A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan sun tsaya sunyi sallah tayi tunanin tura masa message shiyasa ta tura masa Amma ba reply daman tasan bazaiyi ba mene na damun kanta, sai yamma lis suka isa da tambaya sukaje unguwar har suka karasa kofar gidan, gida ne matsakai ci na rufin asiri gefen sa kuma gidane mekyau ba laifi, sallama tayi a kofar gidan aka amsa shigowa tayi matar dake zaune ta tashi tana Mata lalle da fillanci ta bata wuri ta zauna ta kawo Mata ruwa mai sanyi ta ajje mata suka gaisa cikin fillanci, cikin fillancin matar tace Mata ‘” ban gane ki ba Bingyal daga ina?
Itama cikin fillancin ta mayar Mata tace’ Baki sanni ba, sai dai ina tambaya nanne gidan Abdullah Abdul shakur? Da matar sa Mariya ? Suna da ‘ya’ya biyu zulaihat da kuma Abdallah,
Cikin mamaki matar tace’ eh nan ne ke wace?
Wani dattijo ne ya fito Yana dogarawa yace’wai me nake ji ne, ji nayi ana anbatar zulaihat da kuma Abdullahi,
Matar ta tashi ta karaso da Shi ya zauna sannan ta fada masa abinda akace da kuma tambayar da ta Mata,shima yace’ fada mana ke wace?
Ni matar jikanku ne wanda ‘yarku ta tafi ta bari,
A tare suka ce a tare suka ce TASHI KI FITA……….
Tofah ????????♀️
~*Ayi sallah lafiya~*????????
By: Hijjart
Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
27
Baba be saurareshi yaci gaba,
yace’ ranar da muka tsinceka acan wani kauyen ne, kusa da Adamawa ba nisa, mun tsaya don zainab tayi fitsari taje zatayi taga wani jariri a wuri dayake yarinya ce a lokacin sai da tayi fitsarin ta dauko yaran ta kawo tace Baba kaga a can wurin na ganshi,karbar Shi nayi na Kare masa kallo, ya kurkurje kuma idan ba lura kayi ba dakyau tsab zakace Baya numfashi, da kuma hannu sa Wanda ya kumbura,dayan hannun kuma shaida ce ta daga asibiti aka dauko Shi Wanda ake mannawa yara shaida, da number, ita mahaifiyar ta ma tazaci ya mutu, mukaje muka duba ta nuna mana inda taga yaran ga kuma towel can a gefe, daukan towel din mukayi,ta rufe Shi tace ya mutu,nine nace Mata be mutu ba,gashi kuma bakowa a wurin mu ba gidan dagaci muka sani ba, tausayin yaran yasata cewa mu tafi dashi,haka ma zainab banki ta tasu ba muka dawo dashi Amma sai da mukaje asibiti aka bashi taimakon gaggawa tukunna, sa’a Muka wucs gida,sai muna zuwa gida labari yasha banban, tsab ya kwashe komai ya fada masu har zuwan da yake yi da kuma zuwan Shi na karshe sa’a nan yayi shiru,
Tunda Baba ya fara yake sauraran Shi be taba sanin saboda dashi ne basa zuwa wurin Anfa da Fendo, hawaye ne ya fara zarya a kumatunsa Shi shikenan beda uwa be da Uba? Gashi de wulgar dashi akayi ai kuma mutane sun shaida haka? Sun San basa son sa meyasa suka haifeshi da hanzari ya dade da mutuwa da ba’a ceci rayuwar Shi ba,tunda aka fara ya fara comparing rayuwar sa da ta Ummusalma beda iyaye kamar yarda itama bata da iyaye inama zai ganta.
Anty ce ta kwantar da kanshi a cinyarta,
tace’ lokacin da naga hoton Ummusalma na hango tsan tsar kamar ku, sai dai Kai Baka ga hakan ba sam,tun a sannan na dasa ayar tambaya a kanta shin Baku da alaka ne? Har hotan na turawa Baba shima kuma ya gani sai dai yace’ min yana yawan ganinta a airport din London tana raka wata ita kuma sai ta dawo, Ashe shima Yana tunanin kamar yarda nake, daga baya ne yadena ganinta besan dalili ba, beyi wani Abu akai ba Shi a zatan sa ‘yar can ce. Koda yayi bincike a kanta sai ya tarar ba haka bane ba, ba iyayenta bane sai dai be tsananta binciken ba ya barshi iya haka.
Baffa dake sauraran kowa yace’ ita wannan din da kuke fada Wacece?
Anan suka bashi labarin abinda suka sani, sannan ummu ta Basu kaf diary dinta da ga karanta sosai kuwa abin ya Basu mamakin haka ga kuma news din da sukaji ranar Saturday Amma ita ummu bata ma San anyi ba. Shiru kowa yayi Yana tunanin wani Abu ransa, shidai Uncle abinda yake ji kadai ya ishe Shi,
Ummu tace’ Baffa da mukazo naji kace Kanwar Shi kun Santa ne?
Baffa yace’ tabbas tazo anan ta kwana, yau da safe ta tafi kuma bakowa ne yace ta tafi ba sai ni,nine tun farko naja komai me ake da zuciya irin tawa?
Baba yace’ Anfa kadena fadar haka mana, Wacece ita har tazo nan?
Baffa kasa magana yayi gani yake duk Shi yaja komai da ace bece ta tashi ta fita ba da duk haka bata faru ba,
Inna tace’ Yarinyar tazo gidan nan,itace ta fara ankarar mu abinda babu Wanda ya fada mana, itace ta daidaita komai tsakanin mu da ku, itace silar komai, gashi ta tafi, sai dai tace’ ita Sirakace a gare mu domin Dan zulaihat take aure.
Dan zulaihat ?? Baba ya maimaita,
Jinjina masa Kai tayi tace’ ehh haka ta fada mana,
Anty tace’ me tace maku sunanta ?
Ummusalma tace, kuma a gaskiya Nima Naga kama sosai da sosai Dan Zama a Iya cewa ‘yan biyu ne,
Mijin Anty yace’ to ya akayi kuka barta ta tafi?
Inna tace’ kayya yaro kuskure an rigada na tafka Shi sai kuma gudun yin wani,
Yace’ to Baku tambayeta komai game da ita ba?
Gaskiya bamu tambaya ba, bamu Sami damar yin hakan ba,
Shiru yayi Yana nazarin wani Abu,kowa shiru yayi can ya dago,
yace’ kunsan ita zulaihat dinne? Da tace’ danta take aure?
Inna tace’ ‘yar muce zulaihat wacce ta bata shekara da shekaru,
Yace’ to ko kunsan inda take? Nufina gidan mijin ta ?
Baba yace’ gaskiya bazan ceba,don nikam rabona dashi na manta ko a hanya zai iya wucewa na wuce bamu gane juna ba, ko gidan ma ni bazan iya kaika ba,
Inna tace’ Ada suna zuwa daga Baya ne kuma suka dena muma kuma muka dena shikenan zumunci yayi nisa kuma,
Shiru yayi yace’ yanzu dole muna bukatar saninin inda gidan yake,dole sai anyi bincike indai muna San mu San idan suna alaka da Abdullah,
Kowa kuma yayi na’am da zancen sa daga nan kowa shiru yayi shidai uncle ba Baka sai kunne Shi bega amfanin Nemo subama tunda sune suka yar dashi ai.
Sai bayan sallahn Isha Baban Ummu yacet zai tafi hakan, zai barsu anan don su ga ‘yan uwa da abokai, tunda Yana da wata matar,ita de ummu bata so ba, gashi lokacin basirar ta ta dauke batace makaranta ba,haka ya taho a jirgi Allah yasa ya tafi da passport din Shi ya barsu ba ranar dawowa .
????????????????????????
Yusuf ne da Yaseer suna zaune a tsakar gidan su,kowa yayi jigum Yana kallan wani wuri, suna wani tunanin na daban, gaba daya sun rame sabida tunanin da suka sawa kansu danma suna Dan debe kewa idan da nepa,to yau kusan sati ma babu nepar Shiyasa suka fito suka zauna,
Yusuf ne ya kalli yaseer,
yace’ kasan menake tunani?
Yaseer yace’ a,a sai Ka fada,
Ina tunanin Ummu ne,nasan tadena surutu yanzu sabida rashin mu,
Yaseer yace’ nasan dahaka,Amma Kai Baka tunanin Mama?
Murmushin takaici Yusuf yayi yace’ me zanyi tunanin akai? Ita da suka raba uwa ‘da, uba da ‘da?
Karka manta sune suka raba yaya salama da Babanta da kuma yayunta guda uku,har ‘ya’ya hudu? Hakan be ishe suba sai da suka nemi su watsa Mata tarbiyar ta a matsayin ta na mace,hakan be ishesu ba suka kuma turata karatu Akan manufar su,ko ca aka ce masu kowannne dane ake turawa yake watsewa oho, kuma kana min zancen su? Banyi ba kuma bazanyi ba,
Shima yaseer murmushi yayi yace’ nagode daka tuna min hakan,Amma kasani no matter how bad they are, they still our parent, don’t ever forget mufa maza ne aljannar mu na kasan su,ba Mata bane da aka ce aljannar su na kasan mijin su, koda matanne ma ba’a ce sabawa iyayen su ba, and kuma idan ma duba acikin 100% Maza kalilanne ke bin iyayen su musamman idan basuyi dacen Mata ta gari ba, Mata kuwa zaka samu kusan rabi da kwata basa bin iyayen su, Bana so mu Zama masu sabawa iyaye kuma fa sun bamu gwargwadon ikan su, suna San mu fiye da tunanin Ka,