A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ehhmmm I see,

Shigowa yayi yaja hannunta yace’ an min kwalliya amma an kunshe a hijabi ba’a nuna ba,

To bakai ne ba?

Nayi me?

Kace nasa,

Hmmm haka de akace,

Tace’ kabarni na tafi pleaseeeeee

Wani iri taji a Baki,bazata iya tuna when last tace please ba,Amma yanzu gashi tafada,

Yace’ kikayi musu? To kwana zakiyi,
Zaunar da ita yayi akam kujeran da ya zauna, ya cire Mata hijabin lumshe Ido tayi sabida kusanci yayi kusa dayawa ta jingina da kujeran, kwanciya yayi a jikinta ya rungume ta sosai ya lumshe Ido,bude Ido tayi,
tace’ ka daga ni,

Idanshi a rufe yace’ a,a

Nifa Ka danne ni,

Yace’ ramawa nake,Nima dazu haka kika min harda su gyara kwanciya bakisan menaji bane shiyasa,

Tace’ to nidai Ka dagani kamin nauyi dakyar ma nake iya numfashi,

Haka shiyasa Naga kina magana,

To nidai dagani Allah kana da nauyi,

Zan daga ki Amma sai kinji abinda naji dazu,tukunna,

Ai naji, tuntuni ma,

Bude idanshi yayi ya kalleta sai wani hade fuska take, murmushi ya danyi yace’ to fada min mekikaji?

Taya za’ayi kuma nafada maka? Nidai naji ai, kawai Ka dagani,

Lumshe Ido yayi ya bude su be sauke a Kona ba sai baki ta,ta bude zatayi magana Kenan taji suyi wani mai kama da kiss kuma be saketaba sai ma Kara yi yake.

????????????????????????????

Wai kekam Ummu shikenan daga zaman daki sai daki? Nifa nakasa gane kanku wallahi daga ke har Abdullah Har gwara shima Yana fitowa yayi yawo har yana bin Walid kasuwa Amma ke narasa Kan gadanki Sam wallahi, su yaran da suka bata Baki ma sani ba ko sun mutum kinbi kinsawa kanki damuwa,

Tashi tayi tace’ gaskiya Inna kin dameni,tafiya zanyi bazan iyaba, dame zanji? Tun sanda mukazo kika addabeni kika hanano sukuni eh? Ni banzan iya ba,

Inna tace’ na dameki ko? Haka kika ce, shikenan zaki zo ki sameni, yarinya de infada maki kuma nan zaku dawo da Zama daga ke har uwar taki tunda ubanki naji labari zai dawo nan da aiki, kuma dole azo nan gidan kuma dole na damun mutum,

Inna ta tashi ta fita,wani marayan kuka tasa itakam wallahi bazata zauna anan ba, gidan Anty furera( kishiyar Mamanta) zata tafi kawai bazata zauna ba, gashi ko wayarta bata dauko ba bare ta Kira Babanta taji dagaske ne? Sosai take kuka harwanj sarkewa takeyi, kullum sai Inna ta Mata fada akan zaman daki, Yana parlour Yana jinsu har Inna ta fito ya jima a tsaye Yana kallanta da’ace da yarda zaiyi to da yayi shima Baya San zaman garin nan, farin cikinta shine nasa, shigowa yayi ya durkusa zai dagota har ya kama kafadar ta sai ya tuna da da yanzu ba daya bane, karasa Zama yayi abakin katifar,

yace’ kiyi hakuri kinji, zanje Kano nasake bincikawa duk yarda akayi zakiji ni Insha Allah, yau Zan tafi,Amma karki fadawa kowa Zan tafi kinji? Zan dawo Nanda Monday zan dawo duk abinda ake ciki Zan nemeki, ta waya,

Tace’ ban zo dawaya naba, na barshi a gida,

Badamuwa Zan kiraki ta wayar Anty ko Fendo kinji?
Sallama sukayi ya tafi,dakin Baffa ya Shiga ya Debi kudin Shi ya fito yana fitowa yasami abun hawa ya hau sai airport,kafin magriba sun iso Yana zuwa gidan su Ummu ya wuce direct damma Yana da key din gidan Shiga yayi taje dakinta ya dauko wayarta ganin missed calls dayawa harda na class rep yasan sauran ma du na ‘yan school ne, ya Shiga dakinsa yayi wanka sannan ya fita magriba Yana dawowa gidan su Yusseer yashiga bakowa a gidan sai masu aiki, mai aikin ya tambaya yace’ ina ne dakin su yaseer kuwa?

Mai aikin ta kalle Shi,
tace’ Kai wanene kake neman dakin su?

Yace’ am karki damu ni yayan Ummu ne idan kinsanta Kenan,

Tace’ ehh nasanta koba kawar su din nan ba?
Yace’ eh ita, sannan ta nuna masa dakin,
Shiga yayi parlour har yayi Dan Kura danma wai ba sanyi ake ba, kofar kusa dashi ya bude yaga kitchen ya bude na opposite yaga toilet ne,sai ya bude na gaban Shi daki ne na tarkacen su, Wanda yake opposite dashi ya bude yaga dakinsu Shiga yayi yafara duba abu sai dai babu koda Paper dayane sai hotanta, wayar yaseer ya daya gani akan gado yasashi dauka ganin ya kunna yaga bata kawo ba alamar akashe take, a aljihunsa yasa ya fita, Basu dawo bakuwa Saida ya juna a charge sannan ya fita yin sallahn Isha sai da yaci abinci ya koshi yayi kallo zuwa 9:30 ya tashi ya kashe kallon ya dauki mukullin motar dayagani a Parlour yaje ya daukk Atm dinshi sannan ya fice zuwa store Dan siyo kayan bukata.

✨✨✨✨✨✨✨

A wani store yayi parking yace’ bazaki fito ba?

Tura Baki tayi gaba tace’ ice cream,

Yace’ idan Baki fito ba to bazan siyo ba,

Kara tunzura Baki tayi tare da kumbura Baki murmushi yayi,
yace’ da’alama de kinsan Abu nan ma dazu ko? Mai dadin nan?

Kallanshi tayi tace’wanne Abu Kenan? Meye mai dadin?

Kawo kunnanki kiji rada Mata wani Abu yayi ai bashiri ta bude kofa ta fice tana murmushi Tama Riga shi Shiga store din sabida haka sai tayi hanyar ta, shima da yazo sai yayi hanyar Shi tana cikin tafiya taji tayi gware da Abu dago Kan da zatayi sukayi four eyes da uncle Baki bude take kallanshi kamar yarda shima yake kallanta, murmushi karfin hali yayi

yace’ can I have your contact please?
Yafada yana Mika Mata wayar Shi,wayar tabi da kallo sannan ta karba tasaka masa, murmushi yayi yace’ thank you,
Sannan yace’ Ummu ta Shiga damuwa saboda rashin bestie dinga am I mean Yusuf da yaseer, bayan sun so su nemeki amma Allah beyi ba Sai kaddara ta Riga fata,
Yace’ idan bazaki damu ba inasan zamuyi wata magana,
Duk maganar da yake a sanyaye yake yinta Kala kalar tausayi, a yarda ta lura ma kamar Yana cikin damuwa damuwa mai wuyar fassara wa,

Kasa magana tayi tsabar ta Zama speechless batasan haka Abu yake ba bata san zata cutar da Ummu ba da batayi ba, wayarta ta daga ta Kira Binaif amma bedaga ba, maybe wayan na mota har ya wuce ta da sauri ta sha gabanshi tace’ baka kirani ba,

Murmushi yayi yasan gudun kar ayi ta ta ta da ummu ne shiyasa tace haka, kiranta yayi taga number samun kanta tayi da Saving with Yaya,
Shikuma yayi gaba abinsa, Binaif ne yazo wurin ta Yana neman wani Abu hankali kamar ma be ganta ba sai duduba mutene yake zuwa tayi wurinshi,

tace’ lafiya? Wa kake nema?

Rike hannunta yayi yace’ Neena

Kallanshi tayi dakyau tasaki Baki shida besan Neena ba,? Kara maimaita wa yayi,
yace’ Ehh Neena nagani Amma banga fuskarta ba tana cikin store din nan,

What?…….

Ghen ghen gehn, where u belongs to?

team Umsha

team yusseer

team Mussab????

More comments ???? more typing ✍️✍️

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

 29

Itama fara neman ta tayi Saida babu ita babu dalili ta gajiya tayi,

tace’ Ka saya abinda zaka saya mu tafi,

Yace’ nagama siyan kayana, muje ki dau ice cream dinki mu tafi,

Fitowa sukayi bayan ta dauki ice cream din ya biya kudin, tunda ta fito kafin su karasa wurin motarsu taji ana kallanta daga Baya tsaya tayi ta juyo Amma ba kowa,gaba tayi ta duba namma bataga kowa ba zuwa yayi
yace’ lafiya kuwa?

Idanta ya cicciko da hawaye,
tace’ indai da gaske Neena kake tunanin Ka gani to tabbas itace kuma yanzu ma itace take kallona,idan baza zo inda nake ba nagama nemanta a rayuwa ta har a bada ko naganta Zan nuna ban Santa,
Ta karashe tare da goge hawayenta ta tafi ta barshi a tsaye, Saida taje wurin motar Yana kallanta sannan shima ya yafi,
Sun dau hanya,

tace’ taya Ka gane Neena ce bayan kuma kace bakaga fuskanta ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button