A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yace, “me kuke anan da sassafe haka?”
Yaseer yace, “Abba fa littafi muka dauka kuka fa 7 tayi harda Mintina”.
“To shikenan Baffan Ku Yana gida”.
“Ehh Yana nan Amma yau zai tafi Lagos”.
“To idan an Dan jima Zan zo mu gaisa ina da meeting ne da karde biyu”.
Yusuf yace, “Amma Abba ba’a mota kazo ba”.
“Ina Zan iya tafiyar mota? A airport na ajje motar”.
Yusuf yace, “Abba Bari mu tafi sai kazo”.
Sunje zasu fita kenan da motar su Mai gadi ya bude musu suka ga wata Almajira tana tahowa.
Yaseer yace, “wayyo mahaukaci ya”.
Kallo Daya Yusuf ya Mata ya gane ta bakowa bace sai Mama taka mota yayi zai bi ta kanta yaseer ya kwalla Kara. Dayake glass din su a sauke yake yasa Abba yaji karar sa da sauri ya juyo ya taho wurin su da sauri matar ta matsa gefe gaban ta na faduwa.
Abba ne ya tsayar da Yusuf hakan yasa ya tsaya suka fito, cikin tsananin fada da fushi ya fara yi masa fada.
“Maka da hankali ne Yusuf? Wannan ai ganganci ne meye wannan din kayi?”
Kana kallan fuskar sa zaka San ransa a bace yake.
Yace, “Abba fa matar da kike ganin bata da wani amfani shiyasa zan Dan bigeta”.
“Idan mutu fah?Ka kashe ta Kenan?”
“Haka Allah ya kaddara Amma ni ba niyya ta na Kashe ta na niyya ta na dan ji mata ciwo taji zafi a zuciyar ta”.
Kafa yasa zai bige Shi ta karaso da gudu ta tsugunna tana kuka dan taji abinda suka fada Duka kuma taga kamar Basu gane ta ba.
“Ka kyale Shi ba komai Yana ganin hakan shine Daidai”.
Yaseer dake kusa da Abba ya saki Baki Yana kallan ta can.
Yace, “Mama?”
Abba yace, “Kai bansan shashanci Kai kuma wacce maman? Gizo ta fara yi maka kome? Wannan almajar ce Mama? Get lost”.
Ganin be gane ta ba yasa tace”, Alhaji nice nice de saratun Ka nice wallahi”.
Sai nan Abba ya kare Mata kallo.
Yace, “Alhaji me? Saratun wa? Saratuna a da ba?”
Yusuf yace, “mekika zo kiyi mana bakin ce baza ki zoba? Kalli gidammu be ruguze ba sai ma kyau da yake yi duk bayan wani lokaci kalli Shi dakyau ki gani, yanzu mekika zo yi mana?”
Yaseer yace, “kaya tazo dauka kayan ta kuma tun wacce Shekarar aka Kona su kinga ki tashi ki tafi kafin mu Kira maki ‘yan sanda aka kaiki dawanau a killa ce”.
“Yaseer yanzu ni? Mahaifiyar Ka ce fa?”
“Kin tuna?”
Murmushin takaici Abba yayi ya wuce ciki ya kyale su ko giyar wake yasha bazai dawo da ita ba Shi shawarar Baffa ma zai bi kawai yayi auren sa bari suje kafancan ayi maganar.
Yaseer yace, “sanda muke maki magiyar ki tsaya kin tsaya?”
Yusuf yace, “Kin tuna yanzu tabam da ki kawa Sameera( yau ba yaya kenan Rai ya baci) Yana nan be goge ba sanda nace Zan nuna maki mikace?”
Tuna Mata duk abinda tace sukayi tayi wannan yayi wannan yayi daga karshe suka barta ta tafi ko oho, suna zuwa gida suka tarar da Inni a parlour zasu wuce ta kirasu suka zauna.
Sai da Baffa ya fito sannan suka Fadi abinda ya faru sosai ya musu fada Akan mahaifiyar su ce sunce sun yafe ne kawai, suna shiyarwa suka zarce gidan Sameera suka fada Mata ko kallan su bata yi ba itama dakyar dakyar ta yafe mata.
Abba kuwa Baffa ne yasa ya yafe mata komai ya wuce.
Ashe kullum sai tazo basa nan kullum Mai gadi sai yace Mata basa nan sai ranar tayi sa’a. Da ta kuma dawowa kuwa
A wani paper ya rubuta mata ya bata ya fiyar da suka mata tayi kuka kamar ba gobe.
Gidan Anty taje Anty Kam ta karbe ta hannu biyu ta bata abinci taci sannan tayi wanka daga na. Take neman alfarmar a nuna Mata gidan Ummu taje ta nemi yafiyar su yusuf.
Anty tace, “yanzu Ummu bata gida tana nan gidan kauwar mijin ta Bari nasa a rakai ba nisa”.
Sawa tayi aka rakata har Gidan Ummusalma su Duka suna nan Banda su Yusuf suna zaune da yake da yamma ne kowa na zaune abin sa ana hira ana raha Yara na rarrafe su walida ana taka wa suna yin Gwara kyale su akayi kowa yayi abinda zai iya sai ga Mama tazo.
Surrender tayi ganin Ummusalma sai kuma ya fashe da kuka tana nemna yafitar ta ta kwa ce ta yafe mata Sameera ma tace ta yafe tayi kuka sosai daga nan aka kaita gidan Baffa ta Nemi yafiyar ta anan take sanar dasu Ashe bayan barin ta gida China ta nufa dataje can visan shekara biyu tayi gashi yanzu shekaran ya kare babu kudin komawa ga an Mata sata har passport haka ta koma kwanan kwararo wasu suyi abida suka ga dama da ita su yar abinsu idan taci sa’a ne zasu bata abinci a haka suka binciko ta suka hankado ta kasar ta shima nan tasha wahala kafin tazo Kano yanzu kauyen su zata koma. Sosai aka Mata shatara ta arziki a
Ashe kauye Daya suke da Muja sai da ta koma take Jin labari babu Wanda ta fada wa kuwa Muja tayi gum da bakin ta.
Yau sun tafi gidan Umma bayan ta zubar da wanka Umma suna zuwa ta dauki Takwarar ta ta rike Gam a hannu ita kuma Ummusalma wurin lilo ta tafi taje ta zauna hakan nan ta fara tuno sanda ta zauna a gidan wayan cin lokuta anan suke zama Yana bata labari. Tana lilawa tana murmushi ita daya shine yazo ya zauna a kusa da ita shima ya fara lilawa Yana kallan ta.
Yace, “wannan murmushi da’alama ni ake tunowa”.
Bata San ma ya zauna ba sai maganar Shi da taji kallan sa tayi.
Tace, “nifa bakai nake tunowa ba”?
Matsowa yayi kusa da ita sosai Yana wani murmushi kana ganin sa zaka San Yana cikin farin ciki.
Yace, “naji wannan”.
“Wannan annurin da kake fitar fa na meye?”
Kwanta wa yayi a kan cinyar ta Yana kallan fuskar ta da kyau.
Yace, “Ina fari ciki ne sabida zan angw…”
Rufe masa Baki tayi tace, “kaga nasan karshen zancen daga ni Umma tace zamu je kauye gobe kuma Banda ku iya Mata kawai”.
“Kinsan bazan yarda ba? Wancan zuwa kasa Jura nayi muka biku fa sai muka tarar wai kun tafi kasuwa”.
Dariya tayi sosai.
“Kasan Chatty me yace mun?”
“Um,um”.
“Gulmata ake kuma banzan…”
Kasa karasawa yayi ganin abinda Binaif ya mata kuma yasan zuwane hakan ya faru,koma wa yayi Yana cewa” aikuwa yanzu ya zamu tafi”.
_Alhamdulillah_
Anan na kawo karshen Littafi na Mai suna A BAKIN WAWA akanji magana. Kura kuran dake cikin sa Allah yafe mana abinda muka Karan cikin sa Allah yasa muyi amfani dashi Allah ya rabamu da Hali irin Na Mama da Hajiya.
A gaskiya kuma naji dadin irin yarda kuke nuna min kaunar Ku a gare ni. Har ila yau muna Tare a cikin.
FARIN CIKIN NAH muci gaba da Jin yarda zata kasance.
GODIYA TA MUSAMMAN GA:Amina Muhammad Salis amsie(cwthrt ????)
Nagode sosai da sosai cwthrt ????.
~Taku har kullum.~
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
❤️