A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari danaje school friends dimmu wayanci an Zane su, musamman mata kowa yana fadar abinda aka masa suna cewa bazasu kara ba har abada,ganin irin kukan da suke sha da danasani yasa ni jan bakina nayi shiru bance uffan ba koda suka tambaye nace ni ba amun komai ba,daya daga cikin kawayen na tace' gaskiya iyayenki basa sanki,kikai wannan lokacin a waje kuma ko fada ba'a Miki ba? Anya su suka haifeki ? 

Sosai mukayi fada da ita kaca kaca akan furucinta akan iyayena gani nake duk duniya babu wacce iyayenta suke so sama dani, dakyar aka raba mu da ita,
Tundaga ranar duk wani birthday da za’ayi ko a’ina ina zuwa bakuma na dawowa sai sanda naga dama,sai dai idan naje bana shan ko lemu ko cake din bana ci kawai rawa nake zuwa yi abuna.

Abba Yana da company,idan na zauna nida shi na riga cewa kenan idan nagama makaranta zai bani company daya Nima nake aiki aciki,burina Kenan kawai na zauna a kujera nake juyawa,abinda nake so kenan tun ina karama, a lokacin yakan bani labarin wani abokinsa mai suna Muhammad dashi da Mama suna yawan bani labarin mutumin nan shine ya cucesu ya sace masu yar su sannan ya kashe masu ‘ya’yan su,kafin ni sun haifi ‘ya’ya uku amma duk Shi ke kashe su, tun daga nan naji na tsane shi, idan muka zauna basu da labarin da ya wuce nashi da irin muguntar da yayiwa Abba, koda na tambaye Shi nace yanzu yana ina ca

yace’ Yana Abuja, gidan sa ne ya kama da wuta,
Ban wani tambaya ba sosai,a lokacin na tsani ma Jin labarin,na tsana yaudara da cin amana,karya gabadaya na tsane su.
Ahaka na cigaba da zuwa makaranta ta da islamiyyan da ake min a gida dukda malamin yana hakuri dani idan yazo tun four to sai five ko six zan fito ina fitowa zance aya daya zai Kara min, lokacin banfi hizbi biyu ba da aya daya daya din da yake karamin, dukda malami na ne amma madam yake cemin bama shikadai ba kaf masu aikin gidan nan madam suke cemin idan kuwa basu fada ba to kayiwa aikinka korarka zanyi ba ruwana,ina da tausayi amma kuma Mama takance ba’ajin tausayin talaka,talaka bashi da mutunci,idan kayi masa rana to Shi dare zaiyi maka, sai ta kawo min misalin Wannan mutum mai suna Muhammad shima talakane, ya cuci Abba,da haka tayi tasiri akaina, na dena Jin tausayin wasu, amma ba duka ba idan na fita indai naga kana neman taimako to Zan baka shi.
Akwai watarana nakai yusseer park lokacin ina ss2 munje da su,suna fada da wani yaro suka tarar mai suka masa dukan tsiya sannan suka ji mai ciwo a gefen idan sa, ashe yaran dan dpo ne aikuwa babansa yazo yana zuwa kuwa yace sune suka ji masa dan zuwana kenan daga siyo ice cream bansan me yafaru ba kawai gani nayi za’a tafi da su yusseer aikuwa nace nice, aikuwa aka tafi damu har su,aka rufe ni aka Kira Abba sai ca yace’ baya gari,Mama aka kirata itama tace’ bata gari tare suka tafi da Abba kuma zasuyi sati ne a can,sai suka ce a mayar da su yusseer gida ni kuma a barni a cell, sai da nayi sati biyu a cell sannan Abba yazo yayi bailing dina, yana ta ban hakuri,ko kallansa banyi ba, sai da ya fada min uzurin sa sosai sannan na yarda na hakura.Tun ina ss1 aka dawo dani makarantar nata kawai ni nace inaso saboda frienda dina wasu sun dawo ta, zamushiga ss3 aka min repeating Amma bandamu ba na bisu na cigaba da karatuna tare su har akayi hutun Frist term………..

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

17

Washegarin da akayi hutu shine ranar birthday na, mun fito don na kai su yusseer islamiyya,daga can na wuce nayi siyyayar abinda babu, naga Yayar Mama ko kallanta banyi ba saboda nuna min kiyayyar da takeyi karara, dukda bana haduwa da ita sai dai ta waya kawai, ko da muka fito sun manta abincin su, sai nace Bari naje na dauko masu sai na bita kitchen harda hadawa da gudu don kar su makara, ina shiga sai naga ba abincin a kitchen na fito don naje dining sai dai Jin an ambaci sunana yasani komawa da baya don naji me ake cewa, Yayar Mama ce,

tace’ Wai ni saratu wannan yarinyar ya batun ta ne?

Wacce yarinyar Kennan?

Ummusalma mana nake nufi,

Awww Yaya Kenan ai mungama da shafin yarinyar nan, saboda kwata kwata mun lalata mata tarbiyar ta, mun cusa mata kiyayyar Mahaifin ta don tun bata Kai haka ba muka cusa Mata kiyayyar Shi, in takaice maki yanzu kusan kullum sai ta fita birthday a club bata dawowa kuma sai kusan asuba, kinga kuwa babu wanda zai dora idan sa akan wannan budurwa ya barta indai a club ne.

Yayar Mama tace’ bangane ba taya kuka cusa mata Kiyayyar mahaifin ta meyasa kukayi haka?

Mama tace’ hmmm yaya kenan, ai fada mata mukeyi irin cin amanar da mahaifin ta yayi wa Alhaji,ita fa a tunanin ta mu muka haifeta,alhali kuwa ko renonta banyi ba, idan wannan yarinyar ta kwanta acinyata ji nake kamar wani gagarumin karfen da aka sa shi a wuta haka nake ji,kawai zuciya ta nake dannewa don mu cimma burinmmu,

Yayar mama tace’ yana ina ne shi mahaifinnata ko nace makiyin ta don kun gama komai, cusa kiyayyar d’a da mahaifi ba karamin Abu bane.

Wama yasani ne, ‘ya’yan sa de kinsan ke kika fara wurgar da daya,kuma irin wulgawar da kika masa nasan ya rasa ransa, sai twins din da suka haifa sukuma nace a sace su daga makaranta a yi nesa dasu sannan aka masu kurciya, ashe ma Alhaji yasa a kashe su, ita kuma wannan sai mukaji tausayin ta akalla ma bar masu da daya ai, lokacin ma ai shekarar ta biyu sai muka dauke ta muka cinnawa gidan wuta daman already mun kwashe all important thing din, daga nan kuma sai muka dawo Kano, kinji fa yarda akayi, ai ke lokacin bakya nan kawai wutgar da waccan yaron da kika yi washegari kika tafi Cyprus shiyasa kuma ban fada maki ba,kuma bama samun lokaci sai yau.

Hehehe wallahi kun mun daidai, Nima haka nake gallazawa yayan mijina Amma yanzu ai basa nan yan uwansu sun kwashe su,kuma ko waiwayar su bayayi, hahahaha maganin dan banza, Amma fa naso Muhammadu Amma Allah beyi ba,

Ai da kin aure shi ma dayanzu komai ya dawo hannun mu,

Daban aure shi bama yanzu gashi komai ya dawo hannun ku,riba biyu Kenan,kun tarwatse tarbiyar yarsa kun hanata karatu, kuma kun kwace mata dukiya,

Mama tace’ Yaya Kenan ni ba wanan ba so,yanzu tana ss3 kuma burinta be wuce a bata company daya ba, idan ta gama karatu kuma kinsan ko result dinta beyi kyau ba, dole a bata, ina gudun kar taje ta gano wani abu da zai sa ta fara thinking otherwise,

Hmmmm wannan ai Abu mai sauki ne,kawai ku turata karatu kasar waje,kar ku waiwayeta daga nan kuma kunga shikenan kinga su a can karuwanci ba komai bane ba,idan taji bata da kudi dole ta fada wannan harka ai, don ta biyamawa kanta bukatar rayuwa daman kinga already ta Riga da ta lalace kinga shikenan, ko ya kika ce,

Yaya Kenan wannan shawara taki tayi daidai wallahi,haka za’ayi ma,Amma Zan bari ba yanzu ba sai tana gab da gamawa zanyiwa Alhaji maganar,

Kuma fa infada maki ko dangi bata sani ba,shima iyayensa Alhaji yaje ya hada masu tuggun sun hau sun yarda,bare ma kuma mun cinnawa gidan wuta,

Kai Kai wannan abu ya min dadi wato har iyayensu ma baku kyale ba Kai jama’a wai wai ai hakan yayi kyau wallahi,

Daga nan suka dauko maganar su kuma ta wani abun,

  Yanda na koma da baya ban San lokacin da na sulale ba a bayan kujeran dake kusan da kitchen,kukan ma nemansa nayi na rasa tunani ma kasawa nayi, Jin suna neman tashi don su daura abinci yasani rarrafawa na bi ta kitchen naje ni garden Bansan ma menake yiba,abinda nasani karshe shine zuwan su yusseer daga nan kuma bansan ma me yake faruwa ba sai gani na nayi a gadan asibiti, duk yarda akayi dani na fadi meke damuna kin fada nayi dan ko kallo basu isheni ba,tun daga wannan rana na sauya, na dauko damuwar duniya na daurawa kaina,kulluma muna kan hanyar zuwa asibiti har hawan jini ya kamani harta Kai ta kawo ko mikewa nayi don na tashi sai dai na fadi,yawan faduwar da nakeyi akace wataran stroke zai kamani,hakan yasan na dan rage damuwa sai dai tunanin yarda zanyi na gyara rayuwa ta danake dakuma samun mafita, a haka na sawa kaina salama sai dai bana fita ko ina daga daki sai daki abinci ma dena ci nayi nadawo cin snacks bansan me za'a samin a ciki ba watarana kuma, gashi ni ko gas ban iya kunnawa ba bare kuma ace na Shiga na dafa, ina zaune kamar ko yaushe a daki ina tunani aka zo aka sanar dani malamina yazo, kamar bazan jeba sai kuma na tuna illar da akamin har yanzu na kasa hada uzu biyu cikakke hizbi hudu Kenan, tashi nayi nasa Hijabi na fita, daman da Qur'anin shi yake kara min shi yake zuwa da komai yamin yakara gaba,Amma yau da naje nace yafara min ta Sama kuma shafi zai Kara min, tundaga nan yafara kara min kuma hadda daga nan kuma sai Karatun namu ya bunkasa muke sauran darasat din da yakamata ace mutum ya iya a matsayin sa na musulmi,daga haka Karatun addini na yayi nisa sai ya zamana nasan duk wani  hukunce hukunce na karatun Qurani wanda a da ba ko daya daga ciki dana sani, 

Bama shi kadai ba dayake nasa Karatun a raina sai nake yinsa sosai da sosai hakan sai ya rage min nauyin abinda nakeji, ana haka kuma muka koma makaranta ranar da naje zan shiga ss3 na tuna ashe fa an min repeating haka kuwa akayi na juya na koma ss2 second seat na zauna daga ca wurin bango na samu na zauna wasu sun sanni wasu kuma basu sanni ba, ahaka Yan class dimmu suka ji lbr sukayi ta zuwa suna korafi dukda shirmen da mukeyi su suna karatu kuma suna san karatu nice de bana so,
Sosai sukayi min fadan su na kawaye nidai jinsu kawai nayi batare da nayi magana ba sukayi suka gaji,wata seatmate dina mai suna Amina tazo bata iya yin shiru da bakinta ba nikuma a lokacin so nake nayi tunanin rayuwa ta ta baya ganin friends dina yasani tuno min abubuwa da daman musamman Aliya wacce ta fara cewa anya kuwa iyaye na ne? Wannan Abu na tuno shi kuma tabbas dukwani uba da uwa na gari baza su taba barin yarsu take kaiwa lokacin da na kai ba, Amina ce ta takura min da na fada Mata sunana dakyar na fada Mata daga nan kuma ta ringa bani labarin Inni da Baffa suka dai kawai nasani a gidan su, shigowar Neena wato Amina yasani idan naje school bani da abokin hira sai ita dukda ita kadai take hiran ta idan ba malami a class dimmu, ita take Bani labarin duniya da dama kuma ba laifi ina dauka, a wurin ta naji idan mace bata iya aikin gida ba da girki tsabta to miji sakinta yake, bansan naji ana maganar saki a rayuwa ta,idan naji an saki mace wani irin turirin bakin ciki nake ji tunani ma nake to da me macen ma zatayi da har za’a sake ta, Ashe dai wasu basa da tsabta ne,ranar da ta fada min da akazo dauka na na wuce inda ake koyan abinci, amma daga 2pm zuwa 6pm saboda ina zuwa school, dukda dai idan an tashi sai kowa ya tafi sannan nake tafiya, ahaka na fara zuwa ina koya na sha wahala sosai na kone ba adadi,Amma a haka nake daurewa nakeyi kawai inayi ne don na cimma burina, ranar weekend kuwa cewa nayi zanyi wankin kaya na tunda take ban taba wanki ba komai nawa wanke min ake, basha wahala bakadan hannuna yayi ciwo koda na wanke kayan ma be fita ba,Amma haka na shanyasu na dawo daki shima na hau gyarawa,sai da nayi nafi sati jiki na na ciwo ga kuma koyan abinci ga Karatun both islamiyya dana boko cikin lokacin kan-kani na iya Abubuwa da daman watana shida ina koyan abinci kuma ba laifi na iya,don koda zamu fita dukda duk sati sai munyi competition,nice nazo first kuma naji dadi, snacks drinks ba Wanda ban iya ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button