A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yau suka yanke zuwa gidan Binaif su bashi hakuri kuma su ba matar sa hakuri sai da suka tambayi Daddy sannan ya barsu suka tafi, driver ne ya kaisu suna.
Suna zaune yau su Duka daga su sai su a tsakar gida sun sa carpet da cushions sai hira ake gaba Daya rabin hiran yarda za’ayi bikin su Mas’ud yake tsarawa.
Mus’ab yace, “nidai bazan yi wata dinner ba wani abu babu abinda zanyi irin bikin bb za’amin”.
“Ahh nikuwa zanyi komai ai harda abin da ba’a taba yi ba zanyi”.
“Kai ai daman ba mutum bane ana bin hankali kana kawo zancen shirme”.
“Inyeeee sannu Mai hankali, kinji nace sannu ke akwai Wanda ya kaiki aljanan ci ma? Daman idan nayi aure na haihu ko me Kalar sunan ki bazan Saba kinga duk wani ummu ummu basawa zanyi ba bare nasa ma tayi Mai iron halinki”.
“Nima basa wa zanyi ba bare yabiyo halin ka ai dana sa me?”
“Aikuwa bb yace first born din sa suna na ne?”
“Kasan de abinda uwa take Kira danta da Shi shine yake binsa to sai nake Kira sa da Abba kaga shikenan bazai biyo sunan ka ba tunda akwai masu suna Abba kuma na kaishi makaranta da hakan”.
“Wai yaushe kika fara magana daman ma haka kika yi zaman ki babu im babu um,um”.
Binaif yace, “chatty Ka dame ni fah”.
Zaiyi magana aka turo gidan aka shigo tare da sallama, su Saima ne suka su duka Binaif Yana ganin su ya daure fuska, ita kuma Ummusalma ganin su sun shigo cikin sanyi kana ganin su zaka san Abu na damun su bakadan ba,Kara sowa yayi suka zauna suka gaida Binaif dasu Mas’ud, Mas’ud zoka ga Baki ance masa yaya.
Saima tace, “yaya Dan Allah kayi hakuri baza mu sake ba duk abinda muka yi Ya mas’ud kuyi hakuri duk abinda muka muku”.
Binaif yace, “Daddy ne yasa Ku ko kuma Ku kuka sanku?”
Ameera tace, “mune muka sa Kan mu, don Allah kuyi hakuri”.
Aneesa tace, “Dan Allah fa Yaya Anty kuyi hakuri Dan Allah muyi nadama kuma yanzu mun san Kan mu munsa abinda ya dace da din ma rashin samun tarbiya ne amma yanzu Insha Allah komai ya wuce”.
Fati tace, “Anty kiyi hakuri Yaya Binaif ya mas’ud ya mus’ab kuyi hakuri Dan Allah badan mu ba”.
Ummusalma tace, “kunga komai ya wuce shikenan Ku zauna dakyau Ku tashi daga durkushen nan kunji ko?”
Saima tace, “idan kin hakura Anty su baza su hakura ba, Baki San irin abinda mukayi musu ba, musamman su ya Mas’ud”.
Aneesa tace, “haka ne baza su yafe ba,bamu cancanci yafiya ba, bare kuma su yafe cikin sauki haka, sai dai tabbas munyi nadama kuma hakan bazai sake faruwa ba kuyi hakuri”.
Hawaye ne ya zubo mata, Ameera da Fati kuwa kukan ne ya Hana su magana, Saima itama kawai dauriya ce amma kana kallan idan ta zaka hango hawaye kwance a cikin idan ta.
Saima tace, “Ku tashi mu tafi muna me Kara Baku hakuri kuma baza mu dena ba har karshen raguwar mu Dan kuwa mun cutar Ku sosai kuyi hakuri”.
Tashi suka yi zasu tafi, Ummusalma ta kalle su taga suna Danna waya sannan ta kalli Binaif taga Shi ko a jikin sa ma, Kallan su kawai take kamar sun sani kuwa suka dago Kai, ta Galla musu harara ta tashi daga wurin, sukuwa har sun je bakin gate.
Mus’ab yace, “Fati”.
Ita kawai yaji bakin sa ya iya furta wa, juyo wa tayi yayin da suka kuma zasu fita.
yace, “ki Kira su”.
Sai da suka dawo Mas’ud yace, “komai ya wuce bakomai Allah ya yafe mana gaba Daya”.
Wani irin hawayen farin ciki ne ya sauko a fuskar su.
Fati tace, “amma yaya beyi magana be yafe ma…”
Bakin ta ya rufe dayake tana kusa dashi Shi Kan sa yaji tausayin su Dan da alama sun yi nadamar kamar yarda suka ce, ya share mata hawaye ta tallafi fuskar ta.
yace, “su kuka yiwa laifi Bani ba kuma sunce sun yafe muku mezan ce nikuma?”
Kallan Shi take kamar yarda yake kallan ta,idan ta taf kwalla tace, “Baka san mu ko yaya?”
Murmushi ya Mata ya goge sauran hawayen da ya zubo daga cikin idan ta.
yace, “ina matukar san ku kawai halin Ku ne Bana so kuma yanzu kun gyara I love you both”.
Ya fada Yana rungumota jikin sa,Suma rungume Shi sukayi Duka ya hada su ya rungume.
Su Mas’ud ji sukayi yau kadai sundena Jin tsoron da suke su ko dan suna tare da Ummusalma ne oho?
Murmushi Mas’ud yayi ya tashi.
yace, “Ku kunga yarda kuka yi kyau Ku tsaya a muku hoto for the first time”.
Mus’ab yace, “kowa yayi dariya zaku fi kyau”.
Murmushi sukayi su duka haka yayi ta dauka su, Ummusalma da taji Kiran fati yasa ta tsaya tana kallan su itama tana dariya babu abinda ya kai ‘yan uwa dadi ajiyar zuciya ta sauke tace, “yaushe zaki ne Neena?”
✨✨✨✨✨✨✨
Rayuwa Mai dadi aka fara a kowanne family sun zaune cikin farin cikin da kaunar juna ga wani zumunci da suke kullawa duk sati haka zata sa suje wannan wurin suje wannan wurin, kuma da daddee sosai suke zuwa gidan Baba ko Basu je ba Shi har gida zaiso babu Wanda yasan tana da ciki daga ita sai mijin ta sai Baffa shima be fada wa Inni ba Dan lokacin da suna asibiti ne Binaif ya fada masa a cikin magana, sai kuma wanda ya gane be yi magana ba sai da cikin ta ya fito sosai akasan tana da ciki wasu ma sai da yashiga watan haihuwa suka sani sanda ya fito kowa ya zaci befi wata biyar ba ko shida nan kuwa yama isa haihuwa.
Suna zaune Ida su Mas’ud tana cin Dan malili da ummu tayi mata Dan itama ummu an kamu nata Karami sai dai kuma kana gani zaka San tana da ciki.
Mas’ud yace, “wannan ciki da shegen tsifar tsiya yake, daman dan gulma ba’a fada ba har nake cewa sai na riga ku”.
“Chatty wallahi Kai kam Baka da kunya ko kadan”.
“Na Kai mijin ki?”
Mus’ab yace, “wannan ai professional ne ai amma daga Shi sai matar sa halin su Daya da yaya fa?”
“Ai kaga da yaya da bb bansan wayafi wani ba daman idan kaga suna dariya to tare da aljanun matan sa ne”.
“Kaga bb kullum karuwa abin yake”.
“Kai nifa an cuce ni Ashe shiyasa aka ce sai nan da wata biyar sunsan me suka aikata ai”.
“Chatty Ka dameni”.
Binaif ne ya dawo shida yaya suka zo tare da Ummu tana zuwa tayi wurin Ummusalma, ta zauna.
Tace, “yaya wai yaushe zaki haihu ne?”
“Waya sani na wuce edd na ai”.
“Kina haihuwa sai biki ko?”
“Ko a Bari sai kin haihu ne?”
Wani tsalle Mas’ud yayi sai da yayi cille da plate din dake gaban sa ya fashe dan ma ba komai aciki.
Yace, “idan an Isa na zama tattabara mai tashi kut”.
Mus’ab yace, “ai wallahi Nima bazan yarda ba cab”.
Uncle yace, “ehhhmm bb inaga kawai asa ranar nan nanda five months haka”.
Binaif yace, “uncle fa haka za’ayi kawai asa kaga lokacin ma Babyn bae dina ta girma”.
“Sosai ma”.
“Sai mu fadawa Baffa da Daddy da Baba harda ma Abie wallahi wannan ai cuta ce”.
Ummusalma tace, “ba wannan ba wai me kuke yi ne Kaida yaya kwanan fa sai dare kuke dawowa mene hakan?”
Ummu tace, “wallahi jiya sanda nakira din nan ma be dawo ba, sai dai ya turo su Yusuf fa”.
Kallan juna sukayi sannan suka Sosa keya, mas’ud yace, “kun fiye sa Ido wallahi”.
Ajje abincin tayi ta tashi ta wuce ciki daman tun safe take Jin cikin ta ciwo da bayan ta bata San maran ta bane ba basa bawa tayi ba bare tace hakan.
Zirga zirgan kawai ta fara yi Jin ciwon na karuwa gani take kamar zata iya daure wa amma kuma taji karuwa yake, durkusa wa tayi ta fara Kiran sunan Allah ganin fa ciwon Bana wasa bane yasa ta kwallara wani uban kara ai gaba Dayan su suka yo dakin….
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
????A BAKIN WAWA????
58
Gaba Dayan su Kan ta sukayi suna Kiran Sunan ta Sun Rasa taka mai-mai mezasu yi Mas’ud ne yafi kowa rude wa a guje ya tafi dakin Binaif inda suka ajje key din motar su ya dauko nashi yaje ya kunna motar sannan ya dawo lokacin Binaif ya kinkimo ta sun fito tarar su yayi suka fito aka sata a motar da ya kunna ana Bude masa gate ya fice a dari besu tsaya daukan kowa ba suka fice, ita ke Jin wahalar amma sune suke sun batun memakon suke Karanta mata addu’a inaa ita take yin Kayan ta tsabar Mas’ud ya rude be tsaya a traffic ba horn kawai yake danna har isa asibitin da take awo, suna zuwa suka fitar da ita sai labour room aka Shigar ta. Safa da Marwa kawai suke Sun kasa tafiya gaba dayan su babu Mai rarrashin dan uwan sa sai da Uncle yazo sannan yasa suka zauna.