A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
zatayi magana yusuf yace’ dalla malamai kuyiwa mutene shiru,kunzo gidan mutane kuna masu gulm, kude baza Ku canza ba,kun girma Baku san kun girma ba,
Hada sukayi zasu kwashe da dariya sai kuma aka gimtse aka kowa ya matsa, Yana Dan kunshe dariyar sa,
Yusuf yace’ Munafikai, kamar na Allah,
Basuyi magana ba suka kyale Shi.
A daki Yana Shiga ya ganta ta kwanta inda tayi sallah, ta fara bacci, zuwa yayi yada gata yace’ ba’asan baccin yamma fah,
Turbune fuska tayi tace’ to bakai bane, kaje Ka zauna?
Yace’ to naji,nadena Zama,gaisawa mukayi da mutane da najini masallaci kuma sai muka an taba hira, shine na taho,
Yace’ ba wannan ba kinyi Baki,
Tace’ Nayi Baki ko munyi Baki?
A,a wannan bakin na naki,kuma na musamman ne, sannan ni na kawo su, wanne tukuici za’a Bani,
Murmushi tayi tace’ Zan Baka wani special Abu, Mai kama da…. Guess what?
Kallanta yake yarda take murmushi yasan na mugunta ne, tashi yayi yace’ Bari naje na sallame su tou,
Tace’ a,ah Zan Baka fah,
Yace’ ai Naga kamar wani mugunta za’a ban shiyasa,
Murmushi tayi ta tashi tace’ Bari naje ni nagansu ko lemun ba Baka siyo ba kuma nace Ka siyo,
Riko hannunta yayi yace’ ahaka zaki fita? Kallan kanta tayi ganin jallabiyar sa, tace’ to ai Banda Kaya,
Yace’ Zan ara maki, wata Riga Amma fa ina one condition,
Tace’ eh inaji kaga mun bar su a parlour suna jira kuma na dadi,
Sakinta yayi yaje ya dauko Mata wata doguwar Riga Mai Dan Karen kyau,veil din ta ne kawai karami,
Karba tayi tace’ wow tayi kyau,
Beyi magana ba ya bata ya fita, ita ma a gurguje ta zura rigar ta yafa Dan veil din, rigar cib ita,kuma ta Mata kyau fita kitchen tayi ta taga kayan an ajje wasu a Sama wasu a kasa ga Katan na lemu da ruwa da fruit,
Tace’ Ashe ya siyo kayan Amma be fada ba, yabarni Nayi bacci, lemun kawai ta dauka da fruit ta wanke tasa ‘yar karamar wuka akai, ta dauko masu snacks dayawa ta daura Akan babban tray ta fito parlourn tana dosuwa tafara jin gabanta na faduwa haka kawai, da murmushi a fuskarta tayi sallama bayan ta karaso bata kalle ko Daya daga cikin suba sabanin su da sallamar ta sukaji suka juwa Banda Yusuf dayake Danna waya Suma ganin kwakwaf ne yasa su juyawar sai kuma suka kame,
Sai da ta ajje sannan ta dago da ganta sukayi four eyes da yaseer dake kallanta juyawa gefen yusuf tayi shima ta kalle Shi,ta juyo ta kalli ummu ta kalli Binaif dake musu murmushi, dakyar bakinta ya iya furta
yusseer??
A sukwane yusuf ya dago yaganta,tashi zaune yayi yace’ Yaya? Salama? You?
Girgiza masa Kai tayi hawaye na zubowa daga idanta shima kukan ya fara yaseer ya guje ya taho ya rungume ta gam,shima yusuf zuwa yayi ya rungume ta saura kadan ma su Fadi tare Allah ya tsare, kuka suke su Duka dakyar ta samu karfin hugging back,tana shafa kansu babu abinda take tunawa sai sanda suna Yara da suke rungume ta,
Breaking hug din tayi,tana goge hawayen masu hawaye tace’ ya isa haka yusseer is enough,
Suma hawayen suke goge Mata, murmushi tayi masu taje ta zaunar su a Kan kujera ta Shiga tsakiyar su,
Ta kalli Binaif tace’ a,ina kuka hadu?
Yace’ a kofa nagansu,
Ummu tace’ zuwa mukayi fah, anan unguwar muke,
Yusuf ya dalla Mata harara yace kunzo kwadayi de,
Yaseer yace’ ehh din anzo kwadayin kuma sai muka tarar da wani abu Mai ban mamaki,
Murmushi tayi tana Jin wani farin ciki har cikin zuciyar ta,
Yusuf yace’ Yaya,Amma meyasa? Meyasa Baki dawo ba? Meyasa yaya? Yanzu da mun manta ki fah? Kina ganin yin nesa da gida shine solution? Ehh yaya?
Kwalla ce ta zubo Mata tace’ yusuf bazaka gane ba, ba….
Tashi yayi ya tsaye cikin fada fada da daga murya yace’ mene ban gane ba? Kina tunanin bamu San komai ba? Kome kike so kice?
Tace’ yusuf,
Yaya enough please,Nafa sa Jin dalilinki na kin komawa gida, tunda yanzu gani gaki, Amma kisani ko kin koma ko Baki komaba har yanzu ana bibiyarki, har yanzu Abba be manta kiba, infada maki wani Abu ma, Abba Nemanki yake ruwa a jallo, kinsan inda ya ganki?
A park,store unguwa,
Daga ita har Binaif saranda sukayi suna kallanshi bata taba sannin ya ganta ba, mekenan? Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un,
Yaseer yace’ yaya,
Sai kuma yayi shiru yana kuka, itama kukan take, Binaif ne ya taso ya dawo kusa da ita ya rungumota jikin sa Yana shafa bayanta,
yace’ komai yazo karshe,idan ma bezo ba ya kusa zuwa karshe, komai ya kare Insha Allah,
Yusuf yace’ Haka kuke gani Amma be zoba,yanzu aka fara wasan,
Yace’ Abba next week Monday zai Kai karar ka koto cewan kaje kayi amfani da takardun bogi kace yasai da maka da company Alhali besan anyi ba,Bama ya gari, sannan kuma ya maka wani mugun sharri Ka Shiga gidan sa kamasa data Ka sace takardun mallakin sa, gaba ki daya,
Dagowa kusa da yaseer ya zauna, yace’ ahakan ne komai yazo karshe?
Sai yanzu tunanin Binaif ya kawo masa abinda take nufi da safe,sai yanzu yasan I a ta dosa, tabbas yarda ya fada ne komai yazo karshe.
Wani shegen murmushi yayi na gefen Baki,
Batayi mamaki ba tasan zai aikata,
tace’ Ai beda komai shiyasa yanzu yake so ya fara mallakar Takardun gaskiya,
Binaif yace’ me kike nufi?
Gogen hawayen ta tayi tace’ yanzu beda shago, ya siyar, shagunan sa Duka ya sayar ya dawo namu, yanzu kawai wannan companyn ne guda biyu sai orphanage kuma yafi samun kudi a business dinsu na Lagos, sabida haka dole companyn sa na can zai tsaya cak.
Murmushi tayi ta tashi zaune ta Dora kafa Daya Kan Daya,
Ta kalli Binaif tace’ ya Kai karar Ka, muma zamu Kai tashi.
Yusuf yace’ kamar ya?
Tace’ kamar yarda abin yake,
Ummu ta kalla tace’ Ina uncle dinki,
Gaban Binaif ne yafadi Ashe fa bata San yayi accident ba,
Shiru sukayi hakan ya tabbatar Mata da wani Abu ya same Shi, murmushi kawai tayi batayi magana ba,
Kowa shiru yayi Yana sakawa da kwancewa a ransa,
Yaseer ne ya katse shirun, yace’ Ummu kinga abinda nagani kuwa, yau akwai harka fah,
Dariya tayi tace’ Ai nagani shiru kawai Nayi akwaita Kam,
Yusuf ya balla masu harara yace’ kwadayayyu kawai,
Yaseer ne ya tashi ya dauki tray din data kawo ya baje kafa ita ummu tashi tayi tazo ta zauna suka baje suka fara ci, sai da suka ci dayawa,
yace’ Yaya Zan iya ci kuwa?
Balla masa harara tayi tace’ karkaci Ka zauna,
Yace’ ai lemon ne ba sanyi shiyasa, wallahi Alhaji kazo kaci nidai ba ruwana tam,
Ummu tace’ nan gidan mune yayar mu da yayan mu, koka ya kace Dan uwa,
Ai maganar ki haka take, yaya kawa,yayane, ta o ina mu ba ruwan mu mun hada,
Binaif girgiza Kai yayi ya tashi ya bar masu wurin, Allah yasa ba Mas’ud,duk ranar da Mas’ud ya dawo sum a suka zo yasan akwai ciwon kai.
Yusuf zuwa yayi ya dauka lemu ya fara sha, yana yi Yana hadawa da cincin, sai da sukayi nak,
Tana zaune tana kallansu ji take kamar a mafarki yau gata ga yusseer,
Yaseer ya matsa Kuda Ummu yace’ samana a jaka alkhakin kinji?
Tace’ to, Kar ace mun fiye hadama,
Shiru yayi shidai beyi magana ba, ya kwashe ya mayar Kan table,
Yusuf yace’ Ku tashi mu tafi,
Cab tafiya? Yanzun?
To gidan ku za’a maka?
Ummusalma tace’ Yaseer, kaza tuna wani Zane Dana taba zana maka?
Yace’ wanne Kenan?ai dayawa,
Wani Zane,na wani mutum,
Yace’ awww Yana nan ma Zane, qalau dashi, zanen fah Mai gadin school din mu ne lokacin da kika zana min ma befi da kwana daya ba ko biyu ne ? Ya bar makarantar,
Numfashi taja, tace’ ok,
Yace’ lafiya?