A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da daddare Anty safiya ta shigo dakin Nafisa su biyu ne kawai a dakin sauran duk sun koma Bauchi sai matar Baba Usman da yarta mace guda Daya dayar kuma tayi bata zoba bata da lafiya, sune kadai Basu koma ba,
Anty safiya tace’ Nafisa tashi kije parlour, zamuyi magana,
Fita tayi ta baso waje, Anty Safiya Zama tayi a kusa da ita ta kama hannunta, sai ga Mom yagana matar Baba Usman itama tazo,
tace’ Ummusalma kinga yanzu yarda Allah yake lamarinsa, kinyi aure har zaki tare a gidan ki,ki Kula da mijinki, yanzu kece komai nashi, ke zaki masa komai basai na fada ba kin sani, sannan zaman aure sai hakuri,Idan babu hakuri to babu zaman lafiya sannan ko yakike ciki da mijinki karki Bari kowa da zaizo gidan ki yasan hakan,Karki fadawa kowa kada kowa yaji musamman kawayenki, sannan Ummusalma zaman aure na har abadane babu ranar denashi kamar yarda ba’adena sallah haka shima ba’a denawa ki rike amanar Shi ki rike sirrinsa kiyi biyayya, bansan kuma me Zan kuma cewa Amma wannan Kalmar hakuri ita Zan fada maki,bazaki Ganeba yanzu sai kin je kin gane da zaki San me ake nufi kinji ko?
Mom tace’ Ummusalma Abu na farko da zakiyi shine gudun bacin ran dayanku, duk wani Abu da yake so Shi zaki fara sani,da abinda Baya so, sannan danginsa koda sunzo idan sun Nuna maki wani Abu kada kiyi fada masa ma anyi bare yasani, Abu nagaba biyyaya i Nayi Bari na Bari, tsabta, girki, kyautatawa ba Shi kadai ba bar danginsa kinji ko?
Daga nan suka Shiga Mata nasiha mai ratsa jini da Kashi tare da duk wani lungu da sako na sassan jiki bata San sanda wani hawaye ba ya taho mata, tambayar ta anan shine shin daman haka akeyi? Idan za’a Kai amarya? Koshine dalilin kukan nasu daman?
Umma ce ta Kira wayar Anty safiya ta daga tace bata, a speaker tasa wayar, daga can,
Umma tace’ Salamatu na daukeki ‘ya kamar ‘ya’ya Salamatu ina kaunarki har zuciya ta kamar yarda nake San nawa,na dauke jika kuma ‘ya,
Daga nan fa itama ta daura nata nasiha, tayi kuka kamar ba gobe daga nan Daddy yazo aka fito da ita parlour shima yayi nasa nasihar bashi kadai na har mijin Anty safiya da Hajja sai da sukayi Mata Suma taso, taga gata iya gata tayi kukan dadi, sannan tayi kukan rashin Uwa,sosai kukan ya hade Mata guda biyu,
Daddy ya Ciro kudi ya bawa Antu safiya
yace’ ga sadakinta kya bata,daga duk suka tashi suka fita,wanka mom tasata tayi da turare mai kamshi,ba’a Mata wani kwalliya ba don har yanzu kuka take yaki ya tsaya Mata, sai datayi sallahn Isha aka Shirya ta acikin liffaya tayi kyau sosai, Nafisa da Anty murja ne zasu kaita su kadai,ita kanta Anty safiya taji ba dadi Zama da Ummusalma akwai dadi bata da matsala ko kadan bata kuma da kiwar yin aiki, kwalla taji zata zubo Mata tayi sauri ta koma daki, haka suka sata a mota sukayi Gidan Abdulshakur Binaif da ita.
Gidane palate mai kyau da Shi na daidai zaman Mutum daya a wadace sai wani barin daga gefe,kamar de part biyu ne a gidan sai dai Shi be Kai nata ba, sai compound shima daidai ba wani girma sosai ba daga can Baya kuma garden Wanda bishiyar lemu ce kawai ta girma sauran abubuwa duk Basu wani girma ba wani ma ya mutu alama basa samun kulawa,
Daki daya aka kaita ana ma Anty murja ta Kara yimata wata nasihar dayake da Rana sunzo sun Kara gyara mata sai kawai suka taso suka fito Dan Daddy yace suna kaita su dawo Shi yaso shine ya tafi da ita.
Tayi kuka kamar ba gobe, ita kanta a yanzu da suka tafi suka barta batasan na me take ba, na farin cikin tayi aure ne? Ko kuma na farin cikin kudirin su Abba bai hau kanta ba? Kanta kwa ciwo yake Bana wasa ba,ga gajiya ga kuka ga yunwa,duk sun tarar Mata tun abincin da Umma ta matseta a daki taso Dura Mata tun safe bataci komai ba,koda Anty safiya ta Kai mata bata ciba, kwanciya tayi ta kudundune ita kadai a saban wuri haka? Dakyar ta samu hawayen ya dena zuba ga lifayar da aka nade ta dashi bata iya kwancewa da ta kwance, bacci ne ya fara ya daukata batare da ta Shirya ba,
✨✨✨✨✨✨✨✨
Yana zaune a gaban Daddy,Daddy Yana masa nasiha kamar yarda yayi Mata,haka ma Anty safiya harda Baba Usman, kowa yayi tashi,
Daddy yace’ Binaif ina Mai Kara ja maka kunne kada Kake muzgunawa yarinyar mutane,bata San halinka ba, koni Dana haifeka Bana ce Ka ga halinka bare kuma ita, Ka koyarda yarda zata San halinka Banda fushi Banda zuciya banda bakar magana. Binaif Dan Allah Ka Kula masu da yarinya, tamkar marainiya haka take kazama gatan ta Ka Zama mahaifinta Ka Zama aboki,kazama yaya,kani,abokin wasa, Binaif kake kulada yarinyar mutane Binaif, Binaif kada kaje Ka Kara tafka kuskuran Dana tafka a Baya Binaif duk wani motsin ta idan bata da lafiya ko kuma batajin dadi ko ranta ya baci kayi kokari kayi Shi Binaif Ina Santa kamar yarda nake Sanka ‘yace a gurina kamar yarda kake a gurina, Binaif Bana San ka maimaita abinda na maimaita a baya, na rashin Kula ga iyali,
Kwallace ta ciko idansa ya goge,bazai iya cigaba Dan yanzu sai yayi kuka yana San dansa Allah ma yasani bayasan ya biyo halinshi na rashin kulawa da iyali gani yake rashin Kular sa ce yasa Mahaifiyar guduwa, gani yake rashin damuwa da damuwar ta ne yasa hakan ya faru, tashi yayi zai fita, sabida tuno wani Abu yaji an rungume Shi ta baya tare da sakin kuka ko be fada ba yasan Binaif ne,juyowa yayi shima ya rungume shi,Karo na farko kenan a rayuwar Shi da ya rungume dansa,Karo na farko da yaji tausayin dansa, Karo na farko Daya ga dansa na kuka,raban da ya rungume Shi tun Yana yaro shima ba wani sosai ba, kukansa kuwa be taba gani ba tunda ba’a gabansa aka Rene shi ba,
Sunjima a haka sannan Daddy ya bubbuga bayan sa be iya magana ba kawai yayi breaking hug din ya fice,
Baba Usman ne yazo ya kama hannun Binaif
yace’ ya Isa haka kukan kaji son?
Goge masa hawayen yayi bayan ya zaunar dashi sannan shima ya masu sallama ya wuce,
Anty safiya tace’ kayi hakuri kadena kuka, yanzu idan kaje kana kuka ita tana kuka waye zai rarrashi wani kuma?
Tunawa da ita ma kukan take yanzu haka,ba shiri ya Kara goge hawayen sa, Basu wani jimaba ya tashi zai tafi,
Anty safiya tace’ Ka Bari su Mus’ab su kaika de,Naga tare kuka zo, karkace Kai su zaka Kai sannan Ka wuce,kaji ko?
Da to ya amsa, tace’ muje na fada masu don ba wai na yarda da Kai bane,
Tare sukuje ta fada masu, Mas’ud ne kuwa ya karba key din suka tafi,
Awani slow motion yake tafiya ga wata waka dake tashi a hankali itama lumshe idan sa yayi Shi kawai so yake ya bude ido ya vanshit a gabanta,ko ta dena kukan? Ji yayi sun tsaya a zatanshi sunzo sai ganin su yayi a bakin wani wuri, tsaki yaja ya rufe idansa ya kwanta,
Mas’ud Yana dawowa bayan sun fara tafiya
yace’ fav kar Ka manta idan zai fita Ka hada Shi da wannan ledar,
Mus’ab yace’ Naji,
Yace’ wani twinny ina event din da kace zaka hada mana ne?
Tsaki yaja yace’ kaidai fav barni na so na hada wani event din ai Amma ba lokaci tund kaga aikin nan yamana cikasa gashi ni gobe ma Zan koma, Sai wani weekend din idan na dawo dole ne fa a shirya wata hadaddar Dinner ya kake gani?
Mus’ab yace’ lalle kam zaka Shirya Kai daya,Kai fa wani sa’ilin kanka Baya ja,taya za’ayi ub an gayyatar ya yarda bacin Yana kagane ai,
Mas’ud yace’ kaina kam Baya Dan wallahi ban gane ba mekake nufi ba,Dan fada min kaga shikenan bazan hada ba,
Matso da kunnansa mus’ab yayi ya rada masa wani Abu, atare suka sa dariya suna cafewa,
Mas’ud kanka naja wallahi,kana kawo light kuma fa haka ne, taab kace tun yanzu an fara wataran ma Bama Shiga ba,Amma ni dai ko da ta Sama ne sai na Shiga ko an hanani,
Mus’ab yace’ Kawai wannan weekend din kar mu dawo gida mu Basu privacy Ka de gane ai,
Mas’ud yace’ wallahi kana kawowa sosai fa,Nima de Zan fara kawowa nan ana Abu Zan dago jirgin karka damu,
Ahhh ai daman Kai ne kake kwafsawa ina so na ma signal amma nasan ba ganewa ba zakayi,