A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A Hannunshi ta soka papern tare da kudin tace’ Ka siyo min, ka ajje min ta window,
Ta juya ta tafi.
Tunda ta fara zancen Shi ya Zama statue bambancin Shi da statue Shi Yana ji, zai iya cewa ma numfashin sa daukewa yayi,kunnensa ne kawai yake aiki ganinsa ma besan sanda ya dawo ba,sai da ganinsa ya dawo numfashin sa ma ya samu fitarwa, sai kuma ya rufe ido ya bude,ya kuma rufewa ya bude, jirin da yaji yana neman debansa yasa Shi Jan kafa Yana tafiya dakyar yazo dakin Shi yana zuwa kuwa ya zube a gado ya kulle idan Shi duk abinda ya faru ya fara masa yawo akansa ahankali yafara bin komai daki daki har sanda ta sakala masa kudi a hannunsa, bude idansa yayi da ya koma ja, wannan shine tashin hankali na biyu da ya taba Shiga sanadin wani.
A hankali ya fara tunanin rayuwar sa sanda ya bude ido ya ganshi tare da Anty ummi tana kuladashi, tun Yana karami shekara shida ya fara zuwa hutu Nigeria Amma Anty ummi bata zuwa, sai dai Shi yazo tare da mijinta, ko a lokacin idan yazo Daddyn Shi ke masa wanka ya shiryashi Hajiya bata kulashi, ba abinda take masa sai zagi, da bakar magana,Yana komawa Spain kuwa ya tambayi Anty ummi dama ba ita ta haifeshi ba? Alokacin tace masa mahaifiyarsa ta rasu,da rasuwar mahaifiyarsa ya taso a ransa, Amma kuma be taba mata addu’ah ba betaba neman hotanta ha ,besan ya kamanin ta suke ba, be kuma taba tambayar Yan uwanta ba, To Meyasa???
Kulle Ido yayi ya bude,ya gyara kwanciyar sa, bashi da wata tambayar kuma,yasan da’ace Anty ummi na raye yasan tasan duk wannan tambayar idan ma bata San Duka ba to zatasan rabi da kwata. Besan sanda bacci ya dauke Shi ba a wurin. Be wani jima ba ya tashi saboda be Saba ba,Yana tashi yaga kudi da papern a wurin,har ya fara tambayar kansa na waye,sai kuma ya tuna, Kansa yaji ya Kara Sara masa tunawa da abinda ya faru dazu dazun nan,ajiyewa yayi yashiga toilet yayi wanka,ya Shirya cikin kananun Kaya sai sumar sa da ya taje Sam bayasan tara suma . Yana fita kuwa zaije a aske masa ita a masa gyaran fuska,amma yanzu bashi da wannan lokacin, har zai fita sai kuma ya dawo ganin kudin da ya ajiye akan mirror da zai Shiga wanka,dubu biyu ne sai kuma papern da ya ware ganin abinda ke jiki yasashi dafe Kai yasan zata bukata da gaggawa, da sauri ya fita, yaje wurin drivern gidan,yace ya bashi key, shagon kasan layinsu ya tsaya ya siya ya koma.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ummusalma kuwa data tafi har zata Shiga daki sai kuma ta fasa ta shigo parlour ta dauko bucket din da mopper ta fita dashi waje sannan ta Shiga daki ko hijabin jikinta bata cire ba ta fada Kan katifa ta kwanta rufda ciki,Jin dadin kwanciyar dataji yasata rufe Ido,batasan lokacin da bacci yadauke taba, koda yazo Rasa hanyar da zai bata yayi kawai ya zuge windown dakinta,”wato bata rufe window” abinda yace Kenan, ya saka mata,hangota yayi tana bacci akan katifar ta,da’alama kuma baccin ya Mata dadi, har zai jefa ledar sai kuma yayi tunanin kar ya sameta ya katse mata baccinta,dawowa yayi ta kofar ya bude yashiga ya ajiye mata ledar a kusa da ita daga ganin tana gumi yasa Shi kallan fankar dakin,a kashe take,hakan yasa da zai fita ya kunna mata ya fice, Sai dai kuma Daddy da Hajiya dake zaune a garden sun hango Shi tun lokacin da yazo Amma Shi be lura da suba hankalin shi yayi gaba.
????????????????????
Kimanin wata guda Kenan suna Kiran numbern Isiya driver Amma a kashe kuma gashi babu Wanda yasan gidan Shi bare ya kaisu,tun suna damuwa har suka zo suka saba, kullum suka Kira a kashe, bangaren Anty kuwa koda su Umma suka zo tas ta zayyane masu abinda ya faru, da kuma yarda zasu fara nemanta,sosai hankali su ya kwanta tawani bangaren, ahaka Suka bada goyon baya dari bisa dari, na ganin an nemota sai dai kuma rashin jin drivern yasa su yin jinkirtawa,amma babu Shi babu labarin sa, yau su yusseer suna gidan tun safe sun fara zuwa makaranta kuma dukan su course daya suke karanta mass comm, suna gidan su Ummu suna assignment kasancewar weekend ne lokacin, kowa da system agabansa Yana Mita musamman ummu da yaseer sun fi kowa mita shidai Yusuf sai dai kawai ya kallesu ya hararesu, Ummu ce
tace’ yaya Yusuf don Allah dan bani hint yanda zanyi nawa assignment din ta fada tana masa murmushi yanda wai zai bata,
Ko kallo ma bata isheshiba yaseer
yace’ indai yabaki nima sai yabani,ko kuma na kwafe naki na boye nakai nawa kinga ke sai dai ki samu katuwar CO kinsan beda mutunci malamin,yakarashe da dariya aikuwa kamar jira take yagama ta dauki pillown kujera ta maka masa,aikuwa shima ya dauka ya maka Mata daga nan kuwa aka suka tashi suka fara yar make make Kan kace me sun hargitsa parlourn sun ma ture center table din da center carpet wasu pillows din ma zip din ya bude duk sun zuzzube,
Yusuf ne ya kallesu ya cigaba da aikinsa, kwanan nan ya dena Shiga harkarsu, idan suna shirme ganin yake shi yanzu ya girma ya wuce wurin, daga karshe ma tashi yayi ya koma dining tare da kwashe masu system dinsu gudun kar su fasa suna hauka,
yaseer yace’wai bazaki dena ba? Naga ke kika fara kwada min kuma don na Rama?
Tace’ ai Kai kayi lefi,kace wai sai zanci co sai dai Kai,kaban hakuri Zan dena kuma kace min Anty ummu kiyi hakuri tukun Zan dena…
Ai bata rufe Baki ba taji ya kwade mata Baki da remote,bai Kai ga magana ba itama ta dauki remote ta kwade masa kai,ai kuwa Shima ya dauka ya jefa Mata sai Akan uncle da yake shigowa ita kuma ta sun kuya,daga Shi har ita kamewa sukayi, ga remote din ya bare saboda Yana faduwa a kasa
AA kuwa da ya shigo da sallama yanajin Abu ya bigeshi yasa Shi yin shiru ya dafe goshin sa, da zafi amma ba can sosai ba remote ne bawani Abu ba dazai ji masa ciwo sosai, takaici ma yasa Shi kin yin magana kawai ya wuce ciki,suna ganin ya wuce ta kalle Shi
tace’ kaga abinda ka ja ko?
Kinga abinda kika ja de,aike kika fara,zata Kara magana taji uncle yace’ your knees on the ground,
Kallan kallo sukayi,rabansu da kneel down sun manta, sai yanzu za’ace suyi wani kneel down,
” Sai na Kara maimaitawa ne?
Kafin ma ya rufe baki suka durkusa kowa Yana hararen kowa,irin ai kai ka ja, suna nan har karfe tara, daman dare ne,gashi Basu ci abinci ba, sun zaci idan akayi Isha shikenan amma ganin anyi Isha andawo yace’ su cigaba, Yaseer
yace’ yaya,
Shiru ba amsa,kuma cewa yayi ,yaya, uncle? Uncle?
Namma shiru ganin anyi shuru aN kyaleshi yasa Shi yin shiru, itama,
tace’ uncl, uncle, uncle,yaya?yaya?yaya de? Kaga fa dama shine yamin addu’ah wai sai na samu CO,shine fa kuma ya jefe ni da pillow daga nan kuma ya dauki remote ya wurgomin abaki dan nace ya bani hakuri, kuma shine fa da laifi.
Tana rufe Baki taji yace'” rest up your hands and close your eyes open your mouth,
Kallan juna sukayi cikin rada yaseer,
yace’ kece kadai zakiyi,ai ke kikayi magana kika ja wa kanki,
Batayi magana ba tayi yarda aka ce Mata,Anty da ta fito tagansu
tace’ tun kuna yara kuke bata min parlour yanzu ma kun girma baza ku barshi ba, wataran sai na sa dorina na Zane ku,bar ganin haka,tana me zama a kujera tana karewa parlournta kallo remote take nema don canza channel sai dai hango Shi da tayi a kasa wurin kofa kuma a bare yasata girgiza Kai kurum, taci gaba da kallan Indian ba wai don tana soba, Basu suka tashi ba sai goma kuma sai da suka gyara parlourn tas,har remote din sai da suka nade Shi da zare suka kulle wai sunyi gyara, yusuf kuwa yana zaune Yana dariyan sa kasa kasa Allah ya kaisu gobe zaiyi tsokana. Sai da suka ci abinci tukunna suka tafi gidan su…….
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
15
Hajiya itama tafiya tayi ta bar wurin, cike da farin ciki tunda tayi nasaran korar shegun can to wannan ma zata koreshi ne cikin sauki, tana tafe tana yar shewarta.
Da kallo tabita har ta shige ciki sannan ta dawo da kallanta Kan Binaif da yake kallan wani wurin sai dai ganinsa tayi ya tafi luuu zai fadi yasata yin saurin zuwa gareshi kafin ma taje ya zube ya jingina da jikin kujera, karasowa tayi ta tsugunna a gabansa, batasan meyasa itama bata tafi ba, ci tayi itama gabadaya hankalinta ya tashi, wannan shine karo na biyu da ta Shiga wani hali sakamakon cin zarafinsa da akayi,kodan tana ganin duka saboda ita ne hakan yake faruwa batasani ba, kallanshi take batare da tasan tanayin ba wani irin tausayinshi take ji tundaga cikin zuciyar ta har izuwa gabban jikinta, gabadaya wani irin tausayinshi take ji, tausayin da kanta kadai take ji a da, gashi yanzu tana Jin tausayin wani har cikin har ranta,
Jin dumi Yana sauka akan kafar Shi yasa Shi bude ido,ganinta da yayi a tsugunne a gabanshi tana kallansa tare da zubar da hawaye yasa shi kallan ta, Shi da’aka mara batare da yasan dalili ba baiyi kuka ba sai ita, dalilin kukan ne bai sani ba, kuka take tsakaninta da Allah,rigar dake gefen shi ya dauka ya fara goge mata hawayen yana girgiza Mata Kai, kokari yake ya danne abin amma abin yaci tura yakasa danne abinda da ya faru cigaba da goge mata hawayen yayi Yana kallanta yarda take kallanshi,ga wata sassanyar iska dake kadawa ,ji yayi duk wani abu da yakeji ya fara tafiya a hankali ahankali kuman yaji komai ya fice,sai wani nishadi dayaji ya fara shigar, ahankali kuma sai fara tuno moment dinsu na dazu kafin Abu nan ya faru samun kansa yayi da murmushi, ganin murmushi a fuskar Shi hawayen dake zuba a idanta ya dena zuba kawai ta tsaya sororo tana kallanshi irin kasan mekake kuwa?
Bedauke idan sa daga gare ta ba, cikin wata irin murya mai kama da ta rada,