A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ ina kuma zakije,kurmar yar iska,shegiya munafika, kina kurma kina iskanci,.dawo nan bangama dake ba
Daddy yace’ ke tsaya zuciyar Shi kawai tafasa take,duk abinda ake fada masa Akan dansa yau ya Kara tabbatar wa dakansa hakanne.
Bema iya magana ba tsabar takaici kawai ya juya ya koma ciki,
Ummusalma kanta a kasa ta dawo ta tsugunna ,Anty

tace’ wannan yarinyar mekama da wancan Dan karuwar( Mus’ab) dole daman ai halinsu ya zo daya ai,
Dago Kai tayi ta kalleta sai kuma taji Aneesa na cewa ai itace babbar yar iska ba’a yar iska mace sai namiji, idan bakiyi wasaba wallahi zai Kai ya baro musha suna abin mu, yafada tana shigewa,
Tasan inda maganar su ta dosa,maimakon ma taji haushi,sai wani murmushi takaici da tayi,iya zuciyar ta,abinda yake damun Tama kadai ya isheta, Abu kadai ne ya bata haushi a zaginsu cewa glip( mus’ab) Dan karuwa, ahaka suka kare Mata zagin kare dangi,suka koma daki,itama tashi tayi, ahankali ta juyo don tafiya sai dai kuma ganinshi da tayi rike da moper Yana mopping wurin don har ya goge Kan step din Yana goge kasan parlourn abin ya bata mamaki,saukowa tayi ta nufi inda yake,ta Mika hannu don ta karba,maimakon ya bata Saima jeho Mata tambaya da yayi

yace’ me yasa kika Zama kurma? Bayan nasan ba haka bane?
Kallo daya tamasa ta dauke Kai,takara kawo hannunta zata amsa mopper ya kauda ita daga wurin,

Yace’ tambayanki nake, ko sai na Kara maimaita wa?
Gani kawai yayi tayi hanyar kitchen don tafiya dakinta, sororo ya tsaya Yana kallanta, har ta shige kitchen Sannan ya bi bayanta, Amma be ganta ba,ta fice ta Shiga dakinta, iska ya fesar tare da shapo kansa daya cika da suma. Kawai yabi ta kitchen din shima don komawa dakin Shi,
Tana Shiga ta ji wayanta Yana vibrating,maman Sadiq ce, Kara daurewa tayi ta dauka, suka gaisa sannan maman Sadiq

tace’ Wai sai yaushe zaki zo ne?

Tace’ Nima bansan ranar zuwa na ba?

To yanzu ya za’ayi da furnitures din gidan?

Nima bansan yaza’ayi ba kawai abinda yadace kiyi,Zan turo maki kudin,in yaso sai ki bayar a sayo,

Ba sai na bayar ba,daman zamuje siyan kayan kanwata dake jigawa kuma gobe zata zo sai muje tare da ita,a hada da nakin kawai,

To shikenan hakan ma yayi daidai, Amma yaushe ne tafiyar taki?

Maybe Nanda sati,kuma idan naje gaskiya Zan jima don na Dade banje gida don zanfi wata daya de,abubuwa dayawa banana duk anyi su.

Daga Mata Kai kawai tayi,sai kace Wanda ta tambaya, daga haka sukayi sallama ta takashe wayanta,
Jakarta ta duba ta dauko numbern mai adaidaita tasaka,ta Danna Kira,

Da sallama yadaga, tafada masa itace, sannan,

tace’ akan aikin Dana baka ne, ina so Ka Zama shiri koda yaushe,nanda kwana uku nake so a kammala komai, kaji ai?

Angama Hajiya yarda kika ce hakan za’ayi, amma Hajiya don Allah karki cutar dasu, kinga……

Cikin sauri da masifa ta katseshi tace’ sau nawa Zan fada maka, nace Zan cutar da sune? Bade na baka kudin ka ba? Kuma lokacin kana San kudin ai,Ka amsa yanzu nasan har anyi aikin da za’ayiwa mahaifiyar taka,
Hajiya kiyi hakuri ya kashe wayar,
Wayar tabi da kallo tana Jan tsaki, kudi ta dauko tayi rubutu a takarda ta zura hijab ta fita, tana bude kofar taji zata fita taji an wani irin fusgota, an jata zuwa can cikin garden,bayan bishiyar mangwaro, dukda ta tsorata bakadan ba da irin fizgar da aka Mata Amma bata nuna ba ko kadan, gaban tane yake faduwa bakan ba, Amma ko kadan hakan be nuna ba ajikinta bare kuma fuskar ta ba, ganin shine ma yasata Dan samun relief, Amma mamaki fuzgar da yamata take,me tayi masa, bata Gama tunanin ba taji

yace’ Wacece ke? Mekika zo kiyi gidan nan?

Kallan Shi kawai take tana karantar yanayinsa,har zuciyar shi yake maganar,kuma yarda yake maganar zakasan zuciyar Shi a tafashe take, ganin iri kallan da take masa yasashi,

cewa’ ohh nima pretending din zaki min??
Murmushin takaicin gefen Baki yayi, ya dafa hannun sa a gefen bishiyar ya matso daf da ita,

yace’ Wacece ke???
Shiru tamasa ba amsa, wani iri haushi ne ya Kara kamashi babu abinda yake bashi haushi irin kayiwa mutum magana kuma yana jinka yayi maka shiru,dukda shima Yana share mutane bai zaci hakan suke ji ba sai yau, cikin wata irin muryan bacin rai da kuma tsawa,

yace’ nace Wacece ke??

Dukda ta tsorata da tsawan da yayi Mata hakan be sa tsoro bayyana a tattare da ita ba, ganin zai Kara wata maganar yasata buge hannun sa da ya dafe bishaya dashi ta ture Shi daga gabanta,yayi baya kadan,Yana kallanta itama Shi take kallo,cikin muryan bacin rai itama tayi magana,

tace’ mutumin da besan Wanene shiba,shine yake tambayar wani wanene Shi. Kallanta yayi na irin kina da hankali kuwa?
Tayi folding hannayenta a kirjinta ta Jingina da bishiyar taci gaba da cewa’ ehh baka San wanene Kai ba,nasan koda an tambayeka wanene kai,zaka ce Kai Dane ga Adam Dan Lami na taso a Spain wurin Kanwar mahaifina, nayi karatuna tundaga kan primary har zuwa masters, duk shekara ina zuwa gida don yin hutun karshen shekara, ina yayu biyu Wanda muke sa’anni dasu biyu sai kannai shida, sannan zaka ce duk shekara idan na dawo gida babu me nuna min so da kauna hakan yasa Nima bana San su, Bama jituwa da su kokadan,daga nan kuma kace Ina da Kannan da nake so Mus’ab da Mas’ud,bazaka ce ba yan gida ku bane, sannan sai kace,watarana kwatsam Anty ummi ta rasu sanadin ciwon zuciyan da ba’a San dashiba, daga nan sai kace na koma na karasa masters dina sannan na dawo ban Kara komawa ba, koda nazo daman ina aiki da wani campany sai na nemi da na bude nawa,har na sai fili Amma Mahaifina ya siyar dashi daga karshe,baka damu ba,kacigaba da aikinka, daga nan kuma Ka koma Abuja saboda tsabar gaskiyar ka a wurin aiki yasa aka shirya maka makirci shugaban aikin ya koreka,daga nan baka Kara samun aiki ba, kana zaune a gida ko Ka fita don samuwa saboda bakasan zaman gida,idan kafita baka dawowa sai dare daga nan kuma bakasan me aka shirya maka ba, mahaifinka yace kar Ka Kara fita idan ba masallaci ba,baka iya musu ba Ka hakura, daga nan kuma zakace sai wata yarinyar yar Kanwar Hajiya sa’ar Saima ta saka a gaba da cewan tana sanka. Sai Ka fara aikin gida, Amma ko abincin ci baka samu,Kai kuma ba gwanin girki ba bare Ka girka, dukda Daddy yana da Arziki sosai don siyasa ta karbeshi Yana Shirin Zama takaran deputy governor.

Ta sauke ajiyar zuciya ta gyara tsayuwarta ta kalle Shi tace’ haka zaka ce ko ba haka ba??
Bata jira amsar Saba taci gaba dacewa”, Ka taba tambayar Wacece mahaifiyar Ka? Ka taba tambayar ina mahaifiyarka? Kasan inda mahaifiyarka take??? Ko kuma ka taba tunanin mahaifiyarka?? Ka taba tambayar dangin mahaifiyarka?? Ko ance ta rasu ai tana da Yan uwa,idan batasan Yan uwanta ba, haka ta taso ta ganta ai tana da Marika,idan marikanta sun rasu ai tana da Yan uwan Marika,idan Suma Basu da Yan uwa suna da abokai idan masu da abokai suna da makwabta. Wannan kuma kasan bazai taba yi wuwa ba ace babu ko daya daga ciki. Bama wannan ba Ka taba tunanin Mene yayi sanadiyar ciwon zuciyan Anty ummi?? Ka taba tunani? The answer is capital NO,u don’t know anything about your life,you don’t know everything about your life!. U have to start thinking, before you start asking, u have to do so.

Kallanshi tayi tace’ Idan ka samu cikakken wanene Kai inaga kana shirye ne da kasan Wacece Ummusalma Muhammad.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button