A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace’ wai ni Twiny ina Sameera kuwa kwana biyu,
Wannan yarinyar wallahi Allah ma ya gani tsoron ta nake ji,a waya tsakani na da ita fadar gaskiya shine kawai kuma Tama sani a blacklist,bansan kuma ya za’ayi ba,
Mus’ab yace’ za’a San yarda za’ayi sai mundawo ai,
Daga kuma Sukaci gaba da maganar su iya su,Yana jinsu ne tanka masu Dan beda ta cewa, zasu hadune ai. Har sukaje gidan, dayake babu mai gadi a gidan Mus’ab ne ya fita ya bude, yashiga ya rufe yaje ya dauko ledar Shi, ko kallansu beyi ba ya Shiga cikin gidan Suma binsa sukayi a parlour yaja ya tsaya,
yace’ lafiya? Sai bina ake?
Mas’ud yace’ matar zamuje mugani mana,
Kallan irin Baku da Kai ya masu, yace’ bade kun kawo Mata mijinfa lafiya ba? To Allah ya tashe mu Lafiya, Allahu ya kawo ranar dena tuzoranci,
Juna suka kalla Mas’ud da Baya shiru yace’ dame Ka fimu? Mufa har yanzu bamu Kai 30 ba bare ace mana wani Abu ku …….
Taske masa keya yayi yace’ fita, bazaka zo Ka min rashin kunya ba anan,
Kuma ku bani key Dina,
Mas’ud Yana Dan gunguni yace’ wanne key? Taab ai dashi yazamu tafi idan kana da bukatar wani Abu Ka Kira mu,
Suka tafi shima binsu yayi don ya rufe kofa sai dai suka fita yana rufe gate mas’ud yafito da gudu,
Yaje saitin sa ya rada masa Abu sannan ya dawo da gudu ya koma, girgiza kansa kawai yayi mas’ud beda kunya kokadan Allah ya kawo ranar da zai shiryu. Sai da ya rufe ko ina sannan ya Shiga daki, tana kwance tayi nisa cikin baccinta sosai Kara sowa yayi kusa da ita ya durkuwa a gabanta Yana kallan fuskar ta wacce tayi ja sabida kuka,sai ajiyar zuciya take saukewa alamar har yanzu besake ta ba…….
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: A BAKIN WAWA
Akanji magana
35
Tace’ you?
Runtse idansa yayi ya Danna Kiran wayarta Sai dai bata daga ba,ya kuma Kira namma haka ahaka yayita jera Mata Kira daga karshe ya bude abunda tayi typing yafara karantawa,
Sameera tace’ idan bazakayi magana fine your out,
Numfashi ya ajje sannan ya zaro kafarsa guda Daya waje cikin wani murmushin da kana gani kasan na yake ita kanta Sameeran tasan na yaken ita da akayiwa bare wani kuma,
yace’ Hello,
Banza tayi dashi ta kauda kanta gefe,
Zuciyar sa yaji ta tsinke ji yayi kamar ma ya koma, kallan wayar sa yayi,
Yace’ am sorry
Tace’ yanzu kuma me zaka zo kamin,wancan Ka rabani da saurayi na yau kuma fah? Dame kazo?
Runtse Ido yayi sosai ya Dan kalli wayarsa,
yace’ am kiyi hakuri bansan hakan zai faru ba,daga maki magana?
Tace’kaga ya isa haka,tunda Baka da tace zaka iya tafiya,nidai nasan bansan Ka,bamma taba ganin ka,
Yace’ Insha Allah yanzu zaki sanni idan kin bani dama,
Mtsww kaga Ka tattara inaka inaka Ka barmana gida Bana San na Kara ganin Ka makaryaci kawai,
Kallan wayar Shi ya danyi kafin ya juyo ma har tayi nisa,daga murya yayi yarda zata ji Shi
Yace’ ki gaida yayarki Ummusalma,
Cak ta tsaya ita bata juyo ba ita batayi gaba ba, Gabanta na wani irin faduwa tabbas tana da yaya fa Ashe ko? Amma tana ina? Ya akayi ta mantata? A hankali ta juyo ta kalle Shi Yana kallan wayarsa irin Zama ki dawo, dawowa tayi,
tace’ ya’akayi kasanta?
Yace’ to ai nazaci ke ita ce ma a wancan ranar shiyasa am sorry,
Tace’ kuma meyasa Ka ambaci sunana,
Yace’ na tuna tace tana da kanwa Sameera shiyasa dakika muna Baki sanni ba Nayi tunanin kece,
Tace’ na manta da ita Sam bansan ya hakan ta faru ba,
Yace’ bata nan ne? Rabona da ita shekara shida Kenan,
Tace’ Nima bansani ba, amma Zan tambayi Mama naji? Nifa na manta da ita Sam,idan ba yanzu da kace yayata ba,na tuna ina da yaya Ummusalma yaya salama,
Sauke a jiyar zuciya yayi yace’ ina San Ummusalma sosai Bata da matsala ko ta sisin kwabo,kowa zaiyi alfaharin samunta a matsayin Abokiyar sa,Amma ya akayi ta bata?
Tace’ wallahi bansani ba nifa nace maka na manta ta,a babu rayuwata a wuri daya nake tunata duk sanda Naga abinda bata so ko abunda take so ta shine Zan ce nikuwa wama yake San wannan abun? Amma Zan manta sunan,
Yace’ to mai Hana muyi wani Abu?
Tace’ name fah?
Yace’ karki sanarwa da mama ko Abba naji kince zaki sanar musu, please karki hakan, maybe Suma sun mantata,
Amma meyasa?
Sabida ina so mu nemota kingane?
Nafa manta kamarta,
Karki damu ni ban manta ba,
Tace’ nasan Mama zatayi farin ciki duk ranar da na kawo Yaya salama sosai ma kuwa,
Murmushi gefen Baki kawai yayi, nashi kadai yasani,Abu biyu ne suka hade masa abinda yake karantawa anan ta tsaya,besan bezaice ba kuma, shiyasa yace’ to ni Zan tafi,
Tace’ da wuri haka?
Yace’ ehh Zan tafi Lagos ne yanzu fa inaga ma Sai dare gaskiya,
Tace’ to shikenan,Amma sunanka fah?
Mas’ud,
Kawai?
Adam Dan Lami,
Dan Lami?
Eh,ko kinsan wani haka?
Kamar de munyi school tare da wasu amma seniors Dina ne, Aneesa Dan Lami da Ameera Dan Lami,
Wani murmushi yayi murmushi irin akwai kura Kenan, shifa ta barshi ya tafi haka, babu abin cewa kuma,
Tace’ number fah? Gashi ban fito da wayata ba, kawo na Sama sai Ka kirani,
Yace’ no karki damu Fadi kawai, sai nasa,
Tace’ rowar wayar kake ne?
A,a ba komai,kawai de ki fada kinsan sauri nake,
Fada masa tayi ya rufe kofar sa,
tace’ yanzu kuma sai yaushe Kenan?
Sai next week in Allah ya kaimu,
To Allah ya kaimu Allah ya kiyaye hanya,
Murmurshi yayi yace’ ameen na gode,
Sai da yaga ta Shiga gida ya sauke ajiyar zuciya yace’ ko taya sani? Wannan yarinyar daman Aljana ce nafada ai, Bari naje gidan,
Horn yayi aka bude masa gate,zai go saiga su Ummu nan da yaseer zash shigo sai da ya Bari suka shigo tukunna dayake glass din a sauke yake sai da suka gaida Shi sannan ya suka wuce, shima ya wuce yana fita ya hango mus’ab yaje ya dauke Shi,suka wuce, kayansu suka hada lokacin ma Magriba tayi hakan yasa sai da sukayi sallah sannan suka nufa gidan bb lokacin ana nema ayi Isha,
Mas’ud yace’ Anya fav zamu samu flight kuwa?
Mus’ab yace’ mezai Hana sosai ma,kasan ai gobe Monday kuma duk manya manya nan zasu tafi wasu ma kasar zasj bari kuma dole sai sunyi landing a Abuja ko Lagos sannan wasu kuma direct ne,
Mas’ud yace’ Kai Nima fa inasan naji wataran ana ga Alhaji Mas’ud nan tafe, Alhaji Mas’ud kaza Alhaji Mas’ud Malam lokacin Zan baza hajata nake fada maka,
Mus’ab yayi dariya yace’ zaka baza haka da ‘yan Mata kace,
Wawan burki ya taka Allah yasa lokacin sun shigo anguwa ne babu mutane sosai, San yayi gaba yace’ Kai ana zancen hankali kana wani zance naka da daban abinda yafi so banza kawai ana maka zancen irin idan Nayi kudin nazama Alhaji sai anjirani idan jirgi zai tashi muma yarda ake muke jiran wasu,
Mus’ab yace’ Kai wallahi na tsani Abu nan,Kai kaji takaici waifa kaga wannan tafiyar Sai da mukayi awa biyu a zaune a cikin jirgi, tafiyar da bata 30 min ba, Amma sai da mukayi awa biyu muna jira daga karshe har yazo yafa Shiga kawai ya fito, yace yayi mantuwa, yasha Allah ya isa ba laifi nake fada ma,kuma beyi tafiyar ba,
Mas’ud yace’ Allah sarki kace shiyasa ranar naji muryan Ka wani irin Ashe ashe,
Kaidai Bari twinny, Yana ga Ka kawo mu gidan Anty Safiya bayan munyi Mata sallama tun dazu?
Yace’ Kai yunwa nakeji idan munci sai mu ansa nasu mu kaima su,
Hakan yayi kyau,
✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan sunyi sallah sun kwanta,tana kwance a pillow shikuma yana kwance Yana kallanta ya dafa hannun sa da fuskar shi,ita kuma ta rufe Ido,