A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A waje a ganta a wurin wata bishiya a zaune Akan kujera, Zama yayi a kusa da ita.

yace, “bansan me ta fada maki ba akai ba Amma nasan koma meye ta fada haka yake”.

Kallan Shi taga ba ita yake kallo ba wani wurin ma yake kallo daban.

Itama dauke kanta tayi ta mayar Shi wanj wurin tace, “Ban san me zance ba ta riga da tayi magana da Abba na babu yarda zanyi dole na aminci”.

“Bana san kice dole nafi so ki yarda dani da kanki ki kuma amince ba wai dole ba”.

“A jiya kawai muka hadu ita amma nagane tana da hali Mai kyau tunda har ta shigo rayuwa ta ta taimaka min ba sau daya ba sau biyu nagode sosai”.

“Kin yarda ni?”

“Maybe”.

Kallan ta yayi kawai be iya magana can yace, “friends?”

Itama kallan Shi tayi shima lokacin ya kalle ta tace, “friends”.

Ummu ce ta hango su da zuwan ta Kenan ta nufo wurin tana zuwa Tayi sallama ta kalli Muja.
Tace, “ina wuni”.

“Lafiya qalau”.

“Ya mus’ab ina yaya salama?”

Yace, “Antyn mu ina wuni? ya gida?”

Turo Baki tayi tace, “Haba ya mus’ab meye haka? Wallahi kunya nake ji”.

Murmushi yayi yace, “tun ba’aje ko ina ba? Gashi nan kin kawo Mai abinci?”

“Wallahi bashi na kawo wa ba yaya salama na kawo wa tace harda freshyo nikuma banga niba babu shine na kawo Mata fura da Hollandia shine fa”.

“Naga alama ai, ki Kira ta a waya”.

“Na bar wayar a gida”

Kiran ta yayi da wayar Shi ita kuma ta kalli ya Mika hannu tare da fadin.

“Ummusalma zaki iya Kira na da ummu”.

Mus’ab yace wanne ummu matar yaya ce fa sai dai kice Anty ummu”.

Turbune fuska tayi bata yi magana ba Muja ya Mika Mata hannu. tace, ”Maryam mujahida ko Muja”.

Tace, “karfa ki biye Shi kice wani Anty rabu dashi ko?”

Murmushi tayi kawai bata ce komai ba, shikuma Yana waya da Ummusalma shiyasa beyi magana ba sai da ya gama. yace, ”a rabu Dani ko?” Shikenan Tou nidai nace Antymu sai dai a min Zane ni don na fada bazaki hada ni dashi ba yace Banda kunya”.

Cuno Baki tayi ta ajje kayan hannun ta tayi folding hannayen ta ta hade rai tana gunguni murmushi Muja tayi Dan itakam sun birgeta ba kadan ba.

Ummusalma ce tazo wurin tace, “ummu kin San kin dade tun dazu nake ji yunwa dauriya kawai nake yi”.

“Babu fa abincin ai nayi ma sauri dana dafa”.

“Liar”.

“To Bani da dafa ba?”

“Ehh bake bace ba”.

“Taya kika sani?”

“Ta yarda kika yi magana mana”.

Murmushi tayi tace, “freshyo dinki ce bansamu ba shine Anty ta Bani fura na kawo maki nikumana hado da Hollandia.

“Wow nakuwa gode taho muje kafin wancan uban hadar da da rani yazo ya shanye mu”.

Daukan basket din ummu tayi tayiwa Muja sallama ta wuce, a hankali suke har suka iso dakin suna zaune su uku Binaif da su yusseer ne kawai a dakin sai Shi shikuma idan sa a rufe yana kwance da sallama Ummusalma ta shigo ita kuma ummu a bayan ta kanta a kasa.

Yaseer yace, “Antyn mu harda dake ashe ina wuni?”

Bude idan sa yayi ya hango ta sabida Ummusalma ta matsa shiyasa ya ganta lokacin ta maka wa Yaseer harara tare da irin kallan zamu hadu murmushi yayi kawai ya kuma rufe idon sa.

Binaif yace, ” mu tashi muje dubiya ko ya kuka ce”.

Ummusalma tace, “abinci fa?”

Yana tafiya yace, “banji yunwa”.

Tashi sukayi suka fita ita kuma ta tsaya kikam a tsaye, girgiza Kai Ummusalma tayi sannan taja hannun ta har gaban gadan ta Zaunar ta daura hannun ta Akan m hannun sa sannan ta dauki abin cin ta ta fita.

Jin shiru taki tace komai kuma bata cire hannun ta Akan nashi ba yasa ya Bude Ido ya kalle ta kallan hannun su take bakin ta na motsi alamar takasa cewa komai kuma tana San fada.

Yace, “ba gaisuwa ba sannu da jiki ko?”

Maida kanta kasa tayi tana Mai Jin kunya, ta girgiza Kai, murmushi yayi sosai yace, “Uncle nifa ko kaga wasu wai suyi taji kunyar Uncle dinsu ni kuwa bana Jin kunyar ka kuma bazan ji ba kaji bazan Mata ji ba kuma ko naji to Ka tuna Zan cire ta Dan banga me zanyi yiwa kunya ba ko haka ne ai”.

Ware ido tayi ta kalle Shi ta tashi zata fita da sauri ya riko ta.
yace, “oush! Hannu na kin fama mun wayyo hannun na?”

A rikice ta dawo ta fara jera masa sannu tana rike da hannun shikuma be Dana ba tsabar rikice Vail dinta ya kunce bata sani ba dayake doguwar Riga ce tasaka sai tayi rolling da mayafin rigar sai hula data sa, kallan ta kawai duk tsawan shekarun yaune kawai yake mata kallan da ba na ‘ya ba kallo ne na irin mijin dake San matar sa ganin Dan abinda ya same Shi Amma tabi ta riki ce, ita kuma ganin har yanzu Yana rike da hannun yasa kawai ta rungume Shi ta fara kuka.

Dayan hannun ya fara sha Mata kanta dashi Dan be zaci haka daga wurin ta ba yasan da wuyane tayi kuka sai dai kukan tabara sosai yake shafa ta ya cire hular kanta ya lumshe Ido yana jin kukan ta ita kuma dadin shafar data ji Bata San sanda ta hau gadan dakyau ba tayi shiru tana Jin yarda yake shafa ta bata San sanda bacci yayi gaba da ita ba daman jiya bata yi wani baccin kirki ba.

Fuskar ya leko yaga tayi bacci gashi yamma ce besan tashin ta yasa kawai ya barta duk da kwanciyar bata masa ba Yana Jin wani iri a jikin Shi babu dadi wani Abu na tsarga masa haka ya daure ya kyaleta.

????????????????????????????

“Alhaji Sai fa Ka biya kudin nan su goma ne masu aikin nan tun jiya nake binka Ka Basu kace sai kaje banki yau kaje Baki amma shiru”.

Abba yace, “kefa kika ce abinci ya kare na siyo komai da komai yarda zai isa ya Dade ana amfani dashi yanzu ni banki na miliyan daya ne ya rage ashi zanyi hidi mar biki, idan kin yarda ga dubu hamsi nan ki raba musu ina laifi?”

“Wai ni Alhaji tsaya ina safe din gidan can kawai Ka dauka a fasa ta a kwashe komai mana”.

“Ban fada maki daman?”

“Kace min me?”

“Barayi sun shiga gidan sun kwashe komai daman ba wani kayan kirki bane Wanda yayi saura to sun hada da na dakin nan sun dauke ranar da sukayi kuma gobara ta kama a gidan Alhaji Sammani to ya taba gidan shima kusan rabi ya kone na zaci na fada maki ai”.

“Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un yanzu hakan ta faru baka fada mun ba?”

“Yanzu kin sani”.

“Taab nikam bazan iya Zama a wannan takaicin ba”.

Banza yayi da ita ya ya tashi ya dauko dubu hamsin din ya ajje Mata yace, “idan kiga dama ki Basu daga nan kuma ki sallame su banda kudin bawa masu aiki”.

“Nikuwa bazan iya ba wannan ai cin zarafi ne da tazorci wallahi, ina bazai taba iyu wa ba”.

Har wani huci take tsabar takaici da haushi.

Abba yace, “ai kina da kudi zaki iya cigaba da daukan su amma nikam nayi nawa nagama bazan iya ba”.

“Haba Mahmud Bama Alhaji ba, wannan abun fa abun daba wa ne ya kamata a duba lamarin nan da kyau wazai ke Shara,wanke wanke, wanki, share tsakar gidan nan ma kadai aiki ne, ga wurin wasan su Yusuf ga gyara dakin su du waye zai ke yin wannan?”

“Hmmm sunana ne daman, su zake yi mana waye zai musu kiyi abinda zakiyi su karasa sauran nagama magana”.

“Hehehe Mahmud Kenan Ashe kuwa na kusa barin gidan nan wallahi cab Allah ya sauwake”.

“Ameen”.

Yace, “kinga yau za’a zo auren neman auran Sameera” .

“Na Hana su zuwa ne? Ko kuma nace Kar a zo?”

“Fada maki nayi ne kawai karki ga wai sunzo anyi magana, na kuma Kira abokai na Wanda zasu tsaya mata”.

“To”.

Ya kauda kansa yana Jan carbin sa ya rabu da ita dan Shi Kam ya Gama abin da zaiyi karta sa jinin sa ya hau ya samu yasawa zuciyar sa salama abu Daya ya yanke duk sanda ta nemi takardar saki to zai bata babu takura babu takurawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page