A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace’ Alhaji Nima an min msg din cewan na bada million ashirin yanzu ni ina naga million ashirin din da zan bayar? Na tattara na kai can wani wurin za’a zo a ansa idan ba’a Sami matsala ba zuwa yamma zasu dawo,idan kuma an samu matsala to bani ba ‘ya’ya na, Yanzu saura million biyar, na dai tattara abinda Zan iya,kuma kaga bazanyi katkat ba, ina so Ka kacika min ne sai a basu don Allah Alhaji rayuwar ‘ya’ya na tana cikin hadari.
Wani iri kuka ne ya kubce mata tace don Allah Alhaji yau daya dai ka ajje san kudin nan naka mu temaki rayuwar ‘ya’yan mu,
Cikin kuka sosai ta karashe maganar,janyo ta yayi ya fara lallashinta,

yace’ kiyi hakuri zan cika maki five millions din, Kenan 40 million za’a karba daga wurin mu?
Kukan da takeyi ne yasashi kara Jin wani tausayin ta yana ratsashi, ji sukayi an bankado kofar an shigo da gudu,Da sauri Mama ta tashi Jin yarda gabanta ya fadi, ganin Sameera hankalin ta a tashe yasa ta tambayar lafiya?
Sameera na sauke ajiyar zuciya tace kinga kinga su Yusuf za’a kashe su wallahi kinga,
Ta fada tana nuna wayarta,waftar wayar tayi jikinta na mazari ai kuwa su ne, an daure su acikin wani kango ga suna nan sunyi jina kina suna Kiran Mama da Abba da su taimaka masu zasu kashe su, sunyi jina jina dasu idon su a kumbure, gani tayi na daga wani karfe an makawa karfar su bata iya cigaba da gani ba ta mikawa Abba wayar ta sulale a kan gado, Abba daman da yake leka wayar karba yayi da sauri yacigaba da gani,ganin bayan karfen da aka kwada masu ana neman kara yanka su da wuka yasa shi,shima kashe wayar ya cillar ta saman gado, Sameera ce ta durkusa a gaban su,

tace’. Don Allah Abba ka taimaka kar su kashe su Abba,

ko kallanta bauyi ba yasa kafa ya bar dakin, dukda yasan dare yayi yanzu haka bazai samu dpo ba amma dole yaje, kuma an gargade shi da kada yaje wurin police amma yasa kafa ya Shure zance, Yana isa kuwa Allah ya taimake shi yaga Dpo Yana Shirin komawa gida. Yana ganin shibya fito da sauri

yace’ Ai baka ga ta komawa ba,yanzu yanzu aka min text, anan wurin ya bashi labarin abinda ya faru a tsaitsaye har ganinsu da sukayi a wayan Sameera,

Dpo yace’ gaskiya sai dai ayi tracking numbern mu gani daga ina ne,kuma tunda kace akwai video ma zamu iya samu inda suke,yanzu de mu karasa daga ciki,

Shiga sukayi office din Dpo din suka zauna sannan ya bada numbern da akayi masa message da ita, fita yayi dpo din bai jimaba ya dawo,

yace’ anga wurin,yanzu na tura aje gidan,

Abba yace’ Ai banga ta Zama ba tare zamuje,
Baima saurare shi ba ya tashi, ya fita ganin su har sun Shiga motar su sunja yasa shi shima shigar tashi ya bisu, shima Dpo din tashi yashiga yabi bayan su,

Tafiya suke yana binsu a baya har suka iso gidan a tunanin sa wucewa zasuyi ko kuma gidan kusa dashi ne ganin inda suka fito suka nufa yasa shi bude kofar shi ya fito

yace’ nan fa tsohon gida na ne, yama za’ayi ace anan aka min text din, kai bazai yiwu ba sai dai ko daga nan aka tsaya aka min,haka ne ma ina ga.

DOP da ya fito yace’ nan ne dai inda akayi maka Text din, amma kuma bamu ga videon ba bare muga ko number dayace ko ba daya bace, yanzu kayi yarda suka ce,idan yaso sai mu nemi account number da komai da komai zami samu Insha Allah,

Kirane ya shigo wayar Abba ganin Mamace yasa Shi saurin daga,ji yayi

tace’ Alhaji shikenan zasu kashe su,sunce tunda ka fadawa police ko gawar ‘ya’yan mu baza mu gani ba, tunda suka fada sai sun aiwatar, gashi nan an turo videon nasu sun kashe su,Kai kaja min suka kashe su,kuma sunce idan bamu basu kudin ba to tabbas zasu sace Sameera itama kuma su kasheta shikenan Alhaji ka cuce ni ka rabani da ‘ya’ya na,
Rufe ido yayi yana Jin duk wani kukan ta da jawabinta yana ratsashi,gawani irin tausayin ‘ya’yan shi da yake ji,gashi yanzu babu su a duniyar an kashe su, ga shi kuma abinda matar sa tace, ya cuceta, da wanne zaiji, bajsan sanda ta kashe wayar ba saida Dpo ya taba Shi tukunna yasan ta kashe wayar sannan kuma ga wani dumi da yake ji yana bin fuskar shi,shafowa yayi ganin ruwa ya tabbatar masa da hawaye yake yi,
Da sauri ya juya ya shiga mota,dpo na masa magana amma baiji shi ba, tabbas yayi nadama,nadama ba kadan ba,da yasani da yaji maganar su watakila da gobe ‘ya’yan sa sum dawo,tafiya kawai yake ikon Allah ne ya kawoshi gida, karar da wayar sa tayi yasa gaban Shi faduwa,

Ka hada kudin gobe gobe Ka kawo shi idan bahaka ba a goben zaka ga gawar ‘yar ka acikin gidan ka,idan kunne yaji jiki ya tsira idan kuma baii ba, hmmmmm ba yar ka kadai ba har matar ka sai mun kashe, Ka huta lafiya tare da bacci cikin salama,
Fitowa yayi daga cikin motar ya shigo gidan,yana shigowa mama ta taso taci kwalarsa,

.tace’ Allah ya isa, shikenan gashi nan ai kasa an kashe su, Ka huta yanzu ita ma kashe ta zasuyi, ni yanzu nan ma zan kai kudina bazan iya ba, inaaa bazan iya ba,
Sulalewa tayi a wurin tana wani irin kuka mai cike da ban tausayin,shima sulalewan yayi ya zauna dabas baima damu da wai a bankin kofa yake ba,ko a wani wurin, shima kukan yake don yasan da baiji wurin yan sanda ba da duk haka bata faruba, Sameera ma kuka take jin itace next wacce za’a sace,kuma a kashe shikenan rayuwar ta ta kare.

Mama kuwa kawai surutu takeyi Bama tasanin me take fada, barci barawo ne yayi gaba da su a ranar amma kowanne su a kasa ya kwanta, kana gani kasan baccin wahala sukeyi su duka ukun, Basu tashi ba sai 7am shima wayar da akayi ne ya tashe su, sannan suka tashi,

Mama ko kallan inda Abba yake batayi ba ta tashi ta hau sama, sallah kawai tayi ta fito da mukullin mota, a hannun ta bakowa a parlourn hakan yasa ta sa kai ta fice, banki ta fara zuwa ta Mika check aka bata kudin ta ta fito, mota tashiga ta tafi can bayan gari sannan ta kira numbern nan, gabanta sai faduwa yakeyi, ana dauka taji wata sassanyar murya mai fita a hankali taji muryan tace mata,

‘ ya Akayi ne?

Muryan ta na rawa sosai tace kudin ne na kawo Bansan inda Zan ajje ba,

Yace’ yawwa ashe de kina san raguwa ‘yar ki,ki Shiga daga ciki gefen hagun ki zaki bi,ki mike kadan zaki ga wani kango ki Shiga ki ajje kudin. Kit aka kashe wayar,
Fita tayi tana waige waige ta je ta bude booth ta zuba kudin da ta dauko a banki sannan ta dauko katuwar Ghana most-go din, dakyar take tafiya ,daga baya ma janta ta farayi har ta iso inda aka ce mata, ganin rigunan su ya tabbatar mata da anan aka akashe Mata ‘ya’yan ta,kuka ne ya kufce mata tayi sauri ta share ta ajje bakkon a lungu, ta tattare kayannasu a hannunta ta rike,ta fito tana kuka, a mota ma ta jima tana kuka sannan ta tafi gida.

Shima Abba sallah yayi kawai ya fita banki kudi ya debo sannan yaje inda aka fada masa ya ajje koda ya ajiye samun wuri yayi ya buya ko wai zaiga wanda zaizo ya dauka, tun karfe 8 yake tsaye a wurin amma har Azahar babu wanda yazo wurin hakura yayi kawai ya tafi.

????????????????????

Yaya kaga na fika iya acting gani fa yanda nake narkewa,muna komawa zan shiga film wo ni wo ni yaseer Dan Mahmud,

Banza yusuf yamasa, ko kallansa baiyi ba abinda yake ji ma kawai ya ishe shi,kwana biyu kawai Amma ya gaji so yake yaga ummu yasan tana cikin wani hali ko abinci tana ci ma? Bai ankaraba yaji hawaye nabin kuncinsa,da sauri yasa hannu ya goge gudun kar yaseer ya gani sai dai yaseer juyowar da zaiyi don ya masa magana yaga yarda hankalinsa bama ya kansa yana wani wurin, gashi kuman hawaye a fuskar shi,tasowa yayi ya zo kusa dashi,cikin muryan tausayi,

yace’ Yaya nasan tunanin da kake bai wuce na halin da Ummu zata shiga ba, don Allah kayi hakuri Yaya na wani lokacine komai zai wuce kamar ma ba’ayi ba,
Rungume Shi Yusuf yayi yace’ nasan na wani lokacine amma nasan tana cikin wani hali,mukuma nan muna cikin kwanciyar hankali,a haka zan kwantar da hankali na? Kaima nasan fada kawai kake amma ka matsu da ka ganta, sannan kuma ga Yaya salama again nasan tayi ta jira amma taji shiru?
Shima yaseer rungume shi yayi tare da sakin wani kuka kawai yana daurewa ne,kar Yusuf yaga gazawar shi,shike lallashinsa, sunjima ahaka daga bisani kuma suka zame suka kwanta, daya a kasa daya kuma akan kujera kasancewar a parlour suke, a haka bacci yayi gaba dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button