A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Daman na jima da sani Baffa na so na irin yafi kowa Sona din nan”.
Ummu ce kadai bata zo ba tana can tana fama da cikin ta kasa zaune ta kasa tsaye ita ce tace baza ba, waya ya dauka ta kirashi suna tsaka da hiran su a zabure ya mike ya tashi ya fita ganin haka suka San ba Lafiya sai, Mas’ud zai fita pretty ta fara Kiran sunan sa tana kuka.
Dawowa yayi Yana bata fuska.
yace, “ke ban hanaki cewa chatty ba? Papa zaki ce”.
Yarinya kuwa ta kuma cewa” cati”.
Daukan ta yayi ya dungure Mata hakan yasa shida Binaif ne kawai suka tafi sai au yusuf da suka sulale suka bisu sukuma suka zauna Zaman jiran tsammani kowa shiru yayi yana tunanin.
Bata fi awa biyu Allah ya sauwake Mata ta haihu bata da doguwar labour Basu wani jima ba komai Normal suka dawo gida Rasa inda zasu je sukayi Kawai suka Kira Anty, Anty kuwa tace suje gidan Inni nan suka je suna zuwa aka taso kowa so yake ya dauki abinda aka Haifa ganin Yara biyu Daya a hannun Yusuf Daya a hannun Yaseer yasa kowa mamaki manya ne suka fara karban su itade ummu dakin Neena ta Shiga ta kwanta sai bacci.
A parlour kuwa bayan kowa ya gama ganin yarinyar Mama da Inni suka tafi daki suka barsu anan.
Yaseer yace, “yes wannan ta hannun Yaya ita ce Mata ta”.
Yusuf yace, “ni kuma babbar ce kasan nine babba”.
Sameera tace, “dalla can kuyiwa mutane shiru wani matar Ku”.
Ummusalma tace, “uwar yaran ma tace baza ta bayar ba wai lokacin sun tsufa bansan uban ba”.
Mas’ud yace, “nine uban Yara nan kuma sai na basu wannan a rubuce yake kuji dakyau”.
Tashi tayi itama ta bar wurin ta rabu dasu suna bugawa harda Muja itama ba laifi akwai surutu mijin tane de beda meshi ba daga nan kowa ya watse aka tafi sallah. Suna daki Bayan ta farfado Ummusalma tace, “kunga ki fadawa Umma kafin azo a maimai ta”.
Neena tace, “wannan tsohuwa da Mita take”.
“Wai sai yaushe zaki yi aure ne?”
“Zanyi bakin sa tare za’a hada dasu Anty Saima ba?”
“Bansani ba zamu sha biki”.
“Sosai zaku sha Kam”.
Muja tace, “kinji wani wuri ko kunya babu ko?”
“Wanne kunya ai ni ko kuka bazan yi ba nifa ina so”.
Sameera tace, “wai mu ba yayunki bane? Ko kunyar mu bakya ji ko?”
“Aff sorry Yaya Sameera yi hakuri kinji kafin ya Mas’ud ya fara Kuli Kuli Dani”.
Ummu tace, “Yaya salama kice su dena magana Damu na suke”.
Tace, “kudena magana kuna damun ta”.
Cigaba hirar su sukayi cikin raha.
Ranar suna yara sunci sunan Anty wato zainab da sunan Umma Aisha, Hajiya Umma ana Jin ansa sunan ta ya kada guda harda Kiran masu kidan kwarya ta taka abin ta.
✨✨✨✨✨✨✨
Bayan wani lokaci abubu da yawa sun faru ciki kuwa harda haihuwar Mas’ud da Mus’ab inda Mas’ud ya samu mace shikuma Mus’ab ya samu Namiji pretty tayi wayo sosai har yanzu Chatty take cewa sai dai yanzu tana cewa uncle kullum indai yazo bata fita tana wurin Shi haka idan taje gidan ummu ta nace Sai an bata Yara biyu ta dauke su kuma baza’a karbe su ba da kuka de take baro gidan wata ran kuma ta kwana a can har a gidan Umma tana kwana ko ina inde taje sai ta kwana sukuma su barta sun san bata kuka kuma sannan bata da kiwa.
Yarinyar Mas’ud Sunan Ummusalma yasa amma yace sunan matar yayan su ba ita yake nufi ba inda suke ce mata Banafsha, shikuma Mus’ab sunan Daddy yasa sosai hakan yayiwa Daddy dadi.
Yau ne sunan Ummusalma da ta Kara haihuwa Allah ya bata ‘yan biyu duka zama wannan Karan a gida ta zauna sai waya Mata da Umma ta aiko Mata dashi sosai hakan ya mata dadi ita ke mata komai ga su Sameera kullum suna gidan sai can dare suke tafiya.
Mas’ud yace, “Aljanar kauwata wanne suna kuka saka ne wai? Nifa banji ba yau na makara sallah sunan wa aka sa suna na ko?”
“Chatty! Ka dame ni fa ina ruwan Ka da sunan dana sakawa yara na”.
Yana rike da pretty yace, “wannan yarinyar Zan daka idan Baki fada min ba kin san Zan iya”.
“Daka ta in daka Ka Nima”.
“Kefa kin fiye san kai ko dan karar yaran fari nan bakya yi”.
Sameera tace, “kana san kasan sunan da aka sa?”
Dawowa kusa da ita ya zauna yace, “yawwa my mata fada min”.
Fari tayi da Ido tace, “sai biya zaka sani”.
Me sauran zasu yi na dariya ba, tashi yayi ya fita Yana kumbara fuska girgiza Kai kawai tayi suka ci gaba da hiran su Neena ba tazo ba sabida tsohon cikin dake jikin ta.
Ta tashi dan taje Kiran da Maman Binaif take mata kawai taji an rungume ta ta baya tasan chatty ne yayi hakan.
Tsayawa tayi bata juyo ba, yace, “thank you, thanks you so much Salmomin bb nagode sosai”.
“Kaga ni sake ni kazo kabi kawani makale ni”.
“Kedaman ba’a maki abin arziki ni na tafi”.
Da daddee suna zaune kowa ya watse Sai yasu ya su suka ga Mas’ud yazo da uban kayan wasa da kayan sawa harda oversize kayan wasa Kam kamar ba gobe wai duk na me sunan sa ne, dakin da ya ware acewar sa shine dakin sa yayi ta kaiwa babu Wanda ya masa magana sai pretty da tashi tana murna duk nata ne.
Dauko ta yayi suka fito bayan ya Kai na karshe ya dawo ya zauna ya dauki Mai sunan sa.
Yace, “kaga kayan nan Duka naka ne Kai daya kadan ne na Fav din Ka kaji ko? Kar Ka bawa genios da Banafsha da kowa ma Duka naka ne”.
“Sune ma zasu fara amfani dashi kuwa”.
“Fav bafa nasan haka Bana so”.
“Daga fadar gaskiya”
“Nace Bana so”.
Yaseer yace, “Nima idan nayi kudi Zan siyowa Mata ta dayawa dayawa”.
Ummu tace, “wacce matar?”
“Walida mana”.
“Cab kana mura yaro bazan bayar ba lokacin Ka tsufa harda sandar ka ma”.
“Am just 16 fa”.
“Awwww har yanzu a 16 kake kana last year kana zancen 16 ko?”
Yusuf yace, “aikuwa yarinya solely a bamu tunda Yara sun San mu summa gane mu”.
Binaif tashi tayi ya koma parlourn sa shida Uncle Dan basa iyawa wannan zancen sun San ba tsira sukayi ba ana jima zasu dawo nan.
Yusuf yace, “Yaya salama ya kamata kin na kusa karasa diary dinki?”
“Yusuf daman nasan sai Ka Karanta ai”.
Yaseer yace, “befa Karanta ba Sai da kika dawo daga karatu to ranar da Ummu ta kawo mana Hotan ki ranar muka Karanta”.
Ummu tace, “har sace sun da akayi sai da aka rubuta acikin”.
Murmushi tayi tace, “kuyi hakuri nifa nasace Ku”.
A tare suka tambaya.
Yusuf yace, “sabida me?”
Yaseer kuma yace, “taya?”
“Ranar idan zaku tuna ai na fada maku unguwar da nake to muna Gama waya na Kira wani ya sace Ku”.
Sameera tace, “da Baki fada ba babu Wanda ya sani”.
Yusuf yace, “wa kika sa ya sace mu?”
“Wani Mai napep ne nasa Shi Shi kuma yasa Yan dabar unguwar su shine fa sukayi komai”.
“Tab kinyi kokari kuwa”.
Murmushi kawai tayi yaseer yace tashi muje Ka dauko”.
Muja tace, “kwa Bari safiya tayi ai sai kuje amma yanzu dare yayi”.
“Baki San yaran nan da niyya ba”. Ummusalma tace.
Washegari da sassafe sukayi sammako gidan sunsan Abba Baya nan Baffa yace su maida masa da Companyn sa na Abuja Dana Lagos na Abuja kawai ya ansa shikuma Baffa yake zuwa na Lagos. Sukuma su Mas’ud daman ba bangaren suka Karanta ba a Spain suke aikin su ta online idan ana taro de suna zuwa har Binaif dashi ma yake aiki online.
Sun shiga sun dauko suka fito dan ko Inni bata san sun fito ba, sabida sammakon da suka yi suna cikin rufe kofar Kenan Abba ya dawo shima dayake Baya nan akayi sunan Ummusalma shiyasa ya dawo da wuri dan yaje yaga yara ya koma a yau tunda aka haife su be jeba ganin su yusuf suna rufe gida yasa Shi Danna musu horn.
Juyowa sukayi suka jira ya fito, tare da Kara Sawa suna gaida Shi.