A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ Nima ina Jin yunwar please kace ta aramin kudi idan mun koma Zan bata kaji ko?
Kallansa yayi yace’ ba sai na ganta ba watakil ma tayi tafiyarta ta barmu,
Tana Shiga taga aiki da yawa mai yin aikin dare namiji ne kuma baizoba sabida haka ayyukan ya taru dayawa ga kuma mai bada coffee shima bai zoba yau kusan ma’aikantan duk Basu zoba,har ta fara ta tuno maybe suna can suna nemanta,tunowa da abinda chatty ya Mata yasata kwafa ta cire apron ta fito,hango su tayi suna baza ido da’alama ita suke nema,daure fuska tayi ta karasa wurin da suke bata kalle suba

tace’ follow me,
Ta juya ta wuce,kallan juna sukayi Basu da ta cewa suka bita, kitchen suka nufa,suka uban kayan wanke wanke,kallan kallo aka fara, ita kuwa tasamu kujera tahau ta daura kafa daya kan daya

tace’ sai nace a fara za’a fara ne?
Kafin ma ta ida Kai zance chatty ya nufi wurin ya fara,ganin haka yasa shima Glip zuwa zai fara

tace’ Glip abinci.
Haka kuwa Akayi sukaje suka ci abincinsu suka koshi sunayi Yana bata labari har suka gama,ita ta biya kudin sannan suka dawo tare da Shi,a mamakinta sai taga ya zage tana tikar uban wanke wanke wurin,ko gajiya kuma baiyi ba,Amma daka ganshi kasan Yana Jin yunwa, tausayinsa ne yadan kamata, tafara mai dauraya,ganin haka yasa Glip zuwa Yana jera inda ya kamata ahaka suka gama,sunayi ana kawo wasu,a hakade suka samu suka gama, lokacin Azahar nayi suka je bayan wurin Inda take sallah tayi alwala ta Ciro daddumar ta sai da ta idar ta Basu sukayi sannan ta fito tayi sallama da masu aikin ta wuce,tafiya suke Amma babu mai bakin magana, Mus’ab ne

yace’ meyasa kike aiki a wurin nan?
Bata kalle Shi

tace’ ra’ayi,
Ganin ba fuskar sake tambayar yasa Shi yin shiru bai Kara magana ba,gajiya tayi da tafiyar ta tsaida masu taxi,wannan Karon chatty a gaba ya zauna,a zatan su school zasu wuce Amma sai sukaji ta fadi wani wurin daban, suna zuwa aka Mata sannu da zuwa daga Kai tayi,ogan su

yace’ customers ta kawo masu ne?
Girgiza Kai tayi tace’ brothers dinta ne?
Da tace brothers dinta ne su kawai kallanta suke suna mamakinta sosai,Basu karajin mamaki sai ji tayi tana cewa the same father the same mother,abin kam ya Basu mamaki sosai,amma koma meye hakan ya masu dadi, introducing dinsu tayi a wurin ogansu, wani Dan daki ta nuna musu tace su Shiga su sameta tana zuwa, bayan sun tafi take cewa ogan ai Suma suna San yin aikin tare da su Amma su tun safe zasu ke zuwa har dare,kuma bai wuce suyi Shara ce da mopping zasu nayi,sosai yayi na’am da zancen ta, sanadiyar tane suke Kara samun customers Akan me kuma bazai taimaki relative nata ba.
Shiga tayi tagansu kowa ya zauna yana duba zanikan dake Dan karamin office din nata,Zama tayi ta kallesu

tace’ zaku ke aiki daga safe har dare anan Shara da mopping idan kuma kun iya computer zaku ke editing,
Kallanta kawai sukeyi ca suka ce suna sanyin aiki ne kome?
Ganin irin kallan da suke binta dashine yasata Kara daure fuska tace’ naga ku ba karatu kuke ba zaman banza? Shiyasa na yanke wannan shawaran, weather you like it or not,
Ta juya ta fara zanenta hankali kwance bata ko kallansu,
Sukuma daman gasu da tsoron matan tsiya ga kuma dazu mas’ud yaci Mata mutunci,bayarda suka iya hakan za’ayi ma. Koba komai Suma suna bukatar kudin.
Kallanta sukeyi yarda take zanen ta ahankali kamar ba zata Gama ba, tana cikin zanen aka Kira ta,ta tashi ta fita, tana fita wayarta ta fara ringing kallan juna sukayi sannan mas’ud yace'”Ka daga kace bata nan,
Be kalleshi ba ya Ciro wayar daga cikin jaka ganin suna sahr yayi akai hakan yasa

yace’ wallahi wannan kawar ta tace mai surutun nan bazan daga ba taab,har wayar ta katse aka sake Kira Basu dagaba ganin ba’a sake Kiraba yasa Shi daukar wayar bakomai ajikin wayar, contact ya shiga,yaga mutane shida ne kawai aciki,daga sunan su sai na sahr sai kuma inda take aiki, daga wayar yayi ya kalli mas’ud

yace’ kaga contact dinta mutune shida kawai ne aciki,
Numfashi mas’ud yaja yaja

yace’ lamarinta Yana ban mamaki bakadan ba,
Beyi magana ba ta shigo,hakan yasa Shi yin shiru bai Fadi abinda zai fada ba.
Ajje kayan hannunta tayi sannan ta cigaba da zanenta,zuwa Akayi aka kirasu sannan suka fita.
Sunyi aiki kam ba laifi kuma kokadan Basu nuna gajiyar suba Akan hakan, Itakam tana mamakin su,aiki sai kace da can sun Saba?sai dare sannan suka fita,itace ga biya masu kudin taxi,ana Basu abinci a wurin aikinsu.

Sosai suka shaku da ita dukda bata magana Amma ba laifi,hakan na masu dadi,ga kuma kudin aikinsu da ake biyansu, albashin farko suka bata Amma ko kallansu ma batayi ba bare ta amsa,ahaka sukaci gaba da zuwa abinsu tun safe sai dare,ita kuma daga Azahar zuwa dare tare suke dawowa da su,kowa a wurin yasan su har makwabtan shaguna saboda faran faran din da suke da jama’a ga girmama na gaba,gashi ba ha’inci a aikinsu,hakan ya Mata dadi Itakam,
A haka aka dawo hutu,basa haduwa sai wurin aiki
Shima bawani hiran da sukeyi sai zasu tafi.

    ✨✨✨✨✨✨✨   

A haka suka cigaba da Karatun su, bangaren su mus’ab kuwa daman two years zasuyi,yanzu kuma befi sauran watanni, su gama, gabadaya basa San tafiya,wata irin shakuwa sukayi ta ban mamaki Dan tafi ta da ma za’a ce,ita kuma a yanzu suna year four hatta sahr tasan irin shakuwar dake tsakaninta da su,sai dai itakam har ga Allah suna birgeta don a yarda umsalma ta fada mata Yan uwanta tace mata.
Bangaren su kuwa,sun kasa sanar da ita cewa zasu saura wata daya su koma,sun kasa tunkararta da zance tafiyar su ya kamata ace tasani tun yanzu amma kuma a duk sanda zasu sanar da ita basa iya wa ahaka suka fara exams daga su har ita, su suna zana final exam ita kuma tana zana ta first semester na year four, sun rigata gamawa kasancewar su masters ne,kuma ita tana course biyu ne. A ranar da suka Gama a ranar sahr ta tafi.
Ta shirya don taje wurin aikinta ta fito ta gansu bakin campus fuskar su kawai ta kalla tasan akwai damuwa, Bama su lura da ita ba kowa Yana sakawa da kwancewa a zuciyar Shi,zuwa tayi ta zauna kujeran dake facing din juna,kallansu tayi

tace’ inaji,
Sai anan ma suka lura da ita,har tazo ta zauna amma Basu sani ba,
Numfasawa mus’ab yayi

yace’ gobe zamu tafi,
Jin maganar tayi wani iri a bakin shi, maimaita maganar tayi

tace’ go..be,zaku ta…fi?
Gyada Mata kai sukayi,gani sukayi ta tashi zata tafi da sauri mas’ud ya riko hannunta

yace’ bamusan yazaki dauki maganar ba shiyasa,Amma kiyi hakuri don Allah,ya fada kamar yayi kuka,
Juyowa tayi ta kallesu taga mus’ab har ya fara kuka shikuma chatty hawaye me fal a idonsa, komawa tayi ta zauna jikinta sai yayi sanyi,
Mas’ud ne
yace’ zamu tafi,amma bamusan komai game da juna ba,ina ji a jikina kedin yar uwar muce,amma munkasa nasanar dake hakan,ki gafar cemu ki sanar da mu wani abu daga cikin labarin ki ko zamuyi dace da samun iyayen mu.
Kallansa tayi hawaye na neman zubowa daga idanta

tace’ mekuke san sani a labarina?
share hawayen da ya zubo Mata tayi taci gaba”‘ labari babu irinshi a labaran duniya, babu kuma film din da yake kama da labarina bare kuma a samu yayi kama dashi,Jin labarina tamkar ruguza sauran farin cikina ne, ina rokon ku don Allah kar ku Kara cewa na baku labarina don Allah,
Takare da kuka sosai tare da hada hannayenta alamar ruko.
Mus’ab ne ya sunkuyo ya goge Mata hawayen fuskar Shi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button