A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yace’ ke kika fara fada min zancen mahaifiya ta, sannan kinyi gaskiya da kika ce dole za’a samu ‘yan uwanta, dole tana dasu,Amma abinda lurar anan shine yarda suka barni basa nemana Nima bazan neme su, yarda suka kyaleni Nima haka Zan kyalesu,
Tace’ to idan kuma mahaifiyar Ka tana da Rai fah?
Murmushin takaici yayi,
Yace’ Mi Amor kidena damuwa da damuwa ta,Nima kaina na dena damuwa bare kuma ke, kisawa zuciyar ki salama kidena bin al’amari na,Kinji ko? Idan ina da uwa har yanzu a raye to Yakamata a ce ita ce zata nemi ni,bani ba,itace tasan gidan Mahaifina itace tasanni, tace zata iya nemana,ba Nima,taya Zan fara nemanta duniya fa da fadi,waya sani ma ko kasar da bansani ba taje? Kauyika suna da yawa garuruwa suna da yawa unguwanni suna dayawa,kasasge suna da yawa to yakike so Nayi?
Tace’ at least ya kamata Ka fara,
Yace’ kinga Dan Allah kiyi hakuri Dan Allah karma ki Kara min zancen na dena Karna dena kin gane ai?
Ganin kamar ranshi ya baci abinda kuma bata so Kenan ta bata masa Rai, zuciyar Shi har wani bugawa take alamar abin na masa ciwo, Rasa abinda zatayi tayi kawai ta hade bakinsu daga nan kuma aka Lula.
????????????????????????????????
Suna zaune kowa da system a gaban Shi ana fama da aiki,
yusuf yace’ wai ni ina Alkhakin namu ne, a kawo mana munayi muna ci muna korawa,
Yaseer yace’ taab ai tunda bakaje ba Anyi ba Kai,
Ummu tace’ wallahi kuwa, kaidai Bari,
Yusuf yace’ yanzu de rowa za’amin ko?
Ummu tace’ to muma iya Cincin din nan na dazu aka bamu da alawa kuma mun cinye,sai gobe tace muje mu ansa,
Yusuf yace’ kai karku Rana min hankali mana, wannan cincin din Naga Anty ce tayi,kawai kuce Baku jeba,
Yaseer yace’ to sai me ba’aje ba din,
Ummu tace’ munje basa nan Amma gobe Insha Allah zamu koma,
Yaseer yace’ exactly ‘yar gidana gobe zamuje idan mun dawo daga school yarda zataga irin mun gaji a zubu dayawa ace ku kaiwa Mamanku,
Yusuf yace’ kun Shiga uku da kwadayi kudai wallahi kuma Allah ya yaye maku,
Hakkin mune fah,
Haka yake Dan gidana hakkun maganar Ka gaskiya ce,
Zaiyi magana akayi sallama aka shigo Sameera ce ta shigo,dukan su Ido suka zuba Mata, ta Galla masu harara,
tace’ ba amsa sallama sai zuba min Ido,
Ummu tace’ Yaya Sameera lafiya?
Anty da ta shigo tace’ ba’asani na ina ruwanku kunku tazo?
Sameera tana shigowa tace’ mama Dan Basu taba ganina bane,
Shiru sukayi basuyi magana ba ita kuma suka gaisa da Anty,Abie ya dawo suka gaida shi Anty ta tashi ta tafi,
Sameera dawowa tayi kusa dasu inda suke a kasa ta zauna tace’ yusuf yaseer ina ta jiranku Naga kun dawo kunki nikuma bacci nake ji,
Yusuf yace’ to meya faru yau kuma?
Tace’ tambayar ku zanyi?
Yaseer yace’ munaji,
Tace’ Zaku iya tuna Yaya salama?
Yusuf yace’ meya faru kuma ?
Tace’ na manta da ita sai yau da wani yazo,
Yaseer yace’ wani Mai mota latest CRV, Baka ?
Tace’ eh, Shi,kasan shinee?
Da zamu shigo muka gan Shi,
Tace’ shine,daga na fada masu yarda sukayi,
Tace’bansan ya akayi na manta taba,Sam na manta abin mamamk yake bani kuma har yanzu ban iya tuna kamarta ba ko kadan,
Yusuf yace’ Kin fadawa Mama?
Yace’ Kar na fada masu kawai muyi aikin mu biyu sai ku dana fadawa……
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
39
Abba babu abinda yake zirga zirga a daki shikenan yanzu beda wani shago,sai company biyu da kuma business din da yake Wanda ko matar Shi batasan Yana yi ba, Zama yayi Yana tunanin mafita, mama ce ta shigo,
tace’ Alhaji wai Dan Allah bazaka fada min abinda yake damunka ba? Tun jiya kake cikin damuwa fah,
Numfashi yaja yace’ saratu bazaki gane ba,
Kamar bazan gane ba? Sai dai idan ba’a fada min ba,
Yace’ kinsan de munsai da shagunan mu sannan kuma mun fara gina katafaran asibitin mu,kinsan idan mun Gama zamu Sami kudi sosai a cikin sa, to orphanage din dake Lagos Ai kinsan Shi shine wani bature daga can Paris ya taya Shi, wai ya taba zuwa shine aka bashi number ta,kuma beda lokaci sanda yazo Amma yanzu zai zo sai mu zauna,
Tace’ indai ya taya da kudi dayawa inaga ai ba matsala,
Yace’ kudin, a dollars ma zai bayar da kudin,
Tace’ to kawai a sayar mana,
Yana zaune aka masa waya, dagawa yayi, abinda aka fada masa yayi saurin mikewa, dandanan zufa ta keto masa ya tashi tsaye bema Gama Jin abinda akace ba,ya kashe wayar ya Fadi reras a Ka gado, mama tayi kansa tana Kiran sunansa Mahmud Mahmud Alhaji Ka tashi mana, ruwa ta zuba masa shiru babu motsi ga Yara duk sun tafi makaranta da gudu tayi dakin Sameera itama bata nan bata dawo ba, fita tayi ta Kira driver yazo suka kama Shi suka a mota da gudu ta koma ta dauko hijabinta tana kuka, suka tafi asibiti.
Abba ????
✨✨✨✨✨✨
Dakyar ta tashi ta Shiga kitchen sauran kayan da bata Adana ba ta karasa sa su inda suke, ta hada masu breakfast lafiyayye ta haddan tea yasha kayan Hadi shayi, ta jera a dining, tayi wanke wanke ta gyara inda tayi girki, gidan ta tsab yake shiyasa ma bata tarki Shara ba kawai turaren wuta tayi ta fesa Freshener shikenan, abinda tayi, daki ta Shiga taga har lokacin bacci yake wanka tashiga tayi ta fito ta shirya kayan Sawa ta Rasa Sam ta Rasa wanne zata saka, ita bata San wannan kayan ganewa ce ba’ayi ba, dakyar ta samu wani Riga da skirt English wears masu Dan Karan kyau tasaka ta hada karami bakin Vail ta daura akanta ta Kara fesa turare, ta kalli taga goma saura, yake ta uban bacci ko baza Shi wurin aiki bane.
Gadan ta hau ta kwanta ta shige jikinsa, a hankali ya bude idansa ya ganta rungume ta yayi ta baya,
yace’ Mi Amor,
Tace’ uhm, Ka tashi ko bazaka aiki ba?
Yace’ Amma de kinsan ba tashi na kika so yi ba,
Tashi tayi daga jikinsa tace’ Ka tashi tou,
Yace’ ya jikin?
Harara ta Galla masa tace’ bansani ba,
Murmushi yayi yace’ to shikenan ni Bari na duba na gani ko ya….
Da sauri ta tashi,sai dai bata Ida tashi ba tace’ washh Allah zafi wallahi,
Zuwa yayi yace’ sannu baki Shiga ruwan zafi bako?
Turbune fuska tayi tace’ Naga de da zafi,
Yace’ to naji, taso muje ki Shiga,
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da bracelet din hannunta tana cuno Baki, sunkuyawa yayi daidai kunna ta yace’ hala kina so a Mai maita ko?
Juyowa tayi da sauri sai suka hada goshi sukayi gware kowa dafe goshin sa yayi, atare suka ce
yace’ kinga ko?
Tace’ kaga ko?
Hannunta ya kama suka tafi ita de tana dafe da goshinta tana mulmulawa taji zafi ba laifi, har dakin sa ya kaita,
yace’ jeki hada min ruwan ka,Naga kin warke harda su gyaran parlour,
Marairaice wa tayi tace’ komai fah a hankali nakeyi, daurewa nake,
Shi kansa yasan tana da dauriya,kuma tayi dauriyar Amma sai, yace’ a haka?
Ai bangani ba,
Fakar idansa tayi Yana cire Kaya ta Kara Galla masa harara, ta shige toilet ta hada masa ruwa zata fito sukayi kicibus shikuma zai shigo matsa masa tayi sai da ya shigo zata fita ya rufe kofar, kwalalo Ido tayi zatayi magana,
Yace’ Wana kama?
Gabanta taji Yana faduwa, tace’ to menayi?
Tana kif kifta ido,
Yace’ laifi biyu, kin harareni dazu yanzu ma kuma kinyi, sannan yanzu kuma kinzo zaki bigeni Ashe ma uku ne ba biyu,
Tace’ yaushe din Zan bige Ka?
Ohh kin yarda kin harareni din Kenan?
Juyar da Kai tayi, yace’ ga kuma wani laifin,
Tace’ babu kyau magana a toilet de,
To shikenan karshen magana kawai punishment dinki shine kimin wanka,