A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ kinga tashi ki dauko abinda zaki bukata a saka a ciki Bana San godiyar ki,
Kallanta tayi kawai,kuma har ranta take fada,tashi tayi ta dauko man shafa da turare da inner wears daman ita powder ba mutuniyar ta bace,bare kuma jam Baki,sai lipgloss ta zuba aciki, maman Sadiq ta dauko sabulu da klin dayawa ta zuba Mata su,ta zira handbag dinta Suma aciki daukan wasu kayan tayi
tace’ taje tasaka,sawa tayi ta fito zanin plane ne kuma bata iya daurawa ba,ita skirt ma baso take ba bare kuma wani zani,a haka ta fito ta tattare Shi Sama tana tafiya, lokacin maman Sadiq ta fito daga kitchen itama,sai datayi dariya mai isarta tukunna ta sarara ta koya Mata yarda ake yi, ita dai wannan kayan wahalar baso ba take ba.
Suna cin Abinci tace' ina San na sai gidan da su Amina suka tashi daga cikin sa,zaiyi nawa kike ganin?
Maman Sadiq ta kalleta tace’ idan Abban Sadiq ya dawo zansa ya tambaya maki duk abinda ake ciki zaki jini, daga Kai kurum tayi…..
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
12
Da sallama suka shigo parlourn, kana ganin su zaka San sunyi kuka, sabida idan su da beyi kama da normal ba,amsa sallaman mama tayi tana kallansu taji jikinta yayi sanyi,saboda ummu tana dawowa ta Basu labari kamar yarda suka bata, tabbas suna San wannan yayar tasu,shin ina zasu ganta? Samun kanta tayi dacewa Insha Allah za ma su ganta.
Katse Mata tunani sukayi ta hanyar gaidata,amsawa tayi,
tace’ kuje kuyi breakfast don Naga alama kamar bakuyi ba ko?
Yunwa suke ji bata kadan ba,Amma a halin da suke ciki yasa baza su iya cin abinci ba, Yusuf ne
yace’ a,ah mun koshi sai da muka ci muka fito ma,
Badan ta yarda ba sai don kada ta matsa masu,yasa ta barsu, Kiran ummu tayi,ta tashi ta Shiga ciki,
Tana Shiga ummu na fitowa ganinsu a haka kowa yayi shiru yasata karasowa
tace’ twins dina sannunku ko nace mako besties? A,ah ba besties ba yusseer kuke so??
Tafada tana kallansu,wata harara da Yusuf ya wurga Mata yasa ta fashewa da dariya,
tace’ remember Yaya salama tace ko nayi maku laifi Banda fushi,Banda kallan banza,bare kuma a samu harara ato,
Ta fada tana murguda Baki tare da Zama ta daura kafa daya kan daya,
Ba Wanda ya tanka Mata,don sun san halin kayansu,yanzu suna magana zata ce yaya tace kaz tace kaza,kullum sai ta Kara maganar ta.
Ganin sunyi shiru yasa
tace’ yanzu uncle zai fito sai ku gaisa ko. Daga nan sai muje garden mu tsara yarda za’ayi ko?
Numfasawa Yusuf yayi
yace’ mun samu numbern sa,mun kirashi yace yau bazai samu damar zuwa ba,baya garin,kuma sai jibi zai dawo,
Ya fada Yana kallanta,itama kallansa tayi
tace’ jibi kuma? Meye wani jibi,nifa kunsan bagane wannan abubuwa nake ba,kumin da yaren da zangane mana kwace mun wani jibi,
Ta karashe da daukar remote tana murguda Baki,
Yaseer da tunda yazo bayan gaisuwa bai Kara magana ba,
yace’ muma haka yace mana basani muka yi ba,ya fada Yana hararanta,
Tsabar ta rena masu hankali, idan sun fada Mata sai tace batasani sukuma sai su fada Mata,yaci ace idan karatune to ta hardace,
‘ tace jibin ce Baku sani ba?to kar kusani,
Tayi shiru sai kuma can
tace’ laaaa Monday ce ko? Ita jibin inke nufi?
Bawanda ya daga Kai ya kalleta tv ma suke kallo,suna cikin haka sai ga AA nan yazo zai wuce har yaje Baki kofa zai fita bawanda ya lura dashi sai ita,tana ganin zai fita kuwa ta tashi da gudunta
tace’ uncle Baku gaisa ba da besties din nawa ba,kuma zaka fita,
Sai anan suka lura dashi,basa ganin sa sai bayansa kawai suke gani,
Yace’ haba ummu bakya ganin sauri nake Zan fita, so nake naje na gaida mutane kinsan de Sarai gobe Zan koma ko?
Turo Baki tayi gaba tace’ nasani Amma ai gaisawa ce kawai zakuyi fa? Bata barshi yayi magana ba ta dinga Jan hannunsa,bata yarda janshi take,juyowa yayi kawai suna tafiya don yasan komin dare yadawo sai sun gaisa shiyasa kawai ya zabi su gaisa din yama huta da mitarta,
Tunda ya juyo ya fara tahowa suka kalli juna suka zuba masa ido, bako kiftawa har ya karaso gabansu ya Mika masu hannu Amma basu san ma Yana yi ba sai da, ummu ta tabosu tukunna, Yusuf ne yayi dan yaken da kana ganinsa zaka san iya fuska ne kawai,ya bashi hannu,
yace’ Yusuf,kawai iya cewa don maganar ma kakarewa tayi,
Murmushi yayi yace wannan duk ganin nawa yasa kuke kallo na haka? Kamar na maku kama da wani?
Ya fada Yana mikawa yaseer hannu,maimakon ya Mika masa sai ya zuro hannu a aljihunsa ya ciro hotonta da sauri ya bude ya dauko guda daya,shidai kallansa kawai yake kuma bai dauke hannun nasa ba ganin abinda ya dauko yasa Shi kallan hoton, yaseer kuwa tashi yayi ya Kara hoton a fuskar Shi,
yace’ haba ummu Yama zakiyi kice wannan basa kama,suna kama wallahi, kece Baki ga kamar ba, Yusuf mekagani,
Yusuf bai iya magana ba don Shi tashin ma yakasa yi,ummu ce ta matso,
tace’ laaa uncle kuma fah hakane kuna kama wallahi,
sai kawai tayi dariya, girgiza Kai AA yayi ya amsa hoton a hannun sa
yace’ muga da wacce nake kamar,
Kallanta yayi a fili ya furta student?
Kasantane? Ummu ta tambaya,ehh nasanta mana a school din da nake lecturing take karatu,bata magana yarinyar sai da na ganku a airport kuna yi ,ashe ta warke yanzu tana magana,
Amma fa ni banga kama ba anan,ya fada Yana kallansu,
Yusuf yace’daman Kai ai bazaka ga kama ba,Amma kuna kama fah.
Yaseer da har yanzu yake kallansa yace’ dole akwai alaka a tsakanin ku da ita,
Kallan yaran yayi yace’ Ba kune Kannan taba taya kuma zai Zama da alaka a tsakani na da yarinyar nan, ina da nawa iyayen da suka haifeni,itama kuma tana da nata iyayen tunda har tana da kannai.
Yusuf da ya tsani yaji an alakanta ta da ace iyayensu su suka haifeta,ya tashi cikin wani hargagi ,
yace’ IYAYE ??Wanne iyaye,? Wanne iyaye take dasu? Bata da wani iyaye. Wanne iyayen ne zasu nemi tura yarsu karatu batare da an Kara waiwayar taba? Wanne iyayenne zasu nemi halaka yarsu? Wacce uwa ce wannan da bazata bawa ‘yarta tarbiya ba? Wacce uwa ce da zata tura ‘yarta wani wuri tace tana so ‘yan uwanta su manta ta? Wacce uwa ce wannan? Idan ita ba ‘yarta bace Shi kuma uban fa? Ai Shi ‘yarsa ce ko? To Wanne irin ubane wannan da zai tura ‘yarsa karatu batareda yana tura Mata kudin da zata bukata ba? A yarda yake da wadata meyasa bazai je ya ganta koda sau daya bane ba a shekara? Wanne irin ubane da ‘yarsa zata tafi tayi wannan adadin shekaru batare da yaji daga gareta ba kuma hankalin shi bai tashi ba? Fada min sune zata Kira a matsayin iyayenta ??
Kawo yanzu kuka yaci karfinshi, dauriya kawai yake yi kar hawayen su zubo sai dai kuma bai San da cewar tunda ya fara ba yake zubar da hawayen ba, Saida ya Gama ya zauna,ya dafe kansa Jin yana Sara masa, yaseer ne ya dago dakan sa cikin wani irin low voice
yace’ da’ace nice ita da bazan kirasu da marikana ba,sun san basa santa meyasa suka reneta,sun san basa Santa meyasa Basu wurgar da ita ba,meyasa Basu kaita gidan marayu ba ta tashi acan,meyasa basu bada ita ba ga mai so? Sun manta cewa ‘da na kowa ne? Ka fada mana yakayi shiru uncle??
AA kuwa tunda suka fara maganar yake kallansu,sai yanzu yasan menene matsalar ta, rashin iyaye,
Zama yayi,
Yana kallan ummu yace itace wacce kika bawa Anty labari?
Daga masa Kai tayi,don itakam sun kulle Mata Kai,ai basuyi wannan maganar da ita ba,koda yake bakomai bane daman zasu fada Mata ba,kuma yanzu taji,.
Kallan Yusuf yayi yace’ naji bayan daga wurin ummu tana bawa Anty labari,kuma naji kunce zaku nemota can I join you guys ??
Basu Kai ga magana ba Anty ta fito don fadawa ummu taje tayi gyaran daki,Amma sai ta tarar Yusuf na fadan wannan maganar, kuma basu lura da ita ba,