A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi Yusuf yayi yacet ehh lalle Kace min ka girma u know all this,Nima kuma nasani, Amma abinda sukayi sun kyauta ne? Mema ya kawo wani bin iyaye, inama Ka zancen Ummu ne fa,

Yace’ nasani na fada maka ne don kar wata rana kana irin wannan maganar Ka fada masu ba dadi, shiyasa Amma kayi hakuri,

Yusuf yace’ a gaskiya nafi damuwa da Ummu Akan Mama Nima kuma bansan dalili ba haka kawai, nasan ummu itama hakanne, mama kuwa nasan na wani lokacine,mun fi kowa sannin halin kayanmu,

Murmushi mai kamar dariya dariya yaseer yayi yace’ dude just tell me u fall in ……. Lemme keep my mouth up,

Kai mekake nufi?

Abinda Ka kake nufi Nima Shi nake nufi ai,

Ka kiyayeni wallahi,taam

Ahh ai dole na kiyayi Yayamu,
Yafada da dariya Yana matsawa daga wurin Shi yasan yanzu sai a kawo masa mazga,

Yusuf yace’ Kai wallahi ba abind kake tunanin bane ba,kawai de ina adanawa wani ita ne?

Ohhh shiyasa kake koremata samari ko? Allah ya komar mu can gida zan nuna ma yarda kakeyi idan mun shiga school kar a ma zo wuri mu Banza yayi dashi, shikuwa yaseer cigaba yayi da zancen sa ganin de ba shiru zaiyi ba yasa Shi,

Cewa’ Kai bafa abinda kake tunani bane ba,ni kawai wani Abu nake hangowa ne kawai kuma nasan it will work,

Ehhmmm time will tell,

Daga nan kuma akayi shiru aka fara tunanin yaushe ne ranar fitar su? Sun tunda suke Basu taba gani an dauke masu wuta ba,gashi de a unguwa suke sometime suna Jin hiran samari da yamma ko da dare

✨✨✨✨✨✨✨

Umma tana zaune a parlour Daddy ya shigo sai da suka gaisa,
tace’ yawwa Kai zaka Kaine ko direba ne? Yanzu nake so na tafi kaga de Tara tayi,

Yace’ driver ne zaikai ki ni sai ranar jummu’ah idan za’a daura auren ‘yar mai gari zanzo,

Ummu tace’ afto kaga ni nama manta shaf da zancen auren sa to shikenan hakan yayi kyau Allah ya kaimu,
Tace’ kaga ni Zan tafi kuma bazai iyu na tafi da ‘yar mutane ba, sabida haka idan kaje gida Ka turo Saima ko su Ameera sai su zauna tare da ‘yan albarka kagane ai,

Yace’ to shikenan badamuwa,nace Umma yanzu idan kika tafi sai yaushe Kenan?

Umma tace’ af zancen banza Kenan,ai idan na tafi to sai kawai sai kun ganni Dan bazan dawo ba yanzu ah to,

Idan kunga anyi biki Nayi wata bandawo ba to kawai salin alin ku sallami mai aiki su kuma su koma gidan yayansu audushakuru bazan lamice zaman su su kadai ba ake cewa gidana gidan Maza,

Shidai Daddy shiru yayi don besa tacewa Yana magana zatace zata koma can da Zama shikuma Allah ya gani Baya so yafi so yake Jin ta a kusa dashi, sai can,

yace’ sadakin wannan yarinyar fa na Baki kya bata ko kuma na Bashi,

A,ah safiya zata karba sai ta bata ko kade? Kaga tashi kaje Ka Kira min ‘yan albarka Maza Maza, Zan tafi,

Tashi yayi yaje kofar dakinsu yayi knocking sai da yayi da karfi sukaji, Mas’ud ne ya taso ya bude mai kofar yana mistsika Ido,ai yana ganin Daddy yayi wani Wawa tsalle tare da ihu ya rungume shi, shima Mus’ab tasowa yayi ya rungume shi,

Binaif dayake shiryawa Jin ihu ya fito a dari ganin su da Daddy yasa Shi karasawa Yana mai Dan Jan tsaki sai da ya gaida Daddy, yace’ ku har yanzu bazaku dena shirme bako?
Babu Wanda yayi magana sai sunnde Kai tsaki yaja ya wuce, komawa parlourn l sukayi Umma ta masu sallama har mota suka rakata da kayanta daga nan shima Daddy y wuce suka dawo cikin gida Umma ta fada masu zuwan Saima ko su Ameera baza su iya cewa ga yarda sukaji ba,sai dai baza su iya musu ba, shiyasa suka nuna bakomai hakan, dadin su daya bb Yana nan sai dai kuma yanzu sun lura yana fita aiki idan kuma ya tafi fa? Allah yasa ma zasu tafi interview shine kadai saukinsu,
Yana fitowa yagan su a parlour sunyi jigum kowa Yana saka abubuwa dayawa a ranshi har zai wuce sai kuma ya dawo ya tsaya,

yace’ meke faruwa?
Mus’ab yadago yace’ babu komai kawai de muna Jin tafiyar Umma ne,

Murmushi yayi yace’ waya Riga wani zuwa duniyar ?

Mas’ud yace’ Saima ce zata zo ta zauna anan ko ita ko zu Ameera,

Yace’ sai me Kenan?

Dagowa sukayi suka kalle shi,
Ya jinjina Kai alamar eh,
yace’ idan Baku dena wannan abun naku ba yanzu sai yaushe zaku dena,to idan Baku dena ba wata rana sai kunyi Dakunsa, Dana sani kuwa keyace,
Yasa Kai ya fice ya barsu sude haka suka kare wuni guda babu walwala sai da yamma ne suka Samu suka fita.

Bata dawo ba sai Yamma shima a gajiye ta dawo zaman mota ba sauki, a kofar gida ya ajje ta ta shiga bakowa a gidan da’alama Basu dawo ba daki ta wuce tayi wanka sun tsaya a hanya sunyi sallah, kitchen ta wuce ta zuba abinci ta dawo parlour ta zauna wayarta ta dauka ta Kira, Maman Sadiq daga can maman Sadiq data dauka, tace’ kwana dayawa,
Sai suka Gama gaisawa,

tace’ kindawo ne?

Maman Sadiq tace’ ahh haba de yanzu fa dududu sati befi uku ba sai na cika watan nan ai Insha Allah Zan dawo,

Tace’ to shikenan numbern iya ladi zaki taimaka min dashi Dan Allah,

Okay badamuwa Bari na turo maki, sai da suka Kara gaisawa sannan sukayi sallama,

Tana cikin cin abinci kuwa sai ga number ta shigo sai da suka gaisa tatada Mata abinda zata fada mata sannan sukayi sallama ta kashe wayarta,
Iya ladi ce kadai yanzu hope dinta idan itama ta kasam shikenan kuma batasan me zai faru ba, Nafisa ce ta fafa dawowa sai ummi da Ahmad,

tace’ Anty fa ina taje?

Nafisa tace’ asibiti taje ta inaga yau sai dare zata dawo tunda bata je ta dauko muba,

Tace’ daman tana kaiwa haka?

Indai aikin suna da patient din da babu mai kuka dashi suna kaiwa mana sosai ma sai Wanda zaiyi na Dare yazo sannan sai su dawo,
Jinjina Kai kawai tayi bata iya magana ba,

Nafisa tace’ Anty Dan Allah gobe ki tafi dani raban katin kinji?

Tace’ kuma makarantar fah?

Anty anyi fa hutu ko kin manta ne?

Aikuwa de na manta gaskiya,
Amma nikam nagama nawa gayyatar sai na rakaki kiyi naki,

Dagaske zaki rakani?

Idan kina so zan rakaki mana,

Amma kuma Anty safiya bazata Bari ba,

Zata Bari mana,
Amma wai meyasa kike cemata Anty nagade mamanki ce,

Dariya tayi tace’ mamana ce Amma itace komai nawa, she’s my best friend,my friend,my mom, my everything,

Murmushi Ummusalma tayi a zahiri a badini kuwa kuka ne yake San zuwa mata,meyasa bazata tuna komai ba wai? Sanda tana karamar nan,meyasa bazata iya tuno iyayenta ba when’s she’s two years,
Bama taji abinda Nafisa ke fada Mata ba,sai ji tayi Anty na magana tana fadan ba’a cirewa Ummi Kaya ba ita da Ahmad daga nan de ita tashi tayi ta mai da kwanan kitchen sanda tadawo itakuma Anty tana daki, lokacin kuma anyi magriba, shiyasa ta koma daki itama.

✨✨✨✨✨✨✨

Bayan kwana uku, suna zaune a can wurin hutawar su ita da Anty,

Anty tace’ ummu ya kamata ki Gama duk wani zirga zirgan ki daga yau zuwa gobe Dan inaso a San me za’ayi kinga har anci sati daya yanzu saura sati biyu gashi kuma Umma tace’ ana sauran kwana hudu zamu tafi kije ki ga ‘yan uwa Suma su ganki, don ita Tama yi gaba abinta,

Murmushi tayi tace’ shikenan Insha Allah zanyi daman ina San na fita idan yamma tayi sai na fita nan ba nisa ne ma gidan,
To shikenan tace,

Suna nan zaune aka aiko da dambun nama wai inji Hajja, karba tayi ita daga jiya zuwa yau tana ganin canji daga hajja ko tace Tama ga canji jiya an aiko da tuwon biski yau kuma an aiko da dambu, Anya bata Shirya wani Abu kuwa? Kuma dazu ma da taje gaida tmda Rana nan da fara’a ta amsa haka Suma yau Basu dawo da kuka ba da sukaje da safe, itakam abin ya ba mamaki,
Ummusalma tace’ Anty lafiya de?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button