A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Asuba nayi ta tashi don ta Riga da ta saba, alwala tayi, dan lungu tagani a wurin gefen gadonta a nan ta shimfida daddumar ta tayi raka'atul fajr tana Azkhar har lokacin yayi tayi sallah,tana so tayi karatun Qurani kuma bata so ta tsahi Sahr, tasan bakowa ne yakesan haske ba idan Yana bacci,kamar ita duk baccin da take idan aka kunna haske to sai ta tashi,hakanne yasata kin kunna hasken,kuma babu duhu a dakin kasancewar street light dayake ko ina a wurin hasken yana shigowa dakin.wayarta ta janyo ta bude Qur'an app, kararu ta fara ahankali yarda sautin bazai dame wani ba,tana har gari ya fara haske sannan ta je zata koma gado,Sahr ta ga ta tashi,ta nufi toilet,ita dai kwanciya tayi kawai,Amma kuma ga mamakinta data fito daga toilet din wurin da tayi sallah ta nufa hijab sannan ta gyara sallayan daidai gabas sanna ta tayar da sallah,kawal kallanta take daman musulma ce?
Tana cikin wannan tunanin bacci ne ya dauketa.
Bata tashi ba sai tara,tana tashi toilet ta nufa ta wanke Shi tas sannan tayi wanka,koda ta fito Sahr ta tafi dakinsu,mai ta shafa ta fesa turare,tasa kayanta,gadon ta gyara Duka biyun,sai tayi rolling ta rataya jakarta tana Shirin fita sai ga Sahr tazo,tare suka fita suka je cafeteria,ita de dakyar taci abincin daga karshe ma sandwich da lemo kawai tasha, Sahr na Mata dariya,da haka de suka gama, school din suke zagaya wa Sahr ce ke nuna Mata ko ina sun sha yawo a cikin school din sai da lokacin Azahar yayi suka koma daki,Sahr ta kawo masu abinci ita dai kawai tsakura tayi ta barshi,suna hira dukda rabin da kwatan hiran Sahr ce keyinta,ita nata kawai daga Kai ne da girgiza kai, Sahr kuwa bata damu don yayarta ma haka take bata magana kodan sai ta kama shiyasa bata damuwa don ta saba da hali irinnasu,a ganinta magana ne be dameta ba,har lokacin la’asar yayi suka yi,sannan suka fita zagaya campus,namma de sun zagaya dagana kuma suka samu kujera sukayi zaman su suna kallan mutane kowa na harkarsa,ahaka de suka tashi sukayi magriba, Ummusalma ce tace Sahr ta rakata zatayi siyayya,haka kuwa ta rakata sukayi siyayya,itama Sahr din tayi ba laifi,sun jido Kaya harda na girki komai da komai suka siyo,sungaji iya gajiya,sai tara suka dawo da Kaya nikiniki,wanka ta Shiga,koda ta fito taga Sahr ta jera kayanta a wardrobe,kallanta kawai tayi kafin ma tayi magana Sahr din
tace’Tace’na dawo nan da Zama idan dayar tazo sai muyi exchange da ita ko?
Kai kurum ta daga tama,itama daga nan shiru tayi,
Bayan sunyi sallah ta fito musu da snacks da dambu suka ci suka koshi,suka nemawa kayan su wuri,daga nan sai bacci.
✨✨✨✨✨
Washegari Monday da wuri suka shirya suka fita, direct wurin uncle din Sahr sukaje, Sahr ta masa bayanin komai,amsa takardun yayi yace” zai duba anjima su dawo su amsa, a haka suka tafi.
Dakyar dai yayi cuku-cuku aka samu suka bata course biyu physiology dà kuma business. Amma da sharadin idan batayi kokari zasu kwace daya su bar Mata daya,da haka aka barshi, clearance yayi Mata Duka komai da komai kawai sai lectures kuma ko yau ma zata iya fara Shiga. Sahr din ya Kira suka zo,
Yace’ sun bayar da duka biyun amma gaskiya da sharadin,idan suka ga bata yi kokari ba zasu ansa daya su bar Mata daya ne,don haka,ba ita kadai bama harke,kudage da karatu wannan makarantar tana San masu karatu sosai,kunji ko?
Godiya Sahr tamasa sosai da sosai,Yana tafiya Ummusalma ta rungume Sahr,sai hawaye,lallashinta tayi
tace’ ya isa haka ki dena kuka,yanzu mun Zama daya babu godiya a tsakanin mu ok?
Takarashe da goge Mata hawayen,tacigaba tace kinga muna da lectures yau kinsan yau Monday kuma kema kina ta business guda biyu,ga psychology yau har hudu muke da su ya za’ayi?
Kallanta tayi daga bisani
tace’ ai ba yanzu bane,muje kawai ta psycho din,haka suka tafi suna tafiya, sahr ta Mata hira har suka iso sahr ta zauna a gaba ita kuma Ummusalma ta zauna a bayanta don tafi son zaman seat na biyu,a haka Akayi masu lectures ba laifi don ta gane kusan gabadaya abinda aka masu,sai Azahar suka fito sukaje cafeteria sukaci abinci sannan sukayi dakin,bayan sunyi sallah,suka sake fitowa,wannan Karon tana da business saboda haka sai ta wuce sahr ma ta wuce, tana zuwa taji anacewa lecturer ba zai zoba,komawa tayi wurin sahr, lecturer har yazo Shiga kawai tayi ta zauna.
Washegari Basu da psycho sai ten ita kuma tana lectures 8 don haka ya riga sahr fitowa,koda taje ma ita kadai ce bakowa,abinda aka masu jiya ta fito tana karantawa,sai da kowa ya hallara akace ba zai zoba, direct ta wuce daya lectures.
Ahaka sukayi sati biyu suna suna ci gaba da zuwa lectures abinsu idan tayi Mata clashing sahr na koyamata yarda ya kamata,kuma balaifi tana ganewa sosai don a satin da suka fara lectures a satin ta afara karatu,kuma karatu sosai takeyi,tana googling abubuwan da ba’a musuba ma,sosai take karatu bakadan ba hada course is not easy amma kuma hausawa sunce sa Kai ya fi bauta ciwo.
Yau Friday Basu da psycho Amma ita tana da lectures,shiryawa tayi ta fita,da wuri tana so tayi karatun course din don bai taba zuwa ba amma tasamu abubuwan da zai koya masu kuma ta karanta sosai kamar an koya Mata,bakowa a class din samun wuri tayi ta zauna ta baje littafai tana karatunta hankali kwance abinta,tanayi har aka fara taruwa dahaka har kowa yazo,ita de karatunta kawai take dukda tana Jin hayaniya amma bata dena ba don bata hanata karatu,tana cikin karatu taji anyi shiru,ba’a surutu,a hankali ta dago taga meke faruwa,dagowar da zatayi taji zuciyar ta tayi wata irin buguwa,bata Jin komai sai sautin bugawa da kirjinta keyi,mezata gani BABA??(mutumin da ta zana)Amma kuma wannan yafi Baba haske kuma bashi da tsufan Shi,shikuma Baba a yarda taganshi bashi da wadata,duk bayanin da yake bata ji koda kalma dayace da yake fada ba bata ji komai ba,sai tsinkayo muryarsa da taji Yana fadar sunansa ABDALLAH ABDALLAH,daga nan bata karajin komai ba sai sautin bugawa da kirjinta keyi,tunda ya shigo take faman kallansa,bata kuma dauke kanta ba gashi ita ba sauraran komai take ba bayan sunansa saidai ta lura yayi shiru Yana sauraren wani abu sakamakon gyada kan da yake faman yi, bata Ankara a taji ta gabanta na fadin sunanta da garin da tazo dakuma meyasa take San karantar business, har an gama da kowanne row saura row dinsu,a halinda take ji batajin zata iya magana,bata gama tunaninta ba taji ta gabanta nacewa ta tashi, ita kadai tasan yatakeji a jikinta,gani take kamar kowa yasan halinda take ciki,a zahiri kuwa ba abinda ake gani,tattare da ita,
Ganin anyi shiru ba’a cigaba da maganaba yasa Shi dagowa karaf suka hada ido daman ita shitake kallo,yana dagowa suka hada ido,kallanta kawai yake,wani irin sanyi yaji yana ratsashi na musamman ,a take zuciyarsa tadena bugawa na wani lokaci,a hankali yasaki wata boyayyiyar ajiyar zuciya,sannan
yace’ am listening, your name?
Kallanshi kawai take,batare da tace komai ba,shima ita yake kallo,ganin bata da niyyar magana yasa ya tambayi daya daga cikin class members din, Wanda aka tambaya kuwa ca yace’ ai tunda ta zo babu Wanda ta tabayiwa magan haka take,su suna tunanin ma kurma ce tana ji Amma bazata iya amsawa ba,kallansa ya mayar kanta
yace’ haka ne,?
Batasan ma me akace ba kawai daga Kai tayi alamar ehh, yace ta zauna,Zama tayi akaci gaba da fada,har aka Gama daganan ya fara abinda zaiyi, Ummusalma da kyar tayi nasarar kwabar kanta ta fuskanci abinda ake masu dukda cewa tasan abinda ake Amma kuma rabi gwara ta Kara ganewa ai,sosai kuwa ta gane,suna gamawa ta dawo hostel kafin tadawo sahr ta dafa abinci ta fice,itama abincin taci Amma duk wani iri take ji,bacci tayi har lokacin sallah ya gota,ta tashi wanka tayi ta tayi sallah ta shirya kamar kullum cikin doguwar Riga tayi rolling ta fito,fita tayi tana zagaye gari,wani Dan shago ta gani na kayan pente pente taga kuma yarda mai shagon yake Zane,kayan zanen ta siya ta bada address din campus har dakin su,haka ta gama Dan zagayenta ta dawo,tana zuwa kuwa taga kayan da tasiyo a kofar daki bude dakin tayi ta Shigar da su ta ajje a balcony,ta dawo dàkin ta ,zauna sahr haryanzu batadawo ba,hutawa tayi tafa masu abinci,tayi sallah,Rasa abinda zatayi tayi Dan haka ta je balcony ta zauna tana kallan kasa yarda mutane ke hada hada abinsu, dauko kayan zanen tayi ta hada komai yarda yaka Mata sannan ta fara Zane batare da tasan metake zanawa ba,abinda tasani kawai tana tunanin AA ne(Abdallah Abdallah)koda ta Gama zanen Shi tagani ta zana sanye da bakaken suite yarda yake a tsaye haka ta zana Shi,zana wani ta kuma yi sannan ta zana Baba,a kusa dashi,kalla take tana so tagane menene bambamcin su saidai bataga wani bambanci ba,daukowa tayi ta dawo daki,cikin bedside drawer ta zuba su ciki.
Sai bayan magriba sannan sahr ta dawo, Kallanta tayi