A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana fita ya Kira Ummusalma ya sanar da ita komai gashi doctor Baya nan bare su tafi.

Tace, “to Ka Kira su Baffan mana kace suzo asibiti nasan zasu zo ai muma gamu nan”.

“Ke ki kirasu mana”.

“Chatty Ka kiyaye ni”.

“To Inni aljana kawai”.

Ganin kamar bazai Kira su ba yasa ta kira Inni Ashe har ya fada wa Baffa ma, Binaif ta Kira da Mas’ud sai uncle suka taho.

Basu wani jima ba kowa ya hallara ana jiran dalilin kiran sai ga Mas’ud din nan ya fito ya zo ya Shigar dasu.

Baffa yace, “wai waye ba lafiya kabi Ka daga mana hankali”.

“Baffa kazo mana zaka gani ai”.

Suna zuwa kofar dakin ya kama hannun Sameera suka zame suka fita.

Baffa ne a gaba ya tura dakin ya Shiga Yana kwance idan sa a rufe Yana tunani yaji sallamar sa Bude Ido yayi ya sauke su a kansa koda ace zai sauya sau dubu to tabbas zai gane shi, shima Baffa tas ya gane Shi sabida ya ganshi a biki.

Kokarin tashi yayi Baffa ta yayi sauri ya karasa ya Ida daga shi Abba besan sanda ya rungume Shi ya fara kuka ba kukan dayake kuka ne na taba zuciya da tsantsar Nadama Inni ita kanta ji tayi hawaye zai zu bo mata da sauri ta maida shi tana komawa baya,
Dakyar Abba ya iya Bude Baki Yana kuka sosai.

Yace, “Ka yafe min Ka yafeni Ka..ka..”.

Kasa karasawa yayi sabida wani saban kukan da ya taho masa har Yana sarke Shi, bubbuga Shi Baffa ya fara yi Yana bashi baki.

Dagowa yayi Dan kallan Baffa yarda yake magana cikin taushi da lallamin komai ya wuce idan sa ya Kai kan Ummusalma da itama wani hawaye ne ya zubo Mata.

“Um..mu..sal..ma”.

Ya iya furtawa kawai kasa jurewa tayi take ta rungume Shi tana kuka sosai bema yi magana ba ta fara ta yafe masa haka ma Inni.

Ranar Abba ya zaci karshen mutuwar rayuwar sa ta zo ganin yarda mutumin da be zaci zai yafe masa na sai gashi komai ya wuce idan kuwa ya Bude Baki zaiyi magana da sunan neman yafiya sai kaji sun dauko wani zancen sunayi hakan yasa Shi kawai kallan suya zuba musu Ido ji yayi zuciyar sa tayi fes ta wanke babu wani damuwa bare bacin Rai da bakin ciki Jin sa yake kamar ba’a cikin ciwo ba yake.

????????????????????????

Dubai

Tsawon wannan lokacin suna Dubai suna harkar su Kaya kawai suke sarowa suna aikowa babu abinda ya dame su da gida bare kuma yaran su business kawai suke zubawa babu abinda ya dame su bare ya sha kansu da kudin su suke bishashar su Saida suka tabbatar da sun turo Kaya kusan na miliyan ashirin sannan suka wuce China anan ma sun jida kaya.

Yau sun tashi Basu da kudi sai Wanda zasu hau jirgi gashi an kawo musu kayan Basu biya kudin ba hakan yasa su Bude envelope din da Daddy ya basu dan ganin check din da ya Basu suna parlourn gidan da suka kama haya suna fadar abinda zasu yi.

Hajiya ce ta fara bude wa taci Karo da wata paper ta zaro tana budewa tana magana.

“Kai Alhaji de wallahi sai a barshi mene na…”

Shiru tayi ganin saki biyun da tayi a Hankali ta fara karantawa tsab ta gani kamewa tayi a wurin a zaune.

Anty ma hakan ce ta kasance kowa kasa motsi yayi da ya ga wannan takarda gashi ko sisin kabo babu a ciki sai yanzu suka San wautar da sukayi sai yanzu suke Dana sun sani sun Bude sunga ko nawa ne Amma meyasa be ce musu komai ba?

Jin ana musu knocking shine ya dawo daga su daga duniyar da suka dulmiya masu Kaya ne suka zo dole kuma yau zasu bada kudin nan babu yarda suka iya kudin jirgin su suka biya dashi da canjin hannun su sunyi kuka kamar ba gobe wacce suke turawa Kaya kuwa dakyar dakyar ta hado musu kudin jirgi da na gidan da suke zaune suka dawo Niger, suna zuwa Basu zame ko ina ba sai gidan sa babu kowa a gidan ko Mai gadi babu Dan gidan ma dankareran Padlock suka gani a jiki acikin ‘yan kwanakin nan karamin hauka ne kawai basuyi ba kana gani zaka San sun rame har wani Baki sukayi saki ba Abu bane Mai sauki musamman ma lokacin da Baka shirya ba.

Daga Gidan wacce suke turawa Kaya sukayi suna zuwa aka ce ta tafi saudiyya bayan ta sai da Kayan su wani kuma ta tafi dasu ana Gama fada musu suka zube suka fara kuka wiwi suna tafi ya Akan titi kamar tababbun mahauka ta Gidan Mariya suka je itama Tace tunda suka tashi bata Samu dama taje ba da Rana zasu Sa suje su Duka tayi tayi dasu su tsaya suci abinci amma suka ki suka Tunanin yayi gaba daman su biyu ne anan garin sai Hunaifa, Hunaifa kuwa tana zuwa gidan sosai sai dai suka Samu bata nan ta tafi sunyi tafiya gidan wata kawar su suka je sai da sukaje fada ya kaure a tsakanin su wannan yace kaza wannan yace kaza Abu ya hade musu kwanan su biyu itama tace mijin ta zai dawo idan ya dawo kuma korar kare zai musu hakan yasa suka tattare komatsan su suka tafi gidan su Anty, Tasha fada kuwa a wurin sa musamman dayaji tun yaushe akayi sakin bata nemi gida ba sai yanzu.

Tace, “kayi hakuri kawu dan Allah ni kawai so muke muji me muka masa da zai mana wannan sakin har biyu”.

“To zan neme Shi Insha Allah naji dalilin sakin idan ya mayar Ku to idan kuma be mayar Ku ba sai hakuri da dangana”.

Daga nan ya fara balbale su da masifa daman ita can sabida dashi ne bata San zuwa gidan su yanzu kuma da Shi kadai ya rage mata dolen ta ta ne me Shi.

Fita yayi da kansa yaje ya Kira Shi a waya sai da suka gaisa yake sanar dashi komai Daddy kuwa yace ga Shi nan zuwa.

Sai da yazo ya fede musu biri har witsiya da irin kuma abin da yaji suna fada da abinda zulaihat ta kara fada masa game da Kauwar sa sosai shikan sa ya girgiza da irin abinda sukayi gashi kuma a gaban su ya fada babu daman musu.

Anty kuka ta fara tana magiya.

“Tabbas abin da mukayi bamu kyauta ba Dan Allah Kayi hakuri Ka maida mu”.

“Da’ace baku furta ba bazan ji ba kunsan ance A BAKIN WAWA”.

Kawun ta yace, “akanji magana, Allah ya kyauta kede tawa ce bakuma zan kore ki ba zaki ci gaba da zama ke kuma Hafsa zaki kama hanya ki tafi garin ku

Bazan iya rike Ku ba har Ku biyu Nima nawa iyalin ya ishe ni”.

Sallama Daddy ya musu ya tafi sai da ya masa alkhairi Mai tarin yawa sannan sosai yayi godiya.

Abba kuwa ba laifi yanzu ya warke Sosai sunje kafancan mutane sunyi mamaki Wanda suka San su Kenan gashi kuma Baban su sun dawo an sha koke koke da labari kafin wani lokaci komai ya Zama tarihi Baffa yaja Abba a jikin sa sosai haka su Yusseer yanzu a wurin Inni suke ita ke musu komai har yau babu Wanda ya furtawa Sameera komai dukda tasani itama bata nuna ta sani din ma.

Yau ta kama Friday Inda kowa ya zo gaida Inni da Baffa jiya sukaje gidan Daddy yau kuma suka yo nan kamar hadin baki suka hadu anan sai da suka ci abinci suka sha sun zauna ana ta hira Dan har su Inni sunan mazan kawai basa nan.

Mas’ud ya kalli pretty dake kama center table ta mike ga gashin ta Masha Allah mai tsaya da laushi.

Yace, “so nake yarinyar nan ta min laifi na kama gashi na aske ya dawo na Maza”.

Ummusalma tace, “chatty ko? Daman Kai ne Ka Sace ta Ka Kai ta aka Mata askin suna kaga yarinya tufarkallah”.

Inni tace, “Mas’ud fa da Yana karami shine ya kama Kan walida ya aske itama da tana karama gashin ta yafi na pretty”.

Dariya ayi Banda ita da ta cukume fuska ta daure ta tamau.

Yace, “Amma naji dadi Inni laifi tayi ko na aske gashin”.

“Na manta me ta maka kawai Ka ko kayan wasan Ka ta bata ne ko me tayi tana bacci kaje Ka sami scissors Ka yanke Shi tas ga Kan nan Mai laushi gwanin ban sha’awa Ka yanke kasa Sheva Ka aske Ka kusa Gama wa nikuma na fito daga wanka na ganka kana aiki nan Baban Ku yace kuma bazan dake ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button