A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da wani irin speed ya manna sai inda yayi parking motar Mus’ab ya gani data Uncle babu tashi babu labarin ta, da gudu yayi wurin Mai gadi ya tambaye Shi shikuwa yace ai yaga wani ya fita da ita, hannu ya daura a Ka ya dawo cikin asibiti ya samu wuri a dakin ya zauna yayi jugum yana kallan su abin tausayi Suma sai suka fara jajan ta masa suna masa jajaje duk sai sukayi kalae tausayi.
Bata tashi ba sai da Azahar lokacin duk basa nan sai Binaif shikadai Yana zaune yana kallan ta da ‘yar a hannun sa.
A hankali ta bude ido ganin sa rike da ita yasa ta tashi zaune a hankali tana kallan sa. Gyaran murya tayi hakan yasa ya dago ya kalle ta Shi take kallo murmushi ya sakar mata sannan ya dawo kusa da ita ya daura ‘yar a cinyar ta suna kallan ta tashi yayi dauko Bowl da ruwa yazo ya bata ta wanke bakin ta sannan ya hada Mata shayi Mai kauri ya bata tana kallan ‘yar tana sha.
Yace, “wanne suna za’a sa Mata?”
Bata kalle Shi ba tace, “duk sunan da nace zaka sa Mata?”
“Nifa na tambaye ki”.
Murmushi tayi mai kyau ta dago sannan ta maida Kan ta tayi Kan yarinyar tana kallan ta.
Tace, “Zulaihat”.
“Sunan ya maki? Shi kike so?”
Daga kai tayi alamar eh.
Dago da fuskar ta yayi tana kallan Shi.
yace, “kallan yarinyar ya isa haka sai kace me Jin kunya ta?”
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta kawai anan yarinyar ta farka ta fara kuka jitayi kawai ya zuge zip din rigar ta Yana kallan ta dago wa tayi alamar lafiya?
Yace, “ki bata wai Kar ki Sha wahala shiyasa”.
Girgiza Kai tayi kawai ta fara bata tana sha tare suke kallan ta sai da ta koshi sannan ya karbe ya jijjiga ta ya sannan ya Mata hudu ba sai ga Mas’ud nan ya shigo Yana turbune fuska kamar yayi kuka.
Tace, “a,a chatty me ya faru?”
Yana tura baki gaba ya zauna a wurin kafar ta.
Yace, “duk wannan small jinn dince tasa aka dauke mun mota ta shikenan ta bata motar Amarya”.
“Mtsww Kai kam sai kace wani Wawa taya za’ayi a dauke mota a asibiti? Taya hakan ya faru?”
“Kinga fa na kawo ki sai na bar key din ajiki kuma sai ban ganshi ba”.
“Kuma Basu bane suka dauka? Tun da ai Ka Riga su shigowa sune ma kawai”.
“Aljana tunda kika ce sune sune ma kawai”.
Yace, “kiyi addu’a yarinyar nan ta biyo hali na kyan ‘ya ta gaji uban ta kuma nine”.
Binaif yace, “chatty Chatty maganar Ka ko?”.
“Naji Ku tashi mu tafi na anso takardar sallama”.
Tace, “ina zamu?”
“Uncle yace de gidan Baba za’a kai ki”.
Binaif yace, “ehh nan zamu koma da Zama kafin ayi suna mu koma gidan mu”.
Jinshi kawai take besan halin Umma yarda ta tsara abubuwan ta.
Suna zuwa gidan daman an ware Mata daki ummu ce ogar dauko kaya katuwar akwati ta hado mata da kayan yarinyar da duk wani ita ce tayi suka kwaso suka Shirya Mata Shi a dakin suna zuwa kuwa umma tace su shiga sai da sukazo sannan aka fara Kira Daya bayan Daya ana sanar wa ta kuma sanar da maman Sadiq sosai tayi mamaki dan sun Dan jima Basu hadu ba sai ta waya ko chat. Neena tana ji suka taho da yamma kuwa sun iso a gidan ta sauka nan fa aka fara zuwa kowa Yana so ya ga ‘yarinyar.
Sao dare su Baffa da Inni suka zo ganin ‘ya sosai akayi wasa dariya sannan suka musu Sallama zasu tafi. Anan Baffa ya nemi da yaga Binaif kebe wa sukayi su biyo.
Wasu takardu ya Ciro daga aljihun sa ya Mika masa.
Yace, “gudun mawa tace zuwa gareka Ka rike na Baka ya Zama naka”.
Bude wa yayi yaga company ne a bangaren abinda ya Karanta architect dagowa yayi ya kalli Baffa.
Baffa yace, “Bana San wata godiyar ka nakane kaima Dana ne babu banbanci tsakanin Kai da su”.
“Amma Baffa Ka hadu da uncle munir ne?”
Murmushi Baffa yayi yace, “ehh mun hadu Amma sai bayan mu koma wannan rashin lafiyan ta maman su sannan muka hadu anan yake fada min komai har Paris ai naje daga nan kawai Nayi deciding gina maka naka kaima dukda kana wani aiki ta online but ina so Ka hada biyu”.
“Nagode Baffa bansan mezan ce maka Bama”.
“Nace fa Bana San godiyar ka”.
Murmushi yayi yace, “Baffa gobe idan ba damu wa zamuje wani wuri”.
“To Allah ya kaimu”.
Daga nan hira ta barke tsakanin su baza Ka taba cewa ba siriki da siriki bane ba.
Mas’ud yazo ya zauna yace, “Baffa kafi san bb Akan mu Naga wannan”.
Murmushi Baffa yayi yace, “Kai mus’ab ba zaka canza Hali ba komai Ka tara”.
Turo Baki yayi Shi baza’a masa ba magana kyaleshi Baffa yayi daga nan ya tashi suka tafi.
Ranar suna kowa su Mas’ud da Mus’ab ne sukayi komai da komai duk wani Abu da ake sune suka siyo na siyowa suka bada kudin na bayar wa Binaif duk yarda yaso ya hanasu Kin hanuwa sukayi.
Sai ranar suna suke Jin sunan da aka saka tsabar murna da Daddy yaji rungume Shi yayi harda kwallar sa da yake babu Wanda ya tambaye Shi sunan da yasa mata haka ma Baba sukayi tasa masa Albarka shidai besan me ake ba amsar tambayar sa Naga Ummusalma.
????????????????????????????
“Nifa Mahmud tafiya zanyi gaskiya bazan zauna ba Akan me kawai Ka Rasa Wanda zaka rabawa kudin Ka sai yaran ka? Ka iya Ka siyo mata Kaya har su gado abinda kayi Ka kyauta Kenan?”
“Ban kyauta ba Kenan? Na Basu ne don su rike sabida gaba zaiyi musu amfani yanzu suka fara karatu level two zasu Shiga fah Sameera ita kuma Allah yayi ta Gama idan ta samu aiki mijin ta ya yarda tou idan kuma bata samu ba haka Allah ya kaddara”.
“Hmmm kaje Ka zauna tare da yaran naka nafasa ganin auren sameeran bazan zo naji kunya na tattare yenawa zanyi na bar kasar ma gaba ki dayan ta yau basai gobe ba wallahi, wannan abin kunyar har ina?”
“Abin kunya ne?”
“Abin kunya ne mana”
“Yanzu ke baza ki iya Zama Dani ba daman a halin akwai ko babu?”
“Kaga ina Sanka amma San kudin Ka yafi yawa kuma yanzu na dauki rabo na ni zanyi nan ko sake ni ko Kar ka sake tafiya zanyi”.
Numfashi yaja zuciyar sa na masa kuna sosai da sauri ya tashi ya hau Sama ya sha maganin sa ya kwanta, Yana tunanin inda zai ga Ummusalma Dan tabbas ya ganta da Idan sa.
“Allah yasa na ganki na nemi yafiyar ki ki yafemin ki yafemin”.
Bama iya sanin abinda yake fada kawai wannan ne yake zuwa masa bakinsa Yana furtawa.
Mama kuwa kayan ta ta zuba tsab a akwati ta saka doguwar Riga da mayafi ta hada duk wasu important documents nata ta zuba a cikin jakar hannu ta janyo jakar ta ta Shiga dakin sa, daga bakin kofa ta tsaya.
tace, “to Alhaji Mahmud ada a yanzu kuma Fakiri Mahmud nayi nan bazan iya dauka ba ace kullum nice Zan keyin Abu a cikin gidan nan ko Ka sake ni ko Kar ka sakeni duk uwar uban su daya”.
Ta bankoda kofa ta fito tana sauko wa suna shigowa.
Yusuf yace, “Mama ina zaki?”
Tace, “Dubai Zan tafi”.
Yaseer yace, “ko yaya Sameera zaki siyowa Kaya”.
“Hmmm Yara Kenan tafiya zanyi nagaji da Zama a gidan nan kuci gaba da Zama da ubanku da ya Zama dolen ku amma Bani ba kunga tafiya ta”.
Da sauri suka sha gaban ta.
Yusuf yace, “Abban sakin ki yayi?”
“Wanne saki? Nice nayi ra’ayin tafiya da Kai na babu wani saki”.
Sameera data sauko Dan zuwa kitchen ta zuba abinci taji abinda yake faruwa.
Karaso wa tayi da sauri ta rike jakar tace, “Dan Allah Mama karki tafi ki barmu”.
“Ke Dan uban ki sanda nazo gidan nan ni kadai na tafi yanzu ma ni kadai Zan koma ba shikenan ba?”
Durkusa wa sukayi suka rike ta suna kuka sosai suna rukan ta Banda Yusuf da zuciya ta fara ciwo Shi Yana kallan su Yana kallan ta kafa tasa ta hanka da Sameera data rike kafar ta Saida ta bige da jikin stairs din su goshin ta ya fashe kadan da jini amma bata ji ba ta kuma tashi zata ruko ta yusuf ya tare ta, haka yaseer ma hannun tasa ta falla mishi ta ture Shi tare da Zan jakar ta ta tafi yaseer da gudu zai bita Yusuf ya cakum Shi.