A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Dagowa yayi ya kalleta ganin yarda har yanzu hawayene ke zubowa daga idanta ,goge Mata yayi hawayen yasaki hannunta shima ya goge fuskarshi, mas’ud ne
yace’ wannan kadan Kenan daga cikin takaicacan labarin mu,muna so musan ina iyayen mu suke,muna San sani,shin suna raye ? Ko sun mutu?bamu sani ba.
Kallanshi tayi da idanta da ya Riga da ya sauya,cikin wata irin murya da zai nuna tana cikn bacin Rai
tace’ wanne gari kuke kafin Daddy ya dauko ya kawuku Kano?
Numfasawa mus’ab yayi
yace’ Bama iya tuna sunan garin da muke Amma kuma a Katsina Shi ya dauke mu,
Taya kuka San ku twins ne,ta tambaya,
Bamu manta wannan ba a zuciyar mu,bamu manta sanda mahaifiyar mu ke cewa mu twins bane,bamu manta ba,
Mas’ud
yace’ shikadai zamu iya tunawa,harta sunan su har yau mun gagara tunawa.
Tashi tayi ta tsaya
tace’ ya sunan Daddy,
Adam Dan Lami,
daya daga cikin su ya fada,bata juyo ba kawai wucewa tayi,da ido suka bita har ta Shiga daki,
Ajiyar zuciya suka sauke a kusan tare,suna wurin suka ga fitowarta ta dawo hannunta rike da wata takarda,Zama tayi ta Mika masu takardar,sannan
tace’ ina su idan kunje ku nemin aiki a wannan company din,sannan kuma kuyi binciken sa, sosai.
Daga nan ta tashi ta tafi,kallan takardar da ta miko masu sukayi, address ne na company guda uku da sunan company din daya a Kano dayan Abuja dayan kuma a Lagos yake.
To yanzu ya zasuyi?
Basu da amsan tambayar dole suna bukatar lokaci.
Washegari kashe wayar ta tayi,sunyi Kiran Amma bata Shiga ba,kofarta ma a kulle don a dakinta suka zo sukayi knocking din duniya taki ta bude,bata son Kara saka su a idonta,a yarda take ji. A haka sukayi Mata sallama sannan suka tafi cike da kewarta.
✨✨✨✨
Bayan shekara biyu
Suna zaune a airport ita da sahr,suna hiran su,don ma sahr ce yawanci meyin hiran ita Ummusalma saidai ta daga Kai tace ehh ko a,ah, kuma hiran tasu ta bankwana ce Duka jiya da daddare basuyi bacci ba, sahr harda kukan ta ajiyan.
Suna nan aka fara Kiran su sahr,sai yanzu taji badadi, shikenan fah tafiya zasuyi, maybe Baza su sake haduwa ba,kawai hawaye taji ya zubowa, sahr juyowar da zatayi ta ganta tana kuka,tasan kukan rabuwa da juna ne,bata iya jurewa ba itakama da gudu ta dawo ta rungumeta, dakyar suka rabu,sahr ta tafi.
Lallashin kanta tayi sannan tayi shiru,ta Lula cikin tunani, acikin zuciyar ta take
cewa’ ko idannaje ina zani?komawa zanyi? Zasu karbeni? Ya zanyi?
Bracelet din hannunta ta kalla tace’ Neena mene mafita? Ajiyar zuciya ta ja sannan ta jingina da kujeran da take Kai tare da lumshe ido,tana neman mafita.
Hausar da taji anayi ne a gefenta da’alama kuma yanzu suka zo, bude ido tayi ta sauke su akan yarinyar da batafi 16-17 ba,sosai ta kallao yarinyar yarda take magana tana ta zuba surutu, maganar ta wayance Akan yara biyu ne take bada labari kuma tana ji tana cewa Yusuf da yaseer,sosai taji wata sabuwar kewarsu ta darsu a zuciyar ta,sosai take karajin labarin yarinyar don kawai sunan su yusseer shiyasa ta bada kaimi wurin jinsa,maida idonta tayi ta rufe tana Jin labarin yarinyar.
Yarinyar ce
tace’ kaga fa zanen da suka bani,wai yayar suce takeyinsa, waifa a yarda suka ce tsabar karya wai idan taga Abu komeye tana iya zanawa ko bata zana daidai ba tana iyawa,wai yaseer ma ya taba kwatan tama wani mutum kuma wai ta zana Shi,shine nace karya, shikenan mukayi fada,kuma ko yayar tasu fa Basu San Inda take ba sunce de ta taho London karatu bata dawo ba.
Kuma ko uncle idan muka zauna ba abinda ake min sai labarin yaya kaza yaya kaza,shine da zamuyi candy suka bani wannan zanen nasu suna San zanen wai itace tayi zanen,
Tunda ta fara zancen take jinta bata bude idanta ba sai da taji ance zane,kawai zuciyar ta ce ta bata su yusseer ne,juyowa tayi ta kuma kallan yarinyar dake kusa da ita hannunta ta tabida kallo,aikuwa de zanen su ne lokacin suna yara, a hankali ta Kai hannunta ta dau zanen,tana kallo, yarinyar ce ta juyo tana kallanta kawai, dagowa tayi suka hada ido da ita,kwalla ce taji ta cika Mata ido muryan ta na rawa
tace’ waya Baki wannan zanen ?
Yarinyar
tace’ laaa kema kina Jin Hausa ?
Sunana Ummusalma,
Kefa ta fada tana miko Mata hannu,Mika Mata hannun tayi
tace’ Ummusalma Muhammad,
Kice sunan mu daya ma Ashe Amma fa ni ummu ake cemin, friends Dina kuma guda biyu Yusuf da yaseer suna cemin yaya wani lokacin idan bamuyi fada ba, wannan zanen ma sune suka bani,
Kwalla ce ta zubo,ta share
tace’ can u tell me more about them ?
Ummu tace’ mezai Hana Nigeria zaki je?
Daga Mata Kai tayi tace’ sai nayi ta Baki labarinsu har sai kince ya isheki tukunna,
Tunda tayi maganan yake kallanta yarinyar da akace masa bata magana? To ko yanzu ta fara tunda Shi rabunshi da school din ya jima, maybe ma yanzun tafara,ahaka ya bar maganar,
Jiyayi ummu nacewa kinga uncle dina,sunan sa Abdullah Abdullah,tare zamu tafi grandma Dina kuma ba yanzu ba zasu tafi shiyasa mu zamu tafi am eager to see my mom,
tafada cikin zumudi,dan matsawa tayi kadan sannan ta hango Shi,if she’s not mistaken Kenan wannan yarinyar ce suka hadu da ita years ago,batayi maganaba kamar yarda shima beyi magana ba sai ma Danna wayarsa da yakeyi,
Tana rike da zanen suka Shiga jirgi wuri daya suka zauna,ita da ummu,
Ummu ta kalleta
tace’ Yusuf da yaseer sune best friends Dina kuma nima nice best friends dinsu,amma yanzu munyi fada kuma sunyi fushi da ni sosai,
Ummusalma ta kalleta
.tace’ meya hadaku?
Hmmm ai infada maki bansan abin zaiyi tsamari haka ba,karya tasu nayi Akan sun bani labarin yayarsu ta iya Zane sosai da sosai yaseer ma ya taba kwatan tamata mutumi kuma ta zana shikenan infada maki mukayi fada,daman lokacin munyi candy aka bani labarin kuma Zan taho London hutu, ranar da Zan taho naje gidan su,ko kallo na ma basuyi ba ,daga karshe ma Yusuf ne ya hankado ni daga parlourn su ya kulle,na Basu hakuri sunki hakura,suka sani a blacklist,tunda na taho nake kiransu Amma babu,wani lokacin fa idan mukayi fada suke fara nemana,gashi yanzu nayi hutun nagama saidai ni nakirasu Amma kullum user busy ake cemin. Yanzu kuma nasan kona koma tunda Basu Kirani ba shikenan baza su hakura ba, gashi nayi missing dinsu sosai,
Kallanta tayi
tace’ kina San su yafe miki?
Dasauri ta tace ehhh mana inaso sosai don bazan Kara karyata su ba wallahi,
Idan kinje kice yaya na gaida su, sannan kice masu yaya tace zata dawo very soon kuma ta karbi numbers dinsu zata kirasu sannan ki Basu wannan kice inji yaya photon tane Wanda sahr ta dage sai anyi Mata da graduation gown ajikinta,sai kuma Wanda babu harda Wanda suka je park suna Shan ice cream,kala kala wasu ita daya wasu kuma su biyu,Duka ta basu envelope din,
Karba tayi budewa tayi ta kalli hoton ta kalleta,
tace’ kecen yaya salama daman?
Daga Mata kai tayi
tace’ kiyi hakuri don Allah wallahi bansan ke bace,kinji?
Bakomai tace mata.
tace aikuwa zan fada masu, Amma ai Naga gidan zaki je,
Girgiza Mata Kai tayi
Tace’ karki fada masu mun taho tare dake,ki fada masu a London muka hadu,kinji?
To shikenan Insha Allah Zan fada masu, shikenan mun shirya,cigaba tayi tace suna sanki,Basu da labari sai naki,tun muna js1 aka kawosu makarantar mu,to Yan unguwar mune shikenan muka Saba dasu tare ake kaimu a dauko mu,wasu ma sun zaci ni yargidan suce, yaseer yanzu yaya yake cewa Yusuf shikuma yace masa kanina a haka suke,kuma sundena fada,wai kince masu sudena fada Basu dena ba saida kika tafi sunyi mugun missing dinki.
Jinta kawai takeyi daman tasan bazasu manta da ita ba
A haka ummu tayi ta bata labari daga nan har sukayi bacci suka tashi,idan sunyi bacci antashi sai a daura daga inda aka tsaya a haka har suka sauka lokacin dare yayi karfe 10pm,ba’azo daukan suba son haka zama sukayi a waiting suna cigaba da hira anan ta karbi numbers dinsu da address dinsu,daga nan aka zu daukan su har ya Shiga sai kuma ya fito