A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace, “bb na shigo ina? Bade niba ina matar Ka ita nake nema wallahi inaga tun 7 nake bugawa ga waya ta bansan inda take ba na koma naje nadawo shine har yanzu”.

Tace, “a,a chatty Kaine da sassafe haka?”

“Kinga please it’s urgent please zo muje”.

“Ina?”

Hannun yazo ya kama zai fitar da ita bishi tayi suka fito ganin sun fito zasu bi ta gate yasa ta tsayawa.

Binaif yace, “ina key din da kayi amfani dashi Ka Bude gate”.

Hannun sa ta daga alamar gashi, zuwa yayi ya karba da pretty a hannun sa yaje ya bude kofar ganin gidan sa yasa.

Yace, “bb ko? Daman nan”.
sai kuma yayi shiru ya kalli Ummusalma dake kallan sa.

Yace, “wai bazaki tafi ba?”

Koma wa tayi zata koma gidan ta ya kamo hannun ya marairaice.

Yace, “ki gane mana”.

Harara ta zuba masa sannan ta shiga tana kwance a cikin bargo da’alama Zazzabi ne ya rufe ta sosai komawa tayi ta dauko wani garin magani da Inni ta bata da kuma magani ta dauki mayafin ta koma.

Zama tayi ta yaye bargon data rufa.

Tace, “Sameera tashi kisha magani”.

Muryan mutum Daya ce tasani wannan sai dai yau da asuba ya bata labarin sistern Shi da komai nasa na rayuwa.yace zaije ya Kira sistern shi tasan ita ce wannan.
A hankali ta yaye bargon da rufa ta tashi zaune tana kare wa halittar matar kallo, Kallan ta ta Kai ga Mas’ud dake bakin kofa Yana kallan ta, itama Ummusalma kallan ta take yi hannu ta daga tana nuna Ummusalma.

Tace, “wannan ce sistern naka?”

Daga Mata Kai yayi alamar eh.

Kallan ta takeyi Bako kiftawa kafin.

Tace, “yaya meyasa? Meyasa kika bar gida? Har na manta dake meyasa yaya?”

Murmushi Ummusalma tayi Mata Wanda duk zaman da take da ita a gidan ba taba yi mata tun kafin ta zama kurman shiru.

Tace, “Sameera na gano iyaye na shiyasa ban koma ba Amma kiyi hakuri gashi yanzu mun sake haduwa kin zama in-law kin tashi daga Sameera kin koma Anty Ko yaya sameera”.

“Daman Basu Abba bane Iyayen ki?”

“Basu bane Sameera su kawai rike ni sukayi da amana har suka sani a makaranta kin gane”.

Murmushi itama ta mayar mata Mai kyau.

“Ya wahalar min dake ko?”

Sunkuya da Kai kasa tayi ta fara wasa da hannun ta, hararan Shi tayi sannan ta wuce toilet duk wani taimako da data San zai taimaka Mata Shi tayi sai da taga taci abincin da ya karbo a wurin Binaif ta sha magani sannan ta fita, tare da rankwashin sa aka.

Rayuwa Mai dadi wannan family din suka fara ta kowanne Bari Basu da matsala Maman Binaif ta tare bayan ya sauya musu gida sun koma nasarawa kusa dasu Umma sai dai da Dan nisa tsakanin su, haka su Saima suna Jin dadin Zama da ita. Sameera kuwa ta bawa Ummusalma labarin abinda yafaru har barin mama gidan su yusseer Basu fada mata tasan ba labari bane me dadi. Su ummu sun koma makaranta inda yanzu cikin ta ya tsufa wata ran taje wata ran kuma tayi zaman ta duk da su Binaif ne suka dauki nauyin gidan su Yusuf batare da Abban yasan hakan ba haka ma asibitin da yake zuwa idan ciwon Shi ya tashi duk su suje biyan komai kafin su Yusuf su tafi zasu tabbatar da sun tana dar masa abin dayake bukata wata ran kuma shike musu girki idan sun dawo ciki sun rage zuwa gidan su sabida Samum kaluwar da suke bawa Abba, Abba kuwa wataran yaje kasuwa yaga wani kamar Muhammad hakan yasa yaje wurin Shi ganin bashi bane idana a daurin auren Sameera yaga wani ma kamar Shi sai dai kafin yaje shikuma ya tafi haka nan yaji a jikin sa Muhammad be mutu ba Yana nan da ransa kamar kullum yau ma ya dawo daga kasuwa Yana tunanin Wanda ya kuma gani kamar Muhammad Yana tunanin har yazo gida babu abin da yake sai tunani kitchen ya Shiga Dan tana da abinda ya siyo kawai yaji ya fara tunanin haduwar su tun suna yara da irin Abubuwa da yayi ta yi masa har kawo abinda ya saka masa dashi hawaye ya fara yi sosai ya Dade kirgin sa Yana ambatan Allah

Allah yasa su Yusuf dawowar su kenan suna neman sun shigo kitchen din suka gan Shi a haka da gudu sukayi Kan sa suna Kiran sa, sai asibiti kafin su zo asibitin kuwa ya Suma. anjima a kansa sosai kafin a samu ya farfado Yusuf ya Kira Sameera ya sanar da ita sai gasu sun zo ita da Mas’ud sosai hankalin ta ya tashi bakadan Sai sanda ya farka bata dakin ta tafi tayi sallah iya sune a dakin kawai.

Abba ganin mijin Sameera a gaban sa tare da su Yusuf yasa Shi cire oxygen din da aka sa masa da sauri sukayi kansa hannu ya daga musu sannan Mas’ud ya taimaka masa ya tashi Yana numfashi dakyar ya riko hannun Mas’ud hakan yasa ya zauna, cikin muryan dake nuna alamamun Yana cikin ciwo ya fara magana.

“Ba kasan wanne irin siriki Ka samu ba”.

Dukda mas’ud yasan abinda ya faru kuma yasan dalilin sa na fadar haka Amma.

yace, ”Abba bangane abinda kake fada ba kadena Dan Allah”.

“Mas’ud baza Ka gane ba sai na sanar da Kai komai”.

Ya kalli su yusuf dake Kan sa suna kallan su yaseer sarkin kuka kamar mace.

” ‘ya’ya na idan sukaji abin da na aikata ina ga dena Kula ni zasu yi”.

Hawaye ne ya zubo masa beda mu da ya goge ba.

“Akwai wani babban Abu da na aikata a rayuwa ta Ummusalma da Iyayen ta sai dai duk abinda nayi matar danayi dan na faran ta mata ta tafi ta barni bacin ita ce Wacce ta zigani da nayi hakan haka ma Mahaifiyar data haifeni wacce itace silar faruwar komai yau gashi ta mutu ta bar dubiya batare da ta Nemo yafiyar abinda tayi ba”.

Shiru yayi numfashin sa yana yin Sama Sama Kara damke hannun Mas’ud yayi ya kulle ido, tiryan tiryan ya zayya no musu komai har kawo Sace su da akayi da tura Ummusalma karatu sai da ya Gama.

Yace, “Lokacin Dana fara ganin Ka na gano kamar Muhammad a tare da Kai sannan Maryam, amma kuma ganin Baka da alaka dashi Kai din Dan Adam Dan Lami ne yasa ban kawo komai a rai na ba sai dai har yau idan na kalle Ka Shi nake tunawa, Inaji a jiki na be mutu ba ina Jin wannan a jiki na amma bansan inda Zan ganshi ba ban San inda Zan same Shi ba”.

Shiru yayi na wani lokaci sannan yace.

“Ku Kira min Sameera tasan waye mahaifin ta, tasan mahaifin ta be cancanci yafiya ba daga gare Ku da wannan mutanen”.

Mas’ud yace, “a,a Abba basai an kira ta ba tun da bata sani ba Dan Allah a bar komai anan yayi ya kare Wanda kake fada kuma nasan shi Zan Kan Ka wurin Shi Insha Allah Abba kadena fadar haka kaji ko? Mutanen kuma sun jima da yafe maka kayi hakuri Ka kwantar da hankalin Ka”.

Cikin mamaki yake kallan sa.

“Kasan su? Kasan sun yafe min? Ka kaini wurin su yanzu nan Ka kaini kawai bansani ba ko shine yasa har yanzu nake raye”.

Kokarin tashi yake amma suka rike Shi shikuwa ya dage sai an kai Shi wurin su babu yarda suka iya.

Yace, “Abba Bari naje nagani ko za’a Baka sallama”.

Sameera dake bakin kofa ta rigada taji komai tun sanda ya fara labarin sa farkon ne bata ji ba ga mugun mamakin abinda taji ya fada tasan tayi dacen miji tun sanda sukayi be taba bata Mata Rai ba kullum Yana cikin faran ta mata haka itama Jin zai fito yasa ta tayi saurin komawa bakin ward din ta fara tahowa tana goge sauran hawayen ta gware sukayi dashi ya dago Yana kallan ta ita kuma kanta a kasa, murmushi yayi Mai kyau.

Yace, “crying baby ko pretty bata Kai ki kuka ba ina ga sai nakai ki an zuke hawayen nan ko zuciya ta ta huta da gaba Daya”.

Yarda yayi maganar ne dole ya baka dariya murmushi tayi kawai bata iya magana ba shikuma yasa Kai ya wuce binsa tayi da Ido har ya fita, cikin dakin ta Shiga babu abinda Abba take cewa sai su yafe shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button