A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ Baki iya bada hakuri bane ?
Gani take idan ta kuma dagowa ta kalleshi to ai matsayi yasamu,ko kallo bai isheta ba,ta sa Kai tazo zata fita,ji tayi an riko hannunta, a masifen ce zata masa magana saidai ganin Wanda ke rike da hannunta yasa gabanta faduwa,ta zuba masa na mujiya kawai tana kallansa,shima ita yake tabbas wannan badan ita kadai taji an Haifa ba zata iya cewa dan biyunta ne sabida kamar su ta baci ba kadan ba,komai nasu iri daya banbamcin sa da ita kawai tana da tusar jaki shikima bai daita ta fishi karamin baki,ta kuma fishi eyelashes,wata zuciyar ce tace Mata kawai kama ce bakomai ba,sannan ta sauke wata Ajiyar zuciya,shima kallanta take kuma besaki hannunta ba,

yace’ Ina mai baki hakuri da abinda fav bro ya maki dazu da kuma yanzu kinji?
Yarda yake magana zaka san baida lafiya,gakuma hannnun Shi da ya riketa,zafi kau dashi,ganin tana kallansa yasa dayan

cewa’ in fada maka bazata maka magana ba ai,wannan da Ka ganta tafi BB miskilaci wallahi gwara ma ka kyaleta Ka barta,kar Allah yasa ta hakura din,daman bani na Baki hakuri ba shine ,
Kallanshi tayi bata ce komai ta ajje ledar hannunta ta sa hannun ta cire hannunsa batare da tayi magana ba tayi gaba ta kyalesu,tabe baki Chatty yayi

yace’ dakai daga fada maka kamanninta shikenan sai Ka gane ta kallansa yayi

yace’ yarda kabani labarinta,yarda kayi ta fada Mata magana bata tanka ba nasan itace wannan ganin yarda ka bata Mata hajibi kuma kayi magana Amma bata tanka ba.
Dariya yayi Yana Zama

yace’ Kai mai tsoron Mata ne fa da ace ta tanka maka akan abinda Ka Mata dazu,to yanzu idan hakan ta faru nasan da da gudu zaka bar nan wurin,ya karashe da dariya sosai Duka ya kai masa ya goce

yace’ Kai kuma fa? Har gwara ni ai Akan Kai,ya karashe yana bata fuska,tashi yayi ya fita wai ko zai ganta,Amma bai ganta ba shima fitowa yayi daga nan suka fita.

Tana zuwa daki ko hijabi bata cire ba ta dauko zanen ta ta zana dayan tasa masa glip a sama sunansa. Sannn ta ajje tazo taci abinci tayi shirin bacci ta hau tunanin,ita Allah yasa ma kar su Kara haduwa da su.

Washegari da wuri ta shirya ta fice wurin aiki,wanke wanke ta farayi sannan ta fara taimakawa ana yin abinci, haka sukayi har lokacin tashin su yayi,tana fitowa tagansu zasu shigo,ko kallan inda suke bata kallaba bare su hada ido tayi masu magana, Chatty ne ya hangota zata wuce da sauri yasha gabanta 

yace’ yawwa wana kama? Dabaki fada min wurinba na Allah basa karewa sun fada min? Glip ne ya karaso

yace’ haba mas’ud meye hakan wai?
Kaga mus’ab kyaleni,ni zatayi ma banza ina Mata magana ?
Kallansu kawai take yi,yo ita badan duniya bama da ta sauya mata akwai Wanda ya isa yadaga Mata murya ne bare kuma har ya tsereta Yana fada Mata magana?
Wani banzan kallo tamasa tare da Jan wani wawan tsaki,ta wuce bata tanka masa ba,ai daga mus’ab din har mas’ud cikinsu ne ya duri ruwa Basu iya tankawa ba,dakyar mus’ab

yace’ kaga ni ko?kaga abinda Ka janyo mana,to wallahi nikam ba ruwana bazan Kara Shiga sabgar taba ato.
Ya wuce Shi ya barshi a wurin,ai kuwa de yasha jinin jikinsa ai,jiki a sanyaye ya Shiga ciki shima,mus’ab sai ya kalleshi sai ya kwashe da dariya,

yace’ kaga wata yarinya can jeka ka tambaye ta inda ake Shan ice cream kaji fav bro,
Ya karshe cike da zolaya, lokacin an kawo masu abinda suka bukata,don haka Saida ya fara ci,sanna ya kalleshi ya kalli yarinyar da aka nuna masa sannan

yace’ hmmm kai ai Dan bakaraba wallahi,taab nifa nazaci baza iya yin komai ba.
Wai kaga ma kuwa wani kallo da tayi minne?

Awww Kai kadai tayi wa?tayi mana de zaka ce,
Kasan wani abu lokacin da BB yake cewa shiru shiru va tsoro bane gudun magana ne ban taba yarda ba sai yau,

Jibi ita ba magana tayi mana ba amma gaba daya kallan da tamana yasani Jin Kara tsoron Mata wallahi,

Kai ta kallo take tsakin da taja Kai,

Ni wannan bai dameni ba,wannan kallan,kallo ne na irin gargadin kar ka Kara Shiga harkata,
Dariyan mus’ab yayi

yace’ to yanzu fav bro mas’ud dafatan Ka dauki darasi ko?
Shima dariyan yayi

yace’ darrussa na dauka,ai

Nikam idan mun hadu Zan bata hakuri daga nan sai mu kulla zumunci tunda da ‘alma yar 9ja ce kaga shikenan munyi friend mace de ko?
Tunda yafara zancen zuwa da bata hakuri yake kallanshi tou Shi yanzu ko haduwa yayi da ita ai baya jeba taab.
daga nan yace’ Kai kadai zaka kulla zumunci ka Amma Banda ni,

To naji nima Banda ni kadai shikenan?
Ehh shikenan ya bashi amsa,sanna yaci gaba

Amma nifa twiny wannan yarinyace bata fi bama tafi 17-18 bako?

Kaga fav bro idan kun hadu sai Ka tambaye ta shekarunta inaga hakan yafi ai ko?
Ganin maganar yakeso yasa shi yin shiru Yana cin abincinsa,shima mus’ab din shiru yayi ganin ba’a tanka masa ba.

????????????????????

Aikin banza suzo su addabi mutane kawai idan ya kuskura ya Kara Shiga harkata sai na nuna masa true colour Dina tunda Shi beda mutunci,
Ita kadai take mitar ta tana juyi Akan gado,zaman dakin ne ya isheta yasa ta fitowa fita wurin dayan aikinnata,sai bayan magriba ta dawo, wanka tayi,tay sallah sannan taci abinci ta dau Qurani ta karanta, lokacin Isha nayi,tayi ta kwanta.
Washegari ta makara sakamakon ciwon bayan da ta tashi dashi, gashi batayi wani baccin kirki ba,haka de ta shirya ta fito, fuskar nan kamar kullum,tana tafiya taji tayi kicibus da abu dagowa tayi don ganin da me tayi gware,shima ita yake kallo, hada ido sukayi babu Wanda yayi tunanin dauke idon sa, fuskar juna suke karewa kallo,tunanin inda yasan fuskar take Amma yakasa ,itama tunanin inda tasan Shi takeyi Amma kuma ta kasa tunowa,
ahankali ta fara janye idonta tayi kasa dashi,bahaka yasoba yaso ace sun cigaba da kallan juna wani irin yanayi ya tsinci kansa mai wuyar fassarawa,ganin tana shirun wucewa yasa ya riko hannunta,sai da gaban ta yafadi,Amma bata juyo ba shima bai juyo ba

yace’ can’t you apologize?? U don’t know how to apologize right????
Tabbas tasan muryan nan kuma yarda ya fada haka aka taba fada Mata,Amma a’ina ???
Batare da ya saki hannunta ba taji yace’ maybe ma
Kurma ce, da fillanci yayi maganar,kuma taji abinda yace bataji mamaki ba kasancewar Shigar hausawace tagani a jikin Shi harda hula kuma yayi Kala da Fulanin,
Hannunta tasa ta tacire hannunsa tayi gaba ta barshi Yana binta da Ido,taxi ta Shiga ta barshi a wurin.
Koda taje wurin aikinta dauriya kawai take yi sosai bayan ta ke Mata ciwo indai zatayi period haka takeji,a daddafe ta Gama aikinta har lokacin tashinta yayi,ta dawo hanya,nufar dayan wurin tayi namma yau akwai aiki,Basu Gama sai dare kusan 9pm sannan ta samu kanta shima a hakan sararawa ce Akayi give zasu ci gaba,tafiya kawai take batare da tasan ina zata dosa ba tasan dw tadau hanyar school dinsu,sai ogan su yace zai sauketa tace a’a, tsayawa tayi tana jiran me taxi ganin tafiyar ta gagareta,mota ta gani ta tsayar Shiga kawai tayi ta Fadi inda zataje, har jikin campus ya Shigar da sai da tafito sannan ta fito da kudin Shi zata bashi hannunta ne ya makale ita bata Mika masa ita bata mayar ba,kawai ta tsaya take kallanshi,mutumin dazu ne da sukayi Karo,fitowa yayi ya zagoyo inda take cikin harshen turanci

yace’ da sace mutane nake saidai na sace ki ko? Meke damunki haka?
Ganin bata da niyyar magana yace’ wannan motar ta maki kama da taxi ne ?
Bata kulashi ba sai maida kudinta tayi jaka tana neman tafiya da sauri ya riko hannunta

yace’ sunana Abdulshakur,ana Kirana da Binaif,sai Naga kamar na taba ganinki Amma ba anan ba zan iya sani?
Hannunta ta cire daga hannushi cikin Hausa

tace’ kar Ka Kara tabani,
Ta juya ta barshi a wurin, tabbas ya Santa kuma ya tuno inda yasanta,Amma abin mamakin da ai bahaka take ba meya faru ta dawo shiru shiru haka??
Yana nan tsaye ya daga waya yayi kira, fitowa yayi daga cikin campus din ya samu wuri ya zauna ya Dan jima a zaune sai ga su mus’ab nan sunzo,sun jima kuwa suna bashi labarin abinda ya faru bai nuna musu ya Santa ba har suka gama bai kuma yi magana ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button