A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un, wanne asibiti aka kaisu?
AAA hospital, ne asibitin Shine,
Yace’ gani nan zuwa kuwa yanzu nan, ya kashe wayar,

Dukan su Ido suka zuba masa,suna San Jin ba’asi,
Yace’ wai Abokina ne yayi accident Wanda zai so muyi magana dashi yanzu Yana asibiti, Zan Kira yarona sai ya wuce mu hadu acan din,kun gane?

Umma tace’ Allah ya kiyaye,
Yana sauri ma be amsa addu’ahr ba, sai dai duk jikin su yayi sanyi qalau a haka suka ci abincin su tunda ba zai zo ba asibiti zai wuce…

????????????????????????????????

Sameera ce a zaune a parlour tana kallo babu abinda take tunawa sai abinda ya faru jiya waye Shi? Duk iya tunanin ta takasa samu waye Shi kaf samarinta idan ta hada babu mai kamar shi, bata taba yin mai kalar Saba ma, ya zatayi? Gashi ko sunansa be fada ba, tana zuwa Kaduna suna party amma takasa Nemo Shi, ajiyar zuciya ta sauke,ga kuma wannan yace zata gani mezata gani? Anya ba tarko aka Dana Mata ba kuwa? An rabata da saurayinta daman de bawani San Shi take ba, tanda Wanda take so tana ganin shine daidai da rayuwar ta, shine Wanda zata tsayar a mijin aure nan gaba, ga kuma ya zo, ya zatayi yanzu?

Mamace ta fito da tun daki take kwala Mata Kira Amma a banza tajiba sai da ta fito ta daka Mata tsawa Sannan ta dawo hayyacinta,

Mama tace’ me kike da ina kiranki Baki ba ?

Allah ya taimaketa American film din da ake mai fada ne shiyasa,

Tace’ mama kallo nake, banjiba ne yi hakuri,

Kallo ta watsa Mata tace’ wuce kije ki gyara dakinki da nawa ki wanke toilet tas jiya bakiyi ba yau kuma dole kiyi wuce, banasan kazanta a jima kuma kizo ki daura abinci,

Batayi magana ba ta wuce ita dai kawai a kyaleta tayi tuna Wannan bawan Allahn, sai data Gama tas ta sauko ta daura abinci lokacin 11 da ‘yan mintuna ta daura abinci ta kafin daya ta gama abinda ta girka ta jera a dining, sannan tayi wanka ta kwanta wayarta taji tana Kara dauka tayi ganin number yasa ta ajjewa bata daga ba, sai da akayi four miss called ana biyar din ta daga kuma tayi shiru, daga can,

yace’ Assalamu Alaikum,

Tace’ Hello?

Bakya amsa sallama?

Bada muwar Ka bace,

Nasani sosai Amma kuma ai zaki samu lada, ko bakya so?

Shiru tayi bata tanka masa ba,
Yace’ Baki San Hadithin manzan Allah SAW ba? Dayake cewa a bazaku Shiga Aljnnaba har sai kunyi Imani baza kuyi Imani ba har sai kunso junan ku,
Yake cewa shin bazan fada maku wani Abu ba? Idan kuka aika tashi zaku so junanku, sannan yace…

Ta katse Shi da cewa’ Afshus salama bainkhum, kaga nasan wannan sai me kuma? Mema ya kawo wannan? Kawai Dan ban amsa ba? Ina ruwank Dani?

Yace’ subhanallah ba kawai bane kinyi hasara babba samun lada fah idan kikayi ko kika amsa, meyasa zaki ce haka? Gashi kince kinsani, tunda kinsani sai kike aikatawa kinji?

Wai Kai Dan Allah waye kazo Ka takura min me kake Dani ne wai?

Yace’ am sorry bansan Zan takura maki ba ai, da kin amsa min sallama ta da duk haka bata faru ba, abinda nake so dake shine kiyi hankali da duniya, duniya makaranta ce.
Ki huta lafiya,

Ya kashe wayar bin wayar tayi da kallo tana tunanin waye Wannan din? Ya ilahi.

????????????????

A asibiti kuwa Har yamma Baba be dawo ba shida uncle sai yanzu da ya Kira su yace’ su kawo abinci su Dukan su suzo su duba Shi su koma, hakan kwa akayi Yusuf ne ya jawo su Umma na nuna masa hanya har suka iso asibitin, sude jikin su yayi sanyi tun wayar dasuke Kira ba’a daga wa sai da Baba ya kirasu, suna zuwa yazo ya masu jagora suka fito da kulan abinci suka nufa dakin marar lafiyar Dayake Baba ne a gaba sai ya tsaya a bakin kofar yace’ Banda kuka,Banda kuka,Banda kuka, duk Wanda ya min kuka zai koma,

Yusuf yace’ Baba ina Yaya banganshi ba yana ina ? Ko ya fita?

Baba yace’ Yana ciki, ku shigo,

Umma ce a gaba sai Anty Ummu da Yusuf a tare suka Shiga yaseer ne na karshe, gaba kidayansu saranda sukayi suna kallan shi kamewa sukayi suka dena aiki jininsu yadena zagayawa kwakwalwar su ta dena motsi zuciyar su ta tsaya komai Ido yadena kiftawa kunne yadena ji kaface kawai ta tsayar dasu tamkar statue haka suka tsaya cak sakamakon ganin Abdullah Abdullah a kwance babu mara barshi da gawa oxygen a bakinsa badan zuciyar Shi da suka ga tana harbawa ba tsab zasuce beda Rai,ga karaya a kafa Duka biyun da hannu guda daya, Duka kansu babu Wanda yadawo dai dai Saida sukaji kukan yaseer sannan Suma suka dawo sai kuma sukayi kansa ganin zuciyar sa tana nema ta tafi zero ga wani tari da yakeyi ji sukuyi abin Yana ‘DI’DI ‘DI’DI alamar ya tafi zero,

Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un…….???????????? uncle ????????

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
31

Da wani irin sauri Daddy ya Danna alarm sai ga doctors sun zo, fitar da su akayi waje suka hau kansa, a waje kuwa Yaseer ne kadai mai kuka Banda Shi babu wani mai yin kuka a cikin su, sunana har akayi magriba shiru akayi Isha,sun dawo daga sallahn Isha sun zaci sun fito Amma suka jo shiru sai anan Ummu ta fara kuka gani ma take duk laifin ta ne ita tace masa yazo da safe da duk hakan bata faru ba, tama da cewan indai Allah ya kaddaro Abu babu Wanda ya isa ya kawar dashi, Basu suka fito ba sai Karfe 10 na dare da wasu mintuna sannan suka fito Baba dayake matsayin sa na likita shima kansa fitowa yayi bazai iya yiwa dansa komai ba, Dade ace ma Zainab ce zai iya Basu wani shaku da ita ba kamar yarda ya shaku dashi, Baba da Umma sai Anty su kadai ne sukaje wurin likitan Yaseer da har yanzu kuka kawai yake Bama ya iya magana bare ya tashi yaje yaji ba'asi Ummu da Yusuf kuma basa san suji abinda kunnansu Baya son ji, ga kuma doctors din Basu fito da fara'a ba, 

Office sukaje na likitan,
yace’ sai dai kuyi hakuri yaran ku Yana cikin wani hali numfashin sa na barazanar daukewa sannan kuma Yana inner bleeding, sakamakon bugun da zuciyar sa tayi Allah yasa bata fashe ba, sai kuma kansa dashi ma ya bugu yanzu de anyi masa aiki, sosai fatan mu daya Allah yasa kar ya Shiga comma idan kuwa ya Kai kwana daya zuwa biyu be tashi ba zamu karayi masa wani aikin, muga yarda Allah zai kaddara Allah ya sauwake, numfashi Baba yaja wannan al’amari da yafaru sai kace a mafarki? Ikon Allah Kenan, fitowa sukayi babu Wanda ya iya magana, Baba ya kalli su Ummu da yaseer da suke kuka ya kuma kalli Yusuf da ya zabga uban tagumi,

Baba yace’ kudena kuka kudena duk wani tunani haka Allah yake ikon sa, ki maida komai ba komai ba, mu godewa Allah da be mutuba da sauran ransa a gaba kuma muna fata Allah zai bashi lafiya yanzu da kuke kukan nan kunyi masa addu’ah ko sau daya ne?

Girgiza Kai sukayi, yace’ to kungani? Amma kun zauna kuna kukan da beda amfani ko kadan,yanzu da mutuwar yayi haka zakuyi ta kuka? Shine zai nuna kuna San Shi? Zaiyi alfahari ne daku? Bazaiyi ba, ku maida komai ba komai ba, ku dauki matsayin yayi tafiya mai nisa,tafiyan da bai Fadi ranar dawowar saba, kude na tunanin wai Yana kwancen a asibiti, kunji ko? Hakan da zakuyi shine zai nuna kuna kaunar sa kuci gaba da walwalar ku mutuwa ma bata Hana komai bare kuma jinya, duk Wanda na Kara gani yayi koda tunani to zuwa dashi ma bazan karayi ba,yanzu ku tashi mu koma gida,

Jiki kowa a sabule babu kwari haka suka mike sai dai anyi nasaran da Yaseer ya dena kuka haka ma ummu sai dai sunyi shiru ne kawai, walid Baba ya Kira yazo ya tafi da wasu shima ya dau wasu koda sukaje gida sai da Baba ya Kara masu nisiha sosai sannan suka da ware harda suncin abinci Basu suka kwanta har shabiyu suna nan suna jimamami Amma a zahiri kallo suke, a parlour yusseer da Ummi suka kwana batare da sun Sani ba, washegari Banda su aka koma Shiyasa suka ware suke abubuwan su, ahaka sai da akayi kwana biyu bai tashi ba, zasu sake wani aikin Baba yace a barshi zasu koma dashi London acan za’a cigaba, aikuwa haka akayi ya nemi visa da komai ranar Wednesday zasu daga zuwa Londo sukuma su Ummu su dawo gida don makarantar su, ranar da zasu tafi jirgi daya suka hau,don su Baba a Abuja zasu tashi,sukuma sai sunje Abuja zasu wuce Kano,

Suna zuwa suka zarce gidan Anty, sai da suka taya ta aikim gida tsab komai da komai suka huta  sannan suka wuce nasu gidan, fargaban Shiga suke Basu San bezao faru ba kuma, lokacin da safe sukazo Amma Basu fito ba sai da yamma  a hankali suka tura kofar gate din suka Shiga babu kowa a harabar gidan suka sa Kai suka Shiga ciki, Sameera ce a parlour tana waya da Wanda bata sani ba Wanda tasa Maza preacher mutane ta gani kamar su yusseer mantawa ma tayi tana waya 

tace’ Wa….w…a.na..ke…ga…ni?
Mama ta kwalla Kiran mama,
Mama ki fito wallahi Mama ki fito da sauri Mama!!!! Ta Kara kwalla Mata Kira,

Fitowa mama tayi tace’ ke banasan shirmen banza da hofi ba,meye kike wani kwal…..
Wanda tagani ne yasata saurin karasowa tace’ yu…u ..yu..yu. Si..f,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button