A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ shikenan ta fesa min turare a ido, zandena gani.
Ita de tasan batasa fesa masa ba,Amma yace ta fesa masa zuwa wurin Shi tayi,
tace’ sannu,haka kawai tace wuce toilet dayake zani ne a jikinta tun kayan jiya bata cire ba,sai kawai tayi wankanta ta daura zanin zata fito sai ta tuna maybe yana dakin, leka kanta tayi taga bakowa a dakin yasa ta fitowa,Zama tayi sai da ta goge jikinta tsab ta shafa mainsa ta fesa turarukan sa bude baggonta ta janyo wata doguwar Riga da ta sako aciki tasata ta yafa mayafinta ta fito,
Bakowa a parlourn a gogo ta kalla taga shadaya harda rabi,dakin umma tashiga da sallamar ta ganin tayi a zaune a wurin, ko kallansa batayi ba ta karasa ta gaida Umma cikin kulawa itama Umma ta amsa
tace’ ya kwanan bakunta kuma?
Sunkuyar da Kai kawai tayi batare da amsa ba, Umma tace’ kije kice abinci kinji ko, nasan kina Jin yunwa jiya ma Baki wani ci na kirkiba, tashi tayi ta fita.
Kallan Umma yayi yace’ ni baza’a min tayin abincin ba?
Idan yasamu an kalleshi ta yaci sa’a don ko kallansa batayi ba.
Tashi yayi ya fice hangota da yayi a dining tana zuba abinci yasa shi karasawa wurinta,
yace’ kinyi lefi amma baza ki iya bada hakuri ba ko?
Itade batasan lefi da tayi ba,shiyasa ta dena zuba abincin ta kalle da kyau,
tace’ menayi?
Kujera yaja ya zauna,
yace’ lefika ba laifi Bama zance, yanzu de abani abinci yunwa nakeji idan baso ake kuma amin horon yunwa na na mutu, Wanda ta zuba ta tura gabansa chips da kwai, ta hada masa tea,ta ajje a gabansa ta janyo bread ta tura masa, kallan abinci yakeyi kawai,Amma be tanka ba sai da ta zuba nata,tana niyyar barin wurin,
yace’ Bana cin chips da kwai,bakuma na Shan tea da madara kuma banacin bread Gaya,
Ya karashe da rafka tagumi, juyowa tayi ta kalli inda yake Yana nan zaune yarda ta barshi sai wani uban tagumi da ya rafka,tana sone tasan gaskiya zancen sai dai kuma basu hada ido bare tasan da gasken yake komi, juyawa tayi tayi tafiyar ta,sai da taci ta koshi sannan tazo ta kwashr kayan Yana nan zaune be motsa ba bare kuma ya tashi, kitchen ta nufa ganin mai aiki tana kokarin Dora abincin, gaisawa sukayi, sannan ta tambaye ta ina store yake, doya ta fare yar kadan tayi fatan ta Tasha kifi da kayan Hadi,cikin lokaci kankani ta Gama ta kwashe a karamin flask ta dafa ruwan Lipton kawai ta hada komai ta fito,yadawo parlour Yana zaune, Shi har yama fitar da rai daga abincin, ya hakura yaci na Rana kawai,ganinta da yayi rike da tray yasa shi Jin wani dadi ya kama Shi amma be nuna ba a fuska sai wani bata Rai yake,bata Masan Yana yiba ajjemai tayi a gabansa kasancewar a kasa yake budewa tayi ta fara zubawa a plate ta hada da spoon a zatansa miko masa zatayi amma sai gani yayi ta tashi ta nufi dakin Umma dashi, babu yarda zai ya iya dole kansa ya zuba,da yasamu ma aka masa abincin Kenan,yayi mai dadi sosai har wani lumshe ido yake, tas ya cinye ya dauki kofin da yagani an rufeshi ya sha Jin ruwan buno yasashi ya ajjewa.
Tashi yayi ya koma daki ganin ta shirya masa komai yasa Shi sakin murmushin Jin dadi, amma gani wata akwatin a gefe daga gaba alamar ba’a jera ba budewa yayi ganin kayansa na ciki,kawai ya zuke shima ya ajje bazai taba yarda ta shirya wannan besata Suma haka zata shiryasa su, akwatin takardun sa ya fito da ya dau na dauka ya mayar, system ya dauka ya fara aiki ,wayarsa da yaji tana ringing yasa Shi dauka bayan yagama wayar ya fara tunanin yarda zai bullowa lamarin, murmushi kawai yayi murmushi nan irin na samu hanya, cigaba da aikinsa yayi a system,
Shiga dakin tayi don ita a tunanin ta ma Baya nan, nufar wurin bakkonta tayi ta bude ta janyo Jakarta ta hannu wayarta ta dauko ta kunna, Kiran Maman Sadiq tayi suka gaisa
tace’ Kindawo kuwa?
Maman Sadiq daga dayan barin tace’ bandawo ba, ai nace maki zan dade,akwai wani abune?
Tace’ a,a bakomai kawai daman kayana nake so na dauko daga gidan,
Maman Sadiq tace’ badamuwa Zan fadawa Abban Sadiq idan ya dawo ya bar key za’a karbi sako kar ya koma dashi wurin aiki.
To shikenan,yaushe zaki dawo ne?
Ehh to gaskiya ba Rana duk ranar da nadawo Zan kiraki,don Bansa Rana ba gaskiya. Sallama sukayi ta kashe wayar ta,
Duk abinda tace yana jinta amma kamar beji komai ba gabadaya hankalinsa na Kan system a zahiri Kenan.
Tasowa tayi daga kan kujeran da ta zauna ta dawo gefen gado,
tace’ zaka kaini na dauko kayana kaji ko?
Banza yayi da ita kamar ma badashi take ba, a tunanin ta beji ta Kara maimaita masa,dagowa yayi suka hada ido kawar da kanta tayi,
yace’ Baki San sunana ba ne? Ko kuma umarni kike ma Bani ne?
Bata kalleshi ba don tasan ita yake kallo
tace’ tambaya nayi,
Haka ake tambaya? To ki Bari lokacin kika iya tambaya sai na kaiki ki karbo kayan naki,
Wayartace tayi vibrating dagawa ganin Maman Sadiq daga dayan bangaren Maman Sadiq tace’ na fada masa yama bayar da key din wa oppite dimmu,
To tace,maman Sadiq ta kashe wayar.
Kallansa tayi dakyau ganin hankalin sa Yana Kan aikin sa,
tace’ don Allah Ka kaini na anso sako,
Itafa Allah ya gani a cikin awanin da sukayi tare gabadaya ya dameta,dazu ma haka wai bata iya gaisuwa ba,to ita Zama ta iya kirga adadin mutane da ta gaisar karewa ma Kenan da aka samu ma take gaidawar,ai bata San sanda wata tsuka tayi escaping bakinta,
Kallanta yayi sai dai kuma ganin tana kallan wani wurin bakinta na motsi alamar magana take ita kadai, kuma badashi take ba,Jin Yana kallanta yasa ta Kara daure fuska tajuyo,
tace’ Bani key din,
Wannan kwa Anya tasan metake kuwa? To idan zai bata key ya kaita mana?
Tashi yayi kawai ya shige bayi Jin ana Kiran sallah, Kara daure fuska tayi ta nade hannunta a kirji wai don karma ya kawo Mata reni, koda ya fito ko kallan inda take beyi ba ya fice, kuma be kashe system dinshi ba bekuma sata caji ba,gajiya tayi itama ta tashi taje tayi alwala zatayi sallah taga be rufe ba,rufewa tayi kawai ta jona masa caji sannan ta durata Akan bedside drawer,
Koda ta idar tajima Akan dadduma,bata da niyyan tashi kuma, hannunta ta kalla ganin bracelet din dake hannunta kallansa take kawai ba abinda take tunowa sai moment din su da Neena inda take ce Mata
“‘ Nifa yanzu ko aure akamin Zan zauna,to meye a auren, Zan iya kula da miji daidai gwargwado na Zan yi masa biyayya,na kuma iya ma tambayar miji idan Zan fita, to sai me kuma? Yawwa sai gyarab gidan da girki nasan ma na wuce wurin indai wannan ne sai me kuma? Yawwa sai kuma hakuri kinga hakuri da ake cewa a ringa hakuri hmmm to hakuri shine ma auren,don idan ba hakuri to da gabadaya auren ma bazai zaunu ba, hakuri shine komai fa,uwa uba kuma tsabta,to nikam kinga ai ko an min auren Zama daras ko ya kikace?
A lokacin ko kallanta ma batayi bare ta daga Mata Kai,gani take shirme take yi Mata kawai wata Neena da aure,hauka da aure de.
Batasan Hawaye ya fara zuba a idanta sai taji Yana diga a cinyarta,bata damu ba da ta goge don kukan daman take son tayi shafa bracelet din tayi da dayan hannunta tana cigaba da tuno moment dinsu,
Jin wani soft hand Yana shafa fuskarta yasa ta dago da idanta shine zaune a gabanta Yana goge Mata hawayen batasan sanda ta fada kansa ba ta kamkameshi tana cigaba da kuka,batasan dalili ba amma tana San tajita a jikin wani tana kuka,tana San yau daya a rarrasheta ba ta rarrashi kanta ba, kuka sosai takeyi,beyi yunkunrin hanata ba sai Kara kankameta dayayi Shi gani yake shine yaja Mata wannan kuka.
Tunda Duba da irin rayuwar da tayi can tasaba bata tambayan abu sai de ta fada a yi mata shi, Jin kukan nata yake har cikin jikinshi Baya bawa kowa laifi sai kansa,lumshe ido yayi yana Jin sautin kukanta yarasa takamaimai me yake ji a ajikin Shi burinshi be wuce tayi shiru ko ya dena Jin abinda yakeji,
Sun jima a haka Jin ta dena kukan sai shashsheka yasa shi dago ta daga jikinshi hawayen ya share yana girgiza Mata Kai alamar ya isa,kallo Shi take shima ita yake kallo,sai dai ya goge Mata hawayen tas sannan ya janyo ta ya rungumeta ya cigaba da lallashinta.