A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranar da ta Shiga shekara biyu ranar Mas'ud yace zai hada mata Birthday idan sun taso daga makaranta sai dai a ranar aka neme su aka Rasa ko sama ko kasa kaf fadain Abuja babu su,tun daga nan Ummusalma ta dena walwala tadena dariya kullum ina Masud da Masab kullum zancen ta Kenan, ina suke har wani Zazzabi tayi bata cin abinci sai ance Mata ga su Masab nan zasu zo, a haka de ta Dan warware, kwatsam ranar da aka sallamu daga asibiti da daddare wuta ta kama a gidan mu, tashi mukayi muka fito Ashe daga ganin wuta kwatsam naci Karo da Mahmud, da matarsa Saratu,
Mamaki ya kama mu, sukace dayan biyu ko su bamu, Ummusalma ko kuma su mu Duka mu Kone,bayan yagama min Duka Kenan, komawa ciki nayi dakina, Maryam tace’ kar na Basu,
Nace’ Mata gwara ace ita rayu, nadauketa lokacin kuka take sosai itama ta tsorata ainun, kafin na Basu ita nasan zasu kwashe muhimman takardun ne, hakan yasa na canzawa komai suna nasa Ummu, sunan ‘ya’ya na Kenan,
Ina basu ita suka shiga suka kwashe komai, suka tafi suka Kara cinnawa gidan wuta, Allah yasa akwai wata karamar kofa ta dakina, tana nan muka fice muka tsira da ranmu, a gidan Mai gadin mu ranar muka kwana,gidan kuwa ya kone, washegari kuwa muka yi mukaje kafancan acan naji nakejin labarin Babana ya saki matar sa danta ya dauketa, sannan kuma Baba Umar da Baban sun tashi sun bar garin, muka dawo cike da wasiwasi muka koma Kano da Zama,dukda nasan Yana Kano, Amma haka muka dawo da Zama,bayan shekara Daya muka haifeki, nasha wahala kafin nagano Ummusalma da kuma yarda take, lokacin tana ss3 na Kai ki school din akace sai dai a saki a ss2 nami da a yiwa Ummusalma repeating dan kawai sabida ke, Allah yasa ita ma bata wani performance sosai aka kwayi Mata,sai dai kin komawa da tayi,sai a second term.
Shiru yayi yace’ yanzu kinji? Kinji komai kuma?
Itama shiru tayi can tace’ Amma kasan gidan su?
Yace’ gidan dana San su yanzu basa nan,
Tace’ Baffa waye yace a rabu nida ita ?
Yace’ bansan shiba, da alama de aiko Shi akayi,
Tace’ Baffa zanyi komai,
Inni tace’ ke Baki da hankali daman bansa niba? Mezakiyi Tou?
Tace’ Inni ai da da da yanzu ba Daya bane, nifa yanzu barrister ce, bawani Amina ba, agaban sunana akwai Barrister sannan ace Amina, kinga kwa ai da banbanci,
Baffa yace’ babu abinda zakiyi, kedai kawai kicigaba da taimakon Al’umma duk wata kiji alert ki huta,
Tashi tayi tsaye tace’ Haba Baffa wannan wanne iri Abu ne, a gaskiya bazan yarda ba, dole sai na Kai masu sammaci,
Baffa cikin wata irin tsawar da bai taba Mata bata yace’ Ina cewa Kar kiyi kina cewa sai kinyi?
Inni ma cikin wata irin murya ta tsantsanr bacin Rai tace’ idan kika kuskura kika sa bakinki a cikin zancen nan to ina Mai tabbatar maki, zaki Fadi kasa ne,biyun babu ukun zero,
Baffa tashi yayi ya yace’ kada ki fasa abinda akace,
Ya fita ya barta,
Tace’ Amma inni….
Idan Baki min shiru sai ranki yayi mummunan Baci,kin fimu Santa ne?
Tashi tayi itama inni tace’ Abu daya zan ce dake shine ki nemi yayarki, shine kawai abinda zance maki,
Tashi ge daki, tsugunnawa tayi a wurin ta fashe da kuka wanne irin Abu ne wannan? Sun Rabata da ita yanzu kuma sunzo sunce ta nemeta ta ina zata fara?
By: Hijjart
Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
41
Mama zaune a dakin da aka kwantar da Abba har dare be farfado ba,su yusuf sun tafi gida Sameera tun safe bata zoba, tayi jugum tana kallansa tunanin abinda ya faru kawai take har ya Shiga wannan conditio din, motsin da taga Yana yine ya fargar da ita,ta matso wurin Shi, da sauri taje ta Kira likita yayi gwaje gwaje sa yace’ Kar a fada masa abinda zai tayar masa da hankali,
Yafita,
Zama tayi a kusa dashi tana kallan sa, sannan ta jingina pillow a bayan sa ya da tashi, ta kawo bowl ta masa brush taba Shi Abu Mai Dan ruwa ruwa yasha, sunan zaune Sameera ya shigo,
Mama tace’ sai yanzu zaki zo? Tun safe na kiraki Amma sai yanzu?
Sameera tace’ yanzu ma ba zuwa Nayi ba, nazo ne nace maku na dauki kudi a dakin Abba zanje party, sannan kuma PA din Abba yace nace masa an sayar da companyn sa dake Lagos sabida Wanda suka hada business dasu kowanne gari na manta, sunce kome oho de na manta idan ya samu dama zaizo yayi masa bayani, nikam Nayi nan,
Ta kalli Abbab tace’ Abba Allah ya sauwake ya Karo lafiya,
Mama tace’ idan kika fita sai ranki yayi mummunan Baci wanne party ne zakije yanzu? Goma saura?
Har taje bakin kofa ta juyo tace’ mama Kenan,ai ba yau na fara zuwa ba,yau de kika sani Zan fara zuwa, partyn ma sai 12am za’a fara Shi, kuma bansan yaushe Zan dawo ba, so bye,ki Kula da Abba,
Tana kaiwa nan tasa Kai ta fice, zuciyar Abba wani irin tafasa yakeyi, Abu biyu sun hade masa,mama kuwa wani irin kuka ne ya kufce Mata ‘yarta? Ba yau ta fara ba? Tun yaushe Kenan? Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un,
Abba kansa sai da kwalla ta zubu masa babu bakin magana, yama Rasa mezaice, zuciyar sa ce kawai take bugawa jira yake ta fashe ya mutu ya huta, wani irin tukukin bakin ciki yake ji,ga wani Abu Mai kama da daci ya makale masa a makoshi,
Suna cikin wannan halin Yusuf da yaseer suka shigo,
yaseer yace’ Lafiya? Mama meya faru?
Yusuf yace’ Abba ya jikin?
Mama tace’ Yusuf Sameera ce,
Yace’ Sameera kuma? Me tayi?
Tace’Sameera shikenan nan Sameera fah?
Yace’ to mama sai Sameera Sameera kike cewa me tayi?
Tana kuka tace’ wai party zata je, kuma ba yau ta fara ba,me hakan yake nufi?
Yaseer yace’ ta jima tana zuwa Kenan? Watakila ma acan take kwana,
Yusuf yace’ ehh tabbas hakanne ma, tunda duk weekend batayinsa a gida ba?
Yace’ kawai sai dai hakuri mama kiyi hakuri baga munan ba?
Abba kulle Ido yayi bazai iya Jin wannan abun takaicin ba, tun yanzu? Ya fara ganin ishara? Inaga yaje gaba kuma? Besan sanda bakinsa ya furta Muhammad Maryma ba,
Da sauri mama ta dago da kanta tace’ Alhaji wa naji Ka ambata?
Yana hawaye yace’ abinda kunnan ki yaji,
Shiru tayi tana kallansa, to me ya hada wannan abun da su kuma? Mutanen da sun Dade da barin duniya? Shekaru kusan ashirin da Daya?
Yusuf yace’ Abba me sukayi?
Mama tace’ ba hurumin Ka bane,Ku tashi Ku koma, gida.
Tashi sukayi suka fita,
✨✨✨✨✨✨✨
Yau ta kama Friday suna zaune da yamma a Gaban gidan su,yana Mata tsifa, suna hiran su, suna dariya,shiru tayi
tace’ Baka tunanin zuwa mu gaida mijin Anty ummi?
Dena Mata tsifar yayi yace’ sam Bana wannan tunanin,
Tace’ ya kamata kuwa muje,ina so muje har Spain,
Yace’ Meyasa?
Kawai, inasan naje Naga inda maso……..
Sai kuma tayi shiru Jin Kalmar tayi tayi Mata nauyi a abaki,
Murmushi yayi Mai kyau ya cigaba da Mata tsifar,,
yace’sa ba,
Tace’ manta kawai,
Naki din na manta,
Tace’ azumi saura kwana nawa?
Yace’ maybe sauran sati uku zuwa biyu,bande Sani ba,
Tace’ hmmm, gaskiya muje mu,
Ina,wurinda masoyinki ya zauna ko ina?
Tashi daga Kan cinyarsa zata gudu ya riko ta
yace’ Ina zaki kuma?
Tace’ abinci zanje na daura,
Yace’ a,a indai Dan tani ne na koshi, maci abinda muka ci da Rana,
Zatayi magana ya janyota ta fado kansa,ta kuwa kifa kanta a kirjinshi ta rufe fuskarta,
Yace’ ohh ni Abdulshakur Binaif,nifa banga abin kunya ana ba, kawai daga fadar abinda kika fada?
Yace’ fada min, wai kina ma,
sai kuma yayi shiru yasan ko giyar wake ya sha bazata fada ba, yanzu wata irin kunyar sa take ji, musamman idan suna hira, hira Daya biyu to baza’a kare lafiya ba, daga karshe ma tayi shiru, sunkuyawa yayi daidai kunnan ta,
yace’ nidai wannan kunyar tana cuta ta fah,
Shigewa tayi jikinsa ta kwanta,tana sauke numfashi Sam bata San yake Mata magana acikin kunne,wani irin takeji,
Yace’ ko a daga ni, ko kuma na Rama, ana cuta ta fah, ko dan Baki san menake ji bane idan kin denne ni haka?
Tashi tayi ta zauna tana sunne Kai ta juyar da kanta, kwanciya yayi a cinyarta Yasa hannu ya juyo da kanta yace’ kinsan sanin menake ji?