A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hawayene ya zubo a idan yusuf yace’ yaseer daman ma ace bamu dawo ba,daman ma ba’a dawo damu ba naji wanna takaicin Dana ji,

Ummu tace’ me kuma meya faru, Baka fada komai ba sai Wannan maganar kake?

Yana hawaye Yana murmushin takaici, yace’ idan na fada maku bansan ya zaku dauki lamarin ba,bazan iya fada ba,ku barni kawai duk ranar dana Shirya fada Zan fada,

Yaseer yace’ muma Insha Allah baza mu Kara tambayar Ka ba,

Yusuf yace’ bazamu iya tafiya wani gidan ba?

Idan mun tafi kuma taya zaka Kara Jin abinda kaji? Bansan me kaji b, Amma tabbas nasan koma meye Yana da fita,kuma Yana da bukatar cigaba,har sai an Kamala, idan kuma kammalawa akayi to za’a sake sabon shiri, kuma zamu tafi? Muje ina?

Shiru yayi Yana tuna abinda yaji Abba yana cewa, ga kuma zancen yaseer, yaseer Yana da gaskiya,kam,

Ummu tace’ kada Ka sa damuwa a ranka muna tare dakai,

Tashi yayi ya wuce bedroom,Suma Zama sukayi sukayi jigum tare da tunanin me yaji? Yaseer yace’ tashi muje muyi karatu,nasan ba zuwa school din zamuyi ba,
Batayi musu ba Dan da wannan tunanin gwara Karatun, Basu wani jima da Shiga dakin ba, shima yazo ya fara Karatun, sai Azahar suka tashi sukayi sallah sannan suka wuce gidan su Ummu acan suka ci abinci.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Tace’ bansan ya zanyi da Chatty ba sam ya kasa canzawa,

Binaif yace’ ki tura masa address din su yarinyar sai yaje gidan,

Tace’ hmmm yaje yayi Mata me? A waya yakasa proposal dinta bare Yana ganin fuskarta?

Shiru tayi tace’ ina da idea, Maybe it will work,

Yace’ wacce idea Kenan?

Kaima ba fada ma zanyi bare kuma Shi,

Nikuma banayi?

A,ah kawai de sirrine,

Tace’Ka kwanta bari naje na same su,
Daga mata Kai yayi ya gyara kwanciyar sa,Yana tuna abinda Mas’ud yace Kenan sai Friday Friday kawai yake zuwa to yaje yayi me? Kowa ya tafi gida weekend? Kode orphanage yake zuwa?
Wayar sa yadauka ya Kira Alhaji munir,

Yace’ daman sai Friday Friday yake zuwa? Lagos?

Daga can yace’ Gaskiya bamma San da wannan ba,nade san Yana zuwa duk wata a bashi kasan sa, sannan kuma ai nafada maka,Ashe ba duka ya sayar da orphanage din ba, raba Shi sukayi a biyu Daya nashi na Daya na mutanen,

Binaif yace’ ai Ka fada min wannan,

Sannan ai na Kara bincikawa Ashe suna taso ya sayar masu, dayake beda original copy har yanzu be siyar ba,

Shiru Binaif yayi Yana tunanin yace’ sai kazo ranar asabar din,zamuyi magana,

Tashi yayi shima ya fita,

A parlour kuwa mas’ud Yana ganin ta tun kafin fa zauna
yace’ me zanyi a wannan address din,

Sai da ta zauna tace’ gidan su Sameera zakaje, idan kaje abinda zakayi shine karka nuna Mata Kai ne kake kiranta,kuma kar Ka fito daga mota,

Yace’ Meyasa Tou?

Ya tsine fuska tayi tace’ gudun karka bawa kanka kunya, Ka kasa tsayuwa,

Wallahi kin Renani dayawa har wani Karna kasa tsayuwa?

Tace’ to musa?
Yanzu nan na koma nayi bacci na,

Turo baki yayi ya lankwashe kafa akan kujera Ya fara danna waya,ya Shiga apps yafito ya Shiga camera yafito haka kawai yake,

Tace’ firstly abinda zakayi idan kaje shine, start by saying Hello, this method is direct and simple, doesn’t take a lot of time if you’re nervous you can’t go wrong,

Secondly, ask her questions don’t talk about your self, before you bore someone to death,
The next stop the interrogation ask questions but don’t interrogate her,

Yace’ taabdi duk wannan? Nace Mata may ko June?

Tace’ Kai Ka bansan yazanyi da Kai ba, ban wayarka, Mika matayi yayi ya zauna a kusa da ita Yana lekawa,
yace’ me zakiyi da ita?

Long typing tayi tamika masa tace’ idan kaje Ka kirani,kasa earphone sannan Ka Kira,

Tace’ kafin kace kana Santa sai Ka raba ta da Duka friends dinta idan ba haka ba,zatayi ta blocking Dinka ne, ba’iya friend s ba har samari zaka tabata da su nikam Nayi iya yina hakan ya Isa ai,?

Yace’ Allah yasa na iya,

A zuciyar ta ta amsa Amma a fili tace’ ai Bama zaka iya ba,

Binaif da yazo tun dazo yace’ ina zai iya? Nima zaci zai iya Ashe bazai iyaba,

Mus’ab yace’ Nasan twinny na zai iya zai kuma Baku mamaki,

Tabe Baki tayi tace’ mugani a kasa,

Yace’ naji,kika I should asked her questions but don’t interrogate her,?

Tace’ ehh if she have interest on you,she will ask you questions but if she’s not hmmm Allah ya kiyaye abinda zai faru,

Yace’ bangane ba?

Binaif dariya yayi yace’daman Ka saban Shan marin Mata ai,

Tashi yayi yana kumbura fuska yace’ tafiya zanyi agidan nan an tsaneni,

Mus’ab yace’ Haba twinny da wasa suke fah,

Yace’ barta wai ita tasamu aljanar data rike Mata Baki ta saketa shine wai, take addabar mutane da zancen, komawa yayi ya zauna yace’ nama fasa tafiyar, nikam,

Hira ya dauko anan suka cigaba da hiran su su uku banda ita,har su Baba Usman suka zo sukayi masu sallama suka tafi, har Azahar sannan sukayi sallah Anty safiya ta kirasu suzo su Kai masu abinci, sauran wancan din suka tafi dashi sannan suka kawo wani abincin Rana,

Akasa kamar wancan ya baje masu wannan Karan Friedrich ce da lemo sunci ba laifi suna ci suna hira abinsu, suna nan har akayi la’asar suna la’asar,

Mas’ud yace’ Bari naje nadawo, Fav tashi mu tafi, na ajjeka kokuma mu tafi dashi?
Ya fada Yana kallanta,girgiza masa kai tayi alamar a,a,

Yace’ hmmm aljanar tazo Kenan?

Kallanshi tayi tayi kwafa, ta tashi ta wuce, sukuma suka fita, wanka ta Shiga tayi,don itakam gaba dayanta a tukure take jinta wannan kayan ina,tasaba jinta a baje tayi juyinta nan ta juya can,babu takura.

Tana tsaye a gaban wardrobe tana kumbura Baki ita daya tana gunguni ita kadai tasan abinda take fada, shigowar sa Kenan shima wannan yasake ya shigo ya ganta wannan Karan ko kwallin ma ba’a Saba powder kawai aka sa,sai lipgloss Yana ganin ta ta dauko wannan ta mayar ta dauko ta mayar tana Mita, murmushi yayi yasan doguwar Riga take nema shikuwa jiya da yazo yaga dogayen riguna nta Bari guda ne, ma shine ya kwashe ya mayar dakinsa ina dalili yazo aka fa sa masa doguwar Riga a gida?
Zuwa yayi kusa da ita,ya tsaya a bayanta tare da zaro wasu English wears Riga da skirt,
yace’ kisa wannan,

Juyowa tayi daman ga haushi dayake cinta, tace’ name? Kana gani babu kayan sa nake so? Ga zafi ga komai ma shine zakace nasa wannan abun?

Yace’ to shikenan zafi kike Ashe kamar ni,kinga Nima singlet ce da threel quarter kema tunda kema kina Jin zafin kawai kisa Vest da Mini skirt ba shikenan?
Yafada Yana kunshe dariyar sa ganini irin kallan da take masa,

Juyawa tayi tace’ ehh dole ma,to nida Kai daya ne? Zakace nasa irin Shigarka?

Rungumota yayi fa Baya Yana hura Mata iska a kunne yace’ ashe fa har yanzu bamu Zama daya bako? Yanzu kuwa zamu daya,ko sai anjima?

Jingina tayi da jikinshi ta rike hannunsa dake Kan cikinta tana kallanshi,
tace’ Ai bazamu taba Zama ba, Kai daban Nima daban,

Murmushi yayi ganin bata gane ba, yace’ idan kuma muka Zama fah?

Tace’ Ai bazama mu zaba,kowa matsayin sa daban,

Cigaba da abinda yake yajeyi,fara nokewa tayi tace’kabari Bana so,

Yace’ko naci gaba da dadi ba?

Tace’ a,a Bana so ba dadi,

Yace’ let’s find out,
Bataje ga magana ba ta bude ido taganta a gado zata tashi ya danne ta yace’ na kinje ba dadi ba? Kuma kince bazamu Zama daga bako? Shine za tabbatar,

Baki bude take kallan sa tace’ wai Kam kai,Baka ganewa ne?

Yace’ Dani dake anga Wanda baya ganewa,

Zatayi magana yafara Mata abinda tace bata so.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button