A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ ke! Fita waje bazan iya ba yau zaki koma gidan Ubanki ina dalili haka?
Bata tanka Mata ba don tasan kwanan zancen tagaji da biyota da abinci har daki shikuma Baffa kullum sai yace a kawo Mata shiyasa yau tazo da wannan tijarar harda zagin uba, tashi tayi ko Dan kwali babu ta fita tsakar gidan ta zauna a kusa da Baffa ta fara cin kosan badan Yana Mata dadi ba sai kawai Dan jarabar Inna data lura kullum karowa take, dayan da ta dauka a hannun ta shine bata cinye ba,kamar tana cin magana me da Karen daci haka takejin sa a hankali ko magana ne ma ai zakayi sauri Ka tauna haka take ci, sallama akayi tare da shigowa ko Suma tayi ta farka wannan muryan bazata taba bace Mata ba, daga Kan da zatayi kuwa tayi tozali dasu wani wawan ihu ta daka ta Mike a guje ta rungume su,Suma rungume ta sukayi sai suka saki kuka a tare .(????)
????????????????????????????????
Mama ce zaune a parlour tana kallo kamar ma babu abinda ya faru da ita hankalin ta nakan kallanta, Sameera ta zo tace’ Mama ina kwana?
Da fara’a ta amsa Mata suka gaisa,
Mama tace’ lafiya naganki a shirye haka? Ina zaki kuma?
Sameera tace’ a,a mama zani gidan su kawata tun jiya nace maki zani fah,
Mama tace’ Sameera Bana San fini fah,ki Rasa yaushe zaki je gidan su kawar sai da wuri haka? Ina laifin ki Bari sai da yamma sai kije,
Sameera ta turo Baki gaba tace’ Haba mama tun jiya fa na fada maki zani, kuma na fada Mata ganin nan kinsan daga nan Zan wuce gidan Hajiya Yaya fah datazo ta, kuma yau juma’a kinsan de gidanta yafi dadi da yamma kowa yazo Mata ayi ta hira,
Mama tace’ da wannan kuma,to Kide kiyaye Bana San fitina banasan tarkace tarkace damma kuma Naga yarinyar tana zuwa Amma yawon ki ya isheni haka, tam kuma kidawo da wuri bazan Kara Bari Bama kike kwana a wani wurin,
Sameera tace’ Insha Allah mama Zan dawo, ke yau bazaki fita ba?
Jiya naje babu inda zani, Allah ya kiyaye,
Tace’ to mama abani Dan kudi,
jeki dauka a daki a cikin jakata ki dau ki dubu daya ta isheki,
Komawa tayi tadauka takara yiwa mama sallama ta wuce, tana fita ta kira driver ta fada masa inda zai kaita gidan su kawarta bikinta za’ayi shiyasa zasu fara Shirya abubuwa tun yanzu saura sati biyu ya rage bata wani jimaba ta Kira saurayinta suka tafi shan iska sukayi ta yawon su a gari daga nan suje nan daga karshe sukaje park lokacin har yamma tayi yara kowa sai wasan sa yake,
Sai da sukayi mai isar su babu Wanda ya tanka masu har su Anty da sukaji ihunta daga gidan su Wanda yake Jin na su Inna suka ce baza su koma ba ana zasu zauna, suma sun zo suna kallan ikon Allah,
Taja hannun su ta zaunar ta Shiga tsakiyar su, Koko da kosan ta kalla,
tace’ Inna yanzu fisabilillahi waye ya zubar da wannan abun? Sai kace marar hankali,
Takaici da haushi Inna taji takasa Mata magana Baffa
yace’ idan Banda abinki mai sunan manya ai ke kika zubar kece kiyi wannan ta’asar kina ihun ganin yaran Gobe,
Sude kallanta kawai suke bako kiftawa yarda da ta rame tayi duhu, kanta tun kitson da suka Santa dashine shine de babu canji,
Anty tace’ ai kece marar hankalin mutum ayi kamar mai aljanu,kunga ki tashi muje kuci abinci kamar nasani yau favourite dinku nayi, Maza ku tashi mu tafi,
Ummu tace’inaa ai mama wallahi Nima sai naje,yunwa nakeji nima,
Babu Wanda ya tanka mata suka tashi suka fita har sunje zaure yusuf,
yace’ haka zaki fita?
Sosa keya tayi tace’ ku jirani ganin zuwa,kar ku tafi, ja sukayi suka jiranta da gudu ta koma ta dauko hijabin Inna ta sa a zauren ma ta karasa sawa, a parlour suka zauna Anty ta kawo masu abinci Suma daman Basu ciba su Inna ne de masu ci da wuri kuma kullum Koko da kosai sai kace Ibada, Suma acan favourite din su ake Basu duk wani Abu ana musu, sosai suka zage suka ci abinci har itama Ummun abinda bata taba yi ba Kenan tunda suka tafi sai yau da suka dawo aikuwa tafi kowa haka sai ci take zuba surutu ita da yaseer kamar babu abinda ya faru Baba kawai Jin su yake tare da nazarin yaran lalle akwai laka Mai karfi a tsakanin su, Saida suka ci suka gyatse sannan Anty
tace’ Yusuf ya akayi hakan ta faru?
Yusuf ne ya Basu labrin yarda komai ya kasance har zuwan su Adamawa,
Yaseer yace’ a airport muka neme Shi Muka Rasa sai mai taxi ne yazo yace ance ya dauke mu ya kaimu wani wurin dayake bamu taba zuwa Adamawa a jirgi ba yasa bamu San ita bace sai da aka kawo mo kofar gidan nan aka ajje mana kayanmu ya bamu kudi yace inji Wanda ya kawo mu yace amu,
Anty tace’Yanzu baza ku iya gane shiba?
Yusuf yace’ Antu babu wani sauran bincike tunda mun dawo lafiya shikenan ai,
Yaseer yace’ kwarai kuwa ai Bama za’ayi ba gaskiya kar ma Abie( Baban Ummu) yasan da wannan zancen,
Baba yace’ kamar yafa? A sace ku kuma kuce kar asan da wani zance zancen banza Kai,
Ummu tace’ kufa bayin Allahn nan kunfiye gardama,tunda sunce yafe a barshi ai shikenan, agarin bincike nan a wannan Karon na tabbata Ida aka sace su sai dai wasu ba suba nikuwa mutuwa zanyi daman,
Kowa kuwa yayi na’am da maganar ta karma aje garin nema gyara akara batawa, ahaka suka ci da hiran su Itadai Anty Ummu ta bata mamaki bana wasa ba ace daga dawowar su har ta ware haka?
Suna nan Basu suka tashi ba Saida suka ji Kiran sallah, Ummu tace’ laaa yau nice wai banyi wanka ba har aka Kira sallah,
Anty tace’ kijimu da ‘ya da wanka kike?
Yaseer yace’ haba shiyasa tunda nazo naji wani bashi bashi haka Ashe Ashe de,
Yusuf yace’ Nima naji Ashe de da walakin gyada a miya,
Remote din kusa da ita ta dauka zata wurga masu,
Umma tace’ a,a ajje min bazaki lalata min ba kunsa Saba bata na gidan uwarki ajje min,
Tura Baki tayi, tace’ daman ni an tsaneni a gidan nan haka kawa suke tsokana ta harda cewa wai da walakin goro a miya,
Yusuf yace’ a,a gyada a miya fa nace,
Yaseer yace’ yaushe kika gyara kuma?
Dariya tayi tace’ ina ruwanku kuma da yaushe na gyara ba fa nasan sa Ido,
Baba yace’ ku tashi mu tafi masallaci kar a Shiga muna nan, dukan su tashi sukayi kowa yayi nasa wuri Baba ya nuna masu wani daki suka Shiga, ita kuma ta shiga dakin Anty wanka tashiga tayi ta fito bata da Kaya daman kayan Kala biyu ne Basu San zasu jima haka ba, da sukaje siyo kayan ma ca tace baza ta jeba, babu Wanda yabi ta kanta kuwa sukayi tafiyar su, akwatin Anty ta buda luckily kuwa taga Kaya size dinta harda inner wears dogayen riguna guda uku kowanne da mayafinsu sai atampa guda hudu da takalimi Bama tabi ba’asi ba ta yanke hukunci nata ne, takuwa sa tayi sallah ta fito har lokacin Basu dawo ba kallo takunna ta fara yi yaushe rabon da tayi kallo yau wani shadi takeji ita kanta ta yarda soyayyar su daga Allah ne ahaka suka dawo suka sameta tare da kayan su suka shigo suka Kai daki sannan suka dawo suka zauna,
Ummu tace’ ku kunga yarda kuka rame kuwa? Yarda kuka San tsinke haka kukayi,kamar na ture tsinke da Dan tsaya na guda daya haka kuka koma,
Yaseer yace’ lalle yarinyar ke Baki ga kanki ba ?
Yusuf yace’ kyaleta ita bacin Rama harda Baki,bakin kuwa irin wani shuni shuni takeyi,
Wallahi kun rena min hankali ma kunsan de na fiku fari tunda kufa farin Rama kukayi inaga ma ba jini ajikin ku,
Shiru sukayi babu Wanda yayi magana sun Rasa meza suce Mata ne kawai,
yusuf yace’ a kaima Wrestling ko kuma jikin wata ya fada Mata,