

Shiru sukayi Ummusalma ta Rasa abin fada ta Rasa taya zata ganar da ita cewan ita ce tasa aka dauko ta aka dawo da ita nan, ko kuma tace itace matar yaran ta ba yau ta tsici bakin ta yayi nauyi shikuma Binaif abinda yake tunanin akan ta daban ne dana kowa besan sabida tsananin son datake masa ya rayu bane hakan ta faru, numfashi taja ta ajje sannan.

Tace, “Mama ina ganin Anty ummi taji komai shiyasa ta dauki yaran ki ranar da kika haife Shi ta Hana kowa koda tayi aure tare dashi ta tafi ta bar kasar da shi ita ce ta reni shi har ya girma sai dai Allah be bata yaro ko Daya ba sai yaran da rike sannan kuma sai dai muyi hakuri”.

Cikin mamaki take kallan ta kafin.
tace, “taya kika san itace? Bamma fahima ci inda zancen ki ya dosa ba”.

“Mama wata Antyn Mijina ta taba bani labari irin yarda kika Bani komai naku shiyasa nasan kece kuma nasa itace yarda na fada maki haka ne naji labarin ta”.

“Amma ke to Wacece?”

“Mama zaki san komai, amma Dan Allah kibini mu tafi”.

Mama zatayi magana taji wayar Ummusalma na Kara shiyasa tayi shiru bata yi magana ba ga kuma Pretty da ta fara kuka, kawaici tayi ta ta daga wayar ganin Binaif ne”.

Yace, “kina ina haka? Baki ce zaki jima ba ya kama ta kidawo fa”.

“Nace to ko zaka zo Ka dauke mu, muna gidan Mamaan Sadiq”.

“To ganin but wait, ba kukan Pretty nake ji ba bazaki dauke ta ba?”

“Wayar Ka ce tasa ai”.

“Irin wannan Marta bawa haka? Zaki biye ni zuwa jibi ai ganin nan”.

Murmushi kawai tayi ta kashe wayar mika ita mama tayi ta ansa gaba Daya sai taji kunya ta kama ta takasa shayar da ita a gaban ta. Haka nan Mama taji yarinyar ta burge ta sabida kunyar ta.

Tace, “ki bata mana sai kuka take amma ki Dan rarreshe ta tayi shiru kadan ba’a san shayar da yaro Yana kuka Sosai ki tashi ki Shiga parlour”.

Tashi ta wuce Kan ta a kasa sai da dan rarreshen ta sannan ta bata ta koshi sai bacci goya ta tayi ta fito ganin tana wanki yasa ta je ta fara taya ta wanki ba yawa da wuri suka gama.

Mama tace, “gaskiya ba lalle bane na biki Bana san wani abu ya sami yaro na”.

Murmushi Ummusalma tayi kawai bata kuma cewa komai ba ta tashi zata tafi Kenan wayar ta tayi Kara ganin shine yasa ta daga.

Yace, “ina kofar gidan Ku fito”.

“Ka shigo to ni ina gidan kusa dasu Ka shigo nan din me farar kofa nan please!”

“Ohh! Keko?”

“Please”.

“To ganin nan”.

Dayake bayan sunyi wankin ciki suka koma ita kuma a waje tayi wayar shiyasa itama ta koma ciki sauko da pretty tayi ta kwantar da ita ita kuma mama kitchen ta shiga ta kawo Mata snacks da lemu.

Tace, “kiyi hakuri ko ruwa ban kawo maki ba”.

Murmushi Jin kunya tayi tace, “laa bakomai dayake ai daga gida nake shiyasa”.

Mama tace, “nikam ina Shan kunya sai kace wata sirikar ki”.

Murmushi ta kuma tayi ta, tace, “Mama inaga gashi nan yazo zaku gaisa”.

“Tou! Jeki shigo dashi Bari na dauko mayafi”

Tashi tayi ta fita ita kuma tayi hanyar waje bude masa kofar tayi ya maka harara ita kuma tasa dariya kawai tayi gaba da sauri ya shigo Yana kwafa har parlour ya shiga ya zauna a kusa da pretty sannan ya dauke ta.

Yace, “kawai ki kafa ajje ta a gidan mutane salan ta fado ta fasa Kai”.

Waro Ido tayi tace, “yarinyar da ko cikakken juyi bata yi?”

Harara ya balla mata, murmushi tayi murmushi kasa kasa tace, “wallahi zanyi Zama na a gida ko na tafi Adamawa nayi wayon arba’in acan sannan nadawo”.

“Naji wannan”.

“Yarda fa”.

“Banyi ba”.

Shiru ganin Mama ta fito da murmushi a fuskar ta ta karaso zata zauna Kenan ya dago dan ya gaita da ta gaisuwar da ba’ayi ba Kenan kowa ya kame ita kuma zaman da batayi ba sai ma Kara Mike wa da tayi.

Kama biyu take hangowa a fuskar Shi Daya kamar ta Daya kuma kamar Wanda ko mutuwa tayi ta dawo zata gane shi shikuma babu abinda yake hangowa sai tsantsan kamar shi ga kirginsa da yaji Yana wani irin dokawa kamar ya fito zuciyar sa wani irin sanyi sanyi yaji tana yi sai faduwar gaba haka nan yaji ya kasa dauke idan sa Akan ta itama haka.

Ummusalma tace, “Mama Zaikai ga Baban Mai sunan ki”.

A tare suka maida Idan su Kan ta
kowanne da alamar tambaya a fuskar Shi.

Binaif yace, “mekike nufi Kenan? Wannan ita ce kika Sawa pretty?”

Gingina Kai tayi alamar tabbatar wa.
Lineage Ido yayi ya Bude cikin a kanta.

Yace, “a’ina kika samu ta? Mene hadin mu da ita”.

Kanta ta mayar kasa tana wasa da hannun ta.

“She’s your mother”.

Ba shiri ya mayar da kallan sa ga kanta itama Shi take kallo sun jima a haka babu Wanda ya iya magana daga bisani.

Yace, “Nasan kin san komai kin kuma san dalilin barin ta ta barni bayan Anty ummi tace min ta rasu please tell me everything”.

Mama kuwa takuwa wurin Shi tayi tana kallan sa hawaye na zuba a idan ta ita de ko ba dan ta bane da gaske zata ke daukan sa yaran ta har ta bar duniya, kawai ta rungume Shi shida pretty dake hannun sa lumshe Ido yayi ya Bude su akan Ummusalma dake kallan su. Jin yarinyar ta fara motsi alame zata tashi yasa tayi breaking hug din sai anan yani bugun da zuciyar sa take masa yaji ta dena sai wani sanyin dadi Mai kama dana Jin dadi dake ratsa jikin sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button