A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????

  Washegari da yamma ta shirya ta fito kasancewar Yan gidan basa nan ta lura jiya da yau basu zauna a gida ba, kuma Basu dawo da wuriba,hakan yasa itama kulle dakinta ta fita,tana fitowa taga mai adaidaitar ta fada masa inda zai kaita tayi, tana masa kwantance har kofar gate din, cewa tayi ya jirata tana fitowa ta tura gate din,a bude kuwa yake, sai dai ganin mota da tayi a wurin yasata tunanin tabbas zuwa akayi shiyasa ma taji gate din a bude, zuwa tayi wani lungu ta makale tayiwa mai adaidaita message cewar ya jirata a bakin layin, sannan ta dauko wata Nokia key pad tayi message,ta mayarda ita cikin jakar ta,lallabawa tayi ta Shiga gidan,kallan gidan take tamkar batayi rayuwa acikin sa ba,wani irin tsanar gidan take ji Yana taso mata,dukda ba mutane Amma yana samun gyara akai akai, Jin motsin tafiya yasata saurin buya a dining wurin wani dan lungu ta makale, leko da kanta tayi taganshi yana saukowa, yakara kiba da fari,kana ganinsa zaka san Yana cikin daula da kwanciyar hankali sai dai kuma daga jiya zuwa yau ya zabge ya rame, kallansa takeyi tana tuna abubuwa da dama,Jin ya kusa saukowa yasata saurin Kara labewa har ya sauko ya fita,Yana fita kuwa ta tattare hijabinta da wani iri gudu ta haye sama dakinshi ta Shiga don taga dalilin zuwanshi gidan da suka tashi suka Bari batare da sun zuba yan haya ko sun saida gidan ba, dakin sa ta Shiga sai dai bakomai a dakin hakan yasa ta fito ta Shiga dayan,Yana nan yarda tasan Shi banbamcin kawai ansake  wardrobe ne, Shiga tayi ta bude taga wannan safe din zata bude Kenan taji Yana waya ashe be tafi ba, wani dokawa kirjinta yayi,cikin sauri ta shige bayan wardrobe din data ganin wani dan space, Allah ya taimake ta bata da kiba, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali,tare da numfashi, ji tayi Yana, 

cewa’ yanzu million ashirin fa zan Kai, akan yaran nan million ashirin fa,ba yarda za’ayi a kama Wanda yasace ne?
Bataji me ake cewa ba Amma tasan da Mama yake waya, jitayi yace’ kinga ni ina tsohun gidan mu duk abinda za’ayi saidai ayi don kira zanyi ayi hacking din wannan password din,Naga menene acikinta nagaji da zaman jira sai yaushe ne wannan lokacin da zaiyi million ashirin wasa ce ne akace maki?
Daga nan kuma bataji me yace ba alamar ya gama wayar, sai taji kuma Yana wata wayar daban Yana bude wardrobe din,da turanci yake, Yana fadar yarda safe din take da iya adadin letters din da take dauke dashi,sai taji kuma Yana cewa yanzu de sai Friday zaka iso Kenan? Daga haka kuma sukayi sallama,ya rufe wardrobe din ya fita Amma be rufe dakin ba,alama ce ta nuna zai dawo,tana Jin ya rufe kofar parlourn yasata ta fito, ganin kofar a bude a zuciyar ta sauke tana mamakin ashe bai san password din ba,to ya akayi ita tasani, bata da wani lokacin tunanin mai tsayi yasata kawai bude safe din da tasan itace ta takardun data gani waccan ranar idan bazata manta ba,aikuwa tana budewa taga itace, takardune aciki dayawa,gabadaya ta kwaso su a hannunta ta ajje a kasa ta rufe safe din da wardrobe sannan ta kwashe su ta koma ta buya,Yana zuwa shikuma kawai ya dau abinda ya zai dauka Wanda shima yanzu yake Dan ajjesu abubuwa aciki sannan ya kulle wardrobe din ya janyo kofar ta fita Allah yasota bai rufe dakin ba,sai ta tabbatar da ya fita daga gidan gaba daya sannan itama ta fito ta hada zufa sosai, dakin ta bude ta fito, sai dai kofar parlourn a rufe ta batadamu ba ta bude window ta fice ta sauka kasa shima ta window ta fita,sai da taje waje ne kuma ta Rasa da wacce kofar taza fita,Amma ganin kamar sakata ce kawai a kofar yasa ta budewa ta fita sai da tafi kuma tarasa yarda zatayi ta rufe,wayar ta lalubo ta Kira mai adaidaita shine yazo ya Shiga ya rufe sannan ya hauro katanga ya sauko, sannan ta sami wani relief,
Sauri kawai take taje taga menene acikin wannan uban takardun haka, har yanzu basu dawo ba,bakowa a gidan, direct garden ta nufa can ciki inda tasan ma masu gidan basa zuwa ta tafi da kujera, ta zauna ga wurin yama fi ko ina iska a garden din sobda yanayin bishiyon wurin ga sanyin ruwa,Zama tayi ta fito da takardun daga cikin hijibi,. Tunda ta shigo harabar gidan tana sauri yake ganinta, fitowa yayi don yaje yasameta ko yaji dadin abinda yake ji,kullum da tunanin yake kwana yake tashi tun ranar da ta sanar masa yake kasa bacci sai dai dayake bacci barawo shine yake sace Shi,ganin ta kadai yasashi jin nishadi ya manta da komai,hakan yasa Shi zuwa ya nemi shawararta kuma ya tambayeta,sai dai ganin inda ta dosa yasata shima bin bayanta, a Kan kujera ya ganta ta daura takardu akan Dan dandamalin nan na flowers mai tsayi, tana dubawa daya bayan daya, a hankali shima ya taho Yana dubawa Dan tunda daga nesa yake ganin kamar na company company haka, bata lura ba kuwa taga mutum yasa hannu ya dauki daya, Yana dubawa hannun kawai ta kalla tasan Mr lizard ne,kallo ya bita dashi kallan tuhuma, zaiyi magana amma baisan ma mezai ce ba,kuma wannan takardun original dinne na irin sun jima sosai sai dai kasancewar a ajiye suke yasa Basu ji jiki ba. Dakyar ya buda Baki,

yace’ meyasa???
Please don Allah ki sanar dani ko ke Wacece ko Zan zamu salama please, ummussalma,

Katseshi tayi tace is Ummusalma not ummussalma ,
Sannan tacigaba

tace’ suna nan Ummusalma mahmud …

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

14

Washegari Monday da wuri suka biya suka dauki ummu sannan suka fita,suna tafiya,

tace’ wani ba wanda zai koya min mota ne? Shikenan sai de na zuba ido kuna Jan mota nikuma ina kallo ko?

Yaseer yace’ to da me zakiyi? baki Kai matsayin koyan mota ba sai kin cika 18,

Tace’ ehhh Masha Allah imagine Kai Naga ka iya,kana 16 nikuma da nake 17 ban iya bako?

Yusuf dake driving yace’ yarinya mu ai koya mukayi da Karan bani,idan kema zaki koya Tou,Amma da sharadin ke kadai zaki Shiga ki ja,ko yakace?

Yaseer yace’ haka ne mana yaya, wazai Shiga tukin ganganci,

Yusuf cikin muryan ta idan tana magana

yace’ uncle, uncle, uncle, yaya? Yaya? Yaya de? Kaga fa shine daman,

Rankwashin data sakar masa ne yasashi cewa” ouch ke da zafi fah,

Tace’ daman ai nayi don kaji zafinne, mtsww
Ashe bakwa Sona daman?

Yaseer yace’laaa ni ina wannan saurayin naki dan level four, kuna waya dashi?

Tayi dariya tace’ ni mantawa ma nake dashi wallahi,bafa number ta na bayar ba, numbern Inna na bayar kasan kuma Inna ba turanci take jiba shikuma be iya Hausa ba,kaga shikenan anyi run da come,
Amma Baki da mutunci wallahi,

Yusuf yace’ wallahi kar ki bawa kowss numbern ki, taam nidai ba ruwana atoh,

Babu Wanda ya Kara magana har suka je suka je school din, parking sukayi inda suka saba,kamar kulluma yarda suke tafiya yauma hakan ce ummu a tsakiyar su,sukuma a gefen ta, Dukan idan Ka kallesu zaka ce bahaka suke ba,don a school basa magana ma da wasu,Basu da kawaye sai dai course mate, suna tafiya ummu ta matsa kusa da Yaseer,

tace’ kaga in-law dinmu,tana jiran mu,
Besamu yayi magana ba amma yayi Mata alamar ya gani,saboda sun karaso,Sarai Yusuf yajita Amma be ko tanka musu ba,idan da sabo ya Saba da wannan yarinyar da ta makale masa dukda bata ce tana sanshi ba Amma alamar hakanne da ita, shikuma sai wani basarwa yake,sabida kwata kwata baya san dizgi ita kuma akwaita da wannan,
Ummu ce tace’ Fati, yau ma kin rigamu zuwa Kenan, nikuwa Naga ranar da zamu rigaki zuwa,

Wacca aka Kira da fati tace’ aikuwa bazaku taba rigani zuwa ba,kufa komai kukeyi nikuwa yimin ake,tafada suna Shiga lecture theatre din. Sai da suka Shiga suka tuna cewan basuyi assignment ba, shikuwa yusuf Ko a jikinsa, Dan yayi nasa,kuma Yana sane yaki tuna masu,to Allah yasa su lecturer baizo b. Sai 2 suka gama, sun fito don tafiya fati,

tace’ idan Baku manta na tuna maku kunce zaku je gidanmu yau,kuma ummu ke kika fada,Dan haka tare zamu tafi,
Yusuf wani irin takaici da haushi suka darsu a zuciyar Shi, Sam bayasan wannan yarinyar amma ummu da Yaseer baza sudena kulata ba,mtswww yaja tsaki a zuciyar shi, badan bayasan karya alkawari ba da babu inda zashi shikam, suna tafiya har suka iso wurin motar tundaga nesa ya budeta suna zuwa kuwa yaga ta shiga gaba su kuma sun Shiga baya, wani murmushin yayi shima ya shiga, yana Shiga kuwa ya yatada motar, sai dai be tafi ba sai ma kifa kansa da yayi,ganin shiru shiru Basu tafi ba yasa Fati cewa Yaya lafiya kuwa?( Yarda suke cemasa a makaranta)
Girgiza Mata Kai yayi yace’ kaina ke ciwo kice yaseer yazo ya ja,
Yaseer yaji abinda yace kuma yasan bawani ciwon Kai, kafin ma tayi magana ya fito ya bude kofar ta

yace’ ki koma baya Zan ji dashi,
Bata yi musu ba ta koma baya kusa da ummu,itama umma da tasan kwannan zance batayi magana ba, suna Shiga kuwa yaja motar ya suka tafi,zoo road tace,bayan sunje kuwa ita ke nuna masa hanya har suka iso horn yayi aka bude masu gidan, parking yayi suka fito, parlour ta Shigar dasu,ta wuce kitchen ganin Ummusalma a kitchen din yasata cewa ke kurma yau ke kike abincin? Mai abincin? Bata nan ne?
Daga Mata Kai Ummusalma tayi alamar eh,
Tace’ to ki kaiwa Baki ruwa da abinci suna Parlour, ta juya ta fice, da wata irin uwar harara ta bi bayanta ta tace'” zaki ci uwarki ne,
Ta kofar baya ya shigo ganin ya kwankwasa dakinta bata nan yasashi zuwa kitchen ko zai ganta haka kawai yaji Yana san ganinta shiyasa ya fito takanas don ya ganta,
Kalmar karshen ne ya bashi dariya sai kawai yayai murmushi ya gyara tsayuwar Yana kallanta, yarda take zuba abubuwa a plate sai kace Wanda aka ce Mata mutane goma ne suka zo, ta fita don ta Kai,sai dai Jin muryan take kamar tasan masu muryan, sai dai murya daya zata iya cewa tasani dayan tajinta take kamar tasan irin ita, a haka de ta karasa parlourn sai dai bata je ga Shiga ciki ba ta hango ummu a sukwane ta juyo ta koma da kitchen da harda hadawa da gudu,tana Shiga ta sauke wata ajiyar zuciya Allah yasa Basu ganta ba,ajje kayan tayi, Yana nan be fita,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button