A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mas’ud yace’ ya kake dariya haka? Kana gani ta mareni? Ai baza taci bulus sai na Rama,
Binaif yadan tsagaita dariyan sa yace’ me zaka Rama?
Marin da mun mana,
Killer smile yayi yace’ Wallahi ko a mafarki, sai dai Ka rame,
Ya kallesu yace’ sannu da jiki fa, ganin sunyi shiru suna wani kumbura Baki yasa Shi yin wata dariyar,
yace’ Wallahi Dan na manta waya na a mota kuma kar na koma show daya ya wuce,daman da baka mareta Bama ni Zan mareta,
Mus’ab yace’nifa banganeba Naga ta Shiga dakinka?
Murmushi yayi yacet zaku gane very soon,
Yafada Yana tafiya,sai kuma ya juyo da Baya Yana tafiya, yace’ bye byee,
Da murmushi a fuskarsa Yana daga masu hannu,
Shiru sukayi suka Samu waje suka zauna mus’ab yace’ twinny kamar shati shati nake gani fa?
Shafa fuskar sa yayi yace’ai saura kadan Nayi kuka kawai Dan kar ta renani, Amma to meyasa zai Shiga dakin bacin tana ciki?
Don ya kauda maganar Marin,
Mus’ab murmushi yayi yace’ Kai Baka gane ba?
Yace’ bangane ba,
Duk rashin kunyar taka? Baka gane ba?
Kai ni Ka fada min, meye Ka gane din?
Dariya yayi yace’ a,ah bazan fada ba tunda baka gane ba sai Ka Bari idan sun fito Suma bayani ni ga tafiya ta,
ya fada Yana tafiya dakinsu,
Shifa harga Allah be kawo komai ba,kawia tambayar Shi anan shine taya suka san juna?
Tana Shiga daki ta cire hijabinta, taje gaban wardruppe ta tsaya tana kallan kayanta, Tama Rasa wanne zata sa,Duka kayan nata sai Riga da wando sai skirt da rigunan bacci ta kwashe dogayen rigunan ta tafi da su, ita kuma bata so tsaki taja ita kadai gashi yanzu tana san hira dasu,tana so su tattauna abin yarda zai kasance, kuma tana San hutawa kafin ya dawo, duk kayan da ta dauko sai mayar duk kayan da ta dauko sai mayar Basu Mata ba,itakam ta gaji, rike kugu tayi tana kallan kayannata,
Da murmushi ya shigo a fuskarsa da daya shigo fuskar nan a murtuke take ga yunaa da gajiya ga hayaniyar da ya tarar gashi ancewa matarsa ta Sunna karuwa a lokacin tunanin yarda zaiyi da su yake Amma ganin abinda ya faru yasa komai tafiya, ganinta ma gabadaya ya mantar dashi komai, ya jima Yana kallanta ganin ta kasa zabar kayan yasa Shi karasawa wajenta,batayi aune ba taji a rungume ta tabaya ya Dora kansa Akan kafarta tare da zagoyo da hannunsa ta cikinta, gaba daya komai Mata tsayawa yayi Tama Rasa mezatayi, tunanin ma ta fara me ya kawota gidan???
Ajiyar zuciya ya sauke yayinda itama ta sauke boyayyiyar ajiyar zuciya,ga gabanta da yake faduwa kadan kadan,
Dukda a boye ta sauke amma yaji, lumshe Ido yayi Yana shakar kamshin turarenta, cikin wata kasalliyar murya saitin kunnanta,
yace’ duk missing dinne haka?
Itama rufe Ido tayi,Jin muryarsa a cikin kunnenta daman gashi ta gaji sai yasa Mata kasala ta rufe Ido bata san sanda ta jingina dashiba ta rike hannunsa dake cikin nata jinta dayayi da ajikinsa sosai yasa Shi bude nasa Shi idon Yana Kara meta kallo kamar ba ita tagama masifa ba yanzu,Kara maida kansa yayi ya kwantar, ahankali ya raba hannun sa da nata yakama towel zai kunce don har ya kunce Shi daga inda ta daure a sukwane ta tashi,
.
tace’ mezakayi hakan?
Gabanta Yana dada faduwa,
Yace’ abida kike so mana?
Zaro ido tayi tace’ ni? Mena ce ina so?
Murmushi yayi ya na Kara kama………
By: Hijjart
Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
28
Kama hannun ta yayi tare da janta zuwa bakin gado ya ajjeta shikuma ya tsugunna a gabanta ya kama hannunta,
yace’ kindawo Kenan? Ko zaki koma?
Kallanshi take kamar yarda yake kallanta gaba Daya zuciyarta bugawa take haka kawai, girgiza kanta tayi alamar a,a
Yace’ komawa zakiyi?
Ta daga Kai?
Hannunta ya matsa dake cikin nasa,
yace’ wani kadangare da ina maki magana kina wani nodding?
Ai Yana cewa kadangare nan kawai ta fashe da dariya, har Kwalla, kallan ta kawai ya tsaya yanayi Shi bega abin dariya anan ba daga wannan maganar sai mutum ya fara dariya? Wato ga mahaukici ma Kenan ko?
Ya shagala a kallanta har Baya so ta dena,sai tana cikin dariya tana so ta tsaya kuma sai ta tuno wani abun,sai ta ci gaba ya jima sosai Yana kallanta da kyar ta iya tsai da dariyar ta, still de da murmushi a fuskarta,
tace’ na tuna wani Abu ne shiyasa,
Shi sai datayi magana ma ta tuna da abinda yace,aikuwa ya hade fuska, yace’ a,a ai kin mayarni abin dariya,
Daga nan ya tashi ya Shiga toilet itama tashi tayi ta nemi Kaya tasa Ka Riga da wando, bude wardrobe dinshi tayi taga duk wa wargaza wasu kayan wasu kuma suna nan yarda ta Shirya su, gyara masa ta fara yi tana tuno rayuwar ta a gidan su wani tayi murmushi wani kuma taji haushi idan ta tuna Hajiya, a zuciyar ta take tunanin ba’a ‘yar ki irin ta ba,taci abinda ranta yake so idan girki ne ta girka San ranta ko anyi abinci idan bata so ta Shiga ta girka Hijaya tayi fadan tayi masifar Amma a banza, tana cikin tunanin tana gyarawa har ya fito bata San ya fito ya tsaya a gefen ta ya jingina Yana kallanta yarda take murmushi ita Daya dimple dinta har ya loma, lokacin tana tuna sanda kadangare ya hau kansa, ganin de bata lura dashi ba yasa Shi rike rigar da ta dauka zata Mata ma ajji, kallan sa tayi ganin Shi ahaka yasa kawar da kanta gefe, tare da sake,masa rigar,
yace’ wannan gyara kike ko kuma batawa kike kalla fa kiga?
Kallan wurin kayan tayi taga Tama Kara hargitsa su ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta looking so innocent,
Murmushi kawai Yana sa Kaya,
yace’ yaushe aka fara Jin kunya na kuma?
Juya ma Baya tayi ta koma Kan gado ta zauna kanta a kasa bata dago ba,
Sai da ya Gama ya dawo kusa da ita,
yace’ da’alama de ana tunanin Mi Amor ne hakan ta faru ko?
Kanta ta dago suka hada ido, tace’ waye hakan?
Nuna kansa yayi da hannu,
yace’ gani kuwa? Ni kike tunanin ai,
Bashiri ta tashi tace’ ni tafiya ma zanyi abuna,
Tuni ya marairaice fuska yace’ yunwa nake ji rabona da abinci tun sanda Umma ta tafi, Basu iya abinci ba gishiri suke gambadawa da yaji musaman Mas’ud gashi ina da ulcer daga ruwa sai malt kadai nake sha,
Yarda yayi fuska da yarda yayi maganar tsab zakace gaske,she don’t when it’s comes to him Karatun ta guduwa yake bata iya gane gaskiyar lamarin, ga wani tausayin Shi da taji tana ji, ganin tana kallanshi karfa ta dago jirginsa yasa Shi kwanciya tare da narke murya cikin tsantsar tausayi,
yace’ shikenan to ki tafi kawai daman ai Baki damu Dani ba, kin tafi ba sallama yanzu ma nasan badanni kika zo ba, shikenan ki tafi bakomai damman yau wata ta gayya ce ni cin abinci gidansu ita da kullum sai ta kirani taji lafiya ta yana tashi Yana wuni, jeki kawai zanje can naci kinji ?
Wani irin karfe ne taji ta daki zuciyar ta da Saida taji zafin Shi har kwakwalwar ta, wai wata? For how long suke tare? Haushin taji ba kadan ba, yanzu idan ta tafi bata masa ba can zaije yaci Kenan? Hanyar kofa ta nufa har ta bude,
yace’ haka zaki fita ba dankwali ? Ba hijabi?
Bata juyo ba ita kuma bata fita ba, hijabin ya dauka ya yasa Mata Har kasa, juyowa tayi, tayi raurau da Ido ta kalle Shi ta kalli hijabin, shikuma ya bude Mata kofa yama Mata alamar bismillah zaki iya tafiya,
Wucewa tayi tana cuno Baki ita daya tarasa me yake Mata dadi, wai wata? Wacece ita? A haka ta isa kitchen,
Mas’ud da yake parlour har yanzu be tashi ba,ganin ta tafito yasa Shi tashi ya bita kitchen din, tana Shiga yana Shiga, ta wuce store ta dauko abinda zata dauka ta dawo ta bude fridge shima ta dau na dauka ta dawo wurin sink ta fara aikinta, Jin ana motsi a bayanta yasata juyowa ganinsa ta dauke Kai ta cigaba da abinda take, shine ya shigo ya zaune Akan table din kitchen din,