A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace….

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????

????A BAKIN WAWA????
Akanji magana

 59

Yace, “Sai me dan ta tafi? Ta nuna bata san zama da mahaifin mu da mu kuma, ba Shikenan ba? Kowa ya tafi yayi rayuwar sa muma zamuyi raguwar mu cikin farin ciki da kaunar juna munan zaki dawo ki tarar damu”.

Wani murmushin takaici yayi Yana kallan ta ta tsaya tana Jin abinda yake fada.

Yace, “Hmmmm kin tafi ne sabida Abba beda ko sisi ko? Kin tafi ne sabida yayi karayar arziki ko? Kar kidamu Shi ai kudi ba dashi ake zuwa lahira haka ma ba daura su ake a wuya ana yawo ba naga dubban mutanen da suke rayuwa babu ko sisi Naga mutanen da suke cike da farin ciki Basu da kudi idan kin tafi baza mu mutu ba bakuma zamu ji ciwo ba kwarzane Daya bazai rago daga jikin mu, ki tafi duk inda zaki tafi”.

Kallan Sameera yayi ya nuna ciwon da taji yana jini.

Yace, “lokacin da kika dawo zan nuna maki abinda kika mata Akan hanaki tafiya da tayi daga karshe ki gode wa Allah ‘yar ki bata sallawan ta ba ta Shiga duniya Allah ya tsaida abun iya haka”.

Juyowa ta danyi tana kalla shi, sannan kuma ta juya.

Tace, “Yusuf kenan na yarda kai yaro ne, Zan tafi bazan ma dawo ba bare har na ganku I knew lokacin da Zan dawo gidan nan ya tashi daga gida ya koma kango me Zan dawo nayi kuma? Allah ma ya sauwake ai naga ba yayi gaba na Baya kuwa anan a Baya zai kare idan Banda abinda abinka waka taba gani yayi arziki a lokacin da ya girma? Ai babu sannan Mai kudi har yau Mai kudi ne marar kudi kuma har yau marar kudi ne situation din baya canzawa ko ina kuwa kaje a fadin duniya kaga na tafi”.

Daga nan taja jakar ta tayi gaba, kuka suke sosai Yaseer da Sameera hada su yusuf yayi ya rungume wani hawaye ma dumi Yana zubo masa. Abba kuwa wani irin tausayin su yaji sun taso sun Saba ganin ta yanzu kuma ta tafi zuciyar sa kuna take sosai a hankali ya juya ya tafi dafe da zuciyar sa dake masa zafi gashi be jima da Shan magani ba kwanciyar yayi Yana damke takardar dake hannun sa ta sakin ta da yazo bata.

Cikin parlour ya mayar su ya zaunar sannan yaje ya dauko fisrt aid yana gyara mata ciwon ta sannan ya fara rarrashin su dakyar ya samu sukayi shiru duk da shima zuciyar sa tasa kukan yake so yayi ji yayi duk wani haushin Abba da yake ada sai yaji ya dena ya tattaro da na Abba da Wanda yake yiwa Mama Duka ya hada Mata Yana bubbuga bayan su ya samu suka yi bacci kowanne ya kwanta Shi sai anan wani hawaye ya zuba masa yasa hannu ya goge sannan ya haura sama dakin Abba a kasa ya ganshi Yana numfashi dakyar da gudu yayi kansa Yana Kiran sunan sa Zuwa yayi ya tashe su suka yo dakin da gudu suka ciccibe Shi suka sa Shi a motar da tayi saura a gidan sannan sukayi asibiti suna zuwa aka karbe Shi aka Shigar da shi sunan nan suna safa da marwa hawan jinin sane ya tashi ga damuwa wanda yake nema ya taba masa zuciya.

Su Duka anan suka kwana daman anyi hutu babu makaran ta kwanan su biyu ba’a sallame su ba a kudin da ya Basu na makaran ta anan suke biyan komai da komai.

✨✨✨✨✨✨✨

Baffa da uncle sai Binaif a cikin wani gidan Mai Dan Karan kyau dashi upstairs ne gidan yayi kyau sosai gidan Baffa Wanda suka Gina masa sosai gidan yayi kyau ba kadan ba, Sai da suka Gama gani.

Baffa yace, “amma zaku zo mu zauna koda na kwana Daya ne kafin su Mas’ud suyi aure ina San Naga family na a hade Dan Allah”.

Kowa rike hannun sa yayi.
Binaif yace, “haba Baffa babu zancen hada mu da Allah kaifa babammu ne umarni kawai zaka bamu mubi”.

Uncle yace, “haka ne Baffa Kai da su Baba duk Daya ne Kaine de Ka haife mu su kuma suka Rene mu ko cawa kayi su bar maka ‘ya’yan Ka zasu barma”.

Murmushi yayi Mai kyau yace, “kuma bazan ma ce ba har abada yarda duniya tasan Kai Dan sa ne haka zata cigaba da daukan”.

Tare suka fito suka tafi gidan Baba sukayi Baffa ya ruki alfarmar a bashi su Baba.

Baba yace, “ni yanzu Banda iko Akan su ai sunyi aure fa ko Ka manta? Suna da ikon kansu mu namu idan sunyi ba dai-dai ba shine zamu musu fada”.

Baffa yace, “nagode sosai de har yau ina godiya”.

Baba yace, “ai bikin ma ayi acan a gidan naka shikenan ma kawai sun huta zirga zirga”.

Baffa yace, “to shikenan Allah ya nuna mana”.

✨✨✨✨✨✨

Sun tare a gidan su kowa Yana nan amma Binaif da su Mas’ud ba’anan suke kwana ba a gidan Binaif suke kwana da safe kuma sai su zo suci abinci anan.

Ummusalma kuwa da ‘yar ta wacce suke ce Mata pretty Mas’ud kuma yace Mata genios babu Wanda yake Kula Shi bare ma ayi dashi sosai suke samun kulawa wurin jegon su bata musu idan aka ce tayi yi take yi.

Suna zaune a parlourn kasa iya su ya su yau sati biyu Kenan dayin suna Pretty tana hannun Ummu Dan ita Dan tazo babu Wanda yake daukan ta ko Inni ce ta dauke ta a wurin zata zauna har sai an bata ita.

Mas’ud yace, “Biki saura kwana 10 hehehe waya ganni a babbar riga”.

Ya fada Yana washe baki yana wani kwalalo Ido.

Ummusalma tace, “taaab waya ga Aljani a kwabet”.

Dariya su Ka saka masa shikuma ya daure fuska.

Yace, “nifa da kika haihu kin ma fi surutu wallahi ko mutum be maki magana ba sai kin masa ni daman a rashin maganar ki Kian zauna har yanzu Dani ji dadi”.

“Chatty kake Jin tsoron Allah Naga sanda bana maganar kafi kowa Jin haushi na yanzu ma?”

Neena tace, “taaab inaga Ya mas’ud sanda kuka hadu yarda kake bada labarin nan de lokacin tana magana”.

Mus’ab yace, “Neena kin kuwa Santa a lokacin?”

Mas’ud yace, Kai kyaleta wani irin ta fimu sanin ta din nan”.

“Shekara nawa kuka yi da ita ne?”

“Shekara har biyu mukayi da ita”.

“Nima kusan hakanne ai amma nidai nasan tana magana in fada maka wataran har tazo ta tafi daga school bazata ce uffan ba”.

“Caab Dani ne ai ko taab ai sai tayi”.

Haka suka ci gaba dayi wannan yayi wannan yayi can kuma akayi shiru kowa yayi shiru.
Kallan su tayi taga kowa hankalin sa na kan waya kawai ta tuntsire da dariya kallan ta kowa ya dawo dashi gare ta da’alamar tambaya.

Binaif yace, “Mi Amor what’s?”

Tsagaita dariyan tayi tace, “wallahi Chatty na tuna”.

“Dana yi me?”

“Dan Allah karki tafi wallahi ina sanki nama fi Binaif san ki kinga nadena ce maki aljana na dena ce maki komai na dena tsokanar ki nadena fada da dake nidai Kar ki mutu kinga har Anty Ummusalma Zan ke ce miki karki tafi ki barni Dan Allah kinji I love you so much Walidan Inni kinga ma ko…”

Wurga Mata pillow yayi yace, “kuji sharri fa kida kina cikin halin wuya taya ma kika San wannan nifa bansan sharri nidama idan nayi aure …”

“Babu Wanda zaije gidan Ka idan kuma Ka haihu babu Mai daukar maka yaran Ka”.

Mus’ab ya Kara sa.

Uncle yace, “kasan Mas’ud har mamaki kake Bani? Ace Sam Baka da kunya ko kadan”.

Turo Baki yayi yace, “Ku ai kunyi auren shiyasa amma zaku gani ai babu Mai zuwa min gida Umma ce kawai bata min fada har Inni da Baffa ma duk ba zuwa zasu yi ba”.

“Da wa zaizo muzo aka koyawa ‘yar yarinya ta surutu da Mita da fada da tsoro ko me?”

Tashi yayi ya yo kan ta tana ganin haka ta mike tayi Baya kujera suka fara Binaif kawai kallan su yayi ya girgiza Kai ya cigaba da Danna wayar sa.

“La’ilaha illallahu Muhammadur rasulullah yanzu Dan lalace wa mai jegon ce take gudu? Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un yau ni Zainabu Naga abinda ya fi karfina jego da gudu? Kaii abun nan da ake anya ke kika haihu kuwa? Waima ina su Iyayen naki ne ma wai? Yanzu Maryma din barin ki tayi kina dididar gudu haka?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button