A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace’ ina tsaye a wurin cashier wata tazo bazata wuci kiba a tsayi sai dai da Nikaf a fuskarta itama ta tsaya tana jiran a Gama min itama a Mata zoben hannu na ya gani,
tace’ Zoben Ka yayi kyau a’ina Ka siya don Allah,

Nace’ ba siya Nayi Bani akayi,

Tace’ Zan iya sannin don Allah waya Baka?

Kinsan data min tambayar nan sai da ta kalleta?

Nace’ meyasa Zan fada maki?

Tace’ kawai ina San sanine Naga de zobem kamar na Mata,tunda yawanci irin wannan Yana zuwa da bracelet shiyasa, to bansani ba ko Kai naka yazo iri guda daya ne,

Nace’ Bani akayi,kuma itama bata akayi,

Budar bakinta sai ca tace’ irin na Ummusalma sak, sannan ta tafi ko gama biyan kudin ma batayi ba, sai da ta tafi wani tunani yazo min, nace’ tabbas itace shine fa na fara duba mai irin kalar hijabinta,

Yace’ kuma kinsan Nima nakaina nayi mamakin yarda na zage ina zabga Mata surutu Bana tantama itace,

Murmushi Ummusalma tayi,bata ce komai ba ganin sun dawo hanyar gidan Umma yasa,
tace’ lafiya?

Yana karya kwana yace’ kinyi mantuwa,

Ni babu abinda na manta fa,

Idan munje zaki gani ai,

Shiru tayi don itakam yau taga ta kanta daman ma bata zo ba, a waje yayi parking, ya zagayo ya bude Mata,
yace’ fito,

Tana kumbara Baki ta fito tare da gunguni be kulata ba ya shige suna Shiga parlour suka tarar da Hadaimai suna kallo suna cin abinci Basu fito ba sai da suka tabbatar da sun tafi sannan suka lallaba suka fito, sauran abincin da sukaci suka rage shine suke ci, ko kallan inda suke basuyi ba kamar yarda Suma Basu kalle su ba, sai da suka ce Saima,
tace’ shegiya karuwa mai kama da ifritu,
Sairai Ummusalma taji ta kasancewar itace a Baya shine a gaba, bata tanka Mata Har suka Shiga daki, yaja ya tsaya

tace’ mena manta to?

Zama yayi Akan kujera
yace’ a haka zaki tafi? Bata ganki ba sanda kika fito?

Tace’ wa?

Anty safiya,
Yafada Yana Danna wayar Shi,

tace’ to daka dawo Dani mezanyi?

Yace’ to shikenan Bari mu tafi idan tagano munyi wani Abu kinga gobe ina zuwa zata Bani ke, Bari mu tafi,

Itadai harga Allah bata gane Kan zancen sa ba, to me
Sakayi ganin ya Kai bakin kofa yasa ta bishi har zata bude itama ta fita wani Abu ya fado ranta, ai bashiri ta koma ta canza kayanta data zo dashi ta fito tana tamke fuska, ta Shiga mota dariya ce cinsa Amma ya Maza yayi murmushi kawai sun fara tafiya,

yace’ ai dakin koma da wancan kayan meye laifin su kuma?

Banza tayi dashi, Tama kawar da kanta daga gareshi,
yace’ fine, kici gaba kinsan ba ganin ki kikayi a parlourn Anty ba ko?

Yana rufe Baki
tace’ Haba Mai gida yanzu menayi? Kawai de maganar ce ban gane ba shiyasa,
Ta karashe da yake a fal fuskarta ita dai burin ta ta ganta a gida,

Shiru yayi be Kara magana har suka kusa zuwa, yaji
tace’ Ummu tana cikin damuwa sabida sace su yusseer gobe zasu koma,

Wacece hakan?

Yarinyar da suka zo gidan ku ranar nan,

Yace’ ohh nagene, me dinsu ce?

Kawar suce,

Waya fada maki halinda ta Shiga,

Wanda muke nema,nafada maka daman niece dinshi ce, kuma baya ga haka ma gashi an barsu abubuwa dayawa a school, na zalince su,

Bakomai, Insha Allah komai zai daidai,kin ansa numbern Shi?

Ehh ya Bani,

Saida yaje gidan mai vadi ya bude masu suka Shiga yayi parkin,
yace’ Bani numbern,
Bashi tayi yasa a wayar Shi, sai anan yaga miss called din ta, beyi magana suka fito tare da daukan kayan da ya siyo sukayi part din Anty safiya,
Dukan su suna zaune a parlourn 10:30 babu Wanda yayi bacci har Ummi suna kallan king of heart Ahmad ma yana nan sun kwalalawa tv Ido basa su seen daya ya wuce su idan ba talla aka tafi ba, Da sallama suka shigo amsawa sukayi Amma idansu nakan kallo,
Saida ta zauna ta kalle su yarda kowa ya kwalalo Ido yana kallan yarda abin zai kasance inda roushini tayi accident Shabnap ta dauko ta Amma ba a Nuno fuskar ba shima Binaif tsayawa yayi daga tsaye Yana kallo kawai ta canza channel zuwa sofiya the first, su Duka juyowa sukayi Nafisa ce ta fara magana,cikin marairaice wa,

tace’ Haba Anty don Allah ki bayar mana ankusa gamawa saura talla biyu agama Dan Allah please kinji ?

Anty safiya ta fito tace’ a,a kundawo Amma de yanzu nan don yanzu na tashi naje nayi waya,wai kar in zauna anan basa sun abinda ake fada sunayin missing word,

Ummusalma tace’ yanzu nan nadawo Nayi sallama babu Wanda ya amsa shine na canza,

Binaif shima zuwa yayi ya zauna kusa da ita,
yace’ har wani yanzu kika zo ca zaki ce yanzu makazo nida mijina,

Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un Sam Baya kunyat fadar wannan kalma ita kuwa nauyi take Mata abakin wai mijinta,

Anty safiya girgiza Kai kawai tayi,
tace’ can gidan kikaje ne?

Yace’ a,a haduwa mukayi da ita a traffic suna cikin adaidaita sahu ita da kawarta suna Rabin IV shine fa Mata waya suka dawo mota ta nake kaisu shine na kaita gidan su kawar tasu da suka Gama kuma sai yanzu tace nazo na maida ta gida,

Anty safiya ta yarda 100% da zance shi,ita kuwa Ummusalma sake Baki tayi tana kallan ikon Allah wannan zubit ma’aruf din ai,mintsinta yayi tare da Mata signal din tadena kallan Shi,

Nafisa tace’ dan Allah ki mayar mana muga Wacece, kinji?

Shine ya dauki remote din ya makiwa Nafisa yace’ gashi yi kallan ki, tazo ta takura maku haka akeyi?

Ummi da ta kwalala Ido tana kallan cartoon aikuwa tasa kukan baza’a canza ba,
Yace’ lala aikuwa Nafisa sai dai kiyi hakuri baza’a canza ba, mayar da Aljanunan,

Nafisa tsabar takaici harda su kwalla,tashi ma tayi ta bar parlourn ta Shiga daki,

Anty safiya tace’kin gamu da aiki kuwa na tsani wannan kallan da Baya karewa, Abu a yi tayi de bazai kare ba?

Itama Ummusalma tashi tayi ta bar wurin sai anan ya gaida Anty safiya sannan sukayi wata hiran yace gobe da yamma zai zo ya dauketa su fita.

Kwanciyarta Kenan taji wayanta na vibrating daukowa tayi taga Yaya dagawa tayi suka gaisa sannan kowa yayi shiru sai can,
yace’ Kinyi aure ne?

Waya fada ma?

Shine ya kirani yanzu yana so mu hadu gobe,

Ok, ina ummu?

Tana Adamawa Nima yau nazo rabon zamu hadu ne,

Tun yaushe Kenan?

Tun ranar da kika taho daga can,Ranar muma mukaje,

Jinjina Kai kawai tayi, kamar Yana ganin ta,

Yace’ Saida safe nakirane nafada maki ne daman,

Ok shikenan,Saida safe,

????????????????????????????????

Kun Shirya Duka kayan naku?

Yaseer yace’ mun shirya,Amma oga ina zaka kaimu haka da safe kaga fa 8 ma batayi ba,

Oga yace’ Zan canza maku wurin zamane bazai iyuba ace kuna zaune wuri guda ba,

Sabida haka ku kwashe kaf kayanku har ps dinku idan kunaso,

Yusuf daman beyi magana ba kume beda niyyan yin magana daki kawai ya Shiga ya dauko jakar su wacce suka hada kayan su tun jiya da aka fada masu,

Shima yaseer wurin TV yayi ya hada ps din yasata a kwali yasa a cikin Leda ya rike, suka nufo kofar parlour ji sukayi an rufe su masu Ido da bakin Abu, an karbi kayan hannun su, nasuyi musu ba suka bisu ba, ana masu jagora, motar daf take da kofar gidan suna fita aka sasu a cikin sannan suka dauki hanya Basu San ina ake tafiya ba sai da aka bude musu fuska suka gansu a airport an San sa musu fuskar wasu mutene sannan suka fito kowa,harda ticket dinsu suna zuwa basu wani jimaba jirgi ya daga har suka isa inda zasuje su de Ido ne kawai nasu,

Tana kwance kamar kullum yau hoto take gani su uku a ita tsakiya sanda sukayi birthday dinta babu Wanda yazo sai su kadai Anty ma ca tace baza tayi ba shine su suka Kira mai hoto da kudin su ma suka sai cake din lemuka kuma a gida suka kwasa dukan su suna dariya sun goga cake a fuskar su, tayi nisa cikin tunanin ta Inna ta shig, cikin fada,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button