A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????
Tana Shiga daki wanka tayi taci abinci sannan ta kwanta,sai da ta kwanta tafara tunanin shi,
Abdulshakur tace,meyasa ta manta inda ta sanshi? Tashi tayi ta zauna ji tayi maganar sa tana dawo mata inda yace meke damunki?? Lumshe ido tayi ta bude ba’a taba tambayar abinda yake damun taba,koda can data ke ganiyar kan mulkinta babu Wanda ta taba tambayar damuwarta,haka sahr da suke kwana su tashi tare bata taba ganewa ba sai Shi?? A,ina ta sanshi? Ganin baccin ya gagara yasa ta tashi ta leka window hango su tayi sunsa Shi a tsakiya suna ta maganar su, dariya suke Amma bandashi ga dukkan alamu ya tafi duniyar tunani ne,kallanshi kawai take bako kiftawa, bata San metake ji ba idan tana kallanshi amma koma mene ne hakan Yana Mata dadi sosai. Tashi taga sunyi zasu Shiga mota,kamar yasan ana kallanshi kuwa yatsaya ya kalli saitin windown ta,tasan de baya kallanta sabida filar daki a kashe take, shiyasa ta tsaya,ya Dan jima Yana kallan wurin daga bisani kuma ya tafi.
✨✨✨✨✨✨
Tun daganan bata Kara haduwa da suba hakan ya Mata dadi bakadan ba,bata kuma son Kara ganinsu,musamman Shi da tun sanda ta daura idan ta akanshi take fama da tunanin sa, har aka dawo hutun makaranta wahala ta dawo,dukda wahalar karatu dakuna zirga zirga hakan bai Hana ta yin kyau ba fatarta ta murje,tayi haske da ita,sai dai ba kiba tana nan bata Kara kiba sai abinda ba’a Rasa ba. A haka take samu take biyan kudin makarantar ta kuma tana tara wani tunda shekara shekara,har sun gama year two abinsu,kokari kuwa sai abinda yayi gaba ba baya ba don basa wasa da karatun su ko kadan kuwa. Duk hutu sai sahr tace suje gidan su amma bama ta kallanta bare ta dau zancenta da muhimmanci,har ta hakura ta dena Mata zance.
Shekara daya Kenan Amma kulluma sai tayi tunanin Shi. Gashi yanzu sunyi hutun first semestern na year three,yau weekend tana zaune tana karanta papern Neena mus’ab yazo kusa da ita,daman ta ganshi fuskewa tayi, kuma ya wani zo ya zauna kusa da ita, Amma ganin ya Mata sallama yasa ta ansa,
yace’ am kin….ga …am,da…man. da..da am
Jin Yana in ina yasa ta Kara daure fuska ta dago ta kalleshi tayi shiru
yace’ daman hakuri Zan baki
Akan abinda wancan yaran yayi Miki haka yake Shi sai tsokana Amma kiyi hakuri kinji?.
Ya karashe da lagwabar da Kai,kallansa tayi
tace’ shikenan?
Gani ta mai magana yasa Shi cewa uhhm
Nafadi dayan?? Ya fada cike da fargaba kar tace a’a
Nodding Kai tamasa kawai tana wani lumshe ido alamar bacci takeji, cigaba yayi
yace’ wallahi ina sanki ne daman,gani ta bude ido yashi saurin cewa bafa San soba, so na kawaye dakuma so na Yan uwa musulmai haka nake nufi,amma kiyi hakuri idan bakya so sai na daina sonki shikenan,yafada yana neman tashi ga mamakinshi sai ji yayi
tace’ Ummusalma by name,
A sukwane ya dawo ya zauna,wani irin dadi yaji ya kamashi, sai yaji Shi wani irin free lokaci daya ya daina Jin tsoro tsoronta, numfashi yaja,
yace’ kinsan nazaci bazaki amsa min ba?
Itadai nata kallo ne,tana jinshi,.baidamuba yaci gaba
yace’ twins ne mu amma ba identical ba,ni mus’ab shikuma wancan yaron mas’ud, munyi karatunmu a spain.amma mu yan Nigeria ne kingane?
Daga masa Kai kawai tayi,
yace’ fav bro Yana da tsokana sosai tun muna yara gashi bashi da kunya,bede hakuri,ga Shi da zuciyar masifa, surutu komai ya hada,bejin tsoron komai sai abu daya kinsan menen? Ya tambayeta Yana kallanta, nodding tamasa alamar a,a,cigaba yayi
yace’ Yana da tsoron Mata ko kuma nace muna da tsoron Mata don har gwarani ma ni akan Shi, shiru yayi sannan yaci gaba
yace’ bamu kadai ba har yayammu shima tsoron matanne dashi Amma ba kamar mu ba, BB ya koma 9ja da na hada ku dashi.
Kallanta yayi yace’ kefa fadamin kinsan wani abu a kaina de ko?
Girgiza masa Kai tayi
tace’ Akan Chatty, ba Kai ba,
Chatty kuma? Ya maimaita,.
Daga masa Kai tayi a hankali tace mas’ud,
Dariya yayi
yace’ shine chatty? Bata daga masa Kai ba amma kuma bata kalleshi ba,
Yace’ to ai halin mu daya dashi nikawai Bana da tsokana bana da zuciya kamar tashi shikenan banbamci Amma Duka halinmu iri daya ne kinsan mu twins ne.
Ahaka ya cigaba da bata labarin tsokanar chatty, dayake yi,dukda ba magana take ba Amma tana enjoying jitayi kamar tana tare da Neena,kawai kallanshi take Yana bata labari,sai a labarin bai taba sako iyayen su ba sai dai yace bb.
Suna nan har lokacin magriba sannan ya Mata sallama ya wuce
washegari tare da chatty suka zo amma ko kallansa batayi dukda ya bata hakuri,tun tana shareshi idan Yana sa Baki har take Dan daga masa Kai ko girgiza masa Kai haka suka debe Mata kewa sosai,sukayi exchange number,daga nan kuma Basu sake haduwa ba,sai wani weekend din sosai ta saba dasu tana so ta tambayesu iyayensu fa? Amma kuma batasan mezatace ba tunda ba iya tambayar Abu tayi ba itakam…..
Hope your are enjoying the book ????????
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
9
Yau Monday da wuri ta shirya ta fita,tana fitowa ta hango su suna zaune suna hiran su, ko kallan inda suke batayi ba zata wuce da sauri suja tashi suka bita,glip ne
yace’ Haba ke kuwa ya zaki wuce ko kallo babu kuma Nasan kin gammu,
Ko kallo be isheta ba taci gaba da tafiyar ta, Chatty
yace’ yau yan mutuncin ne kenan ko?
Ya fada Yana Dan Sosa Kai ganin irin kallan da ta watso masa,ganin ma haka yasa shi Jan bakinsa yayi shiru,shima Glip shiru yayi da bakinshi, ahaka suka samu taxi ta Shiga Suma suka Shiga fada masa inda zai kaita,ita da mas’ud a baya mus’ab kuma a gaba, suna baya tafiya tana kallan hanya
tace’ meyasa kuka fito da safiya haka?
Kallanta yayi ganin hankalinta a waje yake kuma yasan badan Allah yasa yaji ba to yasan ba zaiji me tace ba,
Kawai mungaji da Zama wuri daya ne, shiyasa muka fito,
Bata kuma maganab har suka iso, suna ta sauka abinta, zata wuce mus’ab
yace’ kudin Shiga?
Kallan irin ni nace ku Shiga tayi masa,sannan ta juyo ta kalli Shi
tace’ chatty ya bayar,
Ta wuce abinta ko juyowa batayi ba,kallan kallo sukayi sannan mus’ab
yace’ chatty kaine fa zaka bayar
Kallanshi yayi
yace’ Wallahi yarinyar nan ta rena ni,har wani na bayar,wayace Mata Tou mun fito da kudi, mu Bama mu San zamu fito ba yanzu, yar renin hankali danma ta samu an rakota?
Tunda ya fara ta dawo Amma besani sabida ya juya Mata baya, shikuma mus’ab sai signing yake masa Amma idan sa ya rufe kawai yi yake,bema kula yaci gaba da
cewa’ sai na seta Mata burki Wallahi idan bata dena cemin wani Chatty ba,Nasan de na girmeta Wallahi,idan auren kauyena ma ai na haifeta,amma tazo take wani yiwa mutane kallan uku saura kwata ake cewa ko,? Koma mene sai na taka Mata burki tukunna zatasan ta takalo masifa,ya kareshe da kwafa Yana jijjiga Kai,
Mai taxi ne ya fito ya zagoyo yace a bashi kudin Shi,ya bude baki zaiyi magana kawai yaga hannu na miko kudin,Baki a bude ya bi hannun da kallo besauki idonsa a ko ina ba sai a fuskar ta,wani irin bugawa kirjinsa yayi,shikuwa mus’ab mezai yi inba dariya ba,
Kallan mus’ab tayi
tace’ Kai Shi yaga psychiatrist,
Kawai ta wuce ta barshi a wurin,shikuwa ca
yace’ dalla muje Ka bata hakuri kaji ko twiny kaga Kai kuna good time da ita kaji Dan yayana?
Ohhh yau nazama yaya Kenan to babu Inda zani,ba’a cemin yaya sai ana neman abu,kaga ma tafiya ta yunwa nake ji Nasan zata siya min abinci Kai kuma ko oho,ya kareshe da murmushi a fuskarsa Yana tafiya,
Dakyar ya tattaro jarumtar binsu ciki,Yana Shiga yaga mus’ab a tsaye Yana nemanta sai wurga ido yake Amma bai hango ta ba,zuwa yayi ya tsaya wurinsa