A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ Idan ba damuwa Nima ina cikin wannan tawagar can I??
Tafada da guntun murmushin a fuskar ta,bawai tayi murmushin bane don kanta,kuma baikai zuci ba,can kasan zuciyar ta tausayin Ummusalma take tare da tausayin su kansu besties din,tasan halin da suka Shiga to itama zata Shiga ko bai Kai Rabin nasu ba, murmushin tayi don kawai ta kwantar masu da hankali.

Daga yaseer har Yusuf kallansu kawai suke Basu iya magana ba, ummu ce tayi magana dukda itama tana tausayawa besties dinta da wani irin murmushi a fuska ta

tace’ wooww my mom?,my uncle?
Kawai tayi dariya

tace’ daman mama kina son mu haka? Amma kullum sai kin mana fada Ashe kina sonmu,
Ta karasa tareda rungumo mamanta,
Uncle kawai murmurshi yayi don kullum idan aka masu fada sai tace ba’a San su, dukda labari yake ji,kuma wataran ana Mata fada a gabanshi.
Tashi yayi

yace’ni Bari na koma daki na kwanta don tafiya kam na fasata, Zan fadawa su umma.
Anty tace’ ai wani satin Suma zasu dawo, Basu fada maka ba?
Yana tafiya yace’ Basu fada min ba da sai dai naje kuma mudawo.
Itama bata Kara maganaba ta dawo ta zauna, kasancewar a three seater suke da space a tsakanin su,Zama tayi a tsakiyar su ta daura kansu a shoulder dinta tana shafawa

tace’ kudena damuwa Insha Allah komai zai wuce,kamar ba’ayi ba ,kowa da irin kaddaransa,kuma bazamu iya tsallake kaddaran mu ba,duk abinda kukaga yafaru da bawa an rubuta zai faru dashi ne tun kafin yazo duniya, bacin ga haka kaddara tana cikin rukunan Imani, kun tuna da haka?
Bata jira amsar suba taci gaba da cewa,walau me kyau ko marar kyau,idan kuka ga bawa Yana da kudi,kada kuyi tunanin Allah ya fifita Shine Akan wasu a,a Allah Yana jarabtar sane yaga taya zaiyi amfani da kudin? Ta hanya mai kyau ko akasin haka, idan kuma kuka ga Bawa Yana cikin talauci shima jarabtace,shin zai iya rike talaucin sa ko kuma zaiyi wani abun da zai sabawa Shari’a. Allah Yana jarabtar mu ta hanyoyi da dama, batare da munsani ba, Idan Allah ya jarabce mu da kowacce iri ce fatanmu mu mutu Mina masu dacewa .
Haka Allah yasa kuma Haka yaga dama , Allah yasan hakan Shi yafi alkhairi,Amma acikin 100% kalilan ake samun masu fada. Abinda nake so daku shine ku kwantar da hankali ku kunji ko? Bana San hankalin ku ya tashi,ina sanku tamkar ‘ya’yan da na Haifa a cikina, daku da ummu duk daya ne a wuri na, a haka ta cigaba da lallashinsu tun suna kan shouldern ta har suka zame suka kwanta a cinyarta,wata nutsuwa na Kara Shigar su tanayi tana shafa kansu har sukayi bacci. Hakan yasa ta kalli ummu Wace ta zauna a kasan kafarta ta daura kanta kan center table itama tayi baccin.
Ajiyar zuciya ta sauke ta jingina da kujeran ta rufe idanta, wata kwalla taji tana zubo Mata,aduk sanda ta tuna da wani babban al’amari,tasan duk Daren dadadewa dole Gaskiya zatayi halinta. Hannu tasa ta share hawayen,ganin lokacin na tafi yasa ta ajiye kansu a hannun kujeran, ta tashi ta Shiga kitchen don daura abinci.
Basu farka ba sai bayan Azahar, bayan sunyi sallah suka ci abinci,sosai suka ware kamar ba abinda yake damun su, sai da magariba sannan suka koma gidan su,suna Shiga suka ga Mama tana zaune tana kallo kuma tana waya, Zama sukayi Suma suka Dan fara kallan, Mama ta kallesu,

tace’ ya hakuri kuma?
Yusuf ne yace’ hakuri an gode Allah mama,
Yaseer kuwa kawai kallansa yake me yafaru kuma, Yusuf kuwa ganin irin kallan da yake masa na irin karka bada mu,beyi aune ba yaji yaseer nacewa” mama kin ga yarda yayi mutane kuwa, Kai mama Allah yasa muma muyi kyakykyawan karshe , daman fa Shi ba ruwansa, kuma Yana Karatun Qurani ya rasu, gashi ma kuma, maraya ne Akayi adoubting din shi iyayensa sukayi, amma haka suka rike Shi tamkar dansu, Koda suka haifa nasu, sun cigaba da sansa, Hmmmm ai ba’acewa komai mama,
Kallansa tayi tace’ Ya sunansa kuma,
Abdul sunan sa ai, munji mutuwar nan ta girgiza mu, mama, ni har na fara komawa ma ga Allah,yaseer yafada,

Yusuf yace’ kuma mama wallahi idan kinga yarda suke sansa ca zakice dansune,muma bamu saniba sai a wurin mutuwan nan mukeji,munyi mamaki sosai, Akan wani shikuma da ajimmu da rikonsa ake,
Ya kalli yaseer yace bata labari,
Yaseer kuwa

yace’ ai mama ko wallahi mutane suke Jin tsoron Allah,shikuma wai fa rikonshi fa ake don kawai babansa da mamanshi sun rasu, sai ya koma gidan kanin mahaifin Shi to matar gidan bata bashi tarbiya, ta batashi ga kashe kudi,tun muna js2 ya fara shan taba, yanzu kuwa tsabar abin yayi nisa har club yake zuwa abinsa,kuma ba kullum yake kwana ba a gidan, ai lamarin Shi gaba yakeyi, ga yanzu india zai tafi,hmmm Mama tsoron duniyar nan nakeji,
Yafada Yana dan share hawayen kamar gaske,
Mama kuwa tunda yaseer yafara take hada wata uwar zufa, taab ashe itama ta tafka kuskure fa a rayuwar ta, ita har mantawa ma takeyi da abinda ta aikata,koda yake bazata taba kiranshi kuskure ba, ba abinda ma ta aikata ai.
Kallan juna sukayi Yusuf

yace’ Mama lafiya kuwa?? Ko Baki da lafiya ne ?
Bata ji shiba ma itakam ai ta lula duniyar tunanin shin daidai ne abinda tayi ko ba daidai bane?
Suma tashi sukayi suka Shiga daki suna Shiga yaseer

yace’ wai ca kace wa mama mutuwa akayi ne?

Yace ‘ta shigo kana wanka tace me yafaru taga idona yayi ja haka kamar Wanda nayi kuka? Shine nace mata ai wani abokin mu ne ya rasu shine fah,abinda nace Mata,Kai kuma da tuni ka kwafsa mana dan ma dai ka iya tsara zance da Kai da waccen parrot din Bansan wa fi wani ba.
Yafada Yana hayewa kan gadan, tambilin yayi a gadan

yace’ Mama fa ta tsorata wallahi,
Kawai ya saki dariya,

Yace’ wai Kai yaseer sai yaushe zakayi hankali ne ? Baka da aiki sai dirifkiya a kan gado ko? Du kabi ka sawa mutane ciwon jiki,banza kawai,

Ikon Allah,wai Dan Allah dame ka fini ne,da shekara dayan?

Koma da second daya ne na fika de,kuma dole a kirani da yaya Yaseer a toh,

Kai Ka sani,mutum de bazai kirani yaro ba tunda shekaru na 16,16 kuwa ai ba wasa ba.

Dariya kawai Yusuf yayi ya tashi ya Shiga toilet.

????????????????????

Hajiya wannan itace mai aikin naki,kamar de yarda na fada maki ita din kurma ce,tana ji Amma bata iya mayarwa,
Kallanta Hajiya tayi ganin yarda take kalle kalle yasa ta daka Mata tsawa

tace’ ke kurma,
Dukda taji ta,Amma ko gezau batayi ba,kawai tana kallan girman parlourn da za’a ce kullum sai ta share tayi mopping,tunanin irin ciwon bayan da zatayi kawai take yi.

Kara daka Mata wata tsawan tayi sai a sannan ta jiwo ta kalleta,

Hajiya tace’ kinaji na ina maki magana,
Girgiza Kai tayi alamar a,ah,kallan iya ladi Hajiya tayi

tace’ bacin rashin magana harda na rashin ji ma,ni kuwa bazan dauka ba ki sanar da ita tam.

Itakuwa Ummusalma a zuciyar ta tace idan nayi maganinki zakisan Bana ji Bana magana ai.

Kuma yanaga fuskarta a murtuke bata fara’a ne ko kuma saban iskanci ne?
Iya ladi ce me bada hakuri,daga nan ta sallame ta, sannan tace ta kaita dakin ta,Wanda yake bayan jikin gidan amma kofar ta waje ce window dakin kuma daya a ciki zaka iya hango parlour dayan kuma a waje,garden zaka hango. Katifa ce kawai a dakin sai pillow ba bedsheet bare kuma a samu blanket sai wata munafikar wardrobe ta jikin bango siririya da ita, Allah sa Akwai toilet adakin, iya ladi ta kalla,

tace’ haka Zan zauna ba abin shimfida? Ba bargo?
Iya ladi tace’ Bari naje na tambayota, naji ko za’a samu.
Batajira amsar taba ta fita,tana nan tsaye kuwa saiga ta tadawo da bedsheet sai karamin bargo mai laushi, itakam a ganinta daga bedsheet din har bargon ba Wanda yamata,Karba kawai tayi a rashin babu,kudi ta kawo ta bawa iya ladi sosai tamata godiya ta fice.
Bayan ta Kara kallan dakin,babu K’ura a ciki da’alama ana gyarashi, Ghana most go dinta tasa acikin wardrobe din, daga kasa taga tsintsiya da Dustbin karami sai parker, toilet ta shiga shima ba laifi dukda ba bathtub Amma akwai ruwa, kuma akwai kayan wankewa.
Fitowa tayi ta Kara share dakin tsab sannan ta shimfida bedsheet din,ta zauna abakin katifar,tana Zama ana kiranta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button