A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallan data aika masa dashi na irinka dameni fah, shiru yayi Yana kumbara baki, Binaif kuwa kawai Kai ya girgiza Baya ganin akwai ranar da zai dena, da kanshi ya tashi ya je ya dauko kayan abincin ya dawo dasu parlour yaje ya dauko plate da cups ya dawo, Mas’ud ne ya hadawa kowa tea ya sannan ya zuba a plate daya ajajje a tsakiya kowa ya sauko suka fara ci sai dai daga ita har Mas’ud babu Wanda yacj Finkaso ne kuma basa ci,Shi idan yaci to make zaiyi itama haka amai take, shiyasa kawai suka sauko suke kallansu suna Shan tea dinsu,

Mas’ud yace’ Meyasa bakya ci?

Kai meyasa Baka ci?

Ni ai Bana ci,
Kefa?

Cine bazanyi ba,

Ka nida na tambayeki ma, nifa na fara maki tambaya aka kika maido min kuma wai na Baki amsa, mtsww ni din nan ma de wallahi,

Binaif yace’ bakya cine?

Daga masa Kai kurum tayi,

Yace’ Meyasa?

Yatsine fuska tayi tace’ idan naci Amai nake,

. Mus’ab yace’ shima twinny amai yake idan yaci,

Binaif yace’ to yanzu mezaki ci?

Tace’ bakomai kamshin sa kadai ma yagama cika min ciki ko me naci idan ba tea ba to amarya dashi zanyi,sai zuwa can anjima tukunna,

Mas’ud yace’ keda bake bace aka haifemu tare ba bakomai ba,amma bakya cin abinda Bana ci,

Mus’ab yace’ aikuwa komai bakwa ci to dayan ma baya ci,

Mas’ud yace’ ai a London nagani wai yarinyar bb a London munje zamu sai fruit memakon tace ba komai take sha ba tayi shiru ta kyale aka siya komai wai in fada maka sai da muka zo aka bata nata wai kasan kawai me take ci?

Girgiza Kai Binaif yayi alamar a,a, yace’ hmmm kawai Apple da Pineapple sai orange da Mango kawai ta dauka, wai baga sha idan ba leman su akayi ba,Kai kaji takaici gashi Nima ba sha nake ba sai anyi lemon su, Kai kaji takaici kuma wai ta dauka barma su a wurin imagine ta kyauta ?

Dariya Binaif yayi yace’ to mene zaka damu bayan kasan halinta?

Yace’ hmm bb bazaka gane ba yarinyar nan ko? Ni dayane maganinta kuma ba mantawa nayi ba har yanzu ina binki bashin Marin da kika zabga mini,ban manta ba,

Daure fuska tayi, tace’ har yau ma idan Baka dena abinda kake ba wallahi ina daf Dana Kara maka wani, Kai kasan haushin da kuke Bani? Wai mace ta mareku kutsaya sai kace sandunan da aka daure, hmmm,

Mus’ab yace’ lallene dan Baki tashi a yarda Muka taso bane, ba tun muna yaro fah,muke ganin sharrin Mata Kala Kala kwanne da irin tashi,mace kanta bala’i ce, daman ba mune a matsayin ki,

Murmushin takaici Mas’ud yayi yace’ gwara mu sau dubu Akan ita, Gwara mu mun taso Bamu da gata kuma munsan hakan munsan matsayin da muka ajje kammu Amma ita fa,kasan cin amana kuwa? Kasan rashin tarbiya abinda yake haifarwa? Bazaka gane ba,inaga ko?

Murmushi tayi tace’ worry not please!

Binaif yace’ Meyasa tasaka a blacklist?

Yace’ Nima bansan sani ba,kawai gani Nayi tasani,

Ummusalma tace’ tun yaushe Kenan?

Yace’ ehh ba’a jima ba, kusan kwana biyu Kenan, kuma yau nake so na tafi gobe zamuyi Baki daga Chicago,

Tace’ ba ita tasa Kaba,ca akace tasaka, nasan da wannan, Ka Kara kiranta, Amma ba wa’azi zaka cikata dashi ba,kaji ai?

Turo baki yayi yace’ kinsan de ba hira na iya ba ai,

Zaka koya ne ai,
Naji kace Baki wanne Baki zakuyi?

Mus’ab yace’ muma za’ayi wannan bakin Amma mu daga Ghana ne,

Tace’ ok fada maku akayi?

Ehh sun fada,

Tace’ nasan ba daku za’ayi ba,Amma dole ku San yarda kukayi kukejin duk wani meeting dinsu, daga nan sai ku fara dauke documents masu amfani kafin nan,duk abinda zakuyi fa sai kun tabbata Baku bar shaida ko guda daya bace ba, kunji?

Mus’ab yace’ yafi ji da companyn Abuja nan

Mas’ud yace’ Baya zuwa sai sati sati daga Friday sai Friday nikuma wannan Friday din na dawo gida, shima ji nayi a wurin ma’aikatan sai dai Mai Kula da Shi kawai,

Tace’ Friday kuma? To mezaije yayi Friday Bama yaje Monday ba? Dole akwai wani Abu Ka Kara bincikawa,

Binaif yace’ ku dawo next week zanyi bako,

Kallan juna sukayi irin really din nan?
Harara ya watsa masu yace’ bafa nasan gulma,

Mas’ud yace ni ba wannan ba,a fada min me Zan fadawa wancan loron?

Tace’ wai meye wannan loro din yake nufi? Da mi precioso sai dayan ya ma?

Tafada tana kallan Binaif,
Yana Shan tea din Shi,
yace’ no le digas,

Kallan Shi tayi tace’ kar a fada min ko?

Mas’ud yace’ keda bakya ji taya kika san me aka fada?

Mus’ab yace’ to haka yace yaushe zamu wuce,

Banza tayi dasu, tace sai kaje Ka samu Wanda zai fada maka ai,

Yace’ Haba kanwa a wurina, amarya a wurin Abdulshakur Binaif bb,

Daure fuska tayi tace’ oho maka, kuma a tashi a min wanke wanke, tashi ma tayi ta bar mu wurin,

Mas’ud yace’ wannan yarinyar ita kanta gaba dayanta aljana ce,

Binaif shima tashi yayi yace’ Yayar kaced de daga yau Anty, kaji ai,

Cab Anty ko tana Suma tana bazance ba,

Mus’ab yace’ kaga tashi mu wanke mu wanke kayan nan mu sannayi ba fitowa ba zasuyi,

Mas’ud yace’ ai nasani Suda su fito sai gobe ko?

Tashi sukayi sukaje su Ka wanke kwaninka tas suak dawo suka zauna, message yaga ni da numbern ta, address ne na gida.

????????????????????????????????

Kusan mene gidan Amarya zamuje idan yamma tayi mu karbi hakkin mu,

Yaseer yace’ daman mun jima bamuje ba,rabon mu da zuwa tun kafin muyi candy ko?

Ummu tace’ ai munyi missing yanzu kuwa zuwa zamuyi, gaskiya baza muyi missing wannan,

Yusuf yace’ wani hakkin ku, kune kuka Mata alkhakin da dublan din? Zaku ce wani hakki, kukam kunji kunya de,

Yaseer yace’ Abu Mai sauki Idan ankawo kadene ci,daman nida besty ne muke debowa Kai sai dai kayi ta wani hararan mutene,

Ummu tace’ Allah yasa ma ta bamu da yawa,

Yaseer yace’ ai shiyasa ma zamuje yau, yarda za’a fi bamu dayawa ko ya kace?

Yusuf yace’ ni bamma San ta yarda kukaga kasan an kawo amarya ba,

Ummu tace’ jiya munje zamu karbo assignment din da Bama nan aka bayar to ai Layin daya anan muka ga mutane da mota shine fa muka tambeyeta tace ‘yan zuwa ganin gidan Amarya ne yau da daddare za’a kawota shine fa,

Yusuf tashi yayi yace’ kunsan kuma muna da Shiga school Bari naje na karbo kudi a wurin Abba Ida kun Gama haukar taku sai ku kirani,

Yaseer yace’ Ka karbo dayawa zamuje mu siyawa Amarya alawa,

Ummu tace’ hakkun baza muje haka sigai sigai ba a bamu Abu mu mu dawo ba,

Daga murya tayi tace’ Dan Allah ya yusuf karka manta fah,

Yaseer yace’ ke rabu dashi idan ma be anso ba ni Zan karbo,

Suna nan zaune shiru shiru be dawo ba, ummu tace’ bafa ya so muje mu gida nan nikuwa yau sai naci Alkhaki da jima banci ba,

Yaseer yace’ sai kinci ko sai naci ai kinga idan Mjka tafi yanzu muna ganin anyi Uku tayi mudawo gida da zaran anyi la’asar mu Shirya,

Ummu tace’ Allah a bamu da yawa Ka gobe Monday Idan munje school ba sai munne abinci ba,

Kedai bari,alkhaki duniya ne,

Ummu zatayi magana Kenan sai ga yusuf nan yadawo jikin sa a sanyaye kamar marar lafiya ga idan sa da ya fara yin ja, Yana zuwa kawai ya zube a kasa Yana sauke numfashi,

Yaseer da ummu da gudu sukayo kansa,suna tambayar lafiya?

Kallansu yayi ya kulle Ido,ya bude ya kalli,
yaseer yace’ mu kuma tamu jarrabawar Kenan? Bamuyi dacen Iyaye bane? Ko kuma zon zuciya ne haka? Shine mu ba ‘ya’ya bane? Bazamu girma bane ba? Ko kuma muma baza’ayi mana abinda sukayi ba? Yaseer a gaskiya bazan iya ba, nagaji nagaji yaseer na tsani gidanan badan iyaye na bane babu abinda zai Hana ni tsa….

Yaseer ya rufe Baki yace’ a,a yusuf ya isa haka Ka tsani gida, ai gidan ma nashi ne,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button