A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bangaren su yusseer suma sun damu kwarai da halin da na shiga,tun suna damuwa Suma har suka dena damuwa, sai dai rashin magana nane yafi damunsu, amma basu taba nunawa ba, haka zasu zo suyi ta min hira bana tankawa a wurinsu kuma tunda inaji haka ya masu dadi, a hankali ahankali nafara rubuta rayuwata Yusuf yafi yaseer wayo bakadan ba sannan Yusuf yana da zuciya,tun ina rubutawa a cikin diary yusuf yake son Karantawa Amma na hanashj badan yaso ba ya hakura.
Bakin cikin danan shiga na biyu shine tafiyar Neena, Neena bata taba fada min su talakawa bane,nasan basu da wadata amma banda talaucin su ya kaisu da zama a gidan haya ba sai da ta tafi,bansan ciwon dake damun mahaifiyar ta ba,ban taba tambaya ba, Zan iya cewa Neena ce mutum na farko da bata gajiya dani,harta friends dina ko mun hadu ko kallo na basayi hakan ba karamin dadi yake min ba, sai dai suna shakka ta kasancewar sun san wacece ni a da. Neena ta zauna dani,Neena ta kaunace ni,,Neena tayi hakuri dani,Neena na Sona,nima kuma ina kaunarta ji nake ita na fara sani duk duniya idan ina tare da ita jinake kamar ina tare da yar uwata ne,wani lokacin munayin fada da ita duk da bana kulata amma wani sa’in idan tayi maganar tayi maganar ban daga mata kai ba to daga nan zata fara min mita da surutun ni bana magana ni kaza ni kaza, a lokacin nima haushi nake ji sai na dauke Kai bana kuma daga bata kai, idan na bata abu kuma bazata taba cewa nagode ba kulluma a ” ban gode ba kuma bazan taba godewa ba” wannan itace maganar Neena hakan ba yana nufin gobe ma bazan kara mata ba,ina san suk abinda Neena ke so, a lokacin da tasan ina zane burinta daya shine na zana mata nida ita,batasan watarana ba ko zamu rabu,Niyya ta idan za’a turani karatu mu tafi da ita sai dai kashh Neena ta tafi ta barni, tafiyar da bansan ina Zan sameta ba.
Ana gobe za ta tafi na hadu da wani mutumin, mutumin da banaji Zan iya manta shi, mutumin da ya fara yi min godiya, mutumin da ya fara samin albarka, mutumin da naji zuciya ta tayi sanyi, zuciya ta tasamu nutsuwa mutumin da yake da annuri acikin fuskarsa, bazan taba mantawa dashi ba,
Tafiya ta London ita ta zanja min komai mutum na biyu bayan Neena itace Sahr, Sahr ta taimake ni taimakon da bazan taba mantawa ba,batasanni ba amma ta kaini wurin uncle dinta aka canja min course tare da suna, aka min komai da komai,itama sosai ta taka rawar gani a rayuwata, sai kuma na hadu da wani lecturer mu mai kama da wannan mutumin dana gani a 9ja, basu da banbanci ko kadan banbanci shine daya saurayi daya kuma dattijo ne, amma harta murmushin su iri daya ne, sosai kaina ya kulle saboda wani tunani da yazo min,kwatsam sai nayi tuntube da wasu kuma daya mai kama Dani daya kuma mai kama da Neena,sosai na shiga tashin hankali tunani na kuma bai kuma bani wani abun ba sai da suka bani labarin su, sannan suka kara tabbatar min da suna jinsu kamar yar uwar su ce ni,sai dai ban nuna masu ba nace su nemi aiki a wani company daya Kano daya Abuja sai daya a Lagos sai dai koda suka dawo suka tabbatar min da basu samu ba,hakan yasa suka koma Spain kasancewar sun sami aiki amma duk da haka suna applying amma basu dace na har shekara biyu basu samu ba, kasancewar aikin na yanzu sai dan wane da wane.
Dawowata tayi daidai da dawowar kawar su yusseer abakin ta naji sun tashi daga wancan gidan,sun dawo sabon gida,kallo daya na Mata nasan tana da surutu kuma zata iya fada masu tare da ita muka dawo dukda na fada mata kar tafada masu amma nasan tabbas zata iya fada.
Ajiyar zuciya ta sauke ta kalle Shi,
tace’ yanzu kasan Wacece Ummusalma Muhammad ko kuma Mahmud ko?
Bata jira amsar Saba taji gaba,
” Ni nasa aka sace su yusseer,kuma na nemi 20 million daga hannunsa sannan kuma target dina nagaba shine sace Sameera.
Tashi tayi ta tsaya
tace’ bansan meyasa na fada maka labarina ba,bansan meyasa nayi trusting naka ba,haka kawai naji ina so na fada maka labarina. Alfarma ta agareka shine kar kayi using opportunity ka tona min asiri batare dana gama aiwatar da qudiri na ba a kansu na ruke ka dan Allah,
Ta juyo tana me hada hannayenta biyu muryanta kuma na rawa alamar kuka take so tayi,
Murmushin yayi murmushin da kana gani kasan na karfin hali ne,
Yace’ babu abinda yafi komai ciwo irin labarin ki, labarinki zan iya cewa yafi nawa muni da rauni, tunda ni an kula dani an Bani ingantacciyar rayuwar da zan iya gina kaina na kuma gina iyalina da mutane baki daya, amma ke kuma iya kula dake akayi ba’a baki gata ba,gata kuwa shine tarbiya musamman ke mace, da Allah besa yusseer sun manta abincin su ba da har yanzu kina cikin duhu da watakila ma yanzu kina cikin muguwar nadama da danasani, amma dayake Allah ba azzalumin bawansa ba yasa kika ji komai, idan ba damuwa zan taimake ki mu hada hannu da hannu mu yaki abu guda,
Kallanshi tayi sosai Jin furucinsa na taimako bata tsammaci haka daga gareshi ba, kasa juran kallansa tayi ganin yarda launin idansa ya soma canzawa alamar Yana cikin bacin Rai, dakyar ta samu tamasa nodding Kai alamar ba damuwa,
Kallanta yayi yace’ dawo ki zauna,
Sai da ta zauna ya kalleta dakyau yace’ idan kin amsa kudin me zakiyi da su?
Tace’ bansaniba,
Yace’ Abu na farko da zakiyi Idan kin amsa kudin shine ki siyo company daya daga cikin companies dinnashi,
tace’kasan me kake fadawa kuwa??
Wani makirin murmushi yayi yace’ yes of course, bakiji bature yace life without risk is not worth living ba?
Dole sai munyi haka,karki damu kina dani komai mai sauki ne.
Shiru tayi kawai daga nan kuma tacigaba da bashi labarin abubuwan da bata bashi ba,har izuwa na dazu da taje ta dauko takardu,
Ganin magriba ta gabato sosai yasashi fara tattare takardun wani envelope ne ya fado yasata dauka tana juya Shi a hannun ta, Mika hannu yayi alamar ta kawo a hada, juyawa tayi kawai a hannunta bata bashi ba, daga bisani dai na bashi ta tashi zata tafi,
yace ansa kuma mana ina zaki je Bonita?? Or should I said Mrs lizard??
Takardun ta karba tasa a hijabi,tana tafiya ta kwashe da dariya,
tace’ ai Kaine Mr lizard bani ba,wai kadangare,
Murmushi yayi mai kyau sannan ya bita, tana jin ya biyota tazo fita kawai ta dawo da gudu
tace’ kadangare kadangare,Yana nan
Ta fada tana buya a bayan shi,ai wani wawa tsalle da ya daka sai ganin Shi tayi ya dane gossiping chairs din wurin dariya takuma kwashewa da ita sosai har tana fadi kasa, ta tashi tace’ ohhh mazaje wai fa ahakan ko?
Yana saukowa kuwa ya bita sai ta sai gudu takwasa a dari ta shige dakinta tana masa gwalo, shima murmushi yayi kawai ya tafi don gabatar da sallah, Daddy dake gefe dasu a harabar gidan, gudun su kawai ya hango da dariyar ta shikuma yana murmushi har yazo ya wuce ta gefen shi bakma Kula dashi ba,wani tunani ne yazo masa lokacin guda, sannan kuma yasaki murmushi yau ko takaicin ma baiki ba,shima tashi yayi don tafiya yin sallah…..
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
18
Zirga zirga kawai yakeyi a cikin rasa yanda zaiyi ya bullowa wannan lamarin shidai a yanda yake jin kudin nan ba yajin zai iya fitar da Naira na gugan Naira million na gugan million har million ashiri, Zama yayi,
yace’ taaabb hauka nakeyi ashirin fa, dayawa ai,inaaa bazan iya ba, bari kawai na kira police na fada masu halin da ake ciki,
Janyo wayar sa yayi don kiran police sai dai msg din da ya gani yasa Shi saurin budewa yana dubawa yaga dai wannan mutumin ne da ya turo masa cewan ga account number nan yayi transfer aciki idan kuma police suka sani shida ‘ya’yan sa har abada,
Wani irin zufa ce ta keto masa shi har ga Allah yana san ‘ya’yan sa, dole yayi yanda suka ce, Yana nan zaune sai ga Mama nan ta shigo cikin kwana daya kacal har ta zabge saboda ‘ya’ya, shigowa tayi ta zauna,sai da ya ja numfashi sannan ya fada mata halin da ake ciki,