A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yace’ gaskiya bangane wannan ba, a,ina nasanta?
Daure fuskayi tace’ gaskiya Kai kana da matsala wallahi ahaka Zan koya ma ?
Uncle yace’ idan fada zakuyi bazaku tsaya yi abinda ya kamata lokaci fa jiran ku zaiyi ba,munan za’ayi magriba su tashi muma mu tashi,
Yace’ to ai itace bani ba,
Tace’ Kaine de,
Mus’ab yace’ kunga wannan haka suke basa jituwa,
Tace’ kaje kuma karyi masu surutu Ka ja ajinka,Banda rawar Kai da kafa,Ka zauna a kusa da ita kaji ai? Sannan kace Ka santa Ka taba ganin ta a Kaduna da taje partyn wani saurayin ta,
Samarin mata Har nawa e haka?
Kai zaka Nemo wannan kuma, yanzu tashi Ka tafi,
Tashi yayi a hankali Yana tafiya yana juyowa Yana kallansu kamar yarda suke kallanshi sai ya tafi sai ya dawo sai ya tafi dawo idan zai dawo harda gudu yake hadawa a na karshe ne yadawo ya,
tace’ danzo na fada maka wani Abu,
Zuwa yayi harda su sunkuya daidai kunnasa, kunnan ta kama,
tace’ karka manta wallahi,taam,
Ta dauki lemo ta Mika masa tace’ ungo wannan Ka rike a hannun Ka kar Ka dawo har sai sun lura ma damu,
Karba yayi yayi gaba sai da yakusa zuwaya juyo alamar zai dawo ai gaba dayansu rufdugu suka masa na Harare ba shiri ya juya ya bude lemon sa yaje wurin, zuciyar sa bugawa take shidai besan ya zaice,yama Mata abinda tace masa yace sallamar kadai ya rike,
Cikin wata irin voice mai cike da sanyi da fargaba sai dai bazaka ce yana cikin fargaba ba,
yace’ Assalamu Alaikum……..
Comments ✍️✍️✍️✍️✍️
By: Hijjart
Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
32
Kawo yanzu abubu sun tafi da yawa zuwan su Ummusalma Bauchi da kuma samun aikin su Mas’ud, komawa makarantar su yusseer Dade sauran Abubuwa, a bangaren Uncle kuma ba sauki dan an tabbatar da zuciyar sa ce ahalinda ake ciki ma ya Shiga comma, du bayan kwana biyu suke zuwa gano Shi Baba da Umma sai Ismail da yaje shima ya ganoshi, kuma baza’a tabbatar da aikin da aka masa yayi ko beyi ba har sai sanda ya farfado sai dai cigaban da aka samu karayar ce kawai take warkewa sabida ba’a taba wa bare a taka,
A bangaren su Abba kuwa ya Sami lawyern Shi ya masa bayani ya kuma biya Shi kudi sunyi duk abinda ya dace,gashi company sai wani cigaba suke samu daga fara aikin su Dan kayan su yana da kyau da kuma inganci Ada ana zuwa 7-7 Amma zuwa Shi ya maida zuwa 8-6 hakan yayiwa ma'aikatan daidai sannan kuma salary din za'ake Basu according to yarda aka samu riba,tunda yau da samu gobe akasin haka,kosa yayi na'am da wannan zancen kuma sun yarda sun gamsu, be yarda da kowa ba bare wani PA shikadai yake gudanar da kudurin Shi masu shawarar Shi su Mus'ab ne sabida beda wani aboki ko daya kuma duk sa'anin Mata ne shiryawa.
Su yusseer kuma sunyi neman numbern ta Amma bata Shiga sunje har unguwar data fada masu Amma shiru har tambaya suke da nuna hotan ta a unguwar amma babu Wanda ya Santa a haka suka hakura suka dena nemanta,
A yau takama alhamis ranar da za’ayi kamu,kamun su iya Mata ne Maza basa zuwa iya Mata ne sai kuma ‘yan yaran da baza’a Rasa ba,
Ummusalma da sa’anni ta Wanda duk sunyi aure sai Wanda suke karatu ne basuyi ba, kuma dayake gidan Umma na kauye Family house aka mayar Shi shiyasa kowa yazo jar Baba Usman shima yazo da iyalin Banda Hajiya da Anty har ‘ya’yan su kuwa babu Wanda yazo acewar su suna bikinne Suma ai, suna zaune a babban parlourn gidan anyi Mata doka an Mata kwalliya irin tasu ta amaren can tasa kayan Fulani, sun sata a tsakiya wannan nayi wannan nayi, Umma itama tana yi don harda ita, itace ma ke Basu labarin auren da, suna dariya daga nan sai a daura zance idan anyi anyi sai taci gaba, ana cikin haka har kazo Kan matsalar idan miji yamaka laifi kar Ka horashi da yunwa kode da wani Abu,
Umma tace’ ku tsaya kuji,
Kowa shiru yayi, umma tace’ Sanda Malam Yana da Rai idan yamin laifi sai nayi abincin da Baya so, Baya san tuwon dawa sannan Baya San asa nama a cikin miya ko asa wake ba’a daka ba, Baya San wannan, nikuwa idan ya min laifi sai ya kawo namansa na tashi Nayi miyata nasa nama a cikin miyar na kawo wake nasaka a ciki, sannan Nayi Tuwon dawa abuna,
Shiru tayi tace’ Allah sarki bawan Allah haka zai kwasu yunwar sa daga kasuwa wani lokacin ma hae cikin Bauchi yake zuwa ya dawo Amma hakan idan na kawo Yana murnar zaici sai yaga abin da Baya so,haka zai zauna sai ya tsince wanken tsa ya dauke Naman sannan yaci, nikuwa ina kallansa ko magana Banayi,
Tace’ Kai Allah ya jikan malam,
Ameen duka suka amsa,sai dai Dan hawayen da suka ga tayi namma fa aka fara tsokanar tuno da sahibi, shiru tayi ta kyale su sai can,
tace’ Sanda ina ‘yam Mata bana daukan reni duk kauyen nan an sanni Bana wasa gani jarababbiya shiyasa kowa yake gudun masifata naki auruwa nikwa ko a jikina sai Malam,Malam Yana da hakuri sosai, Allah ya Baku ‘ya’ya masu hakurin Shi,
Suka amsa da Ameen, Kiran wayar Ummusalma akayi yasa suka bata dayake sunyi hotona shine ake tura Mata, karba tayi ta tashi ta fita daga parlourn shima de tsakar gidan da mutane yasa tayi bayan parlour lokacin har ta katse, Kira tayi, daga can bangaren akace,” tazo gidan, kuma naji suna maganar karshen wata yazo,
Tace’ wanne kalar Kaya ne a jikinta?
Lashi ne sai Hijabi kalar ruwan madara sai nikaf,hijabin ba dogo bane, iya Ka gwiwa ne,
To idan ta fito a kirani,
Shikenan Insha Allah,
Bayan sun kashe tayi message sannan ta,
tace’ kuyi Maza kuje ku inda na tura maka da address din zakuga wata Mata ta fito daga gidan tana sanye da lace sai Hijabi milk da Nikaf kuyi Maza kar ta fito,
Bata jira amsar su ba ta kashe wayarta, A fili ta furta Allah yasa hassashena gaskiya, Ya Allah help me,
Koda ta dawo sai gani tayi an Kara cika a parlourn,sulalewa tayi ta Shiga daki,shima dam yake da jama’a ita tarasa gane wannan taro ko ina kayi da jama’a,duba sauran dakunan tayi dake cikin parlourn suma duk hakane, fitowa tayi ta bi wani lungu sai taga kofa ‘yar karama, aikuwa ta Shiga taga parlour da kofa guda biyu acikin sai wata kofar kuma babba ce da’alama ta waje ce, sai ta Shiga ma ta tuna zuna Zama a ciki dakin Umma ne, aikuwa ta fada dakin da suke zuwa su kwanta mafi lokuta da rana, shine mai ac haka Umma zata a su kunna solar idan na nepa suyi barcin su daman ba aikin da suke yi,
Dakin ma data Shiga duhu hasken kadan ne Wanda ba’a Rasa ba sabida safe safe ne Rana Rana ba yamma ba an kulle ko ina an saki labilaye an kunna ac ga kamshin air freshener dake tashi a dakin, aikuwa ta cire abinda aka murde Shi aka daura Mata da mayafin, ta ware zanen Saman kayan bata da daure Shi ba kawai ta barshi,ta hau gado tayi kwanciyar ta bata jima ba bacci ya dauke sabida kamshin dakin da dadin sa ya Mata dadi.
Acikin gida ana ta neman Amarta kowa yana so ya ganta kafin a yamma a fita kamu Amma ba’a ganta ba,
Wata daga cikin yammatan tace’ to aje a duba dakin da Daddy mana da muke Zama ko taje can,
Umma tace’ ke kam Indo Sam bakya rabuwa da shirme mezataje tayi kuma bacin Maza yau sunzo mijinta ma yau yazo Shi,da tun jiya zaizo bezo ba da na kirashi jiyan namasa Karan dangin shine yau da sassafe yazo min gida, ita tasan inda ta tafi,daman na lura da ita Sam bata da San mutane sai wani nokewa take wai ita kunya, sai kace tsohuwar muna fikar da tayi sata ana nemanta,
Wata tace’ Kai Umma yanzu idan tayi dariya ace bata da kunya,yanzu ma da take Dan nokewar tana nuna kunyarta sai ace Mata munafika? A munafikan wacce tayi sata, Haba Umma mana,
Wata tace’ ni wallahi Sam tunda tazo banga wani aibun taba, bata da musu Sam wallahi,
Umma tace’ to sai ku titsiye ni,tunda Hajju ta dawo da Rai( mahaifiyar ta) yo idan ba hajju ba waye zai maida min magana iye?
Wadanda sukayi magana shiru sukayi Basu Kara ba, wata tace’ hmmmm rashin musunta na banza a Bari ta Shiga daga ciki mana mugani,ai yanzu biyayya zata keyi,
Wata kuma,ai ni wallahi banyarda da ita ba a London fa akace tayi karatu kuma tazo ta har kauye ta zauna tayi sati wajen biyu ma a kauye? Haba de ai da sake wani abun kawai suke nema,