A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daki ya koma ya dauko key din ya bude kofar,
yace’ jeki kirasu,
Tashi tayi ta fita tayi knocking a bakin kofar su shiru,da karfi tayi daga can yaji,
Mas’ud yace’ wai waye ne?
Sarai yasan itace, shiyasa ya fada haka,
Zuwa yayi ya bude yace’ kinzo kin dameni, lafiya?
Banza tayi dashi tace’ kalla agogo,
Tare da balla masa harara ta wuce tayi tafiyar ta,
Komawa yayi ya Kira Mus’ab suka taho tare a hanya suka tarar da ita,
Yace’ ohh mutum na tafiya kamar Hawainiya, ko snail ande ji kunya,
Bata kula shiba ta bude kofar tashiga tana shiga Binaif yace’ yunwa nake ji, akawo mana anan,
Turo Baki tayi, ta wuce Shi ta je ta dauko abincin a dining ta ajje ta kuma komawa ta dauko ta ajje, sai da tagama Shirya komai sannan tazo ta zauna ta zuba mash ita da Binaif ta tura masu gaba su,
Saukowa sukayi kasa Binaif ya matso daf da ita ya hade a plate daya ya fara bata a Baki,
Mas’ud sakar Baki yayi Yana kallan ikon Allah,can de ganin bazai iya daurewa ba, yace’ bb bafa hannunta ke ciwo ba, kawai tsabar tabara ? Wannan jibgegiyar katuwar uwar?
Mus’ab yace’ wai Kai ina ruwan ka ne, kaga a irin haka tam,
Yana cin abincinsa yace’ barni nagani na Tanka ato,
Cigaba da bata yayi,itama ganin haka yasa ta dauki fork ta bashi ya bata ta bashi, sai can,
tace’ wani waye yace Baya cin cheaps da kwai?
Binaif yace’ wani ne Mai kama Mas’ud,
Mas’ud yace’ ni? Yaushe? A’ina? Wacce Rana?
Tace’ waida fah wani ne m yace hakan amma yanzu harda batar hanya,
Mintsinta Binaif yayi yace’ dawa kike?
Ouch! Da zafi fah,kamar cinnaka,
Mas’ud yace’ Kujita irin tasan cinnakan nan,
Mus’ab yace’ da cinnakan ya manna maki gwara kunama ta Dana maki,
Tace’ Amma a wurinka ba’a wurin salama ba, ato,
Binaif yace’ Cinnaka da ya ciji Mas’ud ranar bamuyi bacci ba,tsabr ragwanta,
Mus’ab ya kwashe da dariya yace’ bb ranar kuwa kunama na cijeni Nima,
Binaif Yana murmushi sosai yace’ wai fa da kunama ta ciji Mus’ab da yayi kuka sai yace masa Twinny bafa nasan ragwanta ‘yar kunama ce fah,amma zaka damemu, sai gashi a ranar shima cinnaka ya manna masa, kinga tsalle? Kinga kuka?
Ummusalma tayi dariya tace’ ande ji kunya,
Mus’ab yace’ washeri da kuna ta harbeshi,mune har asibiti, akayi alura Umma tace ya sha kwai danye, yace zai sha ba,Dan mutumin ki cikin dare ya Bani bacci Sai ganin sa Nayi a kitchen ya sha kwai Bakwa,
Mas’ud yace’ sharrin ya isa haka,kunga na maku shiru ko?
Binaif zaiyi magana wayar sa tayi Kara, Ummusalma tace’ kaima kaji kunya,
Yace’ bankai mijin ki ba, Shi a tsoro ma farar Kura ta fishi jarumta,
Tashi yayi ya fita yace’ ga shinan yazo,
Tashi sukayi suna tattare kayan, tace’ kuma ku wanke mun,
Mas’ud yace’ ni bacci zanyi a Parlour nan, zaiyi dadin bacci,
Tace’ bayan an wanke mun kayana hakan zai faru, kuyi sauri mana,
Sai kace wata uwar mu wani muyi sauri anki ayi saurin,
Sannan yayi gaba,daman Mus’ab yana kitchen din ya fara, ita kuma wurin ta Dan gyara sannan ta koma daki,.
Shigowa da bakon yayi parlour ya zauna yace’ Bari akawo ma ruwa,
Sannan yayi hanyar dakinta bema ji abinda yake cemasa ba, Hijabi tasa har kasa tafito suka gaisa Yana kallanta, ta wuce taje ta dauko masa ruwa da lemo ta ajje,
Binaif yace’ Ina su Mas’ud kirasu, su gaisa,
To, tace,
Kitchen ta koma taga har sun Gama tace’ Anya ba jika jika kukayi ba?
Turo Baki mas’ud yayi yace’ Baki aiki sai sa mutane aiki,
Dalle masa Baki tayi tace’ wa keyiwa haka?
Kutruuuu,Kan baban wani kangon gidan? Ni ? Ina yayannaki?
Hannu ya kawo ya Rama,ita ta Rama,zai Kara ramawa ta fito da gudu tana dariya Sam Tama manta da wani bako a gidan tana zuwa bayan Binaif tayi,
tace’ wai sai ya rama,
Bakon kuwa tunda suka fito da gudu ya juyo tare da tashi tsaye Yana kallan su babu tantama wannan Mas’ud ne,ga kuma Mus’ab Daya gani a bayan su,
Mus’ab kuwa wani tunaninne yazo masa wannan abun ma ya taba faruwa,
Binaif yace’ wai meye hakan,
Mas’ud yace’ dukana fah tayi Duka fah? Sai kace kanninta? Ko ita yaya tace,
Jiyayi ance MAS’UD? da wata murya kamar ya Santa, sannan kuma aka yaji ance MUS’AB? a hankali ya juyo ya sauke su fes a bayan Alhaji Munir da ya juya ya furta sunan Mus’ab,
Mus’ab nuna Shi ya farayi da hannu Amma yakasa furta ko kalma Daya ce, juyowar da yayi ce yasa Mas’ud shima fara furtawa Yana nuna Shi da hannu Amma sun kasa fadar sunansa……..
~Fahh fahhh & Waleeda this is for you❤. It's your lunch,
~
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
“`Iife is an adventure! Live it while u can. You can never have today again, tomorrow only comes once,and yesterday it’s gone forever.
MAKE your choice wisely,then live the adventure you create…!
Such is life…
45
Ture Binaif tayi dake gabanta ganin Mas'ud zai fadi,ta taro Shi sai dai ita ma kusan faduwar sukayi da sauri Binaif ya taimaka Mata, mus'ab kuwa sulalewa yayi a wurin, sannan ya suma, wurin sa ta koma tana taba Shi ya tashi Amma shiru, gaba kidaya ta rude ta hada zufa tana kuka cikin kankanin lokaci,
Alhaji munir yace' Shiga da ita ciki, I will handle this,
Shiga yayi da ita zai fito ta rugungume Shi tana kuka, sosai
tace' sun mutu ko?
Girgiza Mata Kai yayi ya cire Mata Hijabin yace' zasu ta Shi fah, kinji? Karki damu,
Daga masa Kai kawai take Amma ta rikeshi gam kaikace abin tsoro tagani, dakyar da dabara sannan ya fita,
A kujera yaga ya kwantar dasu, ya matsa kusa dashi ganin yana tofah masu addu'a a cikin ruwa, Zama yayi a kusa da Mas'ud ya rike hannunsa Yana kallan yarda ya hada wani uban gumi, meko masa ruwan addu'ar yayi,
yace' shafa masa a fuskar Shi da kanshi, sannan Ka yayyafa masa a jikinsa,
Tasowa yayi ya ansa ya koma ya daura kansa a cinyarsa ya fara shafa masa a hankali kamar Yana tsoron Kar ya farka, yagama kuma ya yayyafa masa a jikinsa, wata wawar ni'imtacciyar ajiyar zuciya suka sauke a kusan tare. Sunjima a haka Basu San lokaci ya tafi ba, suna zaune kowa da abinda yake sakawa ransa, can sukaji Mus'ab ya fara juya kansa da sauri da sauri Yana magana, Inni,Inni,Inni,Inni,Inni,Inni, inniiiiii sai ya tashi zaune Yana sauke ajiyar zuciya sai nishi yake, can kuma ya fara addu'a ya koma ya kwanta Yana kallan Sama, sai da ya natsu,
Sannan a hankali ya bude idansa da sukayi jaaa, ya sauke su a Kan Alhaji munir, Kara rufe idansa yayi ya bude a zuciyar Shi daman ba mafarki nake ba? Kara rufewa de yayi ya bude, harda su murza ido ganin shine de yasa ya tashi zaune,
yace' Uncle Muniiiirr?
Sai hawaye kuma,a hankali a hankali komai ya fara dawo masa sosai yaji kansa na Sara masa kamar ana buga guduma zai tarwatse, kama Shi Alhaji munir yayi yace' koma Ka kwanta, beyi musu ba ya koma ya kwanta,
Alhaji munir yace' ya kamata muyi sallah Naga lokaci ya ja sosai,
A hankali ya ajje Shi Akan kujera,ya tashi ya nuna masa wata kofa,
Da alama toilet ne, alwala sukayi suka yi sallah,
Alhaji munir yace' ni bana wuce yanzu,
Binaif yace' Ka tsaya kaci ko abinci ne,ko ruwa Baka sha ba,
Yace' a,a Abdul wucewa zanyi idan Allah ya kaimu gobe Zan dawo so ba dutse Zan koma ba, ina da Dan wani aikinda zanyi anan din,
Binaif yace' to shikenan Allah ya kaimu goben,tare suka fita suka ya raka Shi har bakin motar sa ya bude masa gate Sai da yaga ya tafi sannan ya dawo, dakinta ya wuce ya Shiga ya ganta a Kan sallaya ta kudundune, karasawa yayi ya dauketa ya Dora Akan gado, Yana daukanta tana bude Ido daman ba bacci take ba,
tace' sun tashi ?
Girgiza Mata Kai yayi yace' bacci suke,
Ajiyar zuciya ta sauke ta Kara lafewa Akan gadan,
Rigar jikin Shi ya cire ya cire Mata Hijabi yace' wani idan aka min kwalliya sai a wani kawo mayafi a maka akai, a kawo hijabi asa haka akeyi?
Turo Baki tayi batayi magana ba, gadan ya hau ya rungume ta, ta yarda bata so, ya daura kan Shi a kirginta ya daura Mata kafa,gashi ya rungume ta sosai, kanshi ya fara shafa a hankali,
tace' kasan de bana San haka ko?
Yace' me?
June,
Dagani to,
Naga de kema haka kike min,to laifi ne dannayi Nima?
Meye aciki,
Ni bahaka nake maka ba,
To ya kikeyi?
Kada gani sai na fada,
Ehhhmm naji wannan,
Ajiyar zuciya ta sauke, ta rufe Ido,Sam bata San wannan kwanciyar da ya keyi ita kadai gasan me takeji, gashi Baya Zama wurin Daya da kansa yayi nan yayi nan, Kara Jan wata ajiyar zuciyar tayi, murya kasa kasa, cikin wata irin kasalar da ta dirar mata tana shafar kansa,
tace' Baby!
Idan Shi a rufe ya amsa da uhm,
Tace' Ka dagani,kaga kayi bako,
Shikansa tasa masa kasalar,ya dago da kansa yayi ya kalleta idanta a rufe take wannan maganar, a hankali ya tashi ya matso daf da kanta ya sunkuya daidai bakinta ya fara kissing nata, daga nan aka Lula..
????????????????????????
Kullum sai tazo store din da suka hadu,kullum ne wannan babu fashi Amma bata ganin ko Mai kama da sune, haka zata karaci yawonta ta koma gida Sam Tama ji zaman garin ya isheta transfer zata sa a Mata tace aure zatayi tasan za'a mata, da wannan shawarar taje office dinsu dukda yau weekend Amma tasan za'a dace, yakan je da weekend, aikuwa Yana nan, tana zuwa tayi knocking aka bata izinin Shiga ta shiga,
Ta zauna suka gaisa,
yace' Brr Amina yau kece haka? Ince ba wani case bane ya kawoki,
Murmushi tayi kadan tace' komai lafiya, daman wata alfarma nake nema,
Yace' tame fah?
Tace' daman so nake amin transfer shine kawai,
Shiru yayi ya dawo gaban kujerar dakyau,
yace' barrister bawai naki ta taki ba, Amma kisani kina taimakawa dukda ba wani jimawa kikayi da fara aikin nan ba,Amma kin samu nasarori,cikin kankanin lokaci kinyi sunan a wannan wurin namu, mezai Hana kiyi hakuri kicigaba da zama anan din?
Tace' Barrister bazan iya cigaba da Zama a garin nan ba, idan transfern ya samu kawai amin, idan be samu ba kuma shikenan Zan ajje aikina ne gaba kidaya,
To meyasa? Ko an maki barazana ne?
Karamar kwallar data zubo Mata ta share tace' ko Daya, is family issue,
Daga Kai yayi yace' nagane, to Zan taimaka maki, ganin kin samu din, ko munce aure zakiyi sai an bincika angani dagaske ne ko kuma akasin haka,
Wayar sa ce tayi Kara ya daga, yace' Ummu me kuma ya faru?
Daga can ummu tace' Abie kaga yusuf ko? Wai bazai bane kudi naba, sai munje shopping din,
Yace' ni nace kar ya Baki, karki zubar,wancan Dana Baki ai zubuwar kikayi, sai kace Karamar yarinya, yanzu ko Abdullahi dayake karami bazai zubar da kudi ba Amma kemam Allah ya shirya mana ke,
Tace' to naji Mama tace' za'a je Dani dagaske ne? Za'a Dani?
Ummu gaba kidayan ki ciwon kaice, ina ke ina zuwa? Zaku fara exams din?
Tace' to shikenan yau zaka dawo ?
Kinsan ai idan na tafi kwana nake a waje, stupid ajje min waya,
Ajiyar zuciya ya sauke yace' Ummu Mita,
Amina dake jinsa, tace' 'yar kace?
Yace' eh babbar 'yata ce,Amma karamin gidan yafita yin abin masu hankali,
Murmushi kawai tayi tace' nagode sosai barrister,
Yace' bakomai fatan mu Allah yasa ayi nasara kisamu, Bama San Barin aikin Ku, muna bukatar ku,koda kuwa awani wajen ne,
Sosai ta Kara yi masa godiya daga nan kuma aka suka Dan taba hira a har Kar aikin su sannan tayi masa sallama ta wuce.
✨✨✨✨✨✨✨
Basu suka tashi ba sai yamma, sosai sukaji su garau kamar babu wani Abu dake damunsu, wani irin farin ciki suka tsinci kansu, babu Wanda yayi wa Dan uwansa magana sai dai annurin dake fuskar su ya tabbatar wa da kowanne su beda damuwa, wanka sukayi sannan suka Rama sallahn su, daga nan suka dawo kitchen Mas'ud ya Shiga ya kwasu abincin ya dawo ya Koma ya kwasu musu plate da cup, ya bude fridge Dan ya dauko lemo ganin wani juice a jug yasa ya dauko shi ya kawo musu, ya zuba masu abinci, sun dauko zasu Sa a Baki sai suka hada Ido a tare suka saki wani malalacin murmushi suka furta
" Inni's favourite,
Sai kuma saka, Mus'ab yace' Ka tuna komai? Ka tuna?
Mas'ud Yana murmushi yace' na tuna abinda ya kamata na tuna sanda ina wayo ba?
Mus'ab yace' na manta kamanin su, na manta,
Mas'ud yace' dude manta kawai,the best thing mun tuna mu suwaye, that's all, and gamu ga sistern, ga kuma bb, sannan ga Bros, wannan kadai ma sun ishe mu,
Mus'ab yace' inasan sanin inda suke,
Sai Ka daura damarar neman su,Amma nikam bazan iya ba, Allah ma yagani,bansan ta ina Zan fara ba,idan muna da raban haduwa ba yau ba ko shekara nawa ne zamu hadu koda kuwa su sun rasu ko kuma mu mun rasu, kaddara ce ta raba mu,kuma kaddara ce zata sake hada mu Insha Allahu,
Daga nan shiru sukayi suna cin abincin su, can mas'ud yace'wai suna ina? Sun kyale mutane su kadai,
Mus'ab yace' Kai wai baza ka canza ba?
Tunda hali na Bashi da kyau ko? Kaifa Ka renani,
Waye babba? Naga nine babba ?
Karye ne,nine nan babba,
Naji na baka girman, nine Karami that's all?
Dade yafi, a to, mtsww,
Ka tuna ?
Mefah?
Manta kawai zaka tuna,
Damuwarka,
Damuwar Ka ce,
Aikuwa karya ne, damuwata daban damuwar Ka daban atoh,kuma ba damuwata bace,kamin shiru ina cin abinci ba'a San ana cin abinci ana surutu ( ????),
Banza yayi da shi sai da suka Gama, sannan suka kwashe kayan suka ajje akan dining, juice din da ta hada kuwa tas suka masa, sukayi wanke wanke,
Mus'ab yaje kunna kallo yaga game yace' Fav bro kaga game,
wacce iri ce? Ps?
A,a wannan sega ce,
Jona mana, muyi, Amma football fah,kasanni na iya, kamar Renaldo haka nake,
Gaskiya Kam,a can cikin mafarkin tsuntsuye ba?
Wai Kai mekake nufi Dani ne? Karya nake?
Yana cigaba da hadawa yace' ni na'isa? Bankai matsayin ba,kaifa yaya ne Babban yayaaaaa,
Zama aka gyara aka Kara makewa ance masa yaya, Kai Mas'ud akwaita san girma.
Saida ya Gama Jona masu aka je gaban TV aka fara buga game. Tun ba'aje ko ina ba, aka cinye chatty.
Da suka tashi wanka sukayi sukayi sallah, tace' Bakajin hayaniyar su?
Yace' kyalesu, idan mun fita ma ba abinda zamu musu,
Yace' yunwa fah nake ji,
Kaifa Kace Kar mu fita, kuma kayi wannan korafin?
Yanzu nace mu fita tou,
'yar harara ta zuba masa, zatayi magana ya Riga ta,
yace' karki damu Zan fashe yau din nan, da daddare ba sai gobe ba,
Ware ido tayi tace' kuma wannan dakayi fah?
Wannan ai na missing juna mukayi,kema kinyi,ko bakiyi ba?
Murguda Baki tayi tazaci Bai Ganta ba yace' nagani wannan,
Biyu Kenan, kicigab kece a ruwa Bani ba,
Tashi tayi ta saka hijabin Akan mini skirt din da ya dauko Mata Akan tasa Shi, ta fita tana gunguni, murmushi mugunta yayi yace' Zan fashe shiyasa Bana hanaki,kici gaba, aga waye mai riba sannan shima ya fito,
Taji mugun mamakin ganin su suna dariyan nan suna game gefe kuma an ajje Apple ana yi ana ci, daskarewa tayi a wurin tana kallan ikon Allah har sun ware?
Binaif ne ya dafata tare da Mata side hug suna tafiya,
yace' muje muci abinci, ok?
Wucewa sukayi, sukaje zasu ci tace' Bari ayi warming tun safe fa Nayi abincin,
Zama yayi yace' yunwa nakeji, kafin kiyi na koshi,
Girgiza Kai tayi ta sannan tayi serving dinshi, tana cikin yi
yace' Allah ya shirya ko?
Murmushi gefen baki tayi hakan yasa dimple dinta lomawa ta gefe Daya,
Irin Mata murmushi yayi hakan yasa
tace' me kake Shirya wa?
Jawo abincin sa yayi ya fara ci itama Zama tayi ta zuba kadan tana ci,
yace' me kika gani?
Naga kayi wannan murmushin gulman naka?
Ware ido yayi yace' ni ne gulman?
Tace' a,a nifa ba haka bane,kawai Nayi noticing ne idan kayi wannan murmushin naka to na..na...am...am,Ka gane ai,
Harara ya balla ya cika Baki da abinci, batayi magana ba Amma hararan ya mugun bata dariya, mazewa kawai tayi, sai da suka gama ta tattare kayan ta Kai kitchen ya dawo ta ganshi a wurin, Yana Shan ruwa,
tace' Yau muje mu siyo sauran abinda babu,
Wata hararan ya balla mata, dariya tayi tace' ashe Mr lizard ya iya harara haka ban Sani ba,
Tasowa yayi yace' waye Mr lizard ?
Zai kamata ta goce tasa gudu shikuma ya biyota, sai cikin parlour,
Tana gudu tana dariya tayi nan yayi nan zai kamata sai ta gudu, Mas'ud da Mus'ab tsayawa sukayi kallan ikon Allah yaushe ma da suka wuce Basu gansu ba,
Mas'ud be ankaraba yaji an taka masa kafa, ita kuma tayi tuntube da abinda suka ajje a tsakiyar su, kawai ta zauna a wurin tana dariya, Binaif Yana zuwa ya daga ta
Yace' wana kama?
Tana haki sosai tace' bakowa ba, a kasa ya ajje ta yayi sauri ya kwanta a cinyarta, suna sauke numfashi,
Mas'ud yace' idan na yarda na zama danda kwashi, azo a biyani a kafata,
Mus'ab yace' dadina da kai ragwanta kamar mace, harKa fi ma wata macen,
Yace' ehh naji sai dai kuma ni Bana tsoron kadangare bare cockroach aje ga su tsaka Ku ma, su oo da oo kwa ba'a magana,
Binaif yace' sai Ka Fadi Mai tsoron su ai,
Mas'ud yace' ga mutane dayawa, wata da tana karama tsoron fasifa kamar kamar me,
Tasan da ita shiyasa ta aika masa da sakon harara,
Yana gyara kafarsa yace' wallahi kinji min ciwo,Inga ma karaya ce,
Mus'ab yace' daman tun tana yarinya taje jima so sai kayi hakuri zo mu cigaba da game din mu,
Yace' kaidai Bari wannan yarinyar ai aljana ce na fada maku,
Babu Wanda ya Kula ya Kula Shi suka ci gaba da game, shikuma Binaif yajata da hira iya sune kadai suke Jin hirar su, sunayi suna kallan game dinsu, ganin ana cinye Mas'ud Binaif ya tashi,
yace' kawo nan babu abinda Ka iya sai shirme, kawo kaga yarda ake,
Bashi yayi yace' yawwa bb zo Ka cinye Shi,
Karba yayi Kai kace da gaske yake, Yana karba ana cinsa,
Mas'ud yace' bb ya haka?
Ita kuwa mezatayi ba dariya ba, ganin ana ta cinsu, ya sa ta tashi, taje ta zauna
tace' Ku kawo na maku,
Me kika iya ke kuma? Ball ce fah na cin abinci ba,
Tace' chatty kadena Shiga harkata taam,
Kwace handle din tayi daga hannun Binaif,
Yace' bb ya zaka bata wai?
Binaif yace'kana gani de karfina aka fi ai,
Tagumi yayi yace' shikenan kawai yau Banda sa'a,
Ganin da sukayi ta iya yasa suka hada Ido irin tabamu kunya fah, sai gata ta cinym Mus'ab,
Mus'ab yace' gaskiya ki Basu,Abinsu, bafa a haka,
Inaa Bama taji shiba,
Suna cikin yi su yusuf suka shigo, da sallama babu Wanda ya amsa sai ganin su da sukayi awurin su,
Yusuf yace' taabdi idan Yaya ta fara ko,kawai Ku hakura ma, da game din, Dan abinda yafi zero ma sai Ka tashi dashi,
Yaseer yace' aikuwa de Dan yaya bala'i ce,
Ummu tace' yeeeeess daga masu sunanne,
Ke dalla can da ko handle din kin iya rikewa ne ma?
Na Shaka,Zaka San kayi dani daman yaseer Ka renani tam,
Mas'ud yace' Kai yaseer kadena Rena mutune fah,
Mus'ab yace' kaji babban yayan ana hudu ba,
Ajjewa tayi tace' nagaji, ta Shi yayi ta koma Kan kujera Binaif yazo
yace' Zan fita,
Ina zakaje?
Sunkuyo wa yayi Mata peck yace' Zan je gidan Anty safiya,
Kace ina gaida ta,kace kuma har yau banga su Nafisa ba,
Ganin kallan da yake mata irin ni Dan aikekine? Tace'please baby?
Murmushi yayi ganin yayi murmushi ta tashi ta masa itama peck, acikin kunne tayi masa rada, tace' byee,
Sai da ya tafi ummu ta dawo kusa da ita, sukuma suna can a kasa ana fama sai iho suke, Mas'ud da Yusuf Mus'ab da yaseer,
Ummu tace' Yaya kaina ya kulle bansan ya za'ayi ba,jiya de bata fita ba, bansan yau kuma ba, kuma tana San wani Mas'ud, shine ma damuwar ta,
Kallanta tayi da kyau Jin Abinda tace, tace' kin tabbata haka ta fada maki?
Ehh yaya,
Tace' kinga Mas'ud din da take fada maki can,
Tafada tana nuna Mata Shi,
Mamaki ne sosai a fuskar ummu, tace' Amma yaya taya Kenan?
Anan tabata labarin haduwar Sameera da Mas'ud har jiya da sukayi wayar nan,
tace' yanzu abind za'ayi shine zai dena kiranta, sannan bakin ce kina da shawaran d zaki bata ba?
Bani da wata shawara yaya,na Rasa yarda zanyi ai,
Ni,ina da ita, yau Ida kinje ki taso d maganar jiya,
Shiru tayi tace' sauran maganar Kan Ku tafi Zan maki message incase ki zaki manta ko kuma kin manta sai ki duba, a wayarki kin gane?
Daga Mata Kai tayi alamar eh, tace' laa koma nasa earphone a kunne na,ko? Hakan zai fi ma,
Kiyi de yarda nace maki, din maybe lokacin Nayi bacci, tace' to shikenan yaya.
????????????????????????????
Bata taba tunanin haka so yake ba, sai da ta afka cikin sa, bata San haka yake ba, tasan ta yanke samun farin cikin, a ganinta Wanda take so shine farin cikin mutum kuma ace shima Yana Sanka, Amma ita tasan bazata taba samun wannan walwalar ba, shiri take zata fita Amma tana tunani, dauko jakar ta tayi zata fito taga ummu a bakin kofar,
Ummu ta shigo tace' ina zaki kuma? Kinsan Zan zo mu karasa maganar mu ta jiya ko?
Ajiyar zuciya ta sauke tace' ummu Zan fita ne, fah,
Ummu tace' aikuwa babu inda zaki je, Shi Wanda kike so din ance maki idan yaji kina yawo zai amince ne?
Yaya Sameera let me tell you the truth duk wani Wanda yace maki wannan yawon zuwa partyn da kike shine birgewa to ba makawa Yana neman saki a bata ne, ko kuma ma yasaki, yaya Sameera ki gyara tun yanzu,
Yanzu idan kika fita kika mutu fah? Ehh? Wa gari ya waya? Mutune suna maki kallan Kamila kuma nutstsa me kike tunani?
Idan Baki gyara rayuwar ki tun yanzu ba sai yaushe ?
Tsayawa tayi kawai tana kallanta, fada take Mata tana daga murya kamar itace babbar ita kuma karama, zatayi magana taji,
tace' idan kina tunanin cewan su kawayen naki suna sanki ne, to kirasu kiji, ki Kira su, ki fada masu cewan kin samu wanda kike so, kiji me zasu ce,
Cikin fada itama tace' ke ummu kinsa me kike fada kuwa? Kawayen nawa? Zaki ce basa Sona?
Hmm to kina mamaki ne? Ki Kira mana ai ga waya nan a hannun ki,ki rasu kiji,
Ummuu,
Call them pleaseeeee,
Zatayi magana ummu tace' please,
Wayar ta Ciro daga cikin jaka ta daga ta Kira tasa a speaker,
Daga can aka daga aka ce
" Meera har yanzu Baki zoba, zafa a fara,
Tace' kinga, Seena,bawannan ba Nayi samu wanda nake so,
And so what?
Tace' Ina San shi fah,
To meye kuma? Ko anyi auren ina kowa Karan sa zai ci babu babbaka, kinga Idan zaki zo kizo ki taho mana da kudin Kari, a to,
Tace' seena, mekenan?
Kamar ya? Kinga Karki bata lokaci kiyi sauri kizo, malama,
Ya kashe wayar ta,
Wayar tabi da kallo ta kalli ummu, murmushi ummu ta danyi tace' Daya Kenan, next?
Ajiyar zuciya tayi ya saisaita kanta, ta Kira wata,
Tana. Dagawa tace' Yau ina kika nufa kuma?
Tace' kinga bawannan ba, ina fada cikin tarkon San wani shikuma Baya Sona,
Mtsww kin ban haushi, Abu Mai sauki yanzu nan ki taho mujr wurin Malamin nan danake zuwa wurinsa kawai ayi komai a Gama tuni zaiji babu wacce take so sai ke, kigama cacima ki watsar da shege,
Rufe idanta tayi tace' mekenan?
Me kuwa? Ke ai daman bazaki canza ba, mafita ce fah na nema maki,
Kuma aikin nacun kudi da yawa ki taho da kamar 100k haka,
Tace' to nagode zaki jini sai gobe Amma,
Yawwa yar gari, sai naji ki,
Kashe wayar tayi tayi ta koma da Baya ta zauna Akan gado, ta Dafe Kai,
Ummu itama karasowa tayi tace' next?
Kiran wata wayar tayi aka dauka, tafada mata,
Tace' Haba Meera wallahi kina bada mu, da yaza'ayi ace yasoki, wannan party zaki je sai kisa wani long skirt kiyi kawo Vail ki yafa, wataran har atampa, kawai ki ajje wannan bidi'ar a gefe kisa kayan asali, gaki da kayan aiki,kina sa kayan asali zaki fito duk shegen da ya ganki shikenan,kawai ki bada Kai bor.....
Kashe wayar tayi ta kifa kanta tana kuka, gaba kidayansu babu wacce taba ta shawarar arziki, meye mafita?
Ummu tace' kidena kuka, Mafita Daya ce,ki kaurace masu, kina da kawaye ba lalle sai suba, Amma idan kina tare da su to tabbas akwai aiki ja, abinda ya kamata yanzu, ki ajje batun so a gefe ki raba kanki da makiyan ki,ba ke soke soba kudin ki soke so,
Dagowa tayi tana kuka sosai tace' sune suka fara ,sune suka fara Jan ra'ayina, Ummu daman haka akeji? Ummu
Sai kuka, Rasa abincewa tayi sai rarrashin ta da tayi sai da ta nutsu ta dena kukan, sannan
ummu tace' ki kwanta Amma ki kashe wayar ki, kiyi tunanin da kanki,ki nemowa kanki Mafita Zan tafi,
Fitowa tayi tana tausayin ta, tabbas cin Amana beda dadi ko kadan, Allah ya kaimu gobe komai zai kare.
✨✨✨✨✨✨✨
Sune suka yi komai yau har breakfast sune sukayi sunayi suna fada, har suka Gama sai da suka Gama Mas'ud yaje yayi knocking kofar dakin Binaif,
Yace' bb,aljana Ku tashi, yunwa mukeji,
Jin shiru yasa Shi yi da karfi yace' Ku tashi mana,
Binaif ne ya bude kofar yace' jeka dafa kaci
Gam ya rufe kofar,
Damman an tasheku,
Sannan ya wuce Yana Mita shidaya,
Bayan sun Gama breakfast, Binaif yadauko masu takardun su gaba kidaya aka baje kowa yana gani suna cikin budawa Binaif yaga wata takarda Idan be manta ba,ya taba ganinta lokacin da yafara duba takardun sanda Yana gidan Daddy, dauka yayi ya bude, ganin rubutu a ciki, aikua itace, Yana cikin nadewa idan Shi ya sauka Akan Sunnan Ummusalma,
Dagowa yayi ya kalleta hankalin Yana ga duba wasu abun, Mika Mata takardar yayi, bece komai ba,
Karba tayi tace' tame ce?
Ki karanta,kawai yace,
Warewa tayi dayake ya fara nadewa, ganin rubuta da yawa yasa kawai ta kalli ta kasan layin,
My lovely Daughter Ummusalma Muhammad Uthman Suraj,
Babu abinda yazo Mata Kai irin Kenan Shiyasa Amina take amfani da Muhammad Suraj??
Fara karantawa tayi.
I your father Muhammad Uthman Suraj, My dear daughter.........
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? *A BAKIN WAWA* ????
_Akanji magana_
42
Ummusalma tace' Abba beda lafiya, nasan kuma ita yanzu ba kullum take zuwa school suna siwes, sabida haka kiyi kokari a wannan lokacin kike zuwa gidan da karfi da yaji ki hanata,
Yaya taya Zan hanata bayan kinsa bazan iya ba,
Zaki iya Ummu, Uncle yace Baki taba cewa bazaki iya ba,ko bazaki iyaba to sai kin gwada, yanzu kin gwada? Kinga bazaki iya ba?
Shiru tayi tajin ance uncle, ganin haka Ummu tace' abinda zakiyi,kije take Kara maki karatu daga nan sai kike Jan hankalin ta, amma da zaran kinje gidan ki dauki wayarta kisa a silent ko ki boye Mata, kingane? Sabida Kira,
Tace' Insha Allah zanyi hakan, yaya daman gobe weekend,zanyi kokari Nayi.
Tace' yawwa nasan zakiyi, nagode kinji,
Kai yaya to meye na Godiyar, har kinsa naji kunya ma,
Murmushi tayi tace nade gode.
Fitowa sukayi sukaga Basu dawo ba,samin wuri sukayi suka zauna, Ummusalma tace' fada min me suke aikatawa a makaranta,
Ummu tace' 'yan Mata ne ke crushing Akan su, sai kace wasu manya nan kuwa Basu San 17-16 bane ba,
Ita abin ma dariya ya bata tace' yanzu wannan yaran? Kana gani kasan ba shekaru ne dasuba,
Ummu tace' taab yaya kenan,aikin ga yanzu yarda ake hauka Akan Maza kuwa? Musamman ma idan irin kyakykyawan nan ne anfi hauka akan shi,
Daga an da kyalla Ido an ganshi shikenan,an like masa wani kuma kudin sa, wani kyansa ko beda kudi kuwa,
Ummusalma tace' Allah ya sauwake wannan Abu,bamma San anayi ba, nazaci an Yan canne suke wannan abun Ashe harda Yan nan ma,
Ummu zatayi magana suka shigo, yaseer da gudu ya karaso ya zauna, Ummusalma tace' Yaseer meye haka? Bazaka tafi a hankali ba sai kayi gudu?
Yusuf da ya karaso yace' har yanzu yaran nan yarone,
Yaseer yace' waye yaran?
Kaima mana,waye kuwa idan ba Kai ba, koda wani yaro ne nan,
Allah kadena cemin yaro, kwanan zanyi Shiga 17 taam,kun Renani da yawa,
Mas'ud yace' to andena shikenan ?
Ummusalma tace' first time in history,
Yace' me kika ce?
Tace' ca nace muci abinci kawai,
Sannan ta zuba masa ta zubawa masu ita da ummu,
Mas'ud yace' me hakan yake nufi wai? Sai ki wani zubawa mijinki mu kuma ko oho ko?
Binaif yace' ban Hanaka ba wai? Ehh?
Sunkuyar da akai yayi ya fara gunguni ya zuba masu su hudun a plate daya, suka fara ci,suna ci suna zuba suna karawa Saida suka cinye tas Basu sani ba, suna zuba su dukansu babu sauki haka ma Ummu Binaif da Ummusalma kuwa shiru sukayi kawai suna jinsu,
Saida suka Gama tas, Ummusalma tace' atashi a wanke mun kwanika na,
Mas'ud yace' idan Nayi na kame,
Mus'ab yace' zaku wa Ka kame,
Ummusalma da Ummu suka kwashe kayan tsab suka Kai kitchen, kafin su fito ta gansu sun shigo Mas'ud sai wani cika yake Yana batsewa dake taso tsokana sai,
tace' My chatty me aka maka haka? Sai wani kumbura kake nidai Kar a fashe min a kitchen wannan ai kafin yeasts kumbura, da gudu ya biyota ta kwasa sai waje, kwafa yayi yace' zaki sani ne idan na kama ki,
Gani tayi ma sun dauke carpet din zasu dawo parlourn, parlourn suka zauna,
Yace' ki Shirya muje,
Itama banza tayi dashi irin bansan dawa kake din nan ba, ganin haka yasa,
yace' Ummussalma dake fah nake,
Dago Kai tayi tana kumbura Baki tace' nifah Ummusalma ba Ummussalma ba,
Yace' ohhh Ummussalma? Shikenan to,
Harara zata zuba masa yamata kallan zamu hadu,tuni ta dauke ta fasa, kallo suka kunna sunayi saiga su Mas'ud nan sun fito,
tace' Chatty har kun Gama? Kode an mun jika jika ne kawai?
Hararan ta yayi yace' oho maki, dawani bakin ki a wurin irin na loro,
Tace' oho de bakin iri dayane ko ka manta?
Kekika sani,
Binaif yace' zaku fara ko? To kuje ku shirya zamu unguwa,
Yusuf yace' Ku tashi mu tafi yau bamuje asibiti ba,
Tace' meyasa Tou?
Ummu tace' makaranta ce yau fah tun 7 muka fita sai dazu na,haka ma akwai ta 7pm shine mu kadawo,
Yaseer yace' ai lecturer dinnan ko? Ahaka ma wani be taba shigowa ba,kuma za'ayi exam,
Yusuf yace' Ku tashi mu tafi,
Binaif yace' Amma gobe zaku dawo ko?
Ummu tace' eh zamu dawo Amma sai da yamma ko da dare,
Yace' shikenan kudena parking a waje, kuke shigowa da ita,
Da to suka amsa suna fita Mas'ud ya shigo,
yace' bb kasan me wannan matar taka yimin? Shiyasa Ashe Naga sunyi sauri Ashe dakina suka dauka suka kwashe kayan na suka mayar dakin Twinny ?
Binaif yace' da wace ma ana yarda da ita haka? Ai tana cewan nan muje na tayaka nasan ta Shirya wani Abu,
kallanta Mas'ud yayi yacet yanzu kin kyau ta?
Kamar yayi kuka,
Tace' Allah sarki Chatty daka taya Shi kun gyara da duk haka bata faruba, Amma kayi hakuri kaji?
Mus'ab da yazo yanzu yace' yaude dole dole dole a kwana da karamin yaron da be yiwa budurwa magana ba,
Yace' Zaku gane ne, Amma gobe sai Ka tayani,
Tace' hakan shine daidai ai,
Binaif yace' zamu tafi mu barki,fah
Tashi ta Shiga daki, tana dube dube rigar dazu ta mayar tayi rolling ta fito,tun kafin ta karaso ya tashi ya tareta ya ja hannunta suka koma, suna Shiga daki,
yace' a haka fah zaki fita ko?
Tace' ehh mana,
Be kulata ba yaje ya dauko atampa,
yace' kisa wannan,
Tace' Amma de fi...
Jin bakinshi cikin nata yasa saura maganar komawa,
yace' kina so ki zauna a gida hala?
Turbune fuska tayi ta ansa ta juya zata Shiga toilet ya dawo da ita,
yace' anan zaki sa,
Kuma a gabanka?
A Baya na,
Kumbura tayi tana gunguni,
yace' naji wannan,
Yana kallanta ta cire doguwar Rigar tasaka rigar atampar ta juya,
tace' balle min?
Shikuwa ya kama bra ya balle,
Tace' bafa ita ba,ya za'ayi Ka cire min,
Yace' kika ce na balle?
Ka zuke nake nufi, taya zance Ka balle kaima kasan san abinda nake nufi,
Zukewa yayi yace' taya Zan sani?
Zatasa skirt din taga zani,ta juyo kamar zatayi kuka shikuwa yi yayi kamar be ganta ba, ganin haka yasa ta fara kiciniyar daurawa sai ta daura sai ta kunce, Yana tsaye Yana kallanta Sam bata iya ba, sai dakyayta daura shima bewani yiba, yade fi na Baya, harda sauke ajiyar zuciya Kai kace wani aikin tayi, sannan ya bata hijabi tasaka harda nikaf ta kunshe fuska suka fito,
Mas'ud yace' da tafiya zamuyi fah,
Idan kasan inda za'a tafi ko?
Yace' to meye? Nasan inda zamuje ai,
Binaif da yayi gaba yace' Ku tsaya jaraba Nayi tafiya ta,
Mas'ud ne ya bude gate suka fita, sai da ya Shiga mota yace' wai bb baza'a samu Mai gadi ba?
Tace' muna dakai meye wani Mai gadi,
Mus'ab yace' aikuwa de kayi Kala Kala daman dasu,
Naushi ya Kai masa ya goce yace' bakasan a kule nake da kuba? Taam,
Tace' Chatty na, munce fah kayi hakuri Kar ma Ka kwana damu kuma Ka margaya,
Yace' kut kuji muguwa? so kike na mutu Kenan ko?
A,a ni na'isa? Bankai ba,
Shiru yayi ya kyaleta yace' laaa ga gidan budur wata, a ajjeni, tana Ka biyo? Ashe fah unguwar mu daya,
Binaif kuwa yayi parking yace' to fito,
Haba bb daga fada kuma? Irin fa abin nanne Kar a Rena ni,
Girgiza Kai yayi,ta kalle Shi tace' Allah ya shirya ko?
Kallanta Binaif yayi yace' keko?
Murmushi kawai tayi, suna cigaba da tafiya,
mas'ud yace' Ku hirar nan ma ta masoya bakwa yi,kun wani yi shiru,
Mus'ab yace' to idan zasuyi suna gaba ki zakayi? Yanzu kaji me suka ce? Ina ruwanka? Kafiye gulma da sa Ido,
Mas'ud yace ansa idan,Kai na Sawa? Ehh? Bana San shishigi fah, Ka kiyaye ni,karami da Kai sai Shiga lamarin manya,
Inyeee sannu tou? Babban Yaya,
Dariya Ummusalma ta kwashe dashi ta juyo tace' Glip kasan dazu da Ummu tace masa yayanah har wani bada Fadi yayi harda gyara Zama wai ance masa yaya,
Mus'ab yace' Ashe kin gani,
Ahh nagani ni ai irin Abu banann Bana mantawa dashi ai,
Mas'ud yace' kunsan de Zan Rama ko?
Binaif yace' aikuwa zakayibta ramewa, nikuwa nace Ka Rama marinka?
God bless you BB ba Rama ba Amma very soon za Rama tacigaba da Shiga min hanci idan na tashi fato ta fitt zan fatota, kici gaba,
Tace' bakyau de tuna abinda ya wuce,
Wanne Hadithn?
Zaki ce ba kyau?
Banza tayi da Shi, ganin inda suka zo yasa yace' laa gidan Abban Khalid,
Da bakinka kamar na loro,
Kwafa yayi yace' naji Tou,
Horn yayi Mai gadi ya bude masu suka Shiga, yayi parking suka fito su agaba sukuma a baya da sallama a bakin Shi ya Shiga, amsa masa akayi,
Matar gidan na zaune da yaranta mata mazan sun tafi masallaci,
tace' wanake gani haka?
Muna da manyan Baki gaskiya,
Karasowa suka yi tace' Ku zauna zauna, sai da suka zauna yaran suka gaida su suka tashi, sannan suna suka gaisa
tace' Baku da kirki Sam Binaif shikenan tun bayan rasuwar Ummi befi zuwanka nawa ba, shiru babu amo ba labari sai kawai mukaji wai kayi aure,
Sunkuyar da Kai yayi yasan be kyauta ba Kam, tace' shima a wurin Safiya naji, haka akeyi?
Takalli su Mas'ud tace' Ku mahaka da kuna Dan zuwa De amma daga Baya sai yayan Ku ya koya maku rashin kirkin Shi ko?
Shiru sukayi, Basu tanka ba, Binaif ne yace' ayi hakuri Hajjo Insha za'a gyara,
Tace' a'a yanzu ma idan ba sa'a Amarya ce,tace azo,
Murmushi Binaif yayi yace' Bari muyi sallah,
Tace' kuje to sai kun dawo,
Tace' Amarya ya sunanki? Tunda ko gayyatar mu ba'ayi ba,
Murmushi tayi tace' Ummusalma,
Kice sunan manyane,Bama fada ba, to muje daki sai kiyi Sallah ko? Tashi sukayi tana binta a baya har sukaje dakinta,
Tace' kiyi ko?
Sannan ta fita, toilet ta Shiga ta watsa wa fuskar ta ruwa Dan Kar ace batayi ba, ta rike Nikaf din a hannu, ta fito ta zauna, ta jima a zaune sannan aka shigo da abinci, sai ga Hajjon nan ta shigo itama,
Tace'sauko kici abinci,
Ummusalma tace' a'a na koshi,
Bazade kuci ba,daga ke har su ko?
Murmushi tayi tana,kanta a kasa,
Ummusalma tace' Anty ummi fah ?
Hajjo tayi murmushi tace' Ummi duk inda aka Kai mace Ummi ta Kai, Tunda aka auri Ummi bamu taba samun wani sabini ba,duk muna zuwa can Spain Amma ita bata zuwa nan,duk zuwan da zamuyi ko zaizo to zata bada tsaraba akawo min, haka zaiyi ta Mita Shi bayasan Kaya, Amma a haka take aiko min, ban dauke ta a matsayin kishiya ba, haka kawai na bata wani matsayi na kawa kuma 'yar uwa, ni kaina naji rasuwar ta,
Tace' kinsan tana da ciwon zuciya?
Bansani ba,sai da tazo nan da bata da lafiyar nan Amata aikin nan taki sai bayan ma ta rasu nake ji,
Tace' kayanta nacan fah?
Suna can ai,ba'a dauko ba, dayake har yanzu Yana zuwa jiya ma ya dawo daga can Spain din,
Tace' zoki gaisa da Alhajin,
Sannan ta taso suka Shiga parlourn sa, anan suka ganshi suna ta zuba shida su Mas'ud, Shigowar su yasa su yin shiru,
Gaisawa sukayi dayake a kasa ta Zauna,
yace' Mai sunan Manya da kin zauna asama ni ban surika,
Hajjo tace' aikuwa de mu nan ba'a mana wannan kunyar kode,
Daga nan kuma aka fara hira duk Rabi na Anty ummi ne,
Sai wurin karfe goma sannan suka masu sallama suka tafi,
A mota suna tafiya tace' Zan sha ice cream,
Yace' wayace maki idan ana period ana Shan Abu Mai sanyi? .....
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? *A BAKIN WAWA* ????
_Akanji magana_
46
Is better to have an enemy who slaps you in the face then a brother or a friend who stabs you in the back. My message to yoo maybe take long to reach you, I might die.
Ummusalma bakida kowa a yanzu, you have siblings, Mas'ud and Mus'ab, sun bata a aranar birthday din ki 20 june.
Mutane dake tare dake bana kirki bane Sune suka wargaza rayuwar mu, Allah yayi hakan zai faru Amma sune silan komai, ba komai yaja haka ba, sai hassada da kyashi da ganin kuma na fisu, they don't love you any more they hate You, one more thing You have to know shine akwai wani key na karamin check it out.
Daga nan ya kwashe labarin su ya bata a takaice sannan ya rubuta Mata adadin dukiyar sa, a duk a cikin Papern,
Daga karshe kuma akasa sunanta tare da wannan signing din na Ummu.
Hawayene fal idanta Amma be riga da ya zubo ba, Mas'ud tashi yayi ya dawo kusa da ita ya ansa papern ya karanta ya mikawa bb, shima ya karanta sannan ya mikawa Mus'ab, kowa shiru yayi Yana tunani can,
Ummusalma tace' Me kuka gani?
Binaif yace' kawai mu bari ya Kai mu Kara kotu ko meye sai ayi,
Mus'ab yace' yanzu fah beda komai kome?
Mas'ud yace' ehh gaskiya Dan kaga wanda aka hada businesses din dasu, suka ce baza su yarda ba sai dai companyn din ya zama nasu, to Shine suka siya fah,
Numfashi Binaif yaja yace' ba siya sukayi ba, kudin da suka zuba inaga shine kawai sukayi masu ciko ya dawo nasu,
Ummusalma tace' yanzu abinda za'ayi a raba Shi dana Abuja,
Mas'ud yace' beda komai Kenan?
Malalacin murmushi tayi tace' idan ya wayi garin beda komai din, Banda gidan Shi daya mallaka Wanda ya Gina Shi,da kudin sa zance ko da kudin babammu,
Mas'ud yace' da kudin Baffa de,
Mus'ab yace' yanzu ya za'ayi?
Mas'ud yace' kawai a tura kawu munir ya je ya saya, tunda shima ya fara yin kasa,
Binaif yace' taya hakan zai faru? Yasan Shi fah, idan ya ganshi zai gano komai,
Tace' Ga mafita, asamu wani dake aiki a companyn dake Paris kaga idan Felix zai zo sai su zo tare kawai, inaga hakan shine mafita kawai,
Mas'ud yace' kuma asibitin sa fah,
Idan yaga beda kadara sai wannan gidan nasa shima zai sayar dashi ne ga wani,shima sai mu siya,
To wai da kike cewa ya saya ya saya,da wanne kudin hakan zata faru,
Murmushi tayi Mai kyau, tace' da kudin sa,
Binaif yace' wazaki sace?
Ba sai ansace kowa ba, sato wa zamuyi,
A'ina?
Suka fada a tare,
Tace' a gidan sa, Tsoho mana,
Yau zamuje fah Amma ko?
Ehh, duk yarda akayi,
Mas'ud yace' ga shawara kuma kawai a siye PA din Shi, shima yaji yarda akeji idan anci amanar mutum,
Kallan Shi tayi tace' woow su Chatty kanka ya fara ja fa,
Hannu ya kawo zai bugeta ta goce, kwafa yayi irin zamu hadu,
Binaif yace' sai ku karasa komai,
Daga nan aka cigaba da magana ba su suka tashi ba sai Azahar kitchen ta Shiga ta daura abinci sannan taje tayi sallama. Ta idar zata fito taga Ummu na Mata waya dauka tayi,
tace' ummu ya akayi?
Daga can ummu,
tace' Yaya me zan fada Mata kuma?
Ummusalma tace' abinda ya dace Shi zaki fada Mata,
Me Kenan?
Ya ilahi, ummu this time around you have do it by yourself,
Yaya bansan fah mezance ba,ni ba irin wannan abun na iya ba, kuma ni Banda kawa sai besties,
To ki tsaya da kyau Kiji, daga nan ya shiga fada Mata abinda ya dace,
Sannan sukayi sallama, Ummu tace' yawwa Bari naje na Mata dadin bakina, hahaha ho ni Ummusalma 'ya ga Faisal jikar Adamu, hehehe,
Yaseer dake zaune a kusa da ita yaja tsaki yace' mutum sai hauka,
Pillow ta dauka ta wurga masa,
tace' Wallahi Ka kiyaye ni, am I your mate? Ehh? Ina wasa dakai?
Hada hannunsa yayi yace' Ana aasfi ya Ummusalma,
Daure fuska tayi tace' dade ya fi, Ku tashi mu tafi,
Yusuf yace' yaushe su Anty zasu tafi ?
Tace' gobe zasu wuce,
Yace' gidan Antyn Ring road zaki koma?
Nima bansani ba,Amma de Zan tambayi Anty idan ta barni sai nadawo gidanku,tunda kace an sallamu Abba kaga Mama Kenan tana na sai Muke kwana da Yaya Sameera, Amma fah sai kun tayani tambayar ta,
Yaseer yace' zata ma Bari Insha Allah,
Tace' to ku tashi de mu tafi,
Tashi sukayi ta suka fita, gidana su yusuf suka tafi, tana zuwa taje ta Kara yiwa Abba sannu da jiki sannan ta wuce dakin Sameera, a kwance ta Ganta tayi rufda ciki idanta a rufe,
Ajiyar zuciya, ta sauke ta karasa Shiga dakin Bayan ta rufe, a bakin gado ta zauna,
tace' Ya Sameera Lafiya ?
Juyowa tayi ta gyara kwanciyar ta tace' ummu bansan ya zanyi ba? Nakasa samuwa kaina mafita,
Ummu tace' mafita Daya ce, ki canza SIM, ki watsar da duk wasu kawayen ki, ki fara sabuwar rayuwa kamar kowa,
Tashi zaune tayi tare da yin wani murmushi takaici,
tace' kina ganin Zan iya rayuwa kamar kowa? Bacin yanzu ma ya dena Kirana? Daman nike kiransa wani sa'ilin, to yanzu Nima nadena ganin ni Daya nake kidana, soyayyar sa kullum karuwa take yi a cikin zuciya ta, Ummu zuciya ta nauyi take min,
Ummu tace' kiyi hakuri Insha Allah komai zaiyi sauki kuma komai zai tafi daidai, trust me,
Tace' I should trust you?
Daga Mata Kai tayi alamar tabbatar wa, tace' Amma farko dole sai kin danni San da kike masa, kin fara sabuwar rayuwa hakan shine hanya mafi sauki da zamu cimma,
Zan gwada hakan,
Fatana kiyi yarda zuciyar ki ta fada maki,ba yarda kawaye suka fada maki ba,
Shiru tayi tana sauraren ta, tana kuma kallanta, ita kuma ummu tayi ta fada Mata kurarenta data yi a baya.
Washegari Binaif Yana zaune a office aka kawo masa sammaci ana neman sa a koto, dayake yasani kuma shima ya shirya sai kawai ya Kira lawyers dinsa guda biyu, Barrister Ibrahim da kuma Barrister Aliyu ya fada masu, sannan ya fito ya shiga motar sa ya wuce,
A kusan tare suka isa kotun sai Basu Shiga ba,Shi yashiga shima akayi komai da komai da ya kama ta sannan aka sa nan da Wednesday za'ayi Zama, zaman iya su ya su, daga su sai alkali da lauyoyin su sai su kuma su kadai za'ayi hakan,bayan sun fito,
Binaif ya dubi Abba yace' yanzu Alhaji haka ne daman abun? Me kake nufi Kenan ?
Murmushi yayi sosai mai kama dana dariya, sannan ya dafa Binaif, yace' yaro Kenan haka abin yake, sai mun hado ranar laraba,
Sannan yayi gaba zai tafi, dasauri Binaif ya sha gabansa ya Dan bubbuga kafadar Shi tare da yin wani murmushin da kana gani kasan na renin hankali ne,
yace' to what's done, chest.
Yayi gaba ya barshi ya wurin ya daskare, ya maimaita To what's done,chest.
Kenna Yana nufin what's done is done, you've made your bed, now lie in it. Mekenan?
Jiyayi zuciyar Shi tana bugawa da sauri, lawyern sa ne ya masa magana sannan suka tafi,
Binaif kuwa Yana zuwa ya Sanar da lawyers Dina da yarda akayi,
Barrister Ibrahim yace' Binaif inaga Zan Mika komai hannun Wani barrister Faisal, Dan lokacin nan Bana nan natafi umara, kuma bansan wannan casa din yasha ruwa dukda de muna da muhimman shaidu kuma mune zamuyi nasara Insha Allah, yau din nan Zan Kai masa komai,
Binaif yace' to shikenan Allah ya dawo da Kai lafiya, duk yarda kayi daidai ne,
Barrister Aliyu yace' Ashe shiyasa tun farko be bamu ba, Amma bakomai Allah ya Shiga tsananin mugu Dana gari, sun jima suna tattaunawa daga nan sukayi sallama har zai koma office sai kuma ya koma gida,
Yana zuwa yaga su mas'ud suna nan basu tafi ba.....
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: *A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
49
Alkali yace'' kana da ja a cikin?"
Yace'' ya Mai shari'a tabbas nasai company a hannun sa, sai dai kuma ba baka mu kayi dashi ba''
Alkali yace'' to meyasa kace anyi haka?''
Yace'' Nima bansani ba,haka kawai naji na fada Amma shine ya sayar min da companyn a hannun sa"
" Ina shaidu?"
Yace'' ga shaidu nan, barrister Ibrahim da Barrister Aliyu, dayan kuma be samu daman zuwa ba"
Kallan su alkali yayi yace'' a gaban Ku akayi?
Jinjina masa Kai sukayi, sannan barrister Ibrahim ya Dan rissina yace'' Anyi haka, sannan kuma shine yace bezo da takardun ba,sai gobe zai bayar"
Barrister Aliyu yace'' kuma shine ya bamu original din takardun wannan company"
Barrister Ibrahim yace'' kuma yanzu yazo yace besan zance ba? Bacin anyi haka ya bamu ya sallame mu? Akwai alamar tambaya anan ya Mai shari'a''
Shiru Mai Shari'a yayi yana nazarin abinda suka fada, barristern Abba yace'' ya me Shari'a wannan abinda suka fada ba haka bane, tunda sunce haka kawai su bada shida su hakan zai sa a gane waye Mai gaskiya"
Jinjina Kai alkali yayi kafin yace'' masu Kara da Wanda aka kawo karar ko sun zo da shaida?
Barrister Ibrahim yace'' ehh munzo d ita"
Sannan ya Mika masa, karba yayi ya duba, Suma su Abba suka Mika masa ya ansa ya duba, ya sosai, ya dago yace'' wannan takardun duka photocopy ne, kuma Yana yi da tsarin rubutun ba iri daya bane, hatta sighing din ba iri daya bane, ko Zan iya ganin original copy din?
Zufa ce ta fara ketowa Abba,da suka zo ai Basu ce masa su lawyers bane,kawai gaisawa sukayi, da sunce su lauyoyi ne da duk haka bata faru ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, alkali yace'' ina Original din?
Ya tambayi Abba Wanda hankalin sa gaba Daya Baya jikin sa,
Dakyar,
yace'' ya Mai girma Mai shari'a an barsu ai wannan sune original din"
Alkali ya bubi Binaif yace'' Kai fah,kana tare da naka shaidar?
Binaif yace'' eh ina tare da Shi"
Jakar sa ya bude ya dauko original copy din takardun na company ya mikawa alkali,karba yayi ya duba dakyau,
yace'' Zan iya karban wannan a matsayin sune na gaskiya, badan komai ba sai dan wannan takardun babu su yanzu''
Barrister Ibrahim yace'' kuma bugu da Kari ma shine ya bamu Shi"
Barristern Abba yace'' ya Mai shari'a wannan ba haka bane"
PA din Abba yace'' ya Mai shari'a tabbas mune muka basu, wannan takardun, a lokacin bamu taho dasu ba, sai washegari na Kai masa,nine na Bashi da hannun na, ina wurin ma ya bayar aka masa copy din shi"
Wani raza nannen, rikitaccan kallo Abba ya shiga yiwa PA din Shi besan sanda bakinsa ya furta "Inuwa??"
Ko kallansa PA beyi ba, ya make ya cigaba da bayani Sai da ya gama, Abba zaiyi magana,
Barrister Aliyu yace'' ya Mai shari'a wannan bashine Karo na farko da wannan bawan Allahn ya Saba yiba, ya yiwa mutane da yawa hakan, duk wani Wanda ya siyi kadarar Shi haka yake masa, haka a shaguna da dama dake cikin saban gari, da kuma kwari, du haka yayi musu"
Barrister Ibrahim yace'' sai sun zuba ma kudan kudin su, sun fara kasuwancin su, sai kawai yazo ya kwace, Basu da kudin Kai Kara, duka sun sa Shi a cikin kasuwan ci, kamar yarda Abdulshakur yayi,shima sai da ya bashi kudin companyn sa sannan yaga ya fara bunkasa yayi wannan aika aikar, a duba irin ta'asar da yakeyi da kuma cin zarafi,kazafi, karya, caca, Da yake yi a biwa mutane hakkin su, ya Mai shari'a"
PA yace'' ya Mai shari'a duk abinda suka fada, tare Dani ake aikata wa nine jagora"
Idan aka ce ga tashin hankalin da Abba yake ciki, bata lokaci ne, Dan wata irin bugawa kirgin sa keyi,ya rasa taka mai Mai zuciyar ce ke bugawa ko kuma de kirjinne ke bugawa?
Bekara tsinkewa da lamarin ba, sai da yaji, Barrister Aliyu ya kuma cewa'' sannan kuma ya Mai shari'a takardun gaskiya yake Basu Bana karya ba"
Mai shari'a wannan Abu ya daure masa Kai, Dan ya tabbatar da maganar su,
yace'' mun daga karar nan zuwa gobe, gobe azo min da mutanen da wannan abu ya faru da su"
Sannan ya tashi ya tafi, kowa tashi yayi Yana fitowa Banda Abba da lawyern sa, sai daga karshe suka fito kuma babu kowa, Abba na Shiga mota ya dafe kirjin sa, babu Abinda yafi komai ciwo irin cin amanar za Inuwa ya masa tambayar anan shine haka cin Amana take???
Ikon Allah!
✨✨✨✨✨✨✨
Koda suka fito Basu tsaya ko ina ba sai company ana suka tsaya sukayi breakfast Sannan,
Binaif yace'' yanzu de ya kuke ganin za'ayi?''
Barrister Ibrahim yace'' Insha Allah Mune da nasara"
Barrister Aliyu yace'' komai ya kare daga gobe inaga, yanzu zai fara neman mutanen da ya siyarwa ne, yanzu ya za'ayi?"
Binaif yace'' ba damuwa, Allah ya kaimu goben"
Barrister Ibrahim yace'' Bari na wuce, sai dai idan mun hadu goben"
Sallama sukayi shima ya wuce,
Coffee ya hada ya tashi ya koma cikin office ya fara aiki, sannan ya Kira Felix shima sukayi magana Akan zasu wani satin daga nan kuma suka fara tsare tsaren su, Baya sunyi sallama ya jima Yana aiki har lokacin sallah sannan yayi sallah, ya dawo ya zauna zai cigaba kawai Ummusalma ta fado masa,ture aikin yayi ya kwashi kayan sa ya fice zuwa gida.
Ya fito Yana tafiya sukayi gware, dagowa yayi yaga dawa sukayi gware haka? Mas'ud yagani sai mulmula wurin da ya bige yakeyi Yana wani shishi da Baki kamar yasha yaji, besan sanda tsaki yayi escaping daga bakin sa ba,
Yace'' Baka ganin gaban Ka?"
Marairaice fuska yayi tare da yin kalar tausayi yace'' Taya Zan gani, waccan aljanar ta Bani sako wajen dubu wai na siyo mata nikuma har ga Allah na manta na farko ma bare na tuna"
Wani tsakin yaja yace'' kuma Ka Kira Ka tambayeta mana"
" Nine nan naki,sai da tace ta maimaita min, nace Allah ya sauwake ai ni din ba na karshe nakeyi a aji ba, ta kuma cewa to tunda sakon dayawa na rubuta maka, nace daman ai ita ta Saba zuwa ta karshe a aji shine na taho kuma wallahi gashi yanzu na manta komai, sakon kuma tun goma ta Bani Shi, yanzu kuma har Azahar tayi, bansan ya zanyi ba, please my sweet bb Ka taimaka min Dan Allah"
Binaif yayi wani murmushi na irin Ka Rena ni, sannan yace'' idan baza ka Kira ta ba, Nima bazan Kira ba,har wani tayi ta bin kanka ma? Kace wani meye meye,harza ce Mata dakikiya har sau biyu kuma kace na taimaka maka, you must be kidding"
Yasa kafa ya fara tafiya wurin motar Shi,bin Shi ya farayi Yana rukonsa,
" bb Haba bb ya zamuyi haka, wallahi bance Mata ba, kasan Allah kuwa, Haba Dan yaya naaa? matar Ka ce,ni kuma kauwata ce, yama za'ayi haka, please mana"
Sai da yaje wurin motar sa ya Shiga shima mas'ud din da sauri yaje ya Shiga ya zauna a gaba, Sai da ya tada motar ya fara tafiya, bedana masa magiya ba, Can,
Binaif yace'' da Sharadi"
" Mene sharadin? Ni indai baza ta Rena ni ba ai shikenan"
" Mtsww, kamin shiru"
" Nayi "
Waya ya dauko yayi dialing numbern ta,
Tana kwance tana tunanin inda Mas'ud ya tsaya gashi Baya picking call dinta, kawai tunanin ya tafi ko wani abun ne ya same Shi, ta dafa farar shinkafa batayi miya ba, tana jiran yadawo tayi miya, har tayi bacci ta farka ta sake wanka shiru, tana cikin tunanin taji karar wayarta ganin sun Binaif yasa ta daga,
tace'' Hello!
Yace'' ya gida?"
" Lafiya ba lafiya ba"
" Me yafaru?"
" Manta kawai,Ka kusa dawowa?"
"Ehh! Mezan taho maki da Shi?"
" Komai ma"
"Kamar me ?"
" Dayawa fa,kaga ko miya banyi na,na aiki Chatty har yanzu be dawo ba"
" Kyale wannan,waya ce maki da ana aikin Shi, sai yamma zaki ga sakon ki idan bakiyi sa'a bama ya manta, ya tafi wurin abokai, ko ya sami majalissa ya zauna kawai kimin message din abinda za'a"
" To shikenan nagode, sai Ka dawo, take care"
Kashewa tayi, Dan kallan mas'ud yayi yace'' sharadin shine zaka Mata hakuri"
A sukwane ya juyo ya kalli Binaif yace'' am..am..daman,shine sharadin? Imagine nine Zan bata hakuri"
Samun gefen hanya yayi yayi parking yace'' then go"
" Haba bb wasa fa nake, ai Zan bata ma, ai kauwata ce,aww yaya ta, Anty Ummusalma Walilin Inni, Zan bata ai"
" Better"
Message din tayi mas'ud yayi sauri ya bude yaga ni sai ca yace'' mtsww Ashe ma wannan abun ne, ai na tuna ma, harda wani ice cream a karshe baza' a siyo din ba "
Kallan Binaif yayi yaga driving kawai yake hankalin sa ma kamar ba a kunsa yake ba, ya kuma hade fuska irin ba wasa nan, yace'' bb to Ka saki fuskar mana,Naga de shan kunun ya kare tunda nace Zan bata hakuri"
Ko ehem bece masa ba, be daddara ba ya kuma cewa'' Haba de mutum sai kace ance gobe zai mutu? Sai cika yake Yana batsewa ai shikenan"
Be tanka Shi ba sai suka je kasuwa,yayi parking ya dauki wayar sa yace'' jeka siyo kayan ina nan ina jiran Ka, idan Ka dade nayi tafiya ta"
" To bani wayar na ga abinda za'a siyo"
" Nazaci Ka tuna,kana bata min lokaci"
Dakyar ya bashi yaje ya siyo abinda tace, sannan ya Karo masu fruit dayawa, ya taho da Kaya Niki Niki, ya bude boot yasa,
ya zauna yace'' bb nagaji wannan matar akwai sa aiki"
Banza yayi dashi ya yaja motat suka tafi, a wani shagon Sai da ice cream ya tsaya yace'' fita"
" Nayi me fa?
" Ice cream zaka siyo Mata"
Wani idi turo Baki yayi ya fara gunguni sannan ya bude motar ya fita, ya siyo ya dawo, Yana dawowa kafin ma ya Shiga motar yasa Shi a seat din baya, sannan ya zauna, be Kara magana ba har suka iso gida.
Tana nan kwance shiru sai kallo da ta kunna tana yi,da sallama suka shigo tashi tayi taje ta tarbe shi ta ansa kayan hannun sa,
Mas'ud yace'' ni kuma fah?
Wata hararan ta wurga masa, tayi gaba, abinta yayi shima da kayan Yana mata magana tayi banza dashi, sai da ta ajje ta fitar Dana fitar wa tasa a fridge ta dauki Wanda zatayi amfani dashi kawai, Shi kuma ya samu waje ya zaune Yana zuba, yana kuma cin guava,
tace'' Ka wanke kazar Ka gyara Ka daura, a takaice de kayi miya, na wuce ni"
A sukwane a sauko daga inda ya zauna yace'' ke kuma meye aikin ki? Ina zakije?''
" Zanje na Kula da Mai house ne"
Ta wuce ta barshi a wurin ya saki Baki Yana binta da kallo sai da ta fita daga kitchen din yace'' marar kunyar banza mijin da ba'a San Shi,Kode tana san shi? Oho de su suka sani"
Koda taje dakin sa yana wanka shiyasa ta fito parlour ta zauna ta kunna kallo tana yi,
Jitayi ya daura kanta a kafadar sa, yace'' me kike tunani haka?
Kallansa tayi tace'' ina tunanin sameera ne"
" Me tayi?''
Gyara kwanciyar ta yai sosai tace'' she's fall for mas'ud"
Ajiyar zuciya ya sauke, yace'' then?
" Gashi ya rabu da ita, yama yi blocking sim dinshi"
" Rabu dashi akwai lokaci"
Shiru sukayi suna kallo babu Wanda yayi magana, sai can ya bata labari abinda ya faru a kotu sai da ya gama,
tace'' Kar Abba yayi wa PA wani abu, ya kamata a buya har zuwa gobe"
" Good idea"
????????????????????????
Ana zuwa ko parking ba'a Gama ba, ya fita ya Shiga cikin gida, Mama na zaune tana kallan TV ga ganshi ya fado kamar Wanda aka jefo Shi Yana neman faduwa,da sauri ta taro Shi tana tambayar sa lafiya?
Babu abinda yake cewa sai ya cuce ni,ya ci amanata, ya ha'ince ni,haka kawai yake cewa, yana girgiza kai.
Mama tace'' wai Alhaji waye haka? Waye ya cuce Ka ne?"
Cikin wata masifa yace'' waye kuwa idan ba Inuwa ba, Inuwa PA da kika sani, shine yaja min komai, shine ma inaga yayi komai, ke shine ma"
" Haba Alhaji wanne Abu ne haka kami biyani dalla dalla mana,sai nafi ganewa ai"
Numfashi yaja sannan kuma ya koma ya jingina da kujera sannan ya bata bayani abinda ya faru kaf a kotu,
Huci ta fara, zuciyar ta wani irin tafasa take yi, tashi tayi ta goya hannun ta a Baya ta shiga zagaya wurin da suke,
tace'' almajirin yaran? Yaran da beda cin yau balle na gobe? Yaran da ko karatu be iya ba? Amma yanzu shine yayi wannan aikin, tabbas ya zama mutum ya gina kansa, wannan Shi ake Kira da daga taimako!
Wuri ta samu ta zauna tace'' Bari muga? Waye zai yi nasara mu ko su?"
Waya ta dauka ta kira Amma bata Shiga ba, dayar kuma ba'a daga ba, ajjewa tayi tana Kara Jin mamaki gami da jimama min wannan abu,
Dun kule hannun ta tayi tana jinjina Kai tare da bubbga kafa daya tace'' sai na koya maka hankali, sai na koya maka hankalin da ko masu kudi Ka gani zaka gudu, sai na sa maka tsoron mu a cikin zuciyar Ka yarda ko maka mantan sunan mu aka an bata sai Ka razana, ba'a taba ba,kuma baza'a fara ba"
Tashi tayi ta wuce Sama ta dauko wata wayar ta, ta Dan jima tana yi sannan ta ajjeta ta fito, kana gani zaka san abun ya Mata zafi sosai.
????????????????????????????
"Ina taya ki murna kin samu transfern lettern ki, kije ki karba a wurin barrister Ibrahim,
Amina da taji dadi sosai tace'" Nagode sosai yanzu Insha Allah zanje na karba"
Yace'' bakomai haka zaman taren yake ai, Kar a yar da zumunci de"
Murmushi tayi sosai tace'' Insha Allah baza'a yar ba, Ka gaida min da ummu"
Dariya yayi yace'' ohh Ummu de zata ji,amma tana 9ja sai dai na gaida Madam"
" To Ka gaida ta nagode"
Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kashe wayar ta, tattara abinta ta fara yi masu amfani sai da ta gama sannan ta fito ta Shiga office din barrister Ibrahim suka gaisa sannan ya bata ta fito.
Tana zuwa gidan kamar kullum suna zaune Yana de bewa Inni kewa Yana bata labari masu dadi yana kuma taya ta aikace-aikace, sallama tayi ta karasa shigowa,
Baffa yace'' Amina lafiya kuwa? Kin dawo da wuri yau"
Inni tace'' gashi kuma Yana yinki ya canza"
Ajje kayan hannun ta,tayi da ragar ta, ta karayin wata Kalar tausay, tace'' a wurin aikin mu ne, aka min transfer, saboda wani case da muka fara ba'a so muyi nasara shine aka min transfer"
Inni tace'' aka maki transfer ko kuma kika yiwa kanki ba?
Baffa yace'' Haba de, kin taba gani mutum yayi wa kansa transfer, kinsan fah aikin yanzu, zai iya iyuwa ma wani Mai kudin ne yace a mata"
Wani kallo Inni fa watsa mata, tace'' ina aka maida ki?
Jakar ta dauka ta dauko papern ta bude tace'' Gumel"
" Mtsww bansan kina fushi ba ai sai kin bar kasar shine zai nuna hakan"
Ta tashi tayi shigewarta daki, Baffa yace'' rabu da ita, bata San duk a cikin iya aiki bane, yaushe ne tafiyar?
Tace'' ko yaushe Baffa"
Yace'' to shikenan jeki huta"
Da Rana suna cin abinci ita de kawai cakulawa take, Baffa yace'' wai meye ne?
Tace'' Baffa inajin haushi ne,yanzu shikenan..."
Sai hawaye, rarrashin ta Baffa yayi yace'' shikenan kiyi hakuri haka Allah ya kaddara,banso ki sawa kanki damuwa"
Abincin ya dibo ya bata ya Kai bakin ta yace'' haaa"
Dan murmushi tayi ta bude bakin, daga nan fah yar Mata aka war tsake,daman tayi hakan Dan Inni ta yarda,Inni kuwa ci kanki bata ce, ko kallan su ma batayi bare ta sa musu baki.
????????????????????????
_London_
Tana kusa dashi tana kallan Uncle da shida gawa babu banbanci a wurin motsi, tana kallan Shi, kawai, yarda yake wani iske, Kai kace lafiyar sa qalau, kafar sa duk ta warke sai abinda ba'a Rasa ba,
Baba yace'' ya kama ta ku koma, ga aiki Ka baro a office"
Abie yace'' ai Baba bakomai"
Umma tace'' gaskiya ya kamata,kunga de jiki gashi nan, de sai dai saukin karaya"
Anty tace'' shikenan zamu tafi tunda korar mu kuke"
Abie yace'' wai da sati zamuyi"
" A,ah Ku tafi kawai, Allah ya bada lada"
✨✨✨✨✨✨✨
Washegari a kotu, kowa ya zo karfe takwas kamar yarda akayi ta jiya babu mutane sai su kadai, kowa ya zaune sai anan Abba yaga PA jinya sunne me shi kamar ba gobe, sai gashi yanzu ya ganshi, kwafa kawai yayi inda aka fara shari'a cikin kware wa da iyawa da ga kuma shaidu sun shaaida hakan ga kuma kwararn takardun gaskiya a hannun su, sai da aka gama Jin da kudin da suka zuba duka.
Alkali yace'' Mahmoud zai biyasu dukkan kudin da suka kashe da kuma kazafin da ya masu shima dole zai biya. Zai ba kowannen su a kalla miliyan daya da rabi, rabi sabida Kaya sun tashi, sannan ya bisu da kudin kazafin da ya musu dubu dari dari, shima Wanda aka kawo kararsa zaka bashi Daidai ga abinda Ka basu wannan shine, nanna da zuwa gobe zaka sallami kowa wannan shine"
Sannan alkali ya hada Shi da police akan lalle lalle ya biya su kudin su,
( Ban iya shari'a ba, abinda yayi ne yaci ace ya biya kudin, ina neman afuwa idan banyi dai-dai ba, nagode)
Tashi yayi ya fita sannan Suma suka fara tashi suna fita, haka police din nan suka tusa kyeyar Abba, a mota ya dauko check yayi ta cikewa Yana Basu, su goma sha biyar ne,sai da ya bada kudi da yawa kowa ya sallame Shi takun ya Shiga mota ji yake kamar ya bada gaba kidaya dukiyar sa, Yana mota yaji ana masa waya, daga wa yayi masu aiki ne sukace sun Gama yazo ya sallame su, kashe wayar yayi batare da ya ji karshen zancen ba, jinshi yake duk wani irin, bema mara sarewa ba sai da yaga ana ta masa debit alert, kawai kashe wayar yayi tsabar takaici Yana sauke numfashi Kai kace gudun tsare yayi.
Bayan wata uku ...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? *A BAKIN WAWA* ????
_Akanji magana_
48
Suna parlour suna game ita wucewa yayi ya Shiga dakin ta ganin bata nan ya kwankwasa toilet namma shiru ya bude yaga bata nan, ya fito kallansu yayi,
yace'' ina take?
Mas'ud yayi saurin cewa'' ita wa?
" Mtsww ita mana"
Mus'ab yace'' tana can parlour"
Wucewa yayi tare da Galla masu harara, tana kwance tana latsa waya Akan kujera, kafar ta ya sauke ya zauna ya daura kafar aka cinyarsa, tashi zaune tayi,
tace'' yau ka dawo wuri'
Balla mata harara yayi yace'' ba sannu da zuwa fah''
Murmushi tayi tace'' Haba Mai gidana yi hakuri tou''
Dan yatsar kafarta yaja,tayi Kara, tace'' da zafi Mai gida"
Zai Kara ja,tayi sauri ta janye kafar ta, tana dariya,
Kumbura fuska yayi yace'' yau...
" Laifi nawa nayi?
Murmushi yayi sosai yace'' Ashe kin San laifin ki"
Tace'' amma Yana ganka kamar kana cikin farin ciki"
Gyarawa yayi ya zame ya kwanta ya daura kansa a cinyarta Yana kallanta, ita Shi take kallo, hannu tasa tafara shafa masa Sumar sa,Yana kallanta, tare da kamo hannun ta guda Daya ya rike, Yana wasa da hannun ya fada Mata yarda akayi, sai da ya gama,
Tace'' amma fah Faisal Adam sunan Baban Ummu ne"
Zaiyi magana wayar sa tayi Kara ganin barrister Ibrahim yasa Shi tashi zaune sannan ya daga,
Barrister yace'' kaga ma yanzu nan na Kira shi dayan barristern yake cemun zaiyi tafiya, kawai inaga Zan zauna,
Binaif yace'' kana ganin ba matsala?
Barrister yace'' babu Insha Allah shikenan sai anjima"
Komawa yayi ya kwanta yace'' yace ma barristern zaiyi tafiya"
" Zuwa dubo uncle a asibiti"
Yace'' sai yaushe mu zamuje?
"Sai ranar da kasa rana"
" Shikenan ba rana kenan"
" Um,um''
" Ina so zanje Spain daga can sai mu wuce mu dubo Shi"
" Kana so zaka je Spain, daga can sai mu wuce mu dubo Shi, damu Kenan za'aje kodani ni kadai"
Hancin yaja, yace'' kekam ko? Sai kace Wanda kika yi psychology"
Murmushi kawai tayi batayi magana ba, ganin Yana neman rufe Ido alamar Yana Jin dadin yarda take shafa masa Kai, ga kuma hannun ta da ya rike shima,
tace'' ita wannan Sumar ba'a askewa ne?
Buda idan yayi yace'' so nake na tara irin taki, Mai yawa, tama fita tsayi"
Ware ido tayi irin really, sai kuma abin ya bata dariya tace'' ina bazai yi ba ma"
" To kisa wasa ki gani"
"Haka kace"
Tace'' ina San fita makota mu gaisa da su"
Juyawa yayi daga kwanciyar yace'' to na hanane? Zaki iya zuwa ko yaushe ma idan Bana gida"
Tace'' Amma gaskiya ya kamata a cire wannu sumar, idan ba haka ba Zan Kai karar Ka wajen Umma"
Juyowa tare yin 'yar Dariya yace'' so kike kawai ki tada min rigima de, Umma bala'i ce"
"Umman kake cewa bala'i?
"Kina wasa da Umma, wannan tsohuwar idan ta kara girma da matsala''
Dariya tayi tace'' to nidai badani ba,Kai da ita kuma Zan fada Mata"
"Kiyi ta fada indai nine, daman tace na tsaneta, sanda taje spain"
"Taje spain?
"Kai tab sanda ciwon kafar ta yayi tsanani wani zuwa da Mijin Anty Ummi yayi gaida ita kawai suka taho tare sai ganinta mukayi, in fada maki, daga nan Ranar da tazo ranar ta fara yi mana jaraba,Anty ummi tace na zubo mata abinci, shikenan ta fara masifa wai Dan ta rena ta yaro ne zai zubo mata abinci eh,eh wannan ai reni ne, eh, bata da kunya, ehh rashin kunyar da takeyi ashe be barta ba, eh"
Dariya tayi Sosai tace" to meye na cewa eh din"
Yace'' Rasa abin fada tayi kuma tana San yin fadan, harda cewa nima na koma dangin nasara, ai Umma Idan tana fada kawai Kar ki kulata, Shikuma Mas'ud sunfi shiri da ita shine me fassara abinda nake cewa da Spainish, sabida wani abun Yana kari"
Tace'' indai chatty ne zai aikata abinda yafi haka ma"
" Meye naji ana cewa chatty me yayi? Wato gulma ta kuke me kuke cewa?
Karasa shigowa yayi ya zauna, a kujeran kusa da ita yace'' kina jin ina maki magana ko?
Tace'' labe Ka koma Kenan?
"Kin manta abinda yafi labe na koma ba labe ba"
" To meya kawo Ka?
" Daman maganar Sameera ce, nace kawai tunda ga su Yusuf nan suma zasu abinda zata yi,ko fiye ma da yarda zatayi, shine nace kawai a bar zancen ta hakan zaifi"
Za tayi magana Binaif ya matse hannunta dake cikin nasa kallan Shi tayi ya girgiza Mata Kai, alamar tayi shiru.
Tace'' to shikenan hakan ma zai yi,Ka barshi kawai"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da fezar da iskar bakin sa, kallan sa kawai tayi ta girgiza kai,
Binaif yace'' sai me kuma,ina mus'ab"
" Gashi can Yana shiryawa wai zai tafi"
"Ina"
"Abuja"
Tace'' okay, sai yaushe kuma?
" Oho masa, idan yazo ki tambaye shi"
Binaif yace'' Kai kuma fah?
" Ni Spain nake so na koma,akwai aikin da zanyi Dana wa dana twinny idan na tafi Zan jima gaskiya"
" Yaushe zaka tafi?
" Nanda sati daya"
" Ka Gama aikin da aka saka?
" Wannan ai ya gamu, sai dai wani kuma"
Tashi zaune yayi yace'' inaga tare zamu tafi"
" Kaima zakaje, harda wannan abar za'aje?
Binaif yace'' eh harda Antyn ku zamu tafi"
Bata fuska yayi ya tashi yace'' har nafara Jin wani ama-mai wai Anty, sai anjima"
Ya karasa fita, tace'' kaima kace wata Anty? Taab kasan me kace ai"
Komawa yayi ya kwanta yace'' zamuje zata inga mi amor dinta yayi rayuwa ko?
" Ehh to kusan haka"
" Maybe mubi ta paris"
" Allah sarki sahr idan munje Dan Allah zan je gidan su, ban taba Kiran ta ba, gaskiya Bani da kirki"
" Damma ke kika fada ba wani ba''
" Eh naji din, Kira mana umma mu gaisa Banda numbern ta"
Wayar ya dauko yace'' nasan sai ta Gama zagin baba Usman tukunna"
Dariya kawai Ummusalma tayi, a speaker yasa wayar tana daga wa kuwa tace'' Assalamu Alaikum, nace batan hanya kayi? Ko kuma bashi ake bina aka kira ni a tuna min? Dan uban ka Adamu ba magana nake maka ba?
Yace'' Umma ina wuni?
" Ehh yayi baya da gudu be dawo ba"
" Haba Umma daga gaisu wa kuma?
" Naga na amsa eh? Kai kaji yaro Ka kiyaye ni, meye kuma aka kirani ?
" Daman nace yaushe zaki dawo nayi kewar ki sosai"
Washe Baki tayi tace'' kaji yaran arziki ai kwanan nan zan dawo ina zuwa sitiret sai gidan audushakuru bawan Allah Mai nema na"
Bashiri ya ta Shi zaune yace'' wanne gidan kenan?
" Kaji dan zakaraw'a kuma kake nema na? Baka so na dawo ko? To wallahi daga nan sai gidan ka, kaji dakyau, nace kaji ai"
Bata rai yayi yace'' daman ban Kira ba"
" Ba mutuwa zanyi ba,kuma ba yaushi zanji ba, daman ba Kira kake ba, munafikar matar Ka ce zata ce Ka kirani"
" Haba ummu me Mata ta tayi maki kuma"
" Ai wannan matar taka tayi ta sinne Kai wai ita kunya, idan tana yi sai kace wata tsohuwar munafikan da tayi sata aka kama haka take Kai Saima zatayi dariya a wani noke Kai ana taba abin hannu iwa sai kuma a danyi murmushi ace Kiki hmm hmm, wai dariya ce hakan"
Kallanta yayi da take kunshe dariya yace" umma Zan fada Mata fah"
" Dan uwar Ka safiya ai ba tsoranta nake ji ba"
" Gaskiya Umma kina da matsala"
" Nice gidan haya,nace nice gidan haya a matsala dan zakaraw'a Kai"
Yace'' kinga sai anjima nadena kuma kiranki"
"Hehehe audushakuru Kenan, daman ba Kira kake ba, Ka gaida dunkun Kumar matar ka idan kaga dama"
" Banida dankun Kumar Mata"
" Taje can ta sani maka"
Kashe wayar yayi yana bata fuska, kallanta yayi yaga ma dauriya take, yace'' duk ke kiga bada wannan shawarar ai, gashi nan zata dawo gidan ai"
Tace'' to ni menayi?
Pillow ya dauka ya wurga mata, tashi tayi daga kusa dashi tare da yi masa gwalo ta fita a guje, ya biyota yana kumbura fuska, a parlour taja ta tsaya ganin Mas'ud da Mus'ab yasa ta tsaya tana saisai ta dariyan ta,
Tace'' lafiya? Naga glip da jaka ina zuwa?
Mas'ud yace'' ciwon mantau ya kama ki"
Binaif da ya karaso ko kallan su beyi ba ya samu wuri ya zauna.
Mas'ud yace'' me kika masa?
"Nasani? Daga yin waya da Umma shikenan ya koma haka"
Mus'ab yace'' idan na biye ku baza Ku kaini airport din nan ba, sai nayi missing flight"
Tashi mas'ud yayi yacei kaga tashi na kaika a bamu key"
Tace'' Yana can parlourn"
Zuwa yayi ya dauko yace'' to muje''
Sallama ya masu suka wuce.
Zuwa tayi ta zauna a kusa dashi tace'' Mai gidanaaaaa,
Ta fada tana jingina da hannun sa ta daura kanta a kafadar sa,
Tace'' zo muje muyi girki"
Yace" sabida?
" Kaga wataran idan Bana nan shikuma sai Ka Shiga Ka girka abinka"
" Kuma ni barin ki zanyi kije wani wurin?
" Sosai ma,sai dai idan abu bai taso ba"
"Naji wannan, tashi muje muyi girkin to"
Tare suka Shiga kitchen suka fara aikin su, sunayi suna hira suna dariya abin su.
Yau za'ayi shari'a Dan haka da wuri kowa ya hallara a kotu Inda za'ayi daga su sai su babu wasu mutane,
Sun zauna kowa a zaune har alkali inda ya Gama Jin wannan karar ta Abba.
Alkali ya dubi Binaif yace'' Abdulshakur shin anyi haka?
Binaif cikin nutsuwa yace" anyi haka ya Mai girma Mai shari'a...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: *????A BAKIN WAWA????*
_Akanji magana_
50
"Alhaji yanzu haka zamuyi ta cigaba da rayuwa? Babu aikin yi? Sai kudi da yake ta tafiya babu aikin yi? Ga rashin lafiyar ka kuma da wanne zamuji?"
Ajiyar zuciya ya sauke yace'' Saratu kina gani duk sana'ar dana fara sai dai muyi asara babba ma kuwa, kuma yanzu kike kawo min wani zancen ki"
Tace'' to mezai Hana mu Saida wannan gidan mu koma karami Mai three bedroom ya ishe mu a wadace de"
" Hakan bazai taba iyuwa ba kuwa"
" Aikuwa hakan shine daidain da zai iyu, sabida ga su yaseer nan suna makaranta, Ka Saida motar su Duka biyun,ga kudin transport shima wani abunne ga kudin abincin su, Haba de ayi tunanin ma, gashi duk wata ana bawa masu aiki kudin su, mu ba kudi ba sai kashe kudi wallahi bazai iyu ba"
" Saratu bansan a kara maimaita min abinda ya faru game da asibitin can,kina kallo har gida aka zo akace ba mallaki na bane, Wanda ya Saida min ba nashi bane,irin masu zuwa a siyar da filin karyar nanne, haka inaji ina kallo basu Bani ko Sisi ba, kudin magada ne shiyasa ba'a Bani ba, sannan kuma zasuyi aijin ruguza ginin da aka far, yanzu idan ba kina so a Kara cutar mu ba, me kike kiyi Kenan? Wannan gidan nawa Shikadai na mallaka,kuma a cikin sa Zan rayu har Allah ya dauki raina, abinda yake cikin zuciya ta ma kadai ya isheni, radadin da nake ji ba? Ciwon abinda nayi nake ji, kunyar kaina nake ji, nasan 'ya'yana idan suka ji wannan labarin har su mutu baza su taba yafe min ba"
Shiru yayi Jin wata, irin kuna da yake ji, a cikin kirgin sa, ji yake tamkar ana hura masa wuta a ciki, babu abinda zai sha ya rage masa wannan radadin, cikin wata murya mai rauni,
yace'' a watan nan zan aurar da Sameera koda kuwa bata da Mai sonta Zan hada ta da wani"
mama tace'' 'ya'ya sani zasu yi? Waye ma zai fada masu to?''
Yace'' ni Zan fada masu, irin abinda nayi,kada suyi koyi da halina"
Tace'' wasa kake, wallahi wasa kake, nidai bazan iya ba ato na fada maka, batun aure kuma zaka iya Mata, wannan kuwa na goyi baya dari bisa bisa, Amma batun wannan kin Saida gida da na kuma fada masu wannan sirrin namu ba Dani ba"
Daga haka ta tashi ta koma Sama runtse idan sa Abba yayi tun sanda Inuwa PA ya aci amanar sa, tun daga nan ya dawo cikin hankalin sa be Ankara ba yaji wani ruwa ruwa na bin kumatun sa Yana gangarowa wuyan sa,hannu yasa ya taba Jin daga kumatun sa yake ya tabbatar masa da hawaye ne ba komai ba, beyi mamaki Dan yanzu ya koma tamkar raguwar mace, tambayar Daya ina zai samu Ummusalma ya bata hakuri?
Da yake a parlour suke, Sameera data shigo gidan Jin suna wannan zancen yasa ta tsaya taji komai, a hankali ya karasa hawa Sama hat ta Shiga dakin ta, wayar ta, ta dauko ta sa numbern sa Wanda ta Riga da ta hadda ce ta a kanta, hawaye ne ya fara zurya a fuskar ta, bata damu ta goge ba,
tace'' kana ina yanzu gashi Abba zaimin aure da wani ba Kai ba, Kai nake so ..."
Sai hawaye ta kifa kanta tayi ta cigaba da kuka, babu Mai rarrashin ta sai ummu yau kuma ummu bata zo ba,da taje ma ta gidan su Basu dawo daga school ba, kukan ta, tayi tayi daga nan bacci ya dauketa.
✨✨✨✨✨✨✨
Suna zaune su hudu suna cin abincin su hankali kwance sunayi suna hira abinsu duk da Rabin hirar su kadai sukeyi Banda ita.
Tace'' gaskiya Chattu Ka dameni,kabar ni naji da yajin da kuka cika mana a abinci mana,Amma sai zuba kake kamar me ma zance da, Haba Ka rabu da mu mana dame zamuji?
Yace'' to Allah yasa ma ba Mas'ud bane yayi abincin Mus'ab ne yayi a to bani ba"
" Fav kake Jin tsoron Allah, sai da nace wannan yajin yayi yawa yace wani ai kin fi San yaji, kema haka kike maku a spain"
Binaif yace'' kunsan Allah zan kora ku,Ku tafi part din ku, kunda meni"
Mas'ud yace'' yi hakuri kaji bb, wannan aljanar matar taka ce ai mai kama da jannu"
Tace'' sannu to, malamin Aljanun duniya, ya mu'allim din jinnu sannu ko?"
" Jiya tsabar daudewa bata San meye Malam da mu'allim ba"
" Shi yasa Naga Kai kasan aljana da jinnu ai''
Ta maka masa harara ta janyo plate din gaban ta, ganin duk sun ajje spoon din su, daman ita da hannu take ci,
" Ci ba kiba, sai kace gara, mutum yayi ta ci,yayi ta ci,yayi ta fama ko gajiya bayayi"
Mas'ud yace'' Fav kafiye sa Ido ina ruwan Ka"
" Bakasan wannan yarinyar bane ba, taaab Kai kasanta kuwa?cabb bb bashi labari da azumi"
Binaif yace'' wa? Bade ni ba, Kai de zaka iya amma nikam kunga nama yi nan"
Ya fada tare da tashi ya mata peck ya fice, mas'ud yace'' me ya faru da azumin? "
" Kai Kar kaso na baka labarin cin abincin ta, daman kullum wani katan bread sai ta cinye Shi tas da asuba kafin mu ya dafa abinci, befi tabar kadan ba, wannan sumun tabi kenan sai nan kuma..."
Spoon Daya ta dauka ta kwada masa, tace'' Bana San karya, daman salan rowa ne, wani indomie da rana, kuma baza'a dafa dayawa sai kadan"
Tashi tayi ta bar musu wurin, Mas'ud yace'' bashi sai na rama,
Mus'ab yace'' basa sunan wani film ba"
Mas'ud ya koma kujera yace'' wai me Ka tsaya yi a Abuja kafin Ka tafi wurin Umma Naga de tun kafin azumi ya saida companyn shi "
Mus'ab yace'' bakomai kasan garin akwai dadi,ina san garin sosai"
Tabe Baki Mas'ud yayi yace'' Kai kasani"
" Fav gist me"
" Kaifa gulma ne da Kai me kake San ji?"
" bb da aljanar ka"
" Munafiki Twinny to kuwa baza Ka ji ba"
Matsowa yayi kusa dashi yace kasan de nida kai ba'a Jin Kan mu ko? "
" Me Zan fada maka? Idan suka tun safe to sai yamma zasu dawo, sai ni kadai, Nima wata ran na bisu wata ran kuma na zauna, wai in fada maka, suka tafi suka barni? Ina bacci?
" Ina?"
" Paris, nake fada maka, wai sai da suka je airport aljanar nan ta kirani da wannan muryan ta ta,sai ca tace to idan Ka ga dama Ka tashi mu muna airport, Kai kaga wata mikewa danayi da kayan bacci ajikina kawai ta dauki jaka ta na goya daman na hada komai na, na dauki waya ta da wallet a dari na fito bamma rude gidan sai Mai gadin ne, ya rufe drivern kwa, kawai gudu yake ganin na fito a haukace, ina zuwa kuwa na Shiga, aikuwa nine last a shiga"
" Sun tashe Ka kaki tashi"
" Wai haushi taji na koma bacci Dana dawo sallah shine aka min wannan abu, kasan ta fa, to jarabar yanzu ta linka ta da"
" Amma ta hadu da wannan kawar ta ta ko? Mai shegen surutu kamar loro"
Gyara Zama yayi ya lankwashe kafa daya,Daya kuma a kasa,
yace'' ai in fada maka, muna sauka na hango su, da tafiya zasuyi su barni, aikuwa na gano su, muka tafi, muna zuwa fa da yamma sai ta Kira sahr wannan 'ya de data zo daukan mu muje gidan su, tun a mota ta ringa zuba take yi, takeyi, ko nace suke yi, Ashe ma 'yar uncle Felix ce,Ashe Kai Baka San Shi ba"
" Nasan Shi ban taba ganin saba de''
'' yawwa to 'yar sace''
" Daga nan muka je London zamu gano Bros sai aka ce sun dawo 9ja shikenan sai muka koma Spain, show ya barka"
" Kai dai bari daman naje''
" Sosai ma"
"Sai me kuma?"
" Ande ji wani wuri kude kam, ohh su glip da gulma sannu to"
Ganinta da bowl Mas'ud da yayi yasa Shi yin shiru sai da ta zauna ya koma kusa da ita yace" Zan sha, kinsa de ni dake tamkar hanta da jini haka muke forever and ever ne"
Mas'ud yace'' andeji kunya,kaima kaje Ka hada naka mana"
Pillow ya dauka ya wurga masa yace'' waye yaji kunyar? Reni ko?"
Shima dauka yayi ya wurga masa, yace'' Kai din fav bro twinny"
Aikuwa sai suka fara daga karshe ma tashi sukayi suna zagaye kujeru suna gudu, su Yusuf ne suka shigo da gudu su Duka ukun sukayi kanta suka rungume ta,
Ihun sune yasa su Mas'ud tsayawa yace'' Ku meye haka? Zaku wani zo ku wani rungume ta, sai kace Yaran da aka gudu aka Bari, dalla Ku sake ta"
Ummu ta mararai ce tace'' Haba yayamu, yanzu yaushe ta dawo mu Dade bamu hadu ba fa, shiyasa"
Wani fasa dadi yake ji duk sanda aka ce masa yaya, dawowa yayi ya zauna yace'' aww haka ne fah, Ashe anjima ba'a hadu ba"
Yusuf yace'' wata uku fah, ai ba wasa ba"
Yaseer yace'' to da waya ce wasa ne"
Bige Shi yusuf yayi yace'' Ka kiyaye ni, Naga reni naso ya Shiga tsakani tam,Kai da wannan yarinyar Ku raba kanku dani"
Hada Baki sukayi shida Ummu suka ce " inyeee sannu babba"
Mus'ab yace'' kude San girman Ku ya maku yawa wallahi,kunji kunya de"
Mas'ud yace'' kasan ance sai Hali yazo Daya ake abota ko?"
Yusuf yace'' shiyasa muke abokan juna ai"
Ummu tace'' yaya salama yunwa nake ji"
Ummusalma tace'' aikuwa ba'ayi abinci ba, Nima na koshi nayi ba, wata indomie aka dafa mana, ba kwai ba komai sai shegen yaji, kuma babu lemun hada wa,sai de kije ki dafa maku wani abun"
Yaseer yace'' daga mana wake da shinkafa yau indomie muka ci fa da safe"
Tashi tayi tace'' haka za'ayi Dan uwa na"
Yusuf banza yayi dasu sunsan Baya son Shinkafa da wake shine zai ce a dafa Dan neman magana,
Yusuf yace'' kasan yayamu ko? Wannan yaran kullum sai sun bata min Rai, narasa me na tsare musu"
"Ai haka Yara suke aboki na, Nima haka nake fama da wannan yaran abin sai addu'ah kawai"
Mus'ab kawai Kai ya girgiza, Mas'ud kuwa yace su fita suyi ball, fita sukayi su duka Banda Ummusalma da tashi ta Shiga kitchen ganin ummu na aikin Dora abincin yasa ta dauko fruit salad tace'' Idan kin daura kizo ki Sha wannan, kafin kuci abinci,ki kuma daura da yawa basai an kuma yin wani abincin ba"
Ummu tace'' to shikenan"
Yoghurt ta dauka ta fito waje, ganin su suna ball amma Banda Mus'ab Shi Yana zaune Yana kallan su.
Zama tayi a kusa dashi, ta taba Shi,sai da ya juyo ya kalleta,
tace'' Wacece ita?"
Kallan ta yayi dakyau ita kuwa bashi take kallo ba, su take kallo,
yace'' banga ne ba?"
" Tunda kaji abinda nace ai shikenan, sunanta?"
Kallan sa ya koma zuwa wurin su, cikin muryan alamar dake nuna tsantsanr damuwa,
yace'' ban san taba, ban san sunan ta ba, ban san gidan su,Dan uwa, kawa, bansan komai ba, kawai ina ganin ta de a unguwar Dana zauna dake Abuja, tana yawan wucewa da yamma, tana cikin damuwa, ina San taimaka Mata,ban san ta inda Zan fara ba, kuma na dena ganin ta, naza ci kawai taimakon ta zanyi, Ashe ba haka bane, Son ta nake ban Sani ba, sai da na dena ganin ta a unguwar kwata kwata,I love her"
Cigaba da sha tayi tace'' da Ka fada Mata tun wuri da duk haka bata faru ba, yan zuma lokaci be Kure ba, Insha Allah za'a samu solution"
"But please don't tell Fav please! Ina san Naga shima ya samu wacce yake so"
Shiru tayu ba tayi magana, sabida ya tuna Mata da Sameera har yanzu tana can tana dankwan san, Wanda yanzu ya tabbata ya manta da ita, ajiyar zuciya ta sauke kawai tana ci gaba da kallan su, ji sukayi an turo gate an shigo da Kaya niki niki an kawo an ajje, drivern gidan Daddy ne,
Mus'ab yace'' Malama Musa kayan waye?"
Yace'' na Umman Alhaji ne ai" sannan ya koma, aikuwa sai ga tana ta shigo,
Mas'ud Yana ganin ta ya kwasu da gudu yazo ya rike ta, saura kadan su fadi badan ya rike ta ba da tuni sun hantsila, cikin bala'i,
tace'' Kai kaji yaro ne, yanzu Dana Fadi ba, ai sai dai wata mai tagwayen sunan bade wannan zainabun ba"
Sandar ta ta dauka zata kwala masa ya rike, yace'' Haba Hajjaty murna ce fa hakan, ai kinsa Dan da uwa idan maman Shi ta dawo haka fah yake Mata"
Kwace sandar tayi ta kalli su Ummusalma da mus'ab tace'' ehh gwara Kai ai, Dan albarka akan wasu da ko kallo Basu ishe ni ba, kuma a gidan nan Zan zauna ko ana suna ko ba'a sona, aji ma dakyau yawwa ana nuna min daki na"
Binaif da yazo yanzu dayake ba'a mota ya fita, ganin ta da yayi yasa ya turbune fuska yace'' ai banyi da dakin ki ba, kima koma inda kika fito Dan nidai baza ki zauna ki mayar min da gida gidan jarababbu ba"
Wani salati ta dauko ta rabfa, Kai mace wani ya mutu, tace'' yanzu ni zaka fadawa haka? Au..au..du..audu shakuru ni? Nice fa na haifi babanka,na haifi Ubanka,na haifi babar Ka, sannan nazo na haifi uwar Ka da ta koya maka rashin kunya, Allah ya jikanta, shine zaka ce min jarababbiya ko? Har kace mema yace?
Ya fada tana kallan Mas'ud, Mas'ud yace'' haka yace baza ki maida masa gida gidan....
Karaso wa yayi ya kai masa naushi ya goce yaje ya buya a bayan ta,
tace'' yau a gida nan zan kwana,Kai Bama kwana daya na, anan za'a jana'iza ta, Dan uban Mai gidan da matar mai gidan ko suna so ko basa su"
Takuma cewa'' kaga nuna min daki, a cikin gidan masu gidan nan"
Mas'ud kuwa kayan ta ya dauka ya, yace'' shigo na kaiki dakin ki"
Tana tafiya tana Mita, tsaki Binaif yayi ya zo ya zauna, Yaseer ya Kara so yace'' yaya Wacece?
Mus'ab yace'' kakar muce"
Yusuf yace'' amma tafiye masifa''
Ummusalma tace'' Idan taji ku kuda ita ne,Kar ku sani a ciki"
Suna cin abinci Umma tace'' wai ba ruwa a gidan nan ne?"
Yusuf yace'' jiya suka dawo, inaga yau kuma aikin gida sukayi"
Ummu tace'' ehh inaga yanzu zasu je su siyo"
Umma tace'' ai ni ina San haka, nayi tambaya,ayi farat a fada min amma masu gidan nan hmmm sai addu'ah"
Girgiza kai Binaif yayi, kawai ya tashi ya tafi dayan parlourn ya zauna, Umma kuwa daga murya tayi tace'' azo a siyo min ruwa dan kaniyar mutum"
Mas'ud yace'' Bari mu Gama daman za'a siyo wasu kayan sai muje"
Sai da suka sha fruit salad sannan suka fita Banda su ummu da suka wuce gida, aka bar Mas'ud da Umma kawai sukuma suka fita.
Sun Gama siyayyar su Ummusalma tace'' ina zuwa bari naje na dauko wani Abu"
Mas'ud yace'' so kike mu tafi mu barki,daman kin daddar mu"
Binaif yace'' muna nan kiyi sauri"
Wurin turare tayi, zatayi kwanar da zatayi ta hango Sameera ita da ummu suna zaba, kallo Daya tayi mata ta hango kwantacciyat damuwa a tare da ita, da wani irin speed ta juyo, ta dawo,
mas'ud yace'' ina abinda kika dauko?"
Matsowa tayi kusa dashi tace'' na kasa kuma banga masu aikin ba, zo muje Ka dauko, ina bb?"
" Ya tafi mota, muje ni na dauko maki,gaba yayi ya barta a baya, ita kuwa a Baya ta tsaya tana tafiya a hankali, tana binsa shikuwa har ma yaje, wurin sai kace yasan me zata dauka, kallan kayan wurin ya fara yi a hankali idansa ya Kai kan wani turare mai kyau dashi hannu yasa zai dauka, itama tasa zata dauka, dago da kan da za tayi kawai ta makale a haka,ita bata dauka ba kuma bata janye hannun ta ba, shima dagowa yayi ganin Wacece haka, ganinta da yayi yasa kirgin sa dokawa,gashi shima ya makale a hakan,kuma ya kasa dena kallan idan ta.
A hankali ta saukar da kanta ta janye hannun ta, ta kakaro wani munafikin murmushi,
tace'' Ashe ana ganin Ku"
Shima janye hannun sa yayi sai dai be dena kallan ta ba,
yace'' uhm"
Tace'' Allah yayi zamu sake haduwa,kafin nayi aure"
Dan dagowa tayi ta kalle Shi,yarda ya kafe ta da ido yasa ta kawar da kanta gefe tana kallan wasu Kayan, dakyar ya furta "aure zakiyi?"
Tace'' eh aure zanyi nanda wata uku zuwa hudu sai anjima"
Ta gefen Shi ya rabe ta wuce,wani siririn hawaye Yana zubota. Kulle idan sa yayi besan dalili ba amma wannan abun da ta fada cewam zata yi aure tamkar an Sami garwashin wuta ne an watsa masa a cikin zuciyar sa haka yaji,
Ummusalma tazo tace'' hey na dauka fah, mu tafi"
Kallanta kawai yayi yaga kuma tayi gaba, hakan yasa kawai ya bita ba Dan yasan me tace ba, a mota ma suna ta surutu shikuwa besan me yake ciki ba.
????????????????????????????
Waya yake amma Baya Jin abinda ake cewa sosai sabida hankalin sa yayi gaba, kashe wayar ma yayi sai da ya shigo yaga dakuna, ya manta wanne tace masa ma,
Wata zuciyar tace'' kamar ten tace"
Hakan yasa Shi tura kofar kusa dashi ya afka, bakowa a cikin dakin sai wani daya gani, Yana kwance kamar ma na Rai a jikin Shi,Amma ganin bugun zuciyar shi yasa Shi matsawa a Hankali ji yayi zuciyar Shi na bugawa da sauri da sauri, gani me kama dashi sak, photocopy din Shi,ban bamcin shi ya tsufa dayan kuma yaro ne, wani Abu yaji Yana masa yawo a cikin zuciya, a Hankali ya mika hannun sa ya shafi fuskar shi,
yace'' da yanzu ina da da kamar wannan"
Kara shafa fuskar yayi sannan ya juya ya tafi, Yana fita zuciyar uncle ta fara bugawa da sauri da sauri, Yana fara wa kuma su Baba na shigowa suka Kira doctors.
Baffa kuwa na fita ya hadu da Amina tace'' laa Baffa nine fah nace, shigo.
Beyi magana ba,ya Shiga ciki ya zauna,Yana Shiga su baba na zuwa,
yace'' an siyo mata maganin ta ne?''
Tace'' yanzu zanje na siyo Kar ta tashi ko tana bukatar wani abu Shiyasa"
"To shikenan kiyi sauri karki zauna"
Fita tayi Shi kuma ya dawo kusa da ita ya rike hannun ta gam, Yana kallan fuskar ta, gaba Daya tausayin ta yake ji, yasan dalilin 'ya'yan ta ne wannan ciwo ya same ta kullum sai tayi kukan rashin su, kullum kwana take tana binsu da addu'a, 'ya'yan da bata san suna da Rai ko Basu da Shi ba, dalilin su ta koma wata silent da ita, ajiyar zuciya ya sauke ya Kara damke hannun ta, Yana tuno fuskar Abdullah.
Saida komai ya lafa, Doctor ya kira Baba yace'' ansa mu cigaba don da alama yaji wani abu ne, shi yasa,kuma da ace an cigaba da magana to ba makawa sai zai iya magana, Bama iya magana ba har tashi zai iya yi"
Baba yace'' to yanzu ya za'ayi?"
" Ya kamata kuke debe masa kewa ko hakan zai sa yake Jin maganar ku har ya tashi,tunda Yana jin, magana ce bazai iya ba da bude Ido"
Shiru Baba yaya yace'' daman Shi Baya gani?"
" Baya gani sai dai yaji,kasan wasu Idan Shiga comma magana ce kawai basa iya yi,wasu kuma basa iya bude idan ma bare su gani, amma suna ji"
Numfashi yaja ya sauke, ya mikawa doctorn hannu suka gaisa sannan ya fito,da ya zo yaga wani a kofar a dakin waye ne yazo?"
Amma ai da'alama ba wurin Shi aka zo ba,tunda yaga dakin da aka Shi Wanda yake kallan nasu ne, dakin ya koma ya duba Shi an masa allurar bacci, kallansa ya kuma to sannan ya fita.
Yana fita Baffa na fitowa Baba a Baya Baffa a gaba, a haka suka fita har suka zo harabar asibiti babu Wanda ya lura da Dan uwansa kowa hankali yayi gaba.
✨✨✨✨✨✨✨
Ummusalma ganin yau Mas'ud ko abincin arziki beci ba,bare yayi hira da tsokana, gashi ana gama breakfast yayi part din su kamar jira yake a Gama, Umma tayi tayi ya fada Mata,Amma yace kansa ke ciwo kawai.
A hankali ta turo kofar parlourn su Yana kwance Akan kujera, Yana kallan saman parlour gaba Daya Yara sa taka maimai meyake ji, kuka ma Shi yake so yayi amma ya kasa, waya kawai yake kifa wa Akan cikin sa da dayab hannun sa,dayan kuma yayi pillow da Shi. Har ta shigo ta zauna besan tana yi ba, center table ta dauko ta zauna a saitin kansa tana kallansa, hannun ta Kai ta shafa goshin sa,
tace'' me yafaru chatty?"
Dauke hannun ta yayi yace'' ki barni,Dan Allah karki Kara samin damu wa"
Murmushi tayi ta kuma maida hannun ta shafi goshin sa zuwa kansa,
tace'' tell me, me yafaru meke damun Ka please! Idan ba so kake Nima na Shiga damuwa ba,Haba mana chatty"
Kulle Ido yayi ya bude suna kanta yace'' aure zata yi, nan da wata hudu or what oho but aure zatayi fa..."
Sai hawaye besan ma yayi ba, kawai ta kifa kansa a cinyarta,bata Hana Shi sai da yasai saita, ya koma ya kwanta ya rufe Ido Yana ja majina,tare da sauke ajiyar zuciya,
Tace'' Wacece zata yi auren?"
Wani kallo ya wurga mata,cikin wani irin kunar zuciya yace'' ita wacce kika hada ni da ita, Sameera nake nufi idan ke bakya gane wa"
Tace'' ohh! Wai Sameera? Shine daman kake wani damun Kan Ka? Naga Baka Santa? Meye abin damu wa? Me zata ma? Tunda gasu Yusuf nan suma ai zasu maka abinda zata yi maka"
Kulle idan Shi yayi gam,ji yayi wani iri sam be kyau ta ba, hawaye ne ya zuba masa ya goge,
yace'' please Ummusalma stop joking, this is not time for joke, ehh?"
Tace'' okay fine, let her go"
A sukwane ya tashi zaune yace'' What?"
Tace'' yes! Let her go...
~This page is for u cwthrt ???? Happy born day!~
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? *A BAKIN WAWA* ????
_Akanji magana_
51
Kallan ta yake yi Wanda Shi kansa bazai ce ga taka mai-mai na meye ba, bare kuma ita da akeyi wa, wani hawayen ne ya zubo masa Mai ciwon gaske, yasa hannu ya share,
yace'' I Shall let her go to where?"
Hawaye na kuma zubo masa,
yace'' to somebody's wife?" I think you are with your sense, please go, please I beg you leave me alone, bansan Kara ganin ki, ki fice kawai, ki barni"
Ajiyar zuciya ta sauke,ta kamo hannun sa,ya fizge, yace'' I said go!''
Kara kamo hannun tayi tace" ohh! Wai Santa kake?"
Fizge hannun sa yayi cikin daga murya yace'' ki fita nace"
Ita dariya ma yake ba, Ashe haka ya iya fada bata sani ba, this is first time taga jarumta hade da fushi a ciki idan sa, sai yanzu tasan shi din na Namijin, murmushi tayi mai kyau Wanda dimple dinta ya Loma,
tace'' Chatty, Sameera loves you too"
Kallan ta yayi, yace'' banga alamar hakan ba, da tana so na ai da ta fada min"
" Macen da tasan amsa sunan ta,macen da take da aji Chatty babu yarda za'ayi tace tana San wani da namiji koda kuwa zaiyi ajalin ta, tambayar anan shine menene dalilin da yasa ta fada maka cewan zata yi aure? Sai tana Sanka hakan zai faru, da'a ce basan Ka take ba, zata ja Ka da surutu ne kuma baza ta fada maka ba sanda zata yi aure ba sai auren ya matso kusa sosai zata sanar da Kai, abinda yasa ta sanar Kai saboda kayi wani Abu akai"
Wani irin farin ciki farin ciki yake ji, har wani irin dariya dariya ya fara, kafin,
yace'' dagaske kike fada kuwa?"
" Da karya nake fada"
Rufe Ido yayi ya Bude yace'' kina fa nufin tana Sona kena?"
" Tabbatar wa zaka tsaya yi ko kuma neman hanyar da Zaka bi Ka same ta"
Hawayen sa ya Kara goge wa yace'' a,a hanyar da Zan same ta nake nema"
" Kaje Ka samu bb Ka fada masa, Shi kuma zai fada wa Daddy"
Daga haka ta tashi ta fita,
Wata ajiyar zuciya ya sauke yana godiya da Allah.
Umma na zaune tana kallo, Ummusalma ta Shiga,
Ummusalma tace'' Umma sannu da hutawa"
Umma tace'' yawwa sannu, nace kinga an kwantar da Nafisa a asibiti ta Kira wayar ku gaba Daya bata Shiga ba, nace ko tafi ya zamuyi ne"
" Sai dai network, kuma kinga bamu sani ba, inaga Shi ya sani be fada ba, Dan kinga dazu ya fita"
Umma zata yi magana sai ga Binaif ya shigo shida Mus'ab, Umma tace'' kai,Kai muke jira kazo Ka Kai mu asibiti"
yace'' daga asibitin nake, sai dai Mas'ud yazo ya Kai Ku"
" Dan jakar uba,Ashe ka sani baka fada ba,wai meke damun ka ne, baza Ka warke ba ko?"
Zama yayi a kusa da matar sa ya daura kansa a cinyar ta,
yace'' nace maki Banda lafiya?"
" Mtsww duk abinda zaka yi sai dai kayi amma nida gidan nan mutuwa ce zata raba,marar kunyar banza,ko nace marasa kunya, karshen lafiya ma kuwa"
Ummusalma tace'' Bani key din, muje mu dawo"
Tashi yayi ya Galla Mata harara yace'' Baki da lafiyar? Sai dai Mas'ud yazo ya Kai Ku"
" Da dan albarka ma lafiyan Shi qalau da ban ma magana ba, Tunda tace Ka bata Ka bata mana, ko bakin cikin samun ladan kake min ne?"
Key din ya Mika Mata,ya tashi ya wuce dayan parlourn ya zauna, itama tashi tayi ta dauko hijabin da jakar, Umma kuwa Mayafi aka yafa, suka fito, Mas'ud daya fito yagan su,
yace'' Umma ina zuwa"
"Za muje duba marar lafiya ne a asibiti"
Yace'' to a dawo lafiya"
" Allah yasa"
Yana kwance ya shigo ya same Shi, zama yayi a kasa, Yana sunne kai,
Yace'' bb"
Bude idan sa yayi ganin Mas'ud a kasa yasa Shi tashi zaune,
yace'' lafiya nagan Ka yau a kasa?"
Kara sunne Kai yayi yace'' da..ma..n..daman am..."
" Kaga meye kake tawani daman daman me?" Nade San ba kunya ta kake ji ba, bare nace wani abu"
Kara sunne Kai yayi ya fara shafa keya,Yana ta motsi da Baki"
Dariya ya bawa Binaif sosai, Binaif yace'' karde kaje,garin sunne Kai,Ka kifa kanka a kasa"
Shiru ya kuma yi sai Dan murmushi murmushi da yake yi,
" kaga nifa ba ca nace Zan Baka, 'ya ta ba,bare kuma kazo kana wani Jin kunya ta, abinda bamma taba gani ba kena, Mas'ud da kunya"
Yace'' daman fah''
Tsaki yayi ya kwalla wa Mus'ab Kira, Mus'ab da yazo a kujeran da Binaif yake ya zauna,
yace'' bb gani"
" Yawwa tambaye Shi, me zai fada min, sai wani sunne Kai yake yi, Yana Jin kunya, idan ya fada maka Ka fada min"
Kallan sa Mus'ab yayi yace'' wonders, yau Kai ne haka? Kunya fah Kenan"
Mintsi nin Mus'ab yayi a kafa, mus'ab
yace'' kut, lalle ma me na maka?
Waya akayiwa Binaif ya tashi yace'' kunfa ni na fita, idan ya fada maka, Ka fada min"
Yana ganin Binaif ya fita shima yayi sauri ya tashi ya dawo kusa da Mus'ab ya lankwashe kafa daya, daya kuma ya sauke ta a kasa yake facing din mus'ab,irin zaman da yake so Kenan, musamman idan zai zuba surutu Baya Zama normal a kujera,
Yace'' Kai dalla,Ka kusa cemin Yaya Mas'ud, Kai da waccar Aljanar, very soon zaku fara"
Mus'ab yace'' to sai Ka samu ai"
" Kai bama yaya ba, na kusa Zama BABA? No ba Baba ba Baba old fashion ne, ABBA? No ba Abba ba, shima ya zama old fashion, DADDY? No ba daddy ba,muna da Daddy, to wa? Yawwa PAPPI, yes pappi ko PAPA, ehh su sun danyi haka ma za'a cemin"
" Wai walili ce ta kusa haihu wa?"
" Mtsww da ita wannan ko cikin tana da Shi ma? Ai sai na haihu yarinya ta ta girma tayi wayo ko yaro na sannan zata haihu, Kai aure fah zanyi Nanda wata hudu kyawawa hehehe na girma na bar wani kasan ance mutum sai yayi aure ko me ko ya cika mutum ko me oho de, shine ma fa yanzu nazo na fadawa bb aje ane ma min auren ta"
Ya fada tana Dan dariya irin ba Yana din nan, Mus'ab shima din dariya yayi Yana dariya,
yace'' Kai yanzu aure zakayi? Shine kake wannan uban lissafin, har Ka fara tunanin samun Yara tun kafin ma asa Rana"
" Kai fa banza ne wani sa'in idan kana abu kamar marar ilimi, Sam Baka da ganiya"
" Fadi komai, kuma zaka San Wanda zeje ya fada wa bb din, bakinsu kace min ma marar hankali din na yarda wallahi na hada maka wani abun"
" Wayyo Dan Allah kayi hakuri, Yaya Mus'ab na manta kai ne, lo siento mucho( am so sorry)"
Dawo wa kasa yayi,yayi kneeling a kasa ya hada hannun sa yana rukan sa, shikuwa mus'ab Dora kafa Daya yayi Kan daya, Yana Kar kada wa, daga karshe ma tashi yayi,
yace'' kaga ni tafiya ta, na wuce asibiti"
Tashi yayi ya wuce,yana tasi shima ya tashi,
yace'' wallahi sai dai muje, tare baza Ku barni ni daya a gida ba, sai kace tsohon maye nayi ta tunanin mi amor dina"
Tsaki mas'ud yaja,yayi gaba ya barshi, sun fito har sunje gate,
Mus'ab yace'' haka zaka bar musu gidan Baka rufe gidan ba?"
" Mtsww har wani ni Zan..."
Sai kuma yace'' aww ohh to ni, Minti Daya ma yayi yawa ina zuwa"
Ya fella da gudu yaje ya dauko key din su, ya dauko wallet din Shi, sannan ya rufe gidan ya fito, Yana haki yazo ya rufe gate din suka tafi, suna tafe Yana zuba masa surutu sa'a sukayi suka mi abi hawa suk hau suka tafi.
✨✨✨✨✨✨✨
" Ai ina San idan ana tafiya Dani ake tafiya a hankali Ashe kema bakya gudu, safiya itama bata gudu, amma Ida aka ce Miki audushakuru da Baban su, ko Adamu ba'a magana Ida suka shararo motar nan ba'a magana"
Ummusalma shiru tayi Dan bata San me zata ce bare ta ci cigaba da magana shiyasa,
tace'' ai yafi dadi rashin gudun"
Parking tayi tace" Umma Bari a sai fruit"
" To jeki mana, zance Kar kije ne"
Fita tayi taje wurin Mai Saida kayan, shikuma Yana yiwa wata yarinya fada baza su wuce sa'anni ba,
Yarinyar tace'' kayi hakuri Dan Allah wallahi haka nake dashi,marar lafiya Zan bawa"
Shikuma yace'' ina ruwa na da wani marar lafiya sai kin ciko min kudi na,da kin san Baki zaki ce a yanka miki, ba zaki tafi ba sai kin ciko min"
Ummusalma tace'' yimin hadan dubu Daya da dari biyar, kasa lemu da Dan yawa"
Yana hada wa Yana masifa, yarinyar gwanin tausayin har ta fara matsar kwalla, tausayi ta bawa Ummusalma sosai kana gani zaka san tana cikin hali na taimako, dauke Kai tayi daga kallanta, tana kallan yarda yake hada wa Yana Bala'i, sai da ya Gama ya cika Leda baka da yellow tab sannan ya miko Mata, bata Karba ba ta zaro dubu uku ta bashi,
tace'' nawa ne kudin Ka na yarinyar nan?"
Yace'' dari uku ne"
Tace'' Ka dauka, Ka Kara Mata, sai Ka bata canjin ta"
Tana fada ta karba ta wuce,kafin ma yarinyar tayi godiya har ta wuce, ta biyo ta Dan ta Mata godiyar kuma sai taga har ta Shiga mota taja tayi gaba daman ba kashe wa tayi ba, tsayawa tayi ta sauke ajiyar zuciya ta dawo tace da Mai lemu,
" Ka dauki kudin ka, Ka Bani sauran kudin,Bana San Karin naka"
Zaiyi magana de sai kawai ya Mata dubu Daya da dari biyu abinta, ta karba, ta wuce ta hau napep tana Mai Jin dadi, da yanzu a kasa zata taka,takuwa ji dadi sosai,
A kusan tare suka je du asibiti Daya ne, ward ne ba Daya ba, su suna dakin dai dai ita kuma tana Mai hada a male ward,
Suna Shiga Umma ta Kira Anty safiya tace'' wanne daki ma kika ce ne?"
Anty safiya tace'' daki na shadaya"
Umma tace'' na goma? Koba na goma ba?"
Anty safiya tace'' shadaya idan kinzo ki tambaya"
Kashe wayar tayi tace'' keni naji goma kika ce,Lamma gomar ce bansani ba ko me, nasani Daya da zero mana, ga kuma Salamatu"
Ummusalma tace'' Umma wanne dakin suke, wai na goma"
" To shikenan Umma Bari ni zanje ganin likita, idan nagama sai nazo"
" To shikenan nanne nasan nan suke zuwa"
Ta fada tana nuna Mata wurin da hannu,
Sannan kowa ya kama gaban sa,
Umma a hankali take tafi har wurin daku nan babu kowa sai wani da ta gani,
tace" bawan Allah ina ne daki na goma"
Nuna mata yayi sannan ya wuce, itama wuce wa tayi tana dogara sandar ta, tana tafiya,har ta iso, tura wa tayi ta bude a fili,
Tace'' mtsww bakowa a dakin sai su bar marar lafiya Shi kadai"
Kara sowa tayi ta Shiga cikin dakin har bakin gadan,gyara glass din idan ta tayi dakyau yaga de Sarai Namiji ne, a kwance,
Tace'' a,a to ko ba nan bane ba"
Fitowa tayi ta Shiga dakin dake opposite,Yana zaune a Kan kujera Amina na zaune a kasa tana cin abinci, ta shigo da sallama, juyowa sukayi suka amsa Mata,
Umma tace'' Kai jama'a wai Yana ke ta mantuwa ne, nifa daki na goma aka ce min,Ashe ba Shi bane na shigo nan ma, da'alama ba Shi bane"
Baffa yace'' Mama inaga kinyi mantuwa ne,nan na tara ne"
Shigo wa tayi tace'' Kai ni nagaji,Bari na zauna, na huta sai na tafi"
Kujera ya tashi ya Mika Mata,ta zauna tana sauke numfashi shikuma ya dauko wata ya zauna, waya ta dauka ta Kira Anty Safiya,
Tace'' ke ni,kinga sai bata nake yi, wanne daki kika ce"
Tace'' daki na shadaya fah"
"Awww ai ke kikayi shirmen Bani ba"
Kashe wa tayi tace'' Ashe daki na shadaya tace, to sannun Ku ya Mai jiki?"
Baffa yace'' da sauki alhamdulilla"
Amina tace'' ina yini"
Umma tace'' ina wuni de ko?" Wani ina yini? "
Murmushi tayi kawai bata ce komai ba, Umma tace'' Bari na tafi,
Baffa yace'' da kin Bari ta raka ki kawai Naga ta Gama ma ai"
Tashi tayi tace'' Bari na raka ki Kawai mama"
Sannan suka tashi suna tafiya har taje dakin tace'' gashi nan, Allah ya sauwake"
Da ameen Umma ta amsa ta Shiga ciki,ita kuma ta juya ta koma, tazo Shiga dakin su, tace'' su wannan basa rufe daki ne? Kome?
Wayar tace tayi Kara shiyasa bata rufe ba,sai kawai ta koma ta fita ma daga ward din gaba Daya, tana daga wayar,
Tace'' ya aiki barrister?
Yace'' alhamdulilla,Naga missed called din ki ban kusa ne da wayar"
Tace'' ehh kamar Kai nagani a asibiti jiya ko?"
" Zaki iya gani na,Dan ankwan tar da kanin Mata ta, shine kuma na samu shigowa"
"Ayyyaahhhh Nima an kwantar da mama na,ciwon ta ya tashi,muna asibitin ma"
"Subhanallah Insha Allah Zan zo shigo zuwa dare"
" To nagode sosai"
Sannan sukayi sallama,
Ko mawa tayi dakin zata Shiga taga an rufe Shi,
tace'' gwara de suke rufewa,Amma daki kullum a bude?"
Ummusalma kuwa ta jima sosai a wurin likita dan harda scanning aka Mata, tazo fita sukayi kicibus da Baba shima zai shigo abin hannun ta suka zube, dagowa tayi ta kalle Shi, tace'' yi hakuri"
Sannan ta Duka ta dauka kayan ta,ta wuce, sai da ta wuce sannan kuma ya bi bayan ta Amma be ganta ba,haak ya dawo jiki a sabule Yama fasa shiga office din ya koma, ita kuwa tana fito wa ta hango wacce suka hadu a wurin Mai lemu tana kuka a zaune a Rana,Kan Dan dakali, shiyasa tayi saurin zuwa inda take,
Tace'' baiwar Allah lafiya?"
Dagowa tayi ta kalle ta,ganin ita ce yasa ta goge hawayen ta,
tace'' nagode sosai da taimakon da kika min,ban samu na maki ba"
Tace'' tashi mu koma inuwa,
Tashi tayi suka koma inuwa sannan suka zauna,
tace'' Meyasa kike kuka?''
" Baba na aka kwantar, kuma Banda kudin da zan sai masa magani, gashi za'ayi masa aiki ga ciwon kafa, bamu da kudi"
" Yan uwan ku fah"
" Suna kauye ban fada masu ba Kar hankali su ya tashi,ko na fada ma sai dai su saida gonar shi ko tasu,yayan Baba na kuma Yana Abuja Kona Kira Shi ba zuwa zaiyi ba"
"Abuja?" Ta maimaita aka san zuciyar ta, tace'' kiyi hakuri muje na biya bill din ayi masa komai"
" Baki sanni faba, zaki taimaka min"
" Kema ai Baki sanni ba,Nima wata ran za iya neman abinda kike nema,no condition is permanent"
Hawaye ne ya zubo mata sosai a fuskar ta, Dan tsabar dadi ma rungume ta,tayi sosai a jikin ta,
Tace'' nagode sosai, nagode"
Sakin ta tayi tana goge hawayen ta, Ummusalma tace'' ya sunan ki"
Murmushi tayi tace'' Maryam,Amma zaki iya cemin Mujahida ko muja,amma duk na fisan muja"
Murmushi tayi tace'' sunan manya, sai na kiraki da Mama na"
Murmushin itama tayi tace'' ke kuma fa?"
" Ummusalma, zaki iya cewa salama,Salma"
"Zan ma iya cewa Salamatu Kenan"
Murmushi tayi sosai tace'' a,a Banda Shi Amma sude ki fada"
Dariya muja tayi tace'' sunan Kaka ne fa dake"
"Ai daga Jin yarda kika fada ma nasan haka ne,
Shiru sukayi kafin Ummusalma tace'' kika ce a Abuja yayan baban ki yake kin taba zuwa?
" Da acan nake ma, to matar sa bata da mutunci jaka ta maida ni,nikuwa na dawo daman Abba na lokacin ya fara ciwon kafa"
" Wanne unguwa"
" Garki"
Gingina Kai kawai tayi, tace'' tashi mu tafi"
Tashi suka yi suka tafi taje ta biya komai da komai har kudi aikin ta biya, sannan taje ta gano Shi, daga nan itama tace zata je ta gano Wanda tazo dubawa, sai da ta koma mota ta dauko fruit din da ta siyo sannan suka tafi, gajiya tayi shiyasa suka rage sauri, har suka shigo, a dakin da aka kwantar da Abdullah, tare suka Shiga,
tace'' bakowa a daki...
Maganar tace ta tsaya ganin Wanda ke kwance akai na gadan kara Sawa tayi bakin gadan tana Kara kallan sa, dakyau, ji tayi idan ta yana nema ya kawo ruwa Hijabin ta tasa ta rufe bakin ta dashi tasa dayan hannun ta, tana taba shi sannan ta furta,
" YA..YA"
Sai hawaye kuma, cikin kukan sosai tace'' yaya Ka tashi, yaya muna da bukatar ka a kusa damu yaya Ka tashi Dan Allah"
Sai kuka, a Hankali Dan yatsan sa daya ya motsa, bata lura ba, ta sunkuyo daidai fuskar sa,
tace'' yaya Ka tashi,ko Dan Baka tashi sabida mu ba,yaya Ka tashi Dan Ummu, Ka tashi sabida Ka rayu da ita yaya, yaya...
Hawayen ta dake diga a fuskar sa yasa ya fara motsa da hannun sa dakyau haka idan sa ya fara motsa wa, alamar zai bude, ganin haka da tayi yasa ta tsaya da maganar tana kallan sa, daga bayan ta taji ance,
" Kina san ya farfado shine baki taba zuwa inda yake ba? Shine Baki damu dashi ba?"
Juyowar da zatayi suka yi four eyes da ...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: *????A BAKIN WAWA????*
_Akanji magana_
52
Daki suka koma ita da Binaif suna Shiga sai ga Anty safiya tazo Dan su tafi gaba Daya ganin dakin ya cika da bakin fuska yasa ta gaida kowa suka gaisa,
Daddy yace'' ya kamata a samu aje a tafi haka nan ga Shi ana neman ayi la'asar"
Baba yace''gaskiya Kam, ya kamata a tafi"
Inni da Baffa dakin su suka koma sannan Baffa yaje yaga likita daga nan aka Basu takardar sallama, Baffa ne ya Kira Amina a wayar ta, tazo ta tattare kayan su sannan suka fito, kowa ya fito inda sukayi parking,
Daddy ya kalli Binaif yace'' Ka kaisu gida daga nan sai ku wuce gida Ku kuma"
Hakan akayi suka shiga, Baffa yashiga gaba su kuma a Baya, Su yusuf daman ba tare suka zo ba, kuma Basu San abinda ya faru ba sunma wuce tun da Dade wa, kowa Shiga yayi ya tafi,
Baffa na nuna masa hanya har suka je, unguwar su da bacirawa can ciki ce, har kofar gidan su, suka je, dukan su suka Shiga bayan yayi Parkinson, gida ne Karami na Mai kyau parlour Daya da two bedroom sai kitchen a waje, da 'yar bishaya Mai a tsakar gidan, Shiga sukayi suka zauna, Baffa da Binaif sukuma daki suka Shiga dan Inni ta huta tana bukatar hutu dukda tana cikin farin ciki,
Binaif yace'' Baffa kayi hakuri da duk abinda nayi maka,bamma san da bakin da zan Baka hakuri ba, ina Mai Baka hakuri nasan bai Zama lalle Ka yafe min ba, kuma zaka dauke marar..."
Baffa ne ya katse Shi ta hanyar cewa'' Baka da laifi, tabbas nine Mai laifi, kasan ma dadi naji? Kowanne uba yana so ya aurar da 'yar sa ga mijin da yake so, naji dadi sosai, wannan ya nuna kana son ta,ya nuna zaka iya kare ta, koda kuwa babu mu, daman babu mu din Ka aure ta kuma Ka zauna da ita,bansan me Zan maka ba, Yana suna Ka?"
Binaif yace'' Abdulshakur ko Binaif"
Murmushi Baffa yayi ya taso daga wurin sa, ya zauna a kujeran dake Binaif ya jingina, ya shafi kansa cikin kulawa, yace'' Kai ba siriki bane, kaji ko? Kai yarona ne, baka da banbanci da su, bansan sirikin nan kaji ko?"
Binaif ji yayi wata nutsuwa na Shigar Shi, gashi yarda yake shafa masa Kai,irin rarrashi a hankali ya zame ya kwanta a cinyar Baffa,
Baffa yace'' tell me more about you,and my children, mamanka ta rasu ne"
Yace'' Taya akayi san haka?"
" I can see, kayi rashin Uwa, kana son uwa, Naga wannan acikin idan Ka"
Kwalla ce ta taru da idan sa yace'' Baffa bansan ta ba,bansan sunan ta ba,ban taba ganin ta ba, but she's gone, ta tafi, I don't know ko tafiya tayi, ko kuma mutuwa tayi, but she's gone forever"
Shiru sukayi babu Wanda yayi magana, Saida ya natsu sannan,
yace'' Mas'ud ya fiye tsoka, Mus'ab kuma ya fiye hakuri"
Murmushi Baffa yayi yace'' Mas'ud tun Yana yaro haka yake,ga Dan Karen tsoro, shiyasa kullum suna fada da Ummusalma basa jituwa sam ita tsokana shima tsokana ga San girma me hali Baya fasa wa"
Murmushi Binaif yayi yace'' har yanzu basa jituwa, ga rashin hakuri haka itama"
Jin ana Kiran sallah yasa su tashi Dan gabatar da sallah, a waje sukayi alwala sannan suka tafi.
A daki kuwa Ummusalma a gata ga Inni haka suka kwanta, tana kallan tana tambayar ta wasu abubuwan na rayuwar ta, a haka bacci yayi gaba da Inni ita kuwa kasa baccin tayi dan yunwa take ji, ji take kamar tayi amai Dan tsabar yunwa amma sai taji bakin ta yayi nauyi tace tana Jin yunwa a bata abinci, gashi Amina tana so tayi mata magana bata, bata dama ba bare ta saurare ta, a hankali ta tashi ta fita alwala tayi tayi sallah a parlour ta idar da sallah kenan,
Amina tace'' Salma"
Banza tayi mata, sai ma jingina tayi da kujera ta rufe ido, tana cigaba da tasbihin ta,
Amina tace'' Haba salma maganar ne bazaki min ba?"
Ummusalma tace'' na'am Neena, shikenan?"
" Ya kamata ace at least ki fada min abinda na maki "
"Mtsww"
Tashi tayi ta kwanta Akan kujera, zuciyar ta ta cigaba da tashi, su Baffa ne suka dawo gani su tayi tare su Mus'ab,
Mas'ud Yana shigowa ya zauna a kusa da Ummusalma,
yace'' dalla can tashi, ki koma gidan Ku,kin wani zo kin zauna mana a gida kowa ya tafi gidan su idan ba tsoro ba"
Baffa yace'' ai itama gidan su ne,sai dai Kai Ka tafi gidan Ku"
Binaif da ya zauna a wurin Kan ta,kamshin turaren kawai taji tasan shine, bude Ido tayi, tace masa "yunwa nake ji"
Dayake kallan ta yake yasan me ta fada, haka ma Amina, tashi tayi ta fita, ta daura abinci sannan ta fice,
Mus'ab yace'' Yawwa Baffa fada masa nan gidan mune"
Baffa yace'' Mas'ud bazaka taba girma ba,Naga ranar da Zaka girma Kai kuwa"
Binaif yace'' Ai Baffa ya kusa girma fa, shida zai yi aure nan da wata biyar?
Baffa yace'' ikon Allah, amma naji dadin wannan maganar sosai Mus'ab fa"
Mas'ud sunne kai akayi irin kunyar nan, besan kunyar tasa dariya take bawa mutane ba, abinka da ba'a Saba ba,
Baffa yace'' mus'ab fa"
Mus'ab sosai kai, yayi ya kalli Ummusalma ko zata yi magana,ita kuwa dauke Kan ta tayi, irin ba ruwan ta Kenan, sosai keya yayi,
yace'' inaga tare za'a hada"
Mas'ud yace'' inji uban wa? Baza'a hada biki nada Yara ba, Kai da budurwa ma Baka da ita,da kama iya zancen ?"
Baffa yace'' Mas'ud!"
Ai tuni ya tashi ya nufi kofa har Yana neman bigewa, ya fice,
Girgiza Kai kawai Baffa yayi, mus'ab yace'' to Baffa kadan Ka gani Indai wannan yaran ne"
Amina ce ta shigo tace'' Ya Mas'ud ya na ganka anan, azaune"
Yace'' kedai bari,leka min kika Baffa Yana nan?"
Shiga tayi taga Baya nan, hakan yasa ta juyo ta girgiza masa Kai, taso wa yayi ya shiga ya gan su suna hiran su Banda Ummusalma da idan ta yake a rufe tsab zaka ce bacci take, zuwa yayi ya zauna, Yana wani daure fuska,
Amina ajje coolern da ta shigo dashi tayi a gaban Ummusalma tace'' ki tashi kici, awara na siyo maki"
Bata tanka Mata ba, ta tashi ta sauko kasa, tare da cire Hijabin ta, ta zauna ta baje kafa tasa coolern a tsakani kafar ta, ta fara ci, gawani yaji Mai dadin gaske, data kawo Mata, gashi awaran da zafin fa Tasha kayan Hadi, ta fara ci tana zirawa,
Mas'ud yace'' Lalle ma Neena mu ina namu"
Dago Kai tayi ta kalli Binaif tace'' mi amor zaka ci?"
Murmushi yayi ya girgiza Mata Kai, yace'' kici ki koshi"
" Ke Neena wai ba Kiran ki nake ba"
Daga waje yaji tace'' Ina zuwa"
Mus'ab yace'' Lalle samun wuri, wai ni nayi kauwa"
" Oho de ba kauwar wani bace, twinny Dinna ce, Daman Ku Kala kuke da aljanu"
Ita de cin kayan ta take sai da ci tayi nak, ta cinye tas saura Daya jal, ta rufe Coolern ta Mika masa,
tace'' kaina bawa ba kowa ba"
Karba yayi Yana wani dar waje baki,
yace'' sai na tuna sanda kika bawa Fav..."
Maganar ce ta makale ganin guda Daya jal a ciki, ya dago yace'' wannan ai rashin mutun ci ne meya hakan?"
Batayi magana ba, ta tashi taje ta wanke hannun ta, tazo ta zauna, tayi refilling,kome za'ayi ayi.
????????????????????????
Babu kowa a gidan suna zaune a daki suna tattauna magana iya su uku ne kawai,
Cikin wata irin fusata,
tace'' Wannan zancen banza ne, wanne irin Abu ne hakan? Ace ta gudu, ta balle kofa? Kai bazai faru ba inaaaa"
Tashi tsaye Anty tayi tana zagaye tace'" shekara talatin bata taba guduwa ba sai yanzu? Me take shirya wa kenan?"
Dayar matar tace'' Dana tambaya ance min batayi ne suka shigo unguwar suka dirar wa gidan"
" Barayin su mahaukata ne da zasu Shiga wannan ribabban gidan?"
Shiru sukayi babu abinda suke sai zagaye a dakin, kowa da abinda yake tunanin can,
Anty tace'' nikam nagaji da zaman jiran haushe Alhaji zai mutu na kwashi dukiya nayi ta kaina, ina so fa na ganni cikin daular da tafi wannan, insan naganni ina juyawa ina fanjama cikin manyan mutanen Mata, Amma Shi Naga besan wannan ba, ina dalili kawai mutun yayi ta zaune a gida kamar jakin jahili? Nagaji daman can ba San Shi nake ba"
Matar tace'' Hajiya bamu taba boyewa juna sirrin mu ba, ya kamata ace ki fada min yau dalilin ki na yin haka"
Zama Hajiya tayi tace'' Ban taba tunanin Alhaji zai so wata Mata ba Sama Dani, sai gashi yaso wannan 'yar fulanin, be fada min ba, amma ni nagane hakan, Yana San ta fiye da tunanin ki, tun daga nan na fara azabtar ta, sai na samu Allah ya zuba mata zurfin cikin mala'i tayi ciki har sau Uku ina barar Shi, wani zuwa da Zuwaira tayi Anty Kenan, kawai ta Bani shawarar na barta ta haihu da kanta zafa gudu tabar min gidan, daga nan sai kika bada shawarar a kashe dan kawai tunda shine zai Bani ciwon kai, sai kuma Zuwaira ta bada shawarar da wata shawarar sanini zata amfani yasa na bi Tata shawarar shine kuma data gudu aka kama ta aka Kai ta wannan ribabban gidan aka sa ta, kinji yarda akayi shine kike zuwa duk wata kike kai mata dan abinci naso ace wahala ta kashe ta da yunwa amma har yanzu bata mutu ba"
" Kuma bakwa tunanin wani yasan wannan zancen naku?"
" Sam Bama yi, tunda babu Wanda yasani sai ke"
Anty tace'' lokaci yayi da zamu kama gaba mu, tun kafin ma asirin mu ya tuno tunda ta gudu waya San inda zata tafi"
Hajiya tace'' shiyasa yanzu Nima nake so dukiyar sa"
" Idan kuka jira sai ya mutu to har asirin Ku zai tuno Amma Idan kuka kashe Shi fah"
Anty tace'' tabbas haka ne kisa ce ta kama ce Shi"
" Idan ya mutu kuma dansa bashi ba gadan sa, haka uwar sa ma"
Zama Anty tayi ta kalli Hajiya a tare suka furta" A kashe Shi kawai..."
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: *????A BAKIN WAWA????*
_Akanji magana_
52
Baffa da ya fito daga dakin dake kallan nasu, ya rufe ganin dakin dake kallan su yasa ya kalle Shi,ita kuma lokacin ta juyo, yasa Kai zai wuce bata San sanda ta ture Baba ba, ya bi bayan sa, da gudu, Yana tafiya a hankali kana ganin fuskar sa zaka san Yana cikin damuwa ba kadan ba, yana tafiya kawai yaji an rungume Shi ta baya irin sosai din nan, ba damar cigaba da tafiya, tsaya wa yayi cak, be juyo ba,itama bata juyo ba, kawai kuka take,kuma ta Rasa takamai mai kukan da take yi, na farin ciki ne ko na aka sin haka.
Shine ya juyo sannan ya dago da fuskar ta, kallan Shi da tayi da fuskar ta da ta riga ta jike da hawaye,
yace'' Wacece ke?"
Cak komai nata ya tsaya, tadena motsi ta dena numfashi, ji tayi ma tana nema faduwa wata hajijiya taji fara debar ta, a hankali kan ta ya fara juyawa, ta rike Kan, zata fadi saura kiris taje kasa, taji an taro ta, ya hada ta da kirjin shi kamshin turaren da taji ne yasa ta rike rigar gam, ta rumtse idan ta, daukan ta yayi ya Shiga daki da Nafisa take,
Suna zaune suka ga an shigo da ita,
Umma tace'' subhanallah meya faru?''
Kwantar da ita yayi kawai a gadan da Nafisa take ganin ba kowa, sannan yaje ya Kira likita,ya kuma ficewa,
Be zarce ki ina ba, sai wurin Baffa da har yanzu Yana nan a tsaye be tafi ba, Yana zuwa, cikin dan muryan bacin Rai dukda Yana so ya danne amma sai da ya nuna,
yace'' Ka kyauta? Ka kyau ta da duk abinda kayi,k kyau ta hakan shine dai-dai uba yayi wa 'yar sa, Kana so Ka Kara Mata damuwa cikin wacce ta Shiga ne?Ko kuma so kake tayi asara abinda ke jikin ta? Kabar ta da damuwar da take ciki ta rashin ku, meyasa zaka Kara mata wata damuwar kuma?" Baffa..."
'' kai waye?
Meye hadin Ka dashi da Zaka zo kana daga masa murya, a haife ya haife ka, idan laifi ya maka why not Ka fada masa cikin mutunci da girmama wa?"
Amina ce ta taji neman Baffa dan zata je gida ta dawo, kuma Inni tana bacci Kar a tafi ba kowa, ganin abinda yake faruwa yasa tayi magana.
Yace'' ohh! Kina san meye hadina dashi?
Zoben hannun sa ya daga ya nuna Mata,cikin muryan da tafu ta waccan,
yace'' wannan ne, wannan ne hadi na dashi,idan kin san wannan ba? To shine hadi na dashi, yanzu kin sani? Ko zaki ce kin manta ni ne? Ko da yake ba laifin ki bane, laifi nane dana zo nake magana dashi, bacin yasan komai"
Dafe kanshi yayi, yace'' ohh! Ashe fa ita bata da iyaye sun mutu a gobora, ba ita kadai ba, su Duka ukun har ita ta hudu Basu da kowa, haka suka taso, kuma zasu cigaba da Zama a haka har lokacin mutuwar su, sukuma haka taso kaddarar take"
Murmushin takaici yayi, yace'' hmmm! Da'ace nine su,bazan Kara cewa ina da Iyaye bare har inajin murnan nagansu suke min tambayar waye ni?, Hmmm wonders should never cease end!"
Ya share zufar data keto masa ya juya ya koma,Baba da ya fito ya biyo ta idan sa komai ya faru, har daukan ta da yayi ya kaita daki da abinda ya fadawa Baffa, a hankali ya taka ya karasa wurin Baffa ya Mika masa hannu,
Baffa da Amina wani irin tension suka Shiga Wanda bazai musul tu ba, musamman Baffa, tambayar Shi anan guda biyu ce, 'ya'yan sa hudu suna nan, sannan kuma aure tayi?
Amina kasa jure tsayuwa tayi ta koma ciji da gudu tana kuka,
Baffa be dawo hankalin sa ba sai da Baba ya Mika masa hannu,
yace'' Abdullah Abdulshakur, mahaifin Dan Ka, Wanda yake wuri na"
Kallan sa baffa yayi be Mika masa hannun ba, cikin wani tsanani mamaki,
yace'' 'Dana?
Zama yayi a kujerun wurin yace'' eh, amma sai Ka Bani damar yin bayani tukun"
Zama shima baffan yayi, sannan yace'' taya hakan ta faru?"
Daga Baba ya bashi labarin komai,har zuwan Ummusalma Adamawa da tayi komai ya fada masa"
Shiru baffa yayi Yama kasa tantance me yake ji, kuka zaiyi ko Mai, babu abinda yake cewa sai alhamdulilla, suna nan zaune lokacin sallah ya wuce sannan suka tashi yaje yayi sallah yajima Yana godiya ga Allah, sannan suka taho direct dakin Abdullah suka Shiga Yana kwance har hanzu Yana so ya motsa ya kasa, sai dai Yana daga hannun sa, haka ma idan sa Yana ta motsi,
A haka ya gan Shi, sai anan hawaye ya zubo a idan sa, ya sauka akan fuskar Abdallah yasa hannu ya shafi fuskar sa,
yace'' 'Dana, Kaine Umar d'ana, kaine Kaine?"
Wani saban hawayenne ya zubo masa, Yana cigaba da shafa fuskar sa, a sukwane ya fice ya Shiga dakin su ya tarar da Innina zaune da alama Amina ta bata labarin abinda ta gani, zata yi magana ya rufe Mata bakin ta, drip din hannun ta ya cire sannan ya kama hannun ta suka fito dakin ya shiga da ita har gaban gadan Abdallah, beyi magana ba Amma abinda ta gani ya bata amsar komai ba, ita koma ma yarda yake nufi ba, zata dauke Shi a matsayin d'an ta,
Kallan Baffa tayi sannan ta kalli Abdallah, da yake motsi da Ido, ta kalli hannun shi, kasa furta kalma Daya tayi kawai ta rungume Shi ta fashe da wani irin kuka mai cike da radadi, a hankali Abdullah ya fara bude idan sa Yana sauke wa akan matar da ya gani rungume Shi,tana kuka bega fuskar ta ba, amma nutsuwar daya samu baza fadu ba,
Baffa ne ya dago ta ya rungume ta, tana cigaba da kuka sosai, binsu da Ido kawai Abdullah yake ganin mutane guda biyu a kansa har Baba na uku, Akan Baba ya tsaida idan sa, hakan yasa ya tako yazo wurin Shi, ya rike hannun sa gam,
yace'' baba na wannan da kake gani sune Iyayen Ka, na tabbatar da hakan, idan kana so akara tabbatar wa sai maku DNA test, kaji ko Baba na?"
Lumshe Ido yayi ya Bude, a hankali bakin sa ya shiga fadin, Ummusalma, Ummusalma, Kara kunnan sa
Baba yace'' ummu?"
Girgiza masa Kai yayi, ya kuma cewa Ummusalma,
Baba yace'' kauwar Ka?"
Daga Kai yayi alamar eh,
Numfashi Baba yaja yace'' ta tafi gida Amma zata dawo zuwa anjima kaji?"
Lumshe Ido yayi ya kuma budewa Yana kallan su Baffa dake kallan sa, daga nan Baba yace zai Kira likita ya kamata su fita, suna fita suka ga, Amina
Inni tace'' ina San ganin Walida ta,( sunan da Inni kece mata) ina san na ganta"
Baffa yace'' bansan dakin da take ba, amma nasan ana wurin take"
Amina tace'' to mu Shiga daki daki muna dubawa"
Haka suka yi suka fara Shiga Daya bayan Daya suna duba wa Baffa na rike da Inni,
" Wai ita wannan aljanar meya same ta?"
Mus'ab yace'' ba tare muka shigo da Shi ba bare ka mana wannan tambayar"
Anty safiya tace'' ai Mas'ud ya iya tambayan renin hankali, tun dazu yake wannan tambayar muna bashi amsa yaki hakura, yanzu Ka tashi kaje wurin doctor Shi yasan me yake damun ta"
Zubura Baki yayi yace'' daman nasan ba Sona ake ba"
Kallan Binaif yayi da ya zauna Yana ya rike hannun ta Yana kallan Shi, Nafisa kuma tana zaune a gefen ta,taji sauki sosai daman ciwon ciki ne kamar baza tayi ba, sai da tasha allurai da drip tukunna Allah yayi, taji sauki ba laifi.
Anty safiya da Umma kuma suna zaune a Kan tabar ma,sukuma su Mas'ud suna Ka Kujera,
Yace'' bb wai me yasa meta ne"
Ko kallan Shi beyi ba, bare yasa ran amsa, ganin haka yasa Shi yaja bakin sa yayi shiru be kara magana ba,
Umma tace'' Kai jama'a a tashi a kaini gida,nagaji da zama anan nazo ganin marar lafiya Ashe ta warke sai na bige da zaman wacce ta kawo ni, a tashi a maida ni gida"
Anty safiya tace'' to Umma tashi mu tafi na ajje ki a gidan Binaif din, sai na wuce gida,sunce zasu dawo kinga sai na sanar da su muma ana jimawa zamu dawo"
Tashi Umma tayi tace'' Haba mutum de yayi ta Zama,zaman jinyar ma da bansan da ita ba"
Gaba tayi tana dogara sandar ta,
Mas'ud yace'' Umma ga mukullin, mu muna nan sai aljana ta farka"
Anty safiya ce ta ansa tare da kwada masa, tace'' Ka manta ba aljana ba, bulokiya ce"
Tafiya tayi zata tafi Nafisa tace'' Momy Nima tafiya zanyi gaskiya, tunda na warke ina San zuwa islamiyya ma kuma"
Bata Hanata ta dauko Hijabin ta suka tafi, ya rage sai su,
Mas'ud yace'' yawwa daman kunyan Anty safiya nakeji Bari na Kira budurwa ta muyi waya da ita"
Mus'ab yace'' mu ai Baka Jin kunyar mu,Amma kana Jin ta bb Ka tuna dazu da kace..."
Da gudu yazo ya rufe masa Baki yace'' kaifa ba'a sirru da Kai,meye na fada kuma? Karka fada Dan Allah kaji my Twinny"
Cire hannun sa yayi yace'' dalla sake ni, Kuma wallahi Ka Bini a hankali tam"
" Eh naji yi hakuri, Yaya Mus'ab"
Tashi yayi ya koma kan gadan take yace'' idan Ka biyo ni Kuma anan zan fada,daman kaga ogan basu da lafiya kaga idan Ka tabo shi, shikenan komai zeeeeerrrro"
Yana so yayi magana Amma yasan Mus'ab tsab zai fada,hakan yasa ya koma ya zauna ya sunkuyar da kansa looking so innocent,
Mus'ab yace'' bb me yasa meta"
Shiru yayi ba amsa har fitar da ran za'a amsa masa don Mas'ud shima matso da kujerar sa yayi kusa da su, zaiyi magana, yaji Binaif yace cikin low voice,
yace'' she saw your Dad"
Kallan juna suka yi, Sannan,
mus'ab yace'' to meyasa bata masa magana ba"
Kallan shi yayi da idan sa da yayi ja dan tsabar takaici, sannan ya dauke kansa ya maida Shi kanta Yana kallan ta, cikin bacin Rai,
yace'' ba magana ta masa, she was happy taga Baban ta, but he's not happy to her, he's"
Shiru yayi Yana Kara tunano abinda ya faru, yace'' he was asking Wacece ita, bayan dukkan alamu sun Nuna yasan ta,Amma wai yake tambayar Wacece ita?
Hmmm abin da ya bata mamaki Kenan da firgice shine ta shiga wannan condition din"
Mas'ud yace'' to me yasa zaiyi haka?, Besan ta ba, I think zai yi farin cikin hakan"
Mus'ab yace'' Kode besan ta ba"
Tsawa Binaif ya daka yace'' kuma shaukin da na gani acikin idan sa nace me? Besan ta ba kome"
Zaiyi magana yaga ta fara bude Ido a hankali da'alama kuma maganar Shi ta tashe ta, a kansa ta bude idan ta fes, Kara rike hannun sa tayi dakr cikin nashi,
tace'' dagaske be sanni ba?"
Rasa ma abinda zai fada yayi,
Mas'ud yace'' kinga ya sanki,zai zo ma idan anjima zai zo kinji ko,ki kwantar da hankalin ki eh?"
Mus'ab yace'' baza su zo ba"
Ji sukayi an turo kofa an shigo, gaba Dayan su Ido suka zuba wa kofar Banda Binaif da yake kallan ta, Yana kissima abubu a Kan ta, yasa a yanzu babu abinda take so irin iyayen ta, amma su kuma bata ita sukeyi ba, maganar Inni ce ta katse masa tunanin sa,
Tace'' Wali..da"
Ita Inni Bama taga su Mus'ab ba,kawai idan ta Akan Ummusalma ya sauka, sai da taji,
mus'ab yace'' Ina kunce Baku San ta ba? Me kuka zo yi Mata"
Ummusalma kallan matar da ta Kira ta walida tayi,ita daba walida ba?
Baffa yace'' munzo ganin 'yar mune"
Binaif yace'' kunzo ganin ta ko kunzo Kara sata?"
Amina tace'' ya kama ta kasan da wa kake magana"
Mus'ab yace'' hmmm sanin dawa yake magana nanne yasa Shi ya bashi amsa, shakarar nawa tayi tana neman sa? Sai Rana tsaka ta ganshi kuma yasa ita ce sannan yake tambayar Wacece ita?
To Bari na fada masa ita din Wacece a yanzu, bakowa bace sai 'yar Adam Dan Lami, Matar Abdulshakur Adam, Shikenan haka yayi ko kuna San karin bayani?"
Inni a hankali ta tako har wurin sa, ta shafi fuskar sa tace'' Mus'ab?"
Ta kalli Mas'ud tace'' Mas'ud"
Kawai ta hada su ta rungume, tace'' na kasa, na kasa,jure rashin Ku, Ku gafar ce mu, Ku yafe mana abi sa abinda muka aikata Ku yafe mana"
Tana fada tana kuka, sai yanzu Binaif ya dago da kansa ya kalleta, ganin irin hawayen dake zuba a fuskar ta, yasa Shi tuno da tashi mahaifiyar, babu abinda yazo masa Rai Sai ko tana,
"Sona?"
Besan afiki ya fada ba, kuma Ummusalma taji Shi,batayi magana ba, sai Kara damke hannun ta datayi acikin nasa, sukuwa kasa hakurin Jin kukan ta sukayi hakan yasa suka rungume ta gam gam,suma suka saki kukan, Baffa ne ya tako barin Ummusalma ya sunkuya ya kamo hannun ta,
yace'' kiyi hakuri 'yata,am sorry,am so sorry,am sorry, am so sorry...
Haka kawai yake fada, kallan Shi tayi ta kalli Binaif ya daga Mata Kai, sannan yasake Mata hannun ya tashi ta fita, itama Amina fita tayi ta Basu wuri.
Sai da suka Gama komai,komai ya lafa, sannan Inni ta tambayi labarin su, Mas'ud tsab ya kwashe ya fada Mata komai, har haduwar su da ita, zuwa auren su ta da Binaif, sosai abin ya bawa Baffa da Inni mamaki, yaran su da suka bata lokaci daban daban sai gashi yau Allah ya hada su a Rana Daya kusan lokacin Daya, ikon Allah yafi karfin wasa,
Suna cikin wannan haka sai ga Daddy ya zo shida su Baba da Umma da su Anty da mijin ta, sun shigo sosai Daddy yafi kowa nuna farin cikin Shi, sai da aka nutsu Ummusalma ta juya taga Baya nan, Mas'ud Daya dawo kusa da ita Akan gado ta zungure Shi da kafar ta, kallan ta yayi irin meye?
Da Ido ta masa alama yana ina?
Yace'' me kika ce?"
Tsaki taja ta tabo mus'ab ta masa alamar Yana ina?
Mus'ab tuni ya gane,
yace'' ya fita, ina gani shine ma ya Kira Daddy"
Tace'' to Kira min Shi, yunwa nake ji"
Tashi yayi ya fita, yana fita ya ganshi shida Amina a zaune suna hira, da'alama kuma ita keyin Rabin maganar, tafiya yayi zaije wuri Shi yaga Mas'ud yazo ya wuce Shi da gudu ya isa, Yana zuwa,
yace'' bb matar ka yunwa take ji fah, kuma naji ma Daddy yace kazo Ka dauke ta Ka maida ta gida Shi zai tafi da su Inni gida tare da mu"
Mus'ab ya karaso yace'' sai kace Kai aka aika"
Girgiza kai ya tashi ya tafi, Amina tace'' ba magana ko?"
Sai nan suka lura da ita, Mas'ud yace'' kut, twinny wallahi na canza wannan ce twinny na,Kai daman kafi kama da aljana"
Taske keyarsa yayi yace'' with respect har yanzu baka samu matar Ka ba"
Zama Mas'ud yayi yace'' Allah ya bawa yaya Mus'ab hakuri"
Tafiya yayi ya barshi a wurin, ya Shiga ciki,
A kusan tare suka Shiga shida Binaif, kansa a sunkuye ya Shiga babu Wanda ya lura dashi sai Baffa, wurin ta yaje ya zaune,
yace'' me zaki ci"
Tace'' kaje dakin da aka kwantar da uncle dakin na goma na ajje fruit Ka dauko min..."
Sai kuka tayi shiru, tuna wani Abu da tayi, kallan drip dinta tayi taga ya saura kadan,
tace'' cire min"
Beyi musu ba, ya cire Mata, ta tashi zaune ta kalli mus'ab tace'' a Abuja wanne unguwa Ka zauna"
Yace'' gidan Daddy dake garki"
Murmushi tayi Mai kyau sannan tace" bb muje dakin yaya"
Kama ta yayi suka tashi, sannan suka fita, dakin suka je, Anna suka ga su ummu suna zaune Shi Baya nan, Zama tayi ummu ta kawo Mata Tasha ta dayawa sai da taji garau, tayi sallah sannan,
tace'' Ina mus'ab? "
Yusuf yace'' bezo ba, iya bb ne kuma shima ya tafi,kina sallah"
Tashi tayi ta hango su, su hudu har Binaif Shi Yana tsaye Yana waya sukuma a zaune Amina da Mas'ud sai zuba ake shikuma Mus'ab Yana binsu da Ido, wuce tayi Basu lura da ita ba, ta wuce male ward har wurin gadan su Muja,
Muja na ganin ta, ta taso ta tarbe ta, suka karasa, sai da ta zauna,
tace'' kuma Baki tsaya ba"
Muja tace'' Ina Zan tsaya kuwa"
Murmushi kawai Tama ta tace'' to shikenan,daman nazo duba ki ne, numbern ki fah"
Muja tace'' Banda waya sai dai numbern Abba na"
" Kash,kinga ban taho da waya ta ba"
" To muje mana, sai na sa maki,wayar Abban ma ma charge bare nace ki saka min Zan Kira ki"
Hakan ya mata dadi, fita suka yi daman ya samu yayi bacci, har suka zo wurin zasu wuce Basu lura da ita ba, a saitin wurin ta tsaya,
tace'' Glip Dan ban Aran wayar Ka"
Dayake amfani yake da ita ya kawai ya miko Mata ta, juyar da Kan da zaiyi kusa sukayi four eyes da Muja, Dan murmushi tayi
tace'' Ina wuni?"
Mas'ud yace'' lafiya qalau"
Shidai be amsa ba,Amma Yana kallan ta, ita kuwa,
tace'' kamar na Sanka,Amma na manta a'ina? "
Janye idan sa yayi, beyi Mata magana Dan besan me zai ce ba,
Ummusalma tace'' zaki iya sanin sa, Dan ya zauna a unguwar ku, a Abuja, haka yake magana bata dame Shi"
Murmushi tayi tace'' Kannan kine?"
Mas'ud ta kalla yarda ya wani wurgo mata harara a fakai ce, tasan da namiji ne yayi maganar sai ya maida masa da martani Amma sanin macece yasa yayi shiru sai boyayyiyar harara, murmushi tayi tace'' a'a yayu na ne, wannan ce kawai kauwata"
Ya fada tana nuna Amina,
Muja tace'' Allah sarki, sannu"
Amina tace'' ina wuni,yi hakuri bamu gaisa ba"
"Bakomai"
Mika Mata tayi wayar tace'' Samin"
Amsa tayi tasa mata sannan tayi musu sallama ta wuce...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: *????A BAKIN WAWA ????*
_Akanji magana_
55
Shiru yayi tunawa da wani abu da yayi mafu soyuwa a zuciyar Shi, kafin ya lumshe Ido ya bude.
Hajiya kuwa da Anty Rasa abin fada suka yi ji kawai suji ya gama abinda zai fada su fadi nasu.
Yace ''Hafsat, Zuwaira nasan duk wani kallu kullan Ku, a yanzu ni tsoro kuke Bani, sabida haka ga wannan kowa yaje yayi business din sa da yake so kowa ya kama gaban sa".
Ya fada Yana Mika masu wata envelope mai kyau da ita, har zuciyar su suka ji wannan Batu jiki na rawa Hajiya ta amsa ta dauki nata ta bawa Anty.
Anty harda durkusa wa ta fara godiya itama Hajiya haka.
Hajiya tace ''Alhaji mun gode sosai Allah ya Kara budu".
Anty tace "Allah yasa kaci wannan takarar deputy governor din da kake nema".
Dariya suke bashi sosai, dukda Baya san yayi amma sai da yayi murmushi ya.
Yace ''Idan zaku tafi, ku tafi Ku kadai kubar min yara na".
Hajiya tace ''Haba Alhaji Muda zamu tafi business wasu kasashen saro Kaya taya zamu tafi da yara kuma?"
Anty tace ''su mana me? Su ba Yara ba ba komai ba?"
Murmushi kawai yayi ya Basu wurin ya tashi ya fita yana Dariyan shi shika dai.
Anty tace ''kinga Bari naje yanzu yanzu na duba Naga wanne jirgi ne zai tashi da kudin wuri na nayi booking".
Hajiya tace "tuni ma da me zamu kira kuma tashi zamuyi ai da kudin mu zamu saro kayan ma wannan kuma sai mu ajje sai mun dawo".
Anty tace ''china zani nikam".
"Ahh ni Dubai zani".
Fitowa sukayi kowa ya Shiga daki yayi booking flight Hajiya ita da yamma ta samu,ita kuma Anty sai gobe shima sai taje Abuja. Dayake Hajiya sai sunje Abuja sai kawai Anty tace zata bita.
✨✨✨✨✨✨✨
Suna zaune su Duka a gidan Umma, bayan sun dawo daga daurin auren Ummu,
Ummusalma tace ''yanzu Umma ai da kin koma mun tafi tare".
Umma tace ''ke rabani da gidan da babu rahama babu iska ko kadan, babu wurin shakar numfashi window an kama an garke, labule an sake Shi daki ba Hasken Rana sai na lantar ki, bazan iya ba ga gida na kana waiga wa zaka ji iska, ka fita waje Ka bishoyo nan, idan naci gaba da Zama a can gawa ta kawai za'a dauko".
Mas'ud yace ''hmmm Umma Kenan ai kinga gidan nan takaici ne a cikin Shi fal, damma ba'ayi haki ba kinan nida da nake da Asthma kullum sai ta tashi".
Binaif yace ''kun dame ni fa".
"A tashi a tafi daman banne mi mutum ba sai da aka ga na gyara gidan nawa sannan za'a ce wani abu".
"Matata ta gyara de".
"Muna Mata de, ai wannan ba matar arziki bace".
"Matar tsiya ce Kenan ko?''
"Oho de, ace har yanzu ba amo ba labarin samun ciki yanzu da a watan da akayi aure a watan ake samun ciki amma banda ita ko nace banda ku ehh nannan wata wacce akayi auren Ku tare a kauye ciki ne da ita wata hudu zuwa biyar har ya dan tasa abin ta abin sha'awa da ita baku ganta ba wallahi".
Mas'ud yayi karaf yace ''zaki sha mamaki Hajjaju idan nayi aure, ke dai bari sai 'ya'ya sun yi wayo sun girma da wayon sa tukun zasu haifi na fari ai idan nayi aure za'a..."
A tare Mus'ab da Binaif suka jefe Shi Mus'ab da pillow Binaif da remote.
Mus'ab yace ''wai sai yaushe kunya zata ishe Ka ne? Ayi yaro bashi da kunya Sam, Kai da ko nema auren har yanzu ba'aje ba kayi ta cika Baki".
Umma tace "ohh! Dan ya Fadi gaskiya? Shine abu? Gaskiya ya fada ai idan bata yi ciki yanzu ba sai yaushe zata yi? Ku nan zaune kuna kunbiya-kunbiya zai haihu ya barku".
Ummusalma tace "kasan de sarai wani ya raga Ka idan ka manta na tuna fatan Ka Allah yasa a Baka kake wani cika baki".
Kalar tausayi yayi ya zame ya kwanta.
Mus'ab yace ''dayafi de".
Umma tace ''kwaji dashi Insha Allahu babu Wanda ya riga shi 'yan bakin ciki".
Binaif yace''Kunga ku tashi mu tafi ba zai iyuba kawai ayi ta zagina da mutunci na da komai".
"Kufi ruwa gudu kuma koda wasa kar a zo min gida".
Tashi yayi ya fita, ita Ummusalma sallama tayi Mata,
tace ''Umma sai anjima".
"Mu jima da yawa har auren 'yan albarka".
Itade tafiya tayi, shima mus'ab tashi yayi ya Mata sallama haka ma Mas'ud suka tafi suna tafiya Mai aikin ta na zuwa Allahn da ya te make ta taya ta hira.
A hanya suna tafiya, Ummusalma tace ''bama je gai she da Daddy ba?"
Mas'ud yace "Bana San zuwa gidan nan nikam".
"Sabida akwai dodannika ba?"
"Dalla can yimin shiru, nasa dake? Bansa da mutum ba ya dena samin Baki a zance na Bana ciki da renin wayo".
"Hmmm haka de za'ayi auren kenan,? thanks God nawa jarumi ne".
"Oho de ke kika sani".
Mus'ab ne ya matso kusa dashi cikin rada.
yace, ''magana fa ta fada maka".
Shima cikin radar yace, ''me tace?"
"Tana nufin wai idan akayi auran babu abinda zaka iya Kenan idan ana yiwa matar Ka wani abu kaga ita nata jarumi ne, tana nufin Kai rago ne ai".
Da karfi Yace, "Kan bala'i wato Dan munafinci yanzu zancen ya koma cikin nadi Kenan bakomai Zan Rama".
Binaif yace, ''mun san wannan word din sai a canza wata as usual sai dai Ka rame".
Turo Baki yayi ya fara gunguni Shi kadai, Yana Mita, har suka je gidan Daddy a bakin gate suka yi parking sannan suka shiga, cikin gidan.
Suna zaune su Duka hudun kowa da waya a hannun sa Banda Fati wacce take karatu da sallama suka Shiga ko daga Kai Basu yi sun kalle su ba bare su amsa sallamar, saida suka Samu wuri kowa ya zauna.
Binaif yace "Baku ji anyi sallama ba ? Ko kuma iya amsawa ne baku iya ba?"
Sai da ya fada sannan suka dago suka kalli su ganin su tare da Ummusalma wacce take Danna wayar ta bata dago ta kalle su ba suka kalli su Mus'ab da Mas'ud a tare suka ja wani wawan tsaki, sannan.
Saima tace, "ai munga anzo da karuwa ne shiyasa, taya za'a mu ansa sallamar karuwar da ko sallah batayi ita da arba babu banbanci Dan bazan ce Christans ba sai dai arna arnan ma kafirai cikin su".
Ameera tace, ''abin takaici wai karuwa ce ta dake mu fah ko?"
Aneesa tace, ''ai watan cin uwar su ne ya kama tsautsayi ne ya kawo ta cikin gidan nan shima Binaif din ba tsoran sa ake ji ba 'ya Tama na rashin kunya wallahi mu balla ta a gun nan".
Fati de bata ce komai ba, Dan iskancin ta tana da tsoro shiyasa ma ta tashi sum sum ta bar wurin.
Binaif kuwa jira kawai yake su gama duk Wanda yayi magana idan sa ne yake komawa kan sa har yazo wurin fati ya zaci zata yi magana sai yaga ta fita. So calm ya tashi ya nufi remote ya dauko ya tsaya yana Yana kallo ganin channel din da suke kallo Boom tv ta waka kawai, yasa Shi yayi murmushi ya Kara volume ya karade gidan, remote din TV ya hango a tsakiyar Saima da Ameera a Kan hannun kujera hakan yasa ya nufi wurin Yana zuwa ya Basu aune ba Dan Basu yi tsammani ganin sa ba ya Gwara kan su, Aneesa da tana magana tasa earphone sai wani karkade kai take sai Jin saukar sani lafiyayyan Mari tayi.
Duk abinda ya faru befi a cikin seconds ba, gaba dayan su gigice sukayi sun ma Rasa me zasu yi gudu wa ko kuma a kasin haka, kasa ya jawo su ya rinka ball dasu idan yayi ball dasu sai sun ture kujera a cikin lokaci kankani sun har gutsa parlour dan dansa yayi masifar baci kana gani zaka sa dukan da ya jima yana Tarawa ne be shi ba ya bude fridge ya dauko kankarori ya jawo su saitin goshin su ya rinka fasa wa akai ihu suke amma ba'a ji bare asan me suke yi sai da ya Kai ihun ma basa iyawa bare suyi azamar gudu wa ganin sunyi lakwas yasa Ummusalma kallan Mas'ud dake kusa da ita.
Tace "kaje Ka taimake su mana".
Alama ya Mata na Bana ji da hannu ya cigaba da kallan sa Yana gyada Kai, haushi ne ya ishe ta tama Rasa me zata yi kawai ta dungure masa kyeya ya juya ta kalli mus'ab da yasa earphone a kunnan sa ya kwanta Yana Danna waya, tsaki tayi ta tashi taje wurin Shi, rasa me zatayi ta Hana Shi dukan su tayi Shi kansa ya hada zufa ba kadan ba, samun kanta tayi da rungume Shi ta baya tare da hannun sa ta daura kanta a bayan sa tana sauke numfashi.
Runtse Ido yayi ya tsaya da dukan nasu Yana nishi, sai da ya dan saitu sannan ya juyo da ita ya rungume ta sosai kamar zai balla ta, ita rungume Shi din tayi sosai kamar yarda ya Mata, kansa ya kwantar a kafadar ta Yana Jin kamshin turaren ta Wanda a kullum yake Kara sa shi nutsuwa. Sai da ya daidaita sannan nemi remote yaja ta kujera suka zauna, rage volume din yayi sosai sannan ya canza channel, ya kalle su yarda suke wani tankwashe wa tsabar radadin da azaba kukan ma ya dena zubowa.
Yace, ''inaga biyo Ku zanyi na janyo Ku".
Bashiri suka nemi tashi sai dai ko rabin daga wa ma Basu yi ba, haka ma rarrafe kin yi yayi, sai da tafiyar miciji suja isa wurin shi. Dauke yayi Yana kallan Ummusalma ya nuna musu ita.
yace ''kunga wannan, Mata ce".
Dagowa yayi ya kalle su yace ''kinsan abind yasa na deke Ku?''
Girgiza Kai sukayi alamar a'a.
"I think dukan be isheku ba kuna nema Kari".
Dasauri suka ce "a,a bamu Santa ba".
"Daga yau Anty,daga yau me?"
"Anty". Suka fada a tare murya can kasa.
"Oohh daga murya zanke yi Kenan ko?"
"A'a".
"Daga yau babu reni a tsakanin Ku da ita babu a tsakanin Ku da Mas'ud Mus'ab babu wannan respect nake so na fara gani kunji ko baku ji ba".
"Munji". Wannan Karan da karfi suka fada.
Daddy yana waje daga Baya Yana Jin disco na tashi yazo Dan musu magana ganin irin dukan da Binaif yake musu yasa Shi ya koma da baya sai yaji kidan ya Ragu sannan ya nufo cikin gidan, a gaban Binaif ya gansu ga parlour an har gutsa sai ya samu kujera ya zauna.
yace, ''Ku kuma duk rawar ce haka kome kunzo kunyi zube a kasa sai kace Wanda aka dake ku gashi kun bata mana parlour lafiya?"
Saima da ta Dan tashi tace, " bakomai Daddy laifi mukayi aka hukun ta mu".
Yace, "Ku tashi Ku gyara parlour nan".
Babu zan cen musu suka tashi suka fara gyara wa dakyar suke aikin Dan sun jigata ba karya.
Gaida Daddy suka yi ya amsa musu Yana tsokanar su, sun jima sosai a gidan tare da Daddy sune har aka Kira la'asar sannan suka tafi.
A mota Ummusalma tace, "ina San na zama ta farko da Zan fadawa Yaya auren sa da Ummu".
"Idan kin isa na make ni zan fada".
"Sai Ka fada mugani ai".
"Ni daman an hada harda ke an zabga Dana ji dadi".
Binaif yace, " idan Baka kiyaye ni ranka zai Baci".
Mus'ab yace, "Gwara tun wuri kayi shiru kafin kaima a Baka naka kasan, don Naga bb idan Yana Duka manta a'ina yake".
"Fav idan aka min wannan dukan ba tabbatar bazan tashi ba woo Kai kaga duka? Daman bb haka kake bamu sani ba taaabb".
"Ai ni babu ruwa na yanzu da Shiga harkar bb".
"Nima de kuwa amma bazan ce wannan aljanar Anty ba a haife ta a gaba na nace Mata Anty ita ko Dan yayan nan bata ce min".
Banza tayi dasu ta kyalesu, Hiran suma suke da Binaif har suka isa asibiti suna zuwa.
Mas'ud ya fita haka ita ma suka bar su Mus'ab a Baya...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? *A BAKIN WAWA ????*
_Akanji magana_
When life gives you a hundred reasons to break down and cry,show life that u have a million reasons to smile and laugh.
Stay strong.“`
54
Wani makirin murmushi,Ya jima da sanin hadin da hadin bakin su, ya jima ya zargin su, Shifa ya auri Zuwaira ne dan ya kunta tawa Hajiya, Yana gani ai kawar tace zata ji zafin abun,ashe bakin su a hade yake wai yau Shi za’a kashe, murmushi yayi Mai sauti, yana tuna shawarar Yayan sa, dan wayar da yayi dashi ne yasa yaji komai ya tafi, ga kuma abin farin ciki da ya samu su Mas’ud, bezai bata komai ba,dukda ya tuno masa babban ciwon abun kaunar sa, a hankali ya wani runtse Ido ya bude Yana tuno duk wani moment nasu, yau ya hadu da yayan ta, bema san yarda akayi ya yarda zumunci haka ba,dole gobe yaje ya Kai gaisuwa.
Tashi yayi ya fita yarda babu Wanda yaji shigowar sa haka ya fita babu Wanda yasani sai dai yanzu Shi kadai ne, ya ansa key a wurin driver sannan ya yace yaje gida yau,
Wayar Binaif yake kira, a lokacin Binaif suna zaune suna cin abinci yaga Kiran Daddy, daga can,
Daddy yace ”Binaif Umma tana gidan Ka ko gidan ta ne?”
Binaif yace ”tana gidan na”
Daddy yace ”kai kana ina?”
“Ina gidan Baffa”
“To shikenan”
Kashe wayar yayi ya dauki hanyar gidan Binaif, koda yaje a zaune ya ganta tana cin abinci tana kallo, da’alama kawo mata akayi Dan yaga cooler a gaban ta,
Da sallama ya shiga, ta amsa ta ciga da abinda take yi,
A kasa ya zauna,
yace ”Umma ina wuni”
” Lafiya, ina ce kaman ta hanyar gidan dan naka”
” Umma ya za’ayi na manta kuma”
” Yoo naga tunda nazo ba’azo an gaida ni ba shiyasa ai”
” Umma jiya fa kika zo”
“Ai yanzu naga rana ta fito”
Shiru yayi ganin yau a Sama take, sai da ta Gama cin abincin ta,
tace” Yanzu ma ba zuwan Allah da Annabi bane, kafin ka zo Dan uwan Ka ya sanar min komai da komai, kuma abinda ya yanke yayi daidai kaji ai”
Sunkuyar da Kai yayi bece komai ba sai
yace “amma Umma zaki koma gidan ki ko?”
” Bazan koma ba”
“Umma ya kamata ki koma, namma fa gidan jikane ba gidan danki ba”
” Ohh! Bukulu zaka min, idan Baka sani ba, kasani gidan nan wani abincin suke ci Mai dadi yauma wata Kala Kala aka mana,irin ‘yan can Mai dadi, shayi ma kadai dadi ne dashi bare abincin su, aitun tana can take mana abin dadi”
“Umma kinga be kama ta ace ni Ida zan gaida ke ba,kullum sai nazo Haba Umma Dan Allah kuma kinsan shima yaya Baya zuwa gidan ‘ya’yan sa yanzu idan yazo shima nan zai zo?”
“Da wannan naji zan koma, dan kace baban su amma da Kai ne bazan koma ba”
“Nagode”
“Gode wa Allah”
Be wani jima ba ya tafi suna gama hira ya wuce.