A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Hajiya tace' sunanki salamatu ko?? Daga Kai tayi, taci gaba to aikinki a gidan nan shine gyaren Parlourn nan, Dana Sama,sai abin da ba'a Rasa ba,muna da mai girki da wanke wanke, sannan Bansan kazanta ko kadan kina ji ai?
Daga Mata Kai tayi alamar ehh,
To tashi ki Bani wuri, sum sum ta tashi ta koma daki, jakar kayanta ta dauko ta ajje lungun katifar,ta bude ta Ciro wayar ta, missed calls din maman Sadiq ta gani, kasancewar sunyi exchanging phone numbers,kiranta tayi bayan sun gaisa maman Sadiq
tace’ maganar gidan nan ne mai gidan yace dari takwas zai Saida,gidan kuma karami ne ,kuma dakunan a jere suke,kamar namu na da,
Ummusalma tace’ Shikenan bakomai,Zan turo maki kudin idan yaso sai a mayarshi Bungalow kamar naku Amma two Bedroom nake so,
Shikenan ba matsala,
Tace’ account numbern karki manta,
Daga nan sukayi sallama,
Kwanciya tayi Akan katifar tace’ tunda nake ban taba kwanan katifa ba sai yau,
Tasaba tajita a Sama tana juyi yanzu kuwa sai dai tajita a kasa idan batayi wasa Bama taji ta mirgono kasa, tana zaune har magariba sannan ta tashi tayi alwala tazo yin sallah ba abin sallah, fita tayi ta ga bakowa a parlourn tsaki taja ta dawo ta cire dankwalin ta tayi sallahn dashi, tana nan har Akayi Isha, Jin tafara Jin yunwa yasata tashi,tana nade dankwalin, ganin kamar mutum yana zaune a garden yasata lekawa,yana zaune ya lumshe idan sa ya daura kafa akan Akan table din da dayake na gossiping chairs din, tana kallan Shi kasancewar windown da yake facing kuma da haske sosai a wurin shiyasa ma bata kunna fitila ba, matsowa tayi jikin window tana kallansa, damuwace sosai a tattare dashi, kuma da’alama mafita yakeso ganin yanda yake karkada kafarsa da kuma bubbuga hannu sa da yakeyi, bata San iya adadin lokacin da ta dauka tana kallansa ba kamar yarda shima baisan adadin lokacin da ya dauka a wurin ba,sai da yabar wurin itama ta juyo ta ajje dankwalin kanta,ta fita don cin abinci, kitchen ta Shiga tunda daman sai tabi ta kitchen zata Shiga cikin parlourn warmers din ta bude taga sauran abincin kadan ne ya rage,don haka ta zauna taci ta koshi ta kora da lemu harda cake abinta, ta koma dakinta har zata kwanta tadawo ta rufe kofar ta bar key din a jiki, kayanta ta cire tasa yar rigarta ta kunna fanka,ta janyo wayar,tana dannawa taga time 11:45,ita a tunanin ta yanzu bai wuce 9 ba haka,tayi mamaki sosai, contact ta shiga taga numbern su Yusuf batasan ta Yusuf ba batasan ta yaseer ba duka yusseer tasa masu,sai ta ummu kuma,sai numbern su chatty da glip ta 9ja,da maman Sadiq,sukadai ne daman suka bayawa ba ,sai number sahr da wurin aikinta shikenan contact dinta, what’s app tayi downloading ta bude, badan komai ba sai don kawai ta ga su yusseer yasata budewa, aikuwa de tana shiga sunansu taga Dukan su online,
Batayi masu magana ba ta kashe tayi addu’ah sai bacci.
Washegari da wuri ta tashi ta shirya ta fara aikinta, tas tas share ko ina ba ha’inci ba komai ta gyara ko ina da ko ina har windows ta buge,tayi mopping sannan tasa turaren wuta ganin burner da tayi a parlourn sama,ta rufe ko ina ta Kara fesa air freshener, ta kunna na tsinke kuma,sosai gidan ya dau kamshi mai dadin gaske,ta kunna ac, sannan ta shiga dakinta,tana zuwa ta baje a kan katifa ta gaji over gabadaya jikinta ciwo yake abinda bata Saba ba sai dai tayi kadan, janyo wayar ta tayi ta duba time ganin Tara saura yasata Kara gyara kwanciya, sai bacci,
Sosai gyaran yayiwa Hajiya kyau a zuciyar ta, abinci aka kaimata ganin tana bacci yasa aka ajje mata, bata farka ba sai shadaya,ganin abinci an ajje a gefe yasata Shiga wanka,bayan ta dau sabulun ta.
Abincin ta bude bayan ta shirya, chips da kwai da bread sai shayi,shayin kam ya huce shiyasa kawai taci chips da kwai, ta kwashe ta kai kitchen.
Ahaka tayi wata a gidan bata fita ko nan da waje sai dai zubar da ruwan mopping amma bade ta zauna ba,daga daki sai parlour shima tana gamawa take komawa daki, Hajiya kuwa zagin da take Mata kuwa ba’a magana,har wani yar Rama tayi daman gashi ita ba kiba ba, kuma kullum cikin bambamta Kaya take bata taba sa complete Hajiya tayi mitar tayi masifar a banza beyi aiki ba ,kuma idan tasa zani saita tattarshi yadawo Sama kauri a waje, ba abinda ya dameta,wataran tana Shiga dakunan su Duka ta gyara sosai yanzu kuwa ta Saba ma da gyaran da masifar Hajiya bama Hajiya kadai ba duka yan gidan basu da mutunci ko kadan har abokiyar zamanta kuwa.
A zaman ta da Hajiya da kuma kishiyarta yarda suke abunsu babu kishi ko kadan na zahiri, ga kuma duk lokacin da suke zance suna ganinta zasuyi shiru,ranar da sukayi Baki taje kaima su lemo sunayin zance tana shigowa,sukayi shiru, bakin ne suka ce ita wannan bata sallama idan zata shigo wuri ne ko yaya? Hajiyar ce tace’ ai kurma ce bata magana,
Dayar bakuwar tace ai irinsh ake so a masu aiki,kinga ba Wanda zaiji sirrin ki,tana fita kuwa ta labe, taji abinda suke cewa,tundaga ranar take yawan Shiga dakin Hajiyar,itama Hajiya tadena wani boye boye ko ta ganta,sai wani yare da takeyi abinta, hankali kwance.
Yau aiki take Amma ba kamar kullum ba bayanta ke ciwo sosai,alamun period dinga na gab,babban tashin hankalin ta be wuce yarda bata da pad ba,kuma ita ba magana ba, kuma bata Jin akwai wani shago a kusa,dauriya kawai takeyi, yau ko turaren da take sawa ma bata saba,so kawai take taje ta kwanta,ko zata ji saukin abinda take ji, saukowa takeyi ahankali hannunta rike da bucket din da tayi mopping, sai da taje tsakiyar steps din ta rike bayanta da dayan hannunta dayan kuma tana rike da bucket din tana cikin tafiya sai ji tayi tayi tuntube da bucket rufe ido kawai tayi tana jinran taji zafin fadowar da zatayi,Amma Jin kamar an riketa kuma ga wani sanyayyen turare da take ji yasata bude ido fes ta sauke idan ta cikin nasa, dukda ba rokota yayi ba,tokareta yayi da hannunsa Duka biyu,
Kallanshi kawai take kamar yarda shima ita yake kallo, babban abinda yasa bata fita kenan bata so su hadu,dukda ita tana yawan ganinshi a garden , shikuma tunani yake me yakawota gidan su,mekuma takeyi? Dukda kallan da sukeyiwa juna hakan be Hana su wannan tunanin ba, yayinda zuciyar ta ta fara abnormal bugawa sakamakon wani yanayi da ta tsinci kanta aciki,shima hakanne a wurinsa, sun jima suna kallan juna yayin da idan ta kifta ido sai yaji an tafi da numfashin sau dubu, Baiki su dawwama a haka ba,
Hajiya ce fa fito don zuwa kitchen ta hado Breakfast ganin su ahaka yasata ta saki wani ihu tare da salati,
tace’ na Shiga uku ni Hafsatu mezan gani??
Banaifu Kaine rungume da mace haka a kirjinka, lahawwala wala quwwata, jama’a ku fito kuga abinda idona yake gane min,
Shikuwa bema San sanda ya rungumo ta din ba abinda yasani kawai yasa hannu ya tokareta kar ta fadi Amma yanzu sai ganinta yayi a Kan kirginsa, ganin da Hajiya tamasa baisa yasaketa ba,kuma be kalli hajiyan ba sabida wani irin haushi da yaji ,ta katse masa Jin dadin sa,ita kuwa Ummusalma kunyan duniya ce ta rufe ta,tunda tazo duniya wannan kadan ne zatace taji kunya,Amma bata wani nuna ba a fuska, expression din be nuna ba, sai motsi take alamar yasake ta,Amma ko gezau beyi ba sai ma Kara kallan ta yake yarda take motsi da baki,da kuma kifkifta ido sai abin ya bashi dariya, kawai yayi murmushi.
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
13
Ihun da tayi ne da kuma salati yasa kowa fitowa daga daki,suka fito Suma cirko cirko sukayi suna kallan ikon Allah,
Hajiya tace’ Alhaji nasha fada maka daman yaran nan ga abinda yakeyi,to har masu aiki ma be ragaw ba,bin matan ma shi har cikin gidan ma zai zo ya maka Shi,
Anty(kishiyarta) ta karbe da
cewa’ indai sune na Saba kamasu da wannan shegiyar ifrituwar kazama kurma kawai,
Wani irin tafasa zuciyar Daddy keyi,wai dansa? Shi mamaki yake,gashi kuma yau har cikin gidan sa, yana rungume da yarinya,kuma ganinsu besa yasake ta ba,
Cikin wata irin murya ta bacin rai Daddy
yace’ sai nace kasaketa zaka sake ta ne?
Murmushin dake Kan fuskar sa be bace ba,don maganar ma da sukayi zai iya cewa beji ba,sai da daddy yayi magana, ita kuwa taji komai,kuma tayi mamaki furucin Anty akanta, Ashe itama ta tsane ta haka?
Ahankali ya saketa Yana cigaba da kallanta,kamar jira take kuwa yana sakinta tana fara tafiya sai dai ko taku daya batayi ba,santsin ruwan da tayi tuntube da bucket din ya zube, ya debe ta zata fadi don saura kiris taje kasa yai sauri ya tarota wannan Karon har sai da ya tsugunna kadan,
Sakinta yayi ya gyara Mata tsayuwa,Tana Shirin tafiya Hajiya ta Kira