A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai ya shagala Yana kallanta, samun kanshi yayi da karasowa a hankali inda take,shima murmushin yakeyi a fuskar sa yau ganinta a haka ba karamin dadi ya jiba dukda yana da damuwa bakadan ba, amma farin cikin ta shine nashi, ita kuwa idan ta dago Kai ta kalle Shi kawai sai ta tuntsire da dariya, abinta.

Hajiya ce tazo nemansa Daddy na kiranshi, tagan Shi ba Riga ita kuma tana dariya, ai tuni ta koma taje ta Kai rahoto amma mutuniyar sai da aka Kara maggi a zancen,

Wani irin Kara kakeji ya karade garden ji kake tassss, tasss, tasss,tassss anwanke Shi da Mari kyawawa guda hudu, unexpected abu daman yafi shiga bare kuma wanan da bai masan da zuwan kowa ba bugu da Kari kuma Yana cikin wani yanayi na nishadi wannan abu ya sameshi,
Ummusalma kuwa kamewa tayi a wurin Baki bude ga dan guntun hawaye nan makale a idanta na dariya, tana zaune batasan sanda ta tashi ba,zata iya cewa wannan shine Karo na farko da aka taba marin babba a gabanta,
Wannan marin kuma yashige Shi dan kallan farko data masa tagane hakan,baya ga haka kuma ga wani irin tsantsan mamakin da ta hango cikin kwayar idanshi, alamun de yayi mamakin marin,ga kuma radadi da kunar zuciya tasan duk yanda akayi yana da zuciya, abinda taji Hajiya na cewa ne yasata Kara kamewa da tsimewa a wuri daya ko daga bacci aka tashe ta taji wannan zancen to tabbas karyatawa zatayi, bare kuma a gabanta ne tana kallan kwayar idanta kaf zancen babu zallan gaskiya bare kuma a samu kwaya daya cikin zancen yazamana gaskiya,

Tace’ Inaa Alhaji Sam bazan iya ba,wai kaga a yarda na gansu kuwa??
Sai ta saki kukan tana sharewa da hannunta tacigaba da cewa'” ai kawai maida yarinyar can zanyi,ya rigada ya bata musu yarinyar su,kawai maida ta zanyi bazan iya ba,daman ban fada maka bane shine ke bata min yaran aikin shiyasa nake dauko tsoffi,gabadaya yan aikina dashi da wancan yaran suke bata su, to su na samu sun fita kai ma kuma sai ka fita da Kai da waccan shegiyar tunda itama biye maka take,ta karashe cike da alhijini, Kai Kace da gaske take,Daddy kuwa wani irin wuta ce take fita daga zuciyar Shi tana sauka a kirjinshi,Yana San dansa sosai kuma bazai so ace ya cigaba da lalata yayan mutane ba don haka ya yanke shawara,batare da yayi magana ba ya wuce ya bar wurin.

Binaif baisan ma mezai yi ba,ashe de lokacin da Anty ummi ta rasu da yayi kuka ji yayi be samu gamsuwar abinda yake jiba,Ashe a wancan lokacin kuka Shine rahama, gashi yanzu kukan yake so yayi Amma ya kasa, bazai taba fassara abinda yake jiba, idan kuma yace ga abinda yake ji tou yayi karya .

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????

[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

 16 

Gefen takardun ya zauna sannan ya kalleta yace’ Mahmud or Muhammad,

Bata bashi amsa ba taci gaba,

tace’. Ummusalma Mahmud, na kasancewa yarinya mai farin jini,walwala,fara’a, surutu,tsiwa,masifa,duk wani kalan rashinji,to na dame kowa na shanye, bana Jin magana koda kuwa ta iyaye na ne, ina da shekara uku a ka haifi Sameera,sai dai tunda aka haifeta, duk wani Abu da zanyi a gida ba’a min magana a lokacin an sani a makaranta sai dai bana zuwa Islamiyya sai dai boko kawai, sai dai kuma bana san karatu kwatakwata wasa ya min yawa,ansha kawo karata daga makarata amma ko dan yatsa Abba baya daga min, bare kuma Mama, ahaka na taso a wani sangarce, ina da shekara shida aka haifi Yusuf tunda aka haifeshi kullum ina dakin,ina ganin yarda ake masa wanka, babu abinda nake so sama dashi,idan naga yana kuka to tsab zan masifen ce mai aiki ba ruwana daman Bana daga masu kafa,ahaka nake daukan sa tun ban iya ba har nazo na kwaya, makaranta kuwa daman sai naga dama, kuma Mama bata taba damuwa ba, ina da shekara bakwai ita kuma Sameera shekara hudu aka haifi yaseer sai yazamana bani da wani lokacin sai nasu,idan na dawo daga makarata ina tare da su a haka suka fara wayo tun ina karama nake masu wanka tun ina sa masu kumfa a ido a min magana na daina, amma da naci sai da na koya masu wanka, sai ya zamana da suka fara baki ni nake koya masu wakokin makaranta #children rhythms, babu abinda na tsana Sama da karatu sana San karatu,Amma saboda su ne yasa na dan fara maida hankali sai naga ashe duk abinda Akayi ma ina iyawa,daga nan kuma sai na dena maida hankalin,a haka na taso ga wani uban kudi da ake bani ina kashewa koda kuwa ban da bukata, ra’ayimmu ya sha bambam da Sameera we are parallel da ita, idan ni nayi gabas to ita tayi yamma, Sameera tana da mutunta mutane,bata da wulakanci gata da San karatu,duk kankantar laifi idan tayi za’ayi mata fada, sabanin ni da ba’amin fada ko me nayi. A haka na taso cikin so da kauna, har na zo js3, lokacin school dimmu boys and girls ce, ina da friends Maza da Mata banda mu ba,kowa ma ni nawa ne,ina da harka da kowa bana ware kowa, ga kuma uban kudin da ake bani ina kashewa hakan yasa ake min taken big girl, indai a school din kake to tabbas kasan big girl idan ma baka san ta ba to kana Jin labarinta. Ina js2 na matsa aka koya min mota, Abba beyi musu ba yasa driverna yake koya min har na kware, tsayi na baya kaiwa naga gaban mota to sai nayi ciko,ahaka na koya lokacin da na shigo js3 na kware abuna, duk weekend ko Thursday and Friday ina dibar su Yusuf mu tafi yawo,

Wata Rana za’ayi birthday din Dan class dimmu, kasancewar mazan class dimmu akwai sha’ani ba laifi, dukda cewan duk wani birthday idan za’ayi to a class ake yinsa, Amma shi sai yace ai baban sa ya yarda yayi a club, ni nafara cewa zanje, ganin ba Wanda yayi magana sai ni yasa nace” ya haka ku baza kuje bane?
Abinda sukace shine”‘ a gida za’a mana fada,
Nikuma nace” Naga sai da yamma basai muje har gidan naku ba kowa mu gayya to Shi ba?
Basu ce komai ba sukayi shiru,ana tashi daga school kuwa bayan na dauko su yusseer kasancewar haka nake ce masu banma Shiga da su gida ba,na fada bin gidajen kowannan mu ina fada,ba laifi kuwa duk an barsu.
Da yamma wasu suka biyo min muka tafi club,shine Karo na farko da na taba zuwa club wani wuri aka ware musamman saboda taron birthday dinshi, tun 5pm aka fara ba’a gama ba sai 12:30am a hakan ma bawai angama bane kawai gajiya nayi nace Zan tafi, tare da su sauran friends dimmu muka fito sosai munga abubuwa abinda bamu taba gani ba koda kuwa a film ne, bamu Kara tsinkewa da lamarin ba sai da muka fito waje ganin dahu yayi sosai kuma lokaci ya ja sosai muka tsorata idan anje gida me za’ayi mana ga goben zamu fara zana jarabawar mu ta BECE ni ce kadai kowa gida ban koma gida ba sai 2:30am, dukda na tsorata Amma na kasance mutum wacce bata nuna emotion dinta, a haka na Shiga gida,ina Shiga naga Abba da Mama a tunanina zasu min fada ko duka ma kamar yarda nake ji za’a zane wasu daga cikin mu daga bakin su, Mama

tace’ Ah ah salama sai yanzu? Ya birthday din?

Abba kuma yace’ ya kika tsaya gobe ma ki dawo duk lokacin da kike so, soyayyar mu a gareki ita ce komai kiyi duk abinda kike so koda kuwa zaki kwana ne bai dame mu ba kinji?

Wani dadi naji kasan ance kuruciya dangin hauka, jinayi duk duniya babu masu sona sama da iyaye na, da gudu na zo na rungume su nace” nagode Abba na,
Yace’ ai bakomai salama komai munayi ne saboda ke farin cikin ki shine namu farin cikin, ina kaunarki yata,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button