A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace’ lalle ma ke din nan haka ake ?
Ba fadar sunana bakomai taab, koda yake daman ni fa Ashe Kai ake cemin sai kace Mai karaton kai,

Gajiya tayi da tsugunna da mitar Shi,Zama tayi a kusa dashi,

Yace’ kinga?

Menagani?

Ko iya Zama ma bakiya a kusa da miji,

Tace’ wai dan Allah ya Jake so Nayi ne?

Yawwa ba wahala abin, nakoya maki?

Daga Kai tayi, yace’ good, na farko za’a fara da Zama ne,idan zaki zauna to a kusa na zaki zauna kingane?

To yanzu a,ina na zauna?

Taab kallafa ratar ai dayawa,

Nikam nagaji yunwa ma nakeji,

Yace’ Nima haka ai,
. Abinci ya dauko ya matsa daf da ita ya debo a spoon yace’ haaa

Bude bakin tayi ta zuba Mata Yana yi Yana zuba zancen Shi har ta koshi,shima ya Mika Mata batayi musu ba ta ansa ta bashi Yana Gama ci Anty Safiya ta shigo

tace’ yawwa daman ina San na fada maka cewan Umma ta Kira tace gobe na kaita,Kai kuma sai ana sauran kwana biyu sai kaje,

Bata fuska yayi yace’ kika ce kuma sai saura kwans hudu?

To ta zanja shawara haka tace da Baka zo Bama tafiya zamuyi, ta tashi ta tafi abinta,

Kwanciya yayi a cinyarta yana kallanta itama kallan Shi take, a hankali tasa hannu ta fara shafa masa sumar sa da har yanzu be rage ba,shikuma ya rufe ido kallan sa kawai take Jin yarda yake sauke numfashi a hankali yasata yi masa peck a goshi,zata dago Kenan yasa hannun sa ya dunkufar da kanta tare da

cewa’ ba’a nan ba,

Zaro ido tayi tace’ daman bakayi ba bacci?

Yace’ Nayi mana wani Abu naji Wanda ya tada ni shiyasa,

Tace’to ni sake min kaina, zaka…..

Jin wani bakon al’amari tayi Yana Wanda ya fi nada,Ashe bakomai Akayi ba.

Bayan sati daya

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

  34

Kallanta yakeyi bako kiftawa tunanin da yake ya tasheya ko a’a yama Rasa me zaiyi,sai yayi kamar ya taba ta sai ya fasa ga wani nannadewa da tayi ta rungume pillow kuma ta kwanta a kanshi sai kace bata da Kashi, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi ya fita a dakin,wanka yaje yayi ya saka kayan bacci sannan ya dawo, wardrobe ya buda ya dauko Mata kayan bacci ya zo fara kunce liffayar jikinta, shikaidai ya fafa mita,”‘ da haka kawai azo a saka wa mutum wannan Abu, shiya ce Yana so ne kome ko kuma ita tasaka oho,
Ganin tana motsi yasa Shi yin shiru kar ta tashi a hankali a hankali yake bita da ita har ya wareta Sannan ya cire Mata kayan bacci kawai yasa Mata doguwar Riga mai laushi sannan ya kashe fitilar yaje ya kwanta Yana sauke numfashi, Sai da ya nutsu ya daidaita kanshi ya masu addu’a ya jawota jikinshi,duk bidirin nan bata San anayi ba, shikuwa samun kansa yayi da murmushi tare shafa bayanta yayi missing moment nan ba kadan ba, tunani ya fara yi, wai yau shine da matar sa kuma a gidan sa? Abinda be taba kawo sa ranae faruwan hakan ba,ina ma Anty ummi tana nan,
Numfashi yaja yana shakar kamshin turarenta maganar Daddy na Kara dowa masa akai, me daddy yayi? Baya kula da Matar Shi ne? Meyasa yace masa Kar ya maimakon abinda ya maimaita? Ya ilahi, tunanin kawai yake ya Rasa mafita, tunani yake idan yaje don ya fada masa ko shin zai fada masa? Ko Baba Usman zai samu?

Kwanciyarta ya gyara mata Jin tana motsi,zata tashi, tashin kuwa tayi sabida yunwa ga bacci fal idanta, jinta da Yayi ta tashi zaune yasa Shi kunna bed side lamp,

yace’ lafiya?

Tana murza idanta tace’ yunwa nakeji,

Tashi yayi ya fita,Yana fita ya hango ledar da Mas’ud ya siyo masa dazu, Godiya yayi wa Mas’ud ya wuce kitchen ya dauko plate da cup,da babu Abu da yanzu ko me zai bata? Wata zuciyar tace sai Ka fita ka siyo,wata kuma tace ina motar,
A fili yace’ salan ma na kirasu su suzaci wani Abu ne,

Yana Shiga ya ganta ta komawa ta kwanta ta Kara kudundune wa abinta, karasowa Yayi, 

yace’ sauko kici?

Make kafada tayi tace’ a,a anan zanci,

Girgiza Kai yayi ya hawo gadan yace’ to jeki wanke bakinki,

Tura Baki tayi gaba itafa yunwa takeji, ganin bata da niyya yasa Shi ya daga ya kaita toilet da kansa ya wanke Mata ita sai layi fuskar da ya wanke Matane yasa ma baccin Dan sakinta,dawowa sukayi ya zaunar ta a kasa ya Shiga Baya kazar da Yogurt tana ci har ya koshi,bawani koshi can sosai ba bacci ne kawai fal idanta kuma yasan duk gajiya ce komawa tayi ta kwanta shima beci wani sosai ba ya tashi ya mayar ya dawo suka kwanta,sai anan bacci ya dauke Shi.

Da Asuba ta Riga Shi tashi,jinta a jikin mutum yasa ta kalli fuskar sa da kyau bata ganin sosai, kasancewar babu haske sosai,a hankali ta zare hannunsa Daya rungume ta dashi ta kunna bedside lamp ta juyo tana kallami zata sauka ta tuna da lifata ce fa ajikinta to waya cire Mata? A hankali kuma ta tuna sanda yake bata abinci, juyowa tayi ta kalleshe dakyau sannan ta tashi ta shiga tayi alwala, ta fito kuma sai ta Rasa yarda zata tashe Shi,kusa dashi taje ta sunkuyo har ta sa hannu zata bubbuga pillown sa sai kuma ta tuno indai zai tasheta to iska yake hura Mata sanda suna gidan Umma, Amma ai ba barinta yake kallo ba gashi an kusa a Kira a Shiga sallah, kamar yasan me take nufi sai gashi ya juyo barinda take, daidai fuskar Shi taje sai kuma ta kasa tasa hannu ta fara shafa masa fuska har ya bude Ido ya saukesu akanta ,ita dai tasan tana shafa masa fuska Amma bata San tunanin da take ba harda su murmushinta mai tsada take aikawa dashi,
Shima murmushi ya mayar Mata ya rike hannun Yana tashi zaune,

yace’ duk acikin shaukin ne? Har an Shiga sallah bakiji ba?

Ai bashiri ta tashi tana sunne Kai,Shi dariya ma take bashi idan tayi wani abun, tashi yayi yaje yayi alwala ya dawo har lokacin batayi sallah ba tana neman Hijabi bata gani ba,shine ya dauko Mata sannan ya jasu sallahr sun jima suna Azkhar har gari ya fara wayewa sannan,ya tashi zai kwanta,

Tace’ Ina kwana?

Saida ya kwanta, yace’ zo,

Ba musu ta tashi taje kusa dashi ta zauna,jawota yayi,tare da cire Mata Hijabin, suka kwanta tare Yana shafa kanta,

yace’ ina kwana kawai? Ba mi amor ba komai? Ina laifin ma kice dear shine ba laifi,Amma kice ina kwana kawai ai sai nazaci ma ba Dani kike ba,

Shiru tayi batayi magana ba,batasan korafi da Mita, tasan idan tayi magana to yanzu zasu fara shikuwa bazak gaji ba ita kuma tanasan tayi bacci, matseta yayi hakan yasa,
tace’ to kayi hakuri, bazan karaba,

Yace’ good girl,

Tace’ Mai gida ina kwana?

Takaici ne ya isheshi kawai ya rufe Ido irin nayi baccin nan,

Murmushi tayi ganin be amsa ba,tasan maganin Shi idan ya takura Mata,itama rufe idan tayi sai bacci.

 Karfe takwas ta tashi sabida tayi bacci ya isheta sabinin Shi da beyi na kirki ba,baccin sa yake hankali kwance, wanka tayi tazo gaban mirror ta shafa mai da kayan kamshi yau de an murza powder ansa kwalli sai lipgloss data sa, wardrobe ta bude donta sa Kaya mezata gani,tarin atampha, lace,shadda, material, English wears kawai aciki babu doguwar Riga koda kuwa ta atampa ce Kota wani abun,ta duba ta duba Amma babu tasan wanna duk Shirin Anty safiya ne, gashi duk Wanda take daukowa zanine,dakyar ta samu Wata atampa Mai kyau gashi taji dinki kuma skirt ne, hakan yasa ta sa ta, taje tayi daurinta daidai yarda zata iya, tayi kyau sosai abinta mayafi ta dauka ta ajje Akan gado sannan ta fita parlour, parlourn ba karamin kyau yayi Mata ba,Shi bacan Katan nan ba bakuma karami ba,kujeru set biyu ne a ciki Amma dayan daga can wurin dining yake, dining din kuma daga wurin kitchen yake idan Zama Shiga ma har da San step din da Zaka bi ta hau befi shida ba zuwa biyar, ba abinda zatace da Daddy sai Allah yasa Ka alkhairi ta kuma bishi da addu'a kitchen tashiga shima ba karamin kyau yamata ba,irin rustic kitchen din nan ne, ga table a tsakiya Mai kujeru hudu Dan karamin m dashi sai kofa data gani tasan store ne, sai wani glass data hango daga gaban kujerun zuwa tayi taga Ashe kofa ce ma, itama komai ya Mata kyau, cupboards din ta duba ta dauko tukunys ta dafa ruwan zafi kawai ta Nemo flask tasa ta Kai dining. Dakin ta dawo ganin baya nan yasata gyara shimfadar ta kuma fita parlour, Ganin su Mas'ud yasata Kara sa ta zauna a kujera, ta kalli mas'ud, 

tace’ meye za’a fa zuwa wa mutene gida da safe?

Yace’ lalle ma yarinya nan ba gaisuwa ba komai sai wani anzo maku gida?

Mus’ab yace’ Anty mu ina kwana?

Murmushi tayi tace’ lafiya qalau glip Ka tashi lafiya?

Yace’ lafiya qalau,

Mas’ud takaicine ya ishe shi,ya kasa magana, sai can kuma,
yace’ yarinyar Kanwar tawa Zan gaidar? Yarinyar da aka haifeta agaba na? God forbid,

Banza tayi da Shi bata tanka masa ba, yace’ kurma yunwa nake ji fah,tun jiya rabona da abinci,

Zaiyi magana Binaif ya fito, gaisawa suka karayi duksa sun gaida Shi daya bude musu kofa, akusa da ita ya zauna,

yace’ ina abincin da kuka kawo?

Mas’ud yace’ bacin matarka tace bazata bamu ba? Wai muma muje muyi auren haka tace,

Binaif yace’ ohhh wato Zama dakai zaisa ta koyi rashin kunya ko?

Daure fuska yayi yace’ waini waini menayi ne? Daga nace Abu daga nayi magana sai ace Banda kunya narasa menayi, kuma wallahi ganewa ce bakwayi fav bro yafini rashin kunya nesa ba kusa ba, kawai de kawai de idan an tsani mutum an tsana, daman na gane ai, Sam ba’a so…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button