A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ita kuwa tashi tayi ta bar wurin tana masifa bayan ta dauki kudin da ya ajje mata.
Tana Shiga suna zuwa abokan nasa sosai ta tarbe su yasa aka kawo musu abun motsa baki sabida ya tana da saboda su, suna zuwa sai ga su Daddy Suma sunzo ba’a wani yi doguwar magana ba tunda harda Baba sai mijin Anty ummi sun san juna babu wani bukatar bincike Daddy ya nema da asa nanda wata biyar Abba yace hakan yayi dan ita ma zata karasa makarantar ta daga nan aka Shiga ‘yar hira sai daf da magariba kowa ya tafi hakan yayi wa Abba dadi sosai baka dan ba”.
✨✨✨✨✨✨✨
Basu suka bar asibiti ba sai dare anan suka ci abinci sannan suka bar ummu su yaseer suka je suka dauko Mata kayan wayan ta acewan Anty, da zasu tafi ummu kamar tayi kuka.
Tace, “Yaya salama wai ni Daya za’a Bari ne?”
“Ummu kiyi hakuri ki zauna kinji ko?”
Uncle yace, “Binaif wai yaushe za’a sallame ni nifa nariga da na warke”.
Binaif yace, “da saura hannun Ka be karasa warke wa ba”.
“Hakkun Naga alama”.
Murmushi kawai Ummusalma tayi ta fadawa ummu abun a kunne sannan suka tafi. Sai da suka sauke su yusseer sannan suka wuce gida.
Ummusalma tace, “yunwa nake ji muje a siyo min fura, furan dazo yamin dadi sosai”.
Binaif kuwa beyi kwanan gidan su ya Mike ya dau hanya.
Mas’ud yace, “wallahi kede sai addu’a wannan ci naki dame yayi kama eh? Kinga yanzu kin koma kin cin abinci sau goma a rana”.
“Kai chatty Bana San sharri har wani goma a rana”.
“To me nace Dan nace goma, fav ringa kirgawa kaga da safe idan ta tashi sai ta sha cornflakes ta dama custard ta sha fa kuma da yawa cemin daya,
Mus’ab yace, “Daya”.
“Kaji Daya? Tam tazo idan zamu ci breakfast nan ma taci ce biyu”.
“Biyu”.
“Tazo ta idan angama ci fa ana jima wa kadan befi da awa ba sai tace yunwa taje ta dafa indomie taci ba uku ko? Tazo kafin aci na rana ta sha fruit salad, hudu Kenan aci na rana da ita…”
“Chatty Bana San sharri Naga tare da Kai muke sha muci komai kayi dani bari naje nayi alawar madara Naga wani yace zai sha ko aka min sintiri a kitchen”.
“Haba Anty salama kinsan Bama haka kece lil sis na my sweet kauwa love you Lodi lodi irin Daya wanan”.
Mus’ab yace, “baza’a Baka ba din nasan ni za’a bawa kasa Banda magana kamar Kai”.
“Baka da maganar kamar chatty amma kafi chatty tsegumi da kini bibi ai?”
Dariya Binaif da Mas’ud suka sa, mas’ud harda rike ciki Dan mugunta.
Yace, “maganin Ka ai wayace ma ana yiwa wannan aljanar kwanin ta”.
Shiru tayi ta kyalesu ganin yayi parking a wani wuri harda su kaza zai fita tace, “a hado da kaza da ice-cream sai kasiyo furar da yawa daga na a hado da fresh milk itama da yawa chatty kuje Ku taho da kayan”.
Tsak Binaif ya tsaya Jin wannan Batu nata, a hankali ya juyo.
yace, “du waye zai sha yaci wannan din?”
Dan murmushi tayi ta Ka fara wasa da abin hannun ta tana cigaba da murmushi, Kai kawai ya girgiza ya karasa fita, sune suka je suka kwaso kayan da ta bukata babu abinda Mas’ud yake sai mita da jaraba an asha aiki Dan ba iya abinda ta ce kawai ba sun Karo abun da yasan tana sha.
Da safe karfe shida tana parlour tana aikin shan fura tana danna waya gashi furan tayi sanyi dai-dai tana shan abin ta. Ganin Kiran Ummu tayi gaban ta ya fadi ta furta “Lafiya?”
Gaban ta na faduwa ta daga wayar tana daga wa taji shashshekar kuka…
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
????A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
57
Gaban ta taji ya kuma faduwa. tace, “Ummu meke faruwa ne?”
Cikin kuka ummu tace, “yaya kizo yaya wallahi…”
“Kinga Ummu ki fada min meke faruwa lafiya? Wani Abu ya samu uncle din? Kiyi magana”.
Ji tayi yace, “ni lafiya nake, ta damu wai sai kinzo shine ta Kira ki tun dare take son Kiran ki na hanata shine yanzu kuma take kuka”.
Wata kunya taji ta kama ta kawai ta kashe wayar ta dauki furar ta ta Shiga kitchen abinci ta hada irin na marasa lafiya marar nauyi tayi kunun gyada ta shirya komai ta dauko su ta Kai parlour sannan ta Shiga daki.
Yana kwance Yana bacci abin sa, ta wuce taje tayi wanka ta fito babu abinda ta saka kawai dan turare ta fesa kadan ta bude drawern sa ta dauko wata doguwar Riga Mai kyan gaske ta saka tayi rolling damma mayafin nata babba ne,Tazo sai tin kan sa ta zauna a bed side drawer tana kallan Shi sunkuya wa tayi tana kallan sa suna hada numfashi ta fara shafa fuskar Shi.
Tace, “audushakuru, audushakuru tashi”.
Ganin ko motsi beyi ba sai ma Kara gyara kwanciya da yayi ya sauke numfashi. Sai tin kunnan sa take ta kwalla ihu “audushakuruuuuuuuu”.
Da sauri ya tashi zaune ganin ta tana dariya yasa ya diro daga Kan gadan a dari ta ta gudu tana zuwa ta rufe Shi da kofa.
tace, “kayi sauri kayi wanka Yaya beda lafiya yanzu nan ummu ta kirani”.
Wucewa yayi yayi wanka ya shirya tsab ya fito tana zaune tana Shan cornflakes ya fito ya zauna a kusa da ita tare da Jan kunan ta.
Yace, “laifin ki karuwa suke basa raguwa kullum sai kin yi laifi ban Sani ba ko Babyn ki yake Kara saki kike yi laifin”.
“Ouch! Da zafi baby yace da zafi Ka sake ni please”.
“Zaki Kara yi min ihu?”
“A’a bazan Kara ba”.
“Zaki kara yi min laifi?”
“A’a baza ta Kara ba”.
Sakin kunnan yayi.
yace, “idan ta Kara fa?”
Murmushi tayi sosai tace, “idan ta kara? A sa Mata albarka dayawa”.
Girgiza Kai yayi ya kalle ta ita Shi take kallo a tare suka furta”Allah ya shirya ko?”
Murmushi tayi shikuma ya dan Harare ta.
yace, “meye aka tashe ni haka da wuri?”
“Yaya ne”.
“Yayi me?”
Sai da ta shanye ragowar cornflakes din ta, tace, “jikinne inaga ni fah”.
“Kuma mune doctors ko?”
Turo Baki tayi ta ta tashi ta dauki kayan da ta hada tace, “ni nayi nan ka tashi mu tafi”.
Murmushi yayi ya mike suka fita ta Shiga ta kunna motar shikuma yaje ya Bude gate, zuwa yayi zai Shiga ya ganta zata yi reverse koma wa yayi Yana kallan ta yarda take yi har ta fita ya rufe ganin ta koma wurin ta yasa.
yace, “yau fa ke zakiyi driving din mu”.
“Baka tsoro?”
“Tsoron me?”
“Driving Dina mana”.
“Hmmm ke ko?”
Shigowa yayi bayan ta koma ta zauna suka fara tafiya shiru sukayi sai da suka kusan zuwa.
yace, “kin yi wani laifin fa tu ba’aje ko’ina ba”.
Tura Baki tafara gunguni a ciki ciki sai dai duk abinda ta fada yaji Sarai sai da ta gama.
Yace, “Biyu Kenan?”
Cikin shagwaba tace, “haba Dan Allah wai menayi ne?”
“Kinga kalli gaban ki ban shirya Zama a asibiti ba Bansan ke ba”.
“Mena maka tou yanzu?”
“Kince ummu Abdallah beda lafiya kuma nasan qalau yake, Ummu ce bata da lafiya”.
“Waya fada maka?”
“Oho?”
Daidai nan suka iso parking tayi suka fito shine ya dauko abincin sannan suka fito suna ‘yar dramern su har suka iso dakin tsayawa suka yi suna kallan juna.
Binaif ya matsa kusa da ita yace, “kema fa ashe kin Shiga…”
Rufe bakin sa tayi tace, “kana karasa wa ina cizon bakin”.
Cire hannun yayi yasa wa bakin sa alamar zip yayi shiru,hararan sa tayi tare da kwafa tana jinjina kai.
Yace, “Madam amana knocking mana”.
“Ban iya ba”.
“Baban Baby yace ayi hakuri”.
Knocking tayi Uncle yazo ya Bude, shigewa tayi ita de ta barsu a wurin suna gaisa wa Akan gado taga Ummu tayi kuka ta gaji. Zama a tayi a kusa da ita ta taba jikin ta taji da zafi sosai ta tashi ta fita bata jima ba sai gata ta dawo da Leda a hannun ta basa dakin sun ajje abincin sun fita.
Dakyar tasa ta taci wani abun ta bata magani ta sha sannan ta koma bacci ganin ta samu bacci yasa ta itama ta fita taje wurin Muja sun jima suna hira sai da taga kiran Mas’ud sannan suka yi sallama.