A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ wai meye a tsakanin ku da bb ne? Naga de Baku San juna ba,labarin juna kawai kuke ji a wurin mu, kuma gashi yanzu kin biyo Shi har dakin Shi ince de lafiya? Kuma taya akayi kika iya fada haka? Daman ke masifarfiya ce? Ki bani amsata yanzu nan kuma in Karo maki wasu, oya inaji, kuma ko sai na abinda kika min Ki dubi tsabar idona ki zabga min mari agaban Mata ai girman ya fadi, ke nifa da…..

Kallan da ta aikamasa dashi ne yasa Shi yin shiru,alabasa ta bashi ya yanka, kallanta yayi,

yace’ haba de ai an wuce wurin,
Ajje masa tayi ta cigaba da abinda take, ganin tayi banza dashi yasa Shi dauka Ya fara yankawa,
yace’ wai ni kam na Rasa meke damunki, inaga aljanu ne dake ko jinnu ko iskokai ko de mutanen boye, wama yasani ko sarauniyar miskilai kika taka? Gaskiya Zan fadawa bb a maki rukiyya,

Tama sa uzurin itakam, tarasa tsakanin Neena da Chatty wafi wani surutu kowa za’a masa wannan shaidar ga Basu da kunyar fadin magana abinsu, to ma wayace masa kowanne da matsayin sa taga duk dayane,banza tayi masa ta kyaleshi abunda take ji ma kadai ya isheta, shikaidai yayi ta maganar sa har suka gama jalloup din shinkafa taji kayan Hadi ga kifi da tasa a cikin sai lemon Kwakwa da sukayi shine ya jera komai a dining suka wanke kwaninka da suka bata sannan ya fice zuwa masallaci itama Allah Allah daman tazo ta fita kafin su dawo, Jakarta kawai ta dauko ta fito ta murda kofa taji ta gam taja taji de a rufe ta dawo ta zauna tana mai Jin haushin wannan lamarin, tunawa tayi da kofar kitchen ta tashi taje ta bude itama taji a rufe tsabar takaici da ta dawo daki cillar da jakar tayi Akan gado ta cire hijabinta shima ta yar ta Shiga toilet kayan sa da ta wanke ta kalla tace’ daman ma ban wanke ba,
Tade yi alwala ta fito,koda akayi sallahr magariba Basu dawoba har sai da akayi Isha suka dawo tana idar da sallah taji zancen su shikuma ya shigo dakin,gabanta yaje ya zauna ya kamo hannunta Yana wani irin murmushin mugunta, kawar da kanta tayi gefe, yasa hannu ya juyo da ita, suka hada Ido ganin murmushi a fuskarshi yasata fashewa da kuka
Gyara zamansa yayi ya janyota ya rungemeta ya fara bubbuga bayanta beyi magana ba sai data tsagaita don kanta,

yace’ kukan na meye kuma?

Ita kanta batasan kukan me take ba haka kawai taji tazo Mata,kuma taji saukin abinda take ji, sai da ta Kara gyara kwanciyar ta a jikin sa,

tace’ bakai ne ba?

Ni kuma? Bawan Allah menayi?

Bata Kula Shi ba sai ma rufe idanta da tayi kwanciyar ta Mata dadi har wani bacci bacci takeji, kallanta yayi y yarda ta rufe Ido tabl tsuke Baki shape dinshi na love ya fito sosai,

yace’ dazu Anty Safiya ta kirani tace har yanzu Baki dawo ba,kuma takira numbern ki bakiyi Picking ba,

Ba shiri ta tashi daga jikin Shi tana kallanshi tace’ me kace kuma?

Yace’ me kuwa nace,ca nace ai kinyi missing mijinki ne shine kika zo kuma kar a dame ki yasa kika sa wayar a silent haka nace,

Tace’ Inna lillahi,

Wa’inna ilaihirraji’un, me ya faru?

Amma haka mukayi dakai?

Oho hakan de zamuyi kuma nace Mata,kince ke a wurin mijinki zaki kwana,

Wai Kai kam meye haka? Haka nace ma? Ya ilahi,

Kinga idan bakya San ki kwana to daga yanzu kafin ki tafi bana San musu zuwa 10 haka sai na maida ki gida kin gane?

Tace’ har 10?

Musun zakiyi?
Dasauri ta girgiza Kai, yace’ oya let’s bet,
Mika masa hannun tayi shima ya miko ita duk jikinya a sanyaye yake, daga nan suka tashi suka fita su Mus’ab suna parlour suka wuce dining Zama yayi itama ta zauna sai ga su mus’ab ne Suma sunzo sun zauna, kallanta Binaif yayi,
yace’ Madam sai nace a zuba min?

Kallanshi na irin yada haka kuma, dago hannu Shi yayi alamar bet, ba yarda ta iya ta tashi ta zuba masa itama ta zuba tasa masa lemon Kwawa ta zauna ya fara ci shima haka, mas’ud lalle ma mukuma bazaki zuba mana ba?

Binaif yace’ idan kaji haushi kayi aure,

Kallansu ya fara yi ya kalli ta ya kalle Shi ya kalli mus’ab,
Mus’ab yace’ Kai kam ai daman kanka Baya ja, sai tarin Rashin kunya da fadar magana tun dazu na gane ita ce matar,sabida yaki fada mana sunanta Yakuma ki nuna mana hotanta,

Mas’ud yace’ lalle kun kyauta dazu matar nan Nayi nayi ta fada min Amma ko uffan bata ce,
Shine yayi serving dinsu,suna cikin ci kowa yayi shiru,

Tace’ Yaushe ne interview din?

Mus’ab yace’ Sai Monday za’ayi da Monday din da ta wuce za’ayi to yanzu an daga sai coming Monday,

Tace’ wanne gari?

Mas’ud yace’ ni Lagos shikuma Abuja,

Tace’ gobe Fridaya sai a Shiga weekend kuyiwa Daddy magana don idan ba Sama maku akayi ba to ko kunci baza ku samu ba,

Mas’ud yace’ naji ma ya Saida companyn Shi na nan Kano har ma an mayar da sunan UMMU ltd.

Ajje spoon din hannunta tayi ta kalli Binaif, tace’ kaji fa har wani ya Riga mu,

Yace’ mu muka siya,

Tace’ Amma baka fada min ba?

Yanzu kinji,

Mus’ab yace’ to meyasa mai dashi Ummu,

Sai da ya cinye na Bakinsa, yace’ haka nagani a takardun naku Duka Wanda nakune haka nagani banda Wanda kowa da Shi abun,
Shiru yayi sannan yaci gaba,

Yace’ M&M Yana nufin Maryam da Muhammad, U&U kuma sunan iyayen sune, Umar shine mahaifin mamanku Uthman kuma shine Sunan mahaifin babanku, sannan takardun gaba daya rabi da kwatar dukiyarsa duk ya mallaka maku kadan ne nashi sai na matar Shi, company dake Paris na Mamanku ne shikaidai ne besan dashi ba da kuma Wanda yake Jigawa da wasu shaguna sukadai ne besan da suba,ko ayanzu idan yasan dasu to sai yasan yarda yayi ya mallakesu,

Su Duka kallansa suke tace’ taya kasan duk wannan?

Murmushi yayi yace’ time will tell,

Jinjina Kai tayi alamar ta gane, mus’ab yace’ muna bukatar Karin bayani taya hakan ta kasance?

Itace ta Basu labari in brief, ta Dora da, cewa’ za’a saki su yusseer, Sameera itace next target dimmu

Yace’ zaki sace tane?

Tace’ tarkon Chatty zata fada,

Kwalalo Ido yayi yace’ kamar ya?

Mus’ab yace’ Ada bansan dalikinki na cewa mu nemi aiki ba,Amma yanzu nasani kuma Zan yi don aikin mu ya tafi daidai,
Ya kalli mas’ud yace’ am ready are you?

Kallanshi Mas’ud yayi yace’ I Sacrifice for her,

Binaif yace’ dole sai mu Nemo Umar,

Tace’ taya Kenan?

Bakin ce lecturer kune ba? Sai munje London Kenan,

Tace’ indai haka ne basai munje ba ina da numbern niece dinshi kuma ranar da zamu dawo tare muka dawo, da su,

Yace’ to kuma sai kun Kara duba takardun nan akwai abinda zaku Kara sani sosai,

Tace’ abari komai ya lafa tukunna sai ayi daga Baya,

Mas’ud yace’ a Bari komai ya lafa ko kuma a Bari ki tari kusa da mijinki tukunna,
Kowa dariya Banda ita da ta daure fuska,

Tace’ Baku tuno sunan Maryam da aka fada ba?

Mus’ab yace’ in Banda abinki Maryam fa dayawa,Maryam Umar suna dayawa a duniya mummayi aji daya da mai irin Sunan,

Mas’ud yace’ Dade munji yarda ake fada Mata maybe mu iya tuno ta,

Shiru sukayi babu Wanda ya Kara magana sai dai Mas’ud da Mus’ab sukadai sukasan yarda sukeji aransu an Rana su da iyayensu sun zo gidan wasu sunyi bauta,an zagesu an dizga su, an masu sharri,an ma masu kazafi,an nemi a bata Kanwar su, mafi soyuwa a garesu a yanzu ita kadai ce familyn su dole suyi wani Abu,

Tashi tayi ta Shiga daki tana zuwa ta dauki Jakarta zata fito ganinsa a bakin kofa yasa ta tura baki gaba ta fara gunguni,

yace’ wakike wa haka?

Kai ta girgiza, yace’ to wa?

Tace’ da jakata nake naji ta danyi nauyi ne,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button