A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cak ta tsaya da kukan tace’ me Kake fada haka Baffa?
Biyun babu? Babu ni babu ita? Mekenan? Kasanta? Meye alakar Ka da ita? ……
????????????
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
37
Kofar gate din ta bude tana budewa ana hankado kofar Allah ya rufa asiri ta matsa, tsayawa tayi sororo tana kallan Ikon Allah, mutane suka Gama shigowa har yara sannan,
Mariya tace’ ke Dan uwarki kina ji an bubbuga maki kofa Amma sai lokacin da kika Dama zaki bude?
Ummusalma kuwa sauran rahamar dake tattare da ita a cikin second daya ta mayar da ita ta tamke fuska,
tace’ Ku shigo,
Yarinya Kenan zaki sani ne wallahi, mu Shiga daga ciki,
Sai da sukayi gaba ta bisu a Baya, Suna Shiga sukaji wani daddan kamshin da sanyi ko makiyi ta burge Amma Banda su,bahaka suka so ba,
Saida suka Gama ya tsine tsine su suka zauna itama ta zauna fuska a daure,
tace’ Ina kwanan ku,
Mariya tace’ kut, ke don uwarki mu zauna ki zauna?
Zakiyya tace’ renin Hankali ne mu zauna ta zauna a kujera ga sa’anni ki ko?
Khadija tace’ wannan ya nuna wata Rana ma hada duwawu zamuyi,Ashe ke a kauyen ma tacacciya da Mai ce ko?
Mabruka tace’ Wallahi babu abinda zai hanani cin uwae ‘yar nan, kutrin renin Hankali,
Habiba tace’ hmmm ai ni duk kun ban mamaki wallahi Anty Mariya, bata San mu suwaye bane Ku Mata uzuri mu fada Mata idan yaso sai ta bata mu girman mu,
Ummusalma tunda suka fara ta sharesu wayarta ma ta dauka da abinci tacigaba da ci tana jinsu tana Danna waya ba Dan tasan me take ba, tana gamawa kuwa ta tashi ta Shiga kitchen ta wanke plate din sauran abincin ta duba ta kawo wa yaran duk santa da yara ki tayi sun fice Mata aka wannan yaran de,
Ajjewa yaran tayi a kasa inda suke suna wasan su, sannan ta juyo ta kalle su a tsayen da take,
tace’ Ina Kwanan Ku?
Akusan tare sukayo kanta ko gigau batayi ba bare ta durkusa rike kuguma tayi, suna kara sowa ta saki wani uban Wawa ihu Tayi kansu sai suka koma da Baya sun zata aljanune, ganin sunyi Baya yasata komawa ta zauna,
tace’ Nasan Ku mana, ba Mariya bace da Zakiyya, Khadija, Mabruka, Habiba, ina kune? To ai nasan Ku sai me kuma? Yayun mijina da kannansa yayu biyu kannai uku haka ko ba haka ba?
Tabbas ni ‘yar kauye ce kuma asalin tushe Kenan,kuma kuma ai a kauyen kuke asalin Ku Kenan, Abu na farko da bazan iya jjraba kuma bazan iya dauka ba shine rashin mutunci Ku da wulakancin Ku bazan dauka ba bakuma Zan laminta ba, idan zaku sasanta kanku Ku sasanta Amma ni dai a’a bade niba,
Murmushi tayi Wanda kana gani kasan na mugunta ne, tace’ idan Ku kama kanku Nima na kama nawa,bature yace’ respect yourself before somebody respect you,
Ohh sorry fah Ashe na manta ba’a San wannan ba,
tace’ tunda ba wurin kuka zo Bari na Kira muku Shi ne ya Dan fita, Amma bansan hayaniya please, kun gane?
Tashi tayi tace’ two min please?
Tayi gaba ta barsu da sakakken Baki suna zara ido,sufa sun zata zasu ganga wata kucaka da ita ‘yar kauye Mai Hi da hya sai gashi sun ga akasin haka,
Khadija tace’ Bari ta fito lalle ma yarinyar nan wallahi ta Gama Rena mana hankali cab zata fito ai,
Mariya tace’ kuyiwa driver magana ya fito mana da kayan mu yasan nayi,
Zama sukayi suna cika suna batsewa zasu fashe, bata jimaba ta fito da jug da Trey a hannun ta ta ajje,
tace’ kunsan gidan Amarya sai ankawo Mata itama sannan ta bayar,
Bata jira cewar su ba tayi gaba tayi shigewarta daki,
Khadija ce ta buda jug din batasan sanda wata uwar ashar ta fito ba daga bakinta ba tace bakin ruwa,ruwan fanfo, ruwan girki ruwan flower shita bawa ‘yan uwan mijinta Bura uba ma,
Zai dawo ai zai hadu damu,ni ai yayar Shi ce Dan uban Shi dole yayi abinda nake so,
Ummusalma kuwa kiranshi tayi,kamar jira yake yadaga, shiru tayi shima shirun yayi,
yace’ sai yanzu kika tashi?
Tace’ uhm,uhm,
Yace’ ohhh damba a kusa nake ba ko?
Tace’ menayi?
Bakiyi komai ba,
Yace’ kin tashi lafiya?
A,ah,
Subhanallah me ya faru ?
Ba Kaine ba?
Ni fah? Danayi me?
Kaine ka,..ka..Ka wannan,
Murmushi yayi ya jingina da kujeran da yake Kai,Yana shafa kansa,
yace’ na me? Fadi ma?
Ka wannan fah uhm uhm Naga de,
Yace’ shikenan tunda kinki fada,abinda za’ayi shine Bari nazo gidan sai ki fada ko?
Zan fada fah,
To inaji,
Daman fa kawai jikina ke min ciwo,
Ikon Allah sannu to,sai ina kuma?
Shiru tayi tana jinsa,Yana magana yarda yakeyi a hankali kamar ma baya so,bata San maganar ta ce ba tasa masa kasala,
yace’ kin yi shiru,
Tace’ idan zaka dawo Dan Allah Ka taho da ruwa,
Yace’ Okay sai me kuma? Da magani ko?
Murtuke fuska tayi tace’ um,um, dade cookies biscuit da chocolate,
Yace’ to yarda kika ce haka za’ayi Mi Amor,
Adiós,
Sai da ya kashe ta tuna bata ce masa sunyi Baki ba,tabe Baki tayi, ta Kira Maman Sadiq,
Maman Sadiq tace’ kinji ni shiru ko?
Tace’ a,a bakomai, kun dawo lafiya?
Maman Sadiq tace’ lafiya qalau alhamdulilla, ina fatan wurin aikin naki normal de,
Murmushi tayi tace’ Maman Sadiq Baki sani bako?
Mefa? Ai sai anfada min zan sani,
Tace’ nafa yi aure,
Ke, auren gaske ko na wasa?
Dariya tayi tace’ na gaske mana,daman ana auran wasa ne? Sai kinzo zaki ji,
Amma Dana fi kowa Murna, kuwa, yau ko gobe zaki ganni kuwa,
Daga dawowan ki?
shima Baya nan, kuma daman nace masa ai Zan fita gaida Yan uwansa kinga na biyo ai,
To shikenan Amma ba biyowa zakiyi ba, zuwana na musamman ne,
Dariya tayi tace’ to shikenan yarda kika ce,
Sallama sukayi ta kashe,tana kashewa ana banko kofar,
Anty Mariya ce da Khadija suka zo,tana daga kwance tagan su,
Tace’ lafiya?
Uwarki nace,
Khadija tace’ ko baki jiba na Kara da ubanki,
Kallan uku saura kwata ta watsa masu
tace’ Dan kunga ina rabuwa da Ku shine zakuyi ta zagar min uwa? Yanzu kuma harda uba? Taaab,
Ta juya ta cigaba da latsa waya,
Bata ankaraba suka fardota daga Kan gadan sai data bige sosai a hannu da kafa,dayake ta iya boye emotion dinta ko a fuska bata nuna ba, har suka kawo ta parlour suka sata a tsakiya wannan ya dungura wannan ya dungura, bata tanka masu ba, ita dai tana zaune a tsakiyar su tana Jin zagin debe albarka da suke bata, ko digon damuwa babu a fuskarta balle tayi musu kuka, kamar daga Sama sukaji ta zuduma uban ihun ta fara kuka ta kuma takure a gefen kujera,
tace’ Dan Allah Anty Mariya kuyi hakuri Dan Allah,kuyi hakuri,
Duk abinda ya faru cikin second din da beze wuce uku zuwa hudu ba Dan kifta ido sukayi suka ganta ahaka,
Ai kamar Kara masu tayi Khadija tace’ shegiya to wallahi ko uban ki da uwarki sunyi kadan tsinanniya kawai,
Mabruka ta daga hannu zata zabga Mata Mari taji ita an zabga Mata wani lafiyayyan ajiyayyen mari, a fuska, a tare suka juyo ganin waye,
Anty Mariya tace’ Binaif?
Yace’ na’am Mariya,
Fuskar nan tayi jajur da ita ya Ciro ya waya ya Kira Daddy, ya fita sai da suka gaisa,
yace’ Daddy kace su Mariya Kar su takara tako min kofar gida bare su shigo min cikin gida, meza sumin Bana bukatar su,
Daddy yace’ ‘yan uwanka ne fah, Binaif idan Basu zo ba waye zaizo ?
Yace’ Daddy Yan uwa fa kace? Daman ina Dan Yan uwan da ya wuce Mas’ud da Mus’ab? Banda su, su kadai ne kawai Yan uwa na,
Daddy yace’ Binaif me haka kake fada ne wai?
Tsabar bakin ciki har wani hawayen takaici yaji ya zubo masa,
yace’ Daddy haduwa sukayi dukan su suna zagar min Mata,ba iya zagi ya tsaya ba harda duka,idan na fada maka bazaka yarda ba, nasani ai, idan ma Baka dau mataki ba akai ba,to ni Zan dauka, daman ai bansan suba,
Murmushi yayi yace’ kodayake ni ba DAN SO bane ba kuma za’a soni ba, sani nasan da haka, Amma daga yau Daddy kasani wannan shine Karo na farko daman Dana taba fada maka Ka dau mataki wannan kuma shine Karo na karshe da Zan sake fada maka wani Abu daya dagance ni, Nagode Dad,
Dad kayi hakuri da abinda na fada Ka huta Lafiya,
Ya kashe wayar sa tare da goge hawayen sa, ya Shiga ciki, tanan yarda ya barta bata motsa ba sukuma sai zaginta suke,be tankawa Daya daga cikin su ba, yaje ya daga ta ya dauke ta cimak ya wuce dakin sa da ita.