A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaskiya wani yayi formatting ina aka taba ganin wrestling da Rana tsaka haka?

Yaseer yace’ to a canza mana wannan aljanun akai mana Bollywood,

Tace’ yawwa wannan kuwa,

Bollywood ta Kai sai dai Fan akeyi sukuma su dukan su sun tsani film din aikuwa,

tace’ wowww my best film ever,
Harda Dan tsallenta,

Yusuf yace’ kinawa Allah ki canza mana kinsan munsan bakya so ko?

Tace’ ohh sorry lokacin da aka sace ku shine fa nayi ta kalla Nayi ta kalla shine naji insa Shi ai,

Anty da ta shigo tace’ ke wai dan Allah ko kunyar Karya bakya ji ne?

Yaseer yace’ yawwa Anty fada Mata de nikuwa kinga ba ruwan ai,

Anty tace’ da ban San asalin barbela ba sai na..

Ummu ce ta katseta tace’ sai kice daga Ghana tazo ta ko?

Dariya yusuf da yaseer sukayi Anty kuwa tashi tayi ta wuce kitchen bazata iya wannan kayan abun haushin ba,

Yusuf yace’ kasan yaseer yanayi missing moment din nan dayawa?

Yaseer yace’ ai bros ni Zan fada maka,su oo ana so ayi haua proverbs ba’a iya ba,

Yusuf yace’ ahakan har littafin su aka suyo aka Hana mu kar mugani,

Yaseer yace’ ehh mana kaidai Bari idan ma mutum zai koma English dinshi ya koma Dan yafi masa,

Yusuf yace’ sosai ma karma muje a kwafasa mana idan munje wani waje,

Tana jinsu tayi banza dasu ta mayar da cartoon dinta tacigaba da kallo bata tanka masu ba,tasan zata fanshe ko bakwai ai ana tare, har aka Kira la’asar sunan daga wannan hiran su dauko Wanana har lokacin Baba bedawo ba itama Umma ta tafi gidan su sai rage sai su kadai ne sai Anty, bayan sundawo sannan sukaci abinci,

Anty tace’ waya Baki kayan jikinki?

Sosai Kai tayi tace’ dauka Nayi Naga kamar nawa shine yasa,

Anty tace’ baca kikace bazaki ba?

To mama kiyi hakuri kinji,? Ki Bani yanzu na siyo kinga drivers Dina sun dawo,
Ta karashe da dariya a fuskarta,

Anty tace’ kudin Bana banza bane bazan bayar ba aje a siyo min kayan shirme kizo ke ba kwalliya ba bakomai ba da tarin ajiya,

Haba Mama kayan Amfani Zan siyo fa, idan na hauka na siyo kawai ki bayar kinji my sweetheart mom,

Anty tace’ naji Zan Baki,
Tace Yusuf idan ta siyo kayan shirme karka biya kudin Kai zanbawa kuma sai ku siyo abinda Baku da Shi,

Tura Baki tayi tace’ haba Anty kibawa Yaseer mana yaza’ayi ki bawa yusuf,

Tace’ daga ke har yaseer banga me hankali ba shiyasa,

Sun Shaka shiyasa ma Basu tanka ba.

✨✨✨✨✨✨✨

Su Duka suna zaune a park wurin kujerun hutawa sai table a tsakiyar su ita tana Shan ice cream gefenta Binaif ne sai kujeran dake facing dinsu su uku ne akai Mus’ab da Mas’ud sai Uncle bayan sun Gama bashi labari da abinda zasuyi shima ya jinjinawa lamarin beyi tunanin abun zai zo cikin sauki ba haka a yanzu da yake Jin ‘yan uwansa a jikin sa damuwar Shi ta raguwa zai iya cewa beda damuwa ko daya a halin yanzu kuma ya yarda ya gamsu Yan uwansa ne koba ma Yan uwansa bane zai karbe su hannu bibbiyo ko matsanan ciyar kamar da suke shida Ummusalma da Mus’ab, sai yanzu yake ganin kamar su sosai da sosai, zai tambayi kuma Bab yaji shaidar wanne asibiti ce aka cince Shi a hannun sa, indai akwai number to akwa shaida, daga nan kuma sukaci gaba da tattauna yarda Abu zai tafi.

Ummusalma ce ta hango wata kusa da daga nesa kadan ita da wani saurayi harda su tafawa kuma suna hira suna dariya, kamar ancewa yarinyar ta juyo kuwa, afili Ummusalma ta furta”‘ Sameera???

Kallanta sukayi sukace lafiya,
Nuna musu ita tayi,

Mas’ud yace’ itace wacce zanyi dating? Naji kince Sameera?
Daga masa Kai tayi,

yace’ yanzu wannan abar zanyi dating? Gaskiya bazan iya ba,

Tace’ dole kuwa kayi,idan akace mus’ab ne zaiyi to zata kamar da muke dashi,

Yace’ to Abu mai sauki kisa mijinki Yayi kawai,

Kara tamke fuska tayi,
tace’ Kai nace kuma Kai zakayi nagama magana,

Dariya ce ta ciwo Mas’ud,
yace’ ohh jealousy, ko?

Mus’ab yace’ to kar tayi? Abinda ake shi akewa kishi ai,

Murmushi kawai uncle yayi wannan yara bade surutu ba Shi haka yake beda magana sosai Ummu ce ma take sa Shi magana,

Shima binaif murmushi kawai yayi, na irin ana kishi nan nawa,

Ummusalma tace’ Chatty ina so kadawo da Sameera yarda take a da,nasan hakkina ne zai bisu Akan ‘yar su Amma ni Bana so ina ganin Sameera tamkar su yusseer ne,ina kaunar Sameera kamar yarda nake kaunar su bana San wani Abu ya faru da ita, a yanzu tana zuwa duk wani night event tana zuwa duk wani party koba ba a garin nan ba, Bana so ta fara kwana a waje idan ba gida ba,dukda wani lokacin tana kwana a gidan su kawayenta wani lokacin kuma a gida take kwana to Bana San tafara kwana a wani wurin, gwara komai ya tsaya daga haka, help me please,

Gaba dayansu kallan ga suke what’s kind of heart she’s have,she have a pure heart, kallansa ya Kai wurin Sameera yaga yanzu ma a wuri daya suke dayake a nesa yake bega wani gap dake tsakanin suba,
Rufe Ido yayi ya jingina zuciyar sa bugawa take be taba zuwa yacewa wata Yana Santa Bata duk iskancinsa Akan Maza yake karewa koda kwa tsokana ce da hausa lokacin Yana Spain sanda suke karatu,

Tace’ ka dauke Sameera kasa sunana Ka dauke kammar ta kasa kamata Ka dauki matsayin nice ita, zaka so ka ganni ahaka? Ko kuma zaka so kaga ina yawon zuwa club,party gari da gari? Zuwa night dinner? Zaka so na kwana a wani wurin koda kuwa gidan wasune ba namu ba?
Yanzu kayi imaging nice waccar a zaune ya zakaji? Please Ka taimaka Mata badanni ba Dan Allah zakayi baya ga haka zata taimaka mana sosai idan ta kware maka zata taimaka mana sannin yau Yana ina,gobe Yana ina,jibi Ina zaije?

Tace’ nasan cewan it is not always easy to gather the courage to speak to a woman. But chances to make a good impression are often limited,so saying the right thing from first moment is important. I want you yanzu kaje kayi Mata magana tuna Allah yasa mum hadu kaji? Please,

A hankali ya bude idonsa da yayi ja, ji yayi bazai iya barinta ba kamr yarda tace yayi imaging itace hakan yayi, kallan mus’ab yayi mus’ab ya daga masa kai ya kalli uncle,

Uncle yace’ babu abinda yafi karfin Dan Adam sai Wanda yace bazai iya ba I want to you to put it on your mind cewan u can do it,u can do it, u can don’t ever Star saying u can’t I know u can, Ummusalma my daughter ko bata iya Abu ba tana gwadawa, Ummusalma kanwata kuwa she’s heroine,bare kuma Kai Namiji,

Kallan Binaif yayi,wani murmushi yayi masa, yace’ bansan me wannan me wannan chatty din ba yake so nace, me zance,
Shiru yayi alamar tunanin, yace’ bb naganni nan ko? Umm wallahi Zan iya komai amma kaga fav bro babu abinda zai iya ya cika tsorom tsiya kamar farar kura,
Murmushi yayi sosai yace’ is now a time that u will show me u can do it, shine kuma Zan yarda oya move on,

Numfashi ya ajje ya tattaro duk maganar su, sannan,
yace’ me zanje nace Mata yanzu?

Gaba dayansu Ido suka zuba Mata,
tace’ a,a lafiya kufa ya tambaya kune maza yaza’ayi ki zuba min Ido,?

Mus’ab yace’ ai tunda kikaga haka to babu Wanda ya taba zuwa wurin budurwa,

Tace’ ni ai na taba zuwa wurin saurayi,
Da zakuce min wani Abu,

Binaif yace’ kifada komai b, yanzu de me zaice,

Tace’ kaje kawai,

Yace’ naje na masu me wai? Nace me? Nace’ mai da yaji kome,

Tace’ idan kaje kayi musu sallama kar kad hi ko Hello Ka kagane?

Yace’ sosai ma sai me kuma,

Sai Mika masa hannun ku gaisa, Ka nuna Ka Santa a wani wurin haka,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button