A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

” Wai ke kam ina kika shiga ne muna ta kiranki amma kinki dagawa mutane waya ke bazaki Kira ba kuma idan an kiraki Kiki dagawa ko? Kuma Sarai nasan kinga missed calls,

Be yarda ya dage sai masifa yake,amma yasan da tana gabansa bazai iya mata wannan abu Yana farawa ma zai dena,kashe wayar yayi ganin hotanta da ummi yasashi Kara kallan sosai ko gidan suka zo ya furta,sosai tayi kyau,Kenan Anty ce ta mata kitso murmusawa yayi ya bude wardrobe ya ciro three quarter da shirt yasaka ya fesa turare wata iska yaji tana shigarsa bacci kawai yake so yayi amma yana Jin yunwa kuma yasan breakfast ne da beci ba,da yaci duk wannan gajiyar ba jinta zaiyi ba, Zama yayi Yana kallan abincin da ta zubo komai biyu ta dauko,aikuwa idan ba’a bashi ba bazai ci ba, ya rufe Ido Kenan ta shigo rike da lemu a hannun ta ajiye,

yace’ sai yanzu ?
Yana ganinta da zata shigo sai da ta leka ko ina sannan ta shigo,
Batayi magana ba ta kawo ta ajje ta janyo plate ta zuba masa abinci itama ta janyo ta zuba sannan ta zuba masa lemu ta tura gabansa tace’ gashi,
Ita kuma ta zauna a kasan carpet ta fara ci ji tayi shima ya sauko kasan kusa da ita ya janyo plate dinta ya hade abincin a plate daya ya jingina da kujera,

yace’ bazan iya ci ba,idan nagaji bana iya cin abinci da kaina bani ake,
Harda su lumeshe ido, yace’ idan kuma ba’a bani a baki ba to har gobe bazan ci ba shikenan sai na fara rashin lafiya, juyowa tayi ta kalle shi yarda ya Jingina da kujerar kallo daya zaka masa daman kasan ya gaji, spoon din hannunta ta dauka ta kai bakinsa,bezata ba sai jin abinci yayi a kusa da bakinsa ai tuni ya bude ido ya zauna dakyau,tana bashi yana aikin kallanta saida yakusa cinyewa yaji ya koshi,ta kawo zata bashi ya kalli hannunta shi sai yanzu ma ya lura da lallan da aka mata,karban spoon din yayi ya kai bakinta, ba yarda ta iya ta bude bakin yasa mata,

yace’ yau dai da’alama so ake a kashe ni idan ba’ayi wasa ba,
Waro Ido tayi waje ta kalleshi

tace’ kashe Ka kuma?

Yace’ manta kawai,
Zatayi magana wayarta tayi kara, tashi tayi ta dauko ta dawo ta zauna abincin yasamata sannan ta daga wayar Glip ne

Yace’ fav bro ya kira ki wai bakiyi magana ba, kuma baki ma daga ba,

Tace’ damuna zaiyi shiyasa ma ban daga ba,

Yace’kuma kin daga kinyi shiru,

Tace’ ni kuma?
Sai kuma ta kalle shi dage mata gira daya yayi,

tace’ yanzu de menene?

Yace’ daman wani albishirne,

Wanne albishir?

Karban wayan Yayi yasa speaker yacigaba da bata abincin,

mus’ab yace’ Mun kusa dawowa mun sami aiki a company nan fa,amma sai dai ba aiki daya bane kuma ba gari daya bane ni a Lagos fav bro Abuja zamu zo interview Nanda sati daya shine daman kiran,

Tace’ amma naji dadi,

Yace’ idan munzo ina zamu sameki?

Kallansa tayi taga ita yake kallo ya miko mata Loma baki,
Daga can Mus’ab yace’ ehh ?

Tace’ amm idan kazo kawai Ka kirani zanzo na dauke ku,

yace’ a,a kema kinsan bb ne zaizo daukan mu ai
Tace’ okay sai anjima?

Jitayi ance ehh da yake shine an dau wayar amma ni kuma ko oho ko?

Damuwar ka, headache kawai,

Takashe wayar cigaba da bata abincin yayi saida ta koshi tukunna ya dauko lemo zai bata ta karba tace Zan iya sha da kaina,kaima nasan haka ne tunda ka koshi har kana bawa wani ko?

Murmushi yayi kawai ya matso kusa da ita sosai har suna gogan juna yace’ nagaji da yawa bacci nake sonyi kuma ina kwanciya za’a la’asar gashi kuma ba’asan baccin yamma ya zanyi ?
Tashi ta tattare kayan

tace’ ina zuwa
Bata jima ba ta dawo wannan Karan ya koma kan gado zama tayi a gefen gadon ta lankwashe kafa daya daya kuma ta kasa, shikuma rufda ciki yayi ya juya kansa, Ta jima tana kallansa batasan kuma me take kallo ba juyowa yayi don ya mata magana sai dai Jin idanta a cikin idansa yasa Shi manta mezai ce mata, dakyar yasa hannu ya janyota ta itama ta kwanta suna fuskarta juna,shafa kitso kanta yayi,

yace’ wa ya maki?

Anty safiya,
ta bashi amsa kamar yarda yayi maganar Shi,jiyayi gaba daya ma ta kara saukar masa kasala, hannunta ya dauko,

yace’ wannan fa? Du itace?

Mai aikin Umma,

Yayi kyau sosai,amma meyasa Baki ce ta miki shuku uku ba?

Murmushi tayi tace’ shuku uku fa,haba dai sai kace wata yarinya,

Ohh ke yanzu ba yarinyar bace?

Ehh,

Banga alama ba,

Wacce alama Kenan?

Gashi dai kina da miji amma ba’a iya Kula dashi ba,

Shiru tayi tama dena kallansa, yace’ okay na gane, baki dauke ni a matsayin miji ba ko,

Girgiza masa kai tayi alamar a,ah,
Yace’ shikenan na gane,to yanzu a dauke maganar miji a ajiye ta a gefe ko?

Daga kai tayi irin eh,
Murmushi yayi sarai ya gane kunya take ji,
Yace’ to shikenan yanzu de na zama Neena,na kuma zama Yaya,na Zama Baba wannan matsayin na bawa kaina an bani ko na janye ?

Daga kai kawai tayi,
yace’ to naji amma dai kin san ba shiru zaki min ba ko? Yanda na bude baki ina magana sai kace wani loro,a loron ma sabo,
Ya karashe tare da gyara kwanciyar sa ya juyo daidai yana fuskantar ta da kyau,

yace’ kuma kallan ma an dena ?

Dagowa tayi suka hada ido ta kuma kawar da nata kan, hannunsa dayake shafawa akanta yasa ta tafara Jin bacci dadi take ji idan Yana shafa mata abinka sabon kitso kuma zafi yake mata shiyasa bata sa mai ba bakuma ta daura dankwali ba,

tace’ me loro yake nufi?

Kina so ki sani,

Ehh,da kuma mi amor,da mi precious,

Dariya ya fashe da Shi,
yace’ mi me? amor? Precious taab, ba ruwana idan suka jiki, idan Banda abinki ai turanci ne precious din,

Kumbura baki tayi zata tashi daga kan gadan sauri yayi ya kamota yace’ Am sorry bazan sake ba,

Ba dariya kake min ba?

Nadena yi hakuri kinji mi precioso, mi amor,

To me yake nufi ,

Karki damu zaki sani ne kinji?

Komawa yayi ya kwanta,
yace’ zoki kwanta a kusa da mij..kusa da Neenanki kinji ko? Daure fuska tayi,
yace’ nace fa Neena ko? Kawai ki dauka ni itace kinji ko?
Bracelet din hannunta ta dago ta kalleshi sannan ta mayar da hannunta ta koma wasa dashi sai dai idanta da ya ciko da hawaye,matsowa yayi kusa da ita ganin hawayen ya zuba tana wasa da bracelet din,wani abu yaji ya tokare shi ya kasa numfashi,dakyar

yace’ waye? Shi?

Dagowa tayi ta kalleshi abinda ta hango a cikin idansa kadai ya tabbatar mata da kishi yake, murmushi ne yayi escaping a bakin ta,

tace’ Ai naga kaine Neena to mene na batan rai kuma ?

Yace’ dariya ma zakiyi?
Goge kukanta tayi ta tashi ta bude wardrobe ta dauko Jakarta a cikin ta dauko wata paper tare da zoben da har har yau bai mata daidai ba, zoben ta dauko ganinsa tayi har yaje bakin kofa ya bude ya fice, itama Jin ana kiran sallah yasata shiga toilet,koda ta idar ta jima akan sallaya ko zata ga ya dawo amma shiru.
Daukan zoben da ta ajiye akan gado tayi ta fita,dakin Umma ta Shiga sallah taga tana yi da’alama makara tayi,fitowa tayi ta nufi kofa ta fita yau kwanan ta biyu a gidan amma bata taba leka tsakar gidan ba, tsakar gidan ya mata kyau madaidai ci dashi sai bishiyo shiyasa gidan yake iska saboda wadatar bishiyo wani dan lungu tagani inuwa tamasa yawa shiyasa ta bi wurin kamar wurin hutawa don harda su lilo a wurin irin na zaman nan wurin ya burgeta sosai ga kuma shuke shuke harda su zogale da wasu abubuwa batasan suba, Zama tayi akan lilon tana kara nazarin wurin tana lilawa ahankali daga karshe kafarta ta nade ta jingina da lilo ta rufe Ido iskar na kadata tare kamshin kasa alamar suna samun ruwa sosai.
Jitayi kamar ana taba lilon kusa da ita bude idanta tayi,ta kalli gefenta ganinsa da tayi akai shima yayi yanda tayi daidai,, da dukkan alama baima san tana wurin ba ko itace batasan yana wurin ba da tazo, numfashi taja ta sauka ko takalmi bata saka ba taje ta zauna a kusa dashi, hannunsa ta kamo ta saka masa zoben,bude ido yayi a hankali yana kallanta ita kuma tana kallan yatsan da tasa zoben,bata dauke idanta a wurin ba, shima bai dauke idansa a kallanta ba,sun jima a haka tana kallan yatsansa dake cikin hannunta shikuma yana kallan fuskarta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button