A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace, “wannan yarinyar Bata dariya ta biyo Aljanar Babar ta”.

Ummu tace, “to aka ce maka yanzu zata fara dariyan”.

Yaseer yace, “Nima naza ci ai yanzu zata fara Nima nayi nayi tayi dariya bata yi”.

Uncle kuwa daure fuska yayi Baya magana, mus’ab yace, “Yaya lafiya kuwa? Naga kayi shiru sai daure fuska kake”.

Harara yayi shiru yace, “Duk ba Ummusalma ce ta ja ba? Nida ba haihuwar tayi ba amma azo a wani wannan”.

Binaif ne kadai yasan Kan zancen Dan dazu yaje wurin Inni yaji tana masa fada besa kunya kuma matar sai gobe idan an Kai masa ita ya cillo ta yace Baya so, murmushi kawai yayi Yana kunshe dariyar sa Ashe ba Shi kadai bane yake jegon.

Mas’ud yace, “Nifa bangane ba”.

“Ina zaka gane Ku kyale ni ko na Karya mutum”.

“Allah ya Baka Hakuri Yaya Dan Naga kaima Halin Ku Daya da oo”.

Mus’ab ne ya tashi ganin wayar sa na kara Mas’ud yace ina zaka je?”

“Kasan ni ba yaro bane ina waya da mata ta wani kuwa har yau banji Yana wayar ba Ande ji asara”.

Biyo Shi yayi da gudu suka sauka kasa wayar ma har ta Riga da ta tsinke.

Inni tace, “meye haka? Bafa nasan shashanci da hauka meye na gudu haka?”.

A tare kowa ya nuna Dan uwansa.

“Ai daman baza’a taba samun waye ba Kun girma Baku San kun girma ba ko? Ku wuce ku ban wuri”.

Kamar jira suke tafada suka Kara mannawa da gudu girgiza Kai kawai tayi ya shige kitchen.

Biki sosai aka fara gudanar wa ta kowanne bangare daura auren Muja aka fara zuwa daga nan akaje na Sameera Baffa babu abinda yace da aka sanar dashi waye sai ma farin ciki da yayi hakan. Ba laifi ‘yan uwan su Sameera sun zo a bangaren Abba sunzo sosai Ashe suna da ‘yan uwa iya Abba yake sada zumunci da Shi kadai sai da bikin nan suka dan San juna sosai akayi biki har auren Daddy an daura, babu abinda akayi bangaren amare ne kawai sukayi kamu kuma da daddare za’a kai amare Mas’ud duk zumudin Shi sai yaji Baya son barin gida gaba Daya ji yayi auren ma ina kuka kawai yake so yayi Shi ko yaji sanyi, duk da yaji dadi sosai da yin auren yasan da badan Ummusalma ba da komai ya watse yasan hakura kawai zaiyi hakuran da zaiyi kuwa dai-dai yake da Mutuwar sa Shi yasan wannan.
Tare suka dawo gidan lokacin anyi Azahar sai da suka tsaya sukayi sannan suka dawo gida kayan su iri Daya inda su Binaif sukayi iri Daya Suma har su yusuf amma su basu biyo su ba kawai da aka daura na Sameera suka tsaya a can Ummu ma tana can ita ce kawa.

Suna Shiga gidan ya kaca me da surutu hayani ya kawai hutunan aka yi suka wuce gidan Baba ba kowa sai su Ummusalma da su Fati Neena ma ta tafi inda ake harka ita da ummu.
Basu ma San suna gidan ba sai da suka je suka gansu kowa harkar sa yake Yana Danna waya.

Ta fito daga kitchen Kenan hannun rike da cup ta gansu.

Tace, “a’ah Alhaji Chatty an daura auren fa ko?”

Kallan Binaif yayi da idan sa da yaji zai kawo ruwa.
yace, “can I hug her?”

Murmushi Kawai Binaif yayi tare da Gama masa Kai.

Tace, “wacce gulmar kake”.

Ganin sa da tayi kawai ya rungume ta Lemar da taji ya taba ya bata tabbcin kuka yake…

BY: Hijjart abdoul
Cwthrt????

???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

         61
      *_last page_*

Abin ya bata mamaki sosai da dayan hannun ta ta rungume shi,du sai taji ba dadi sai da ya gama kukan ya dan share hawayen sannan ita kuma tana bubbuga bayan sa alamar rarrashi can ya dago, ya kama hannun ta ya zaunar a Akan kujera shikuma ya tsugunna a kasa ya kama hannun ta yana kallan ta.

Yace, “bansan ta ina zan fara ba,bansan wanni irin godiya Zan Miki ba, ban kuma san zance maki ba, all I can tell you”.

Shiru yayi yana goge hawayen sa sannan ya kuma kallan ta.

“Thank you”.

Kurban abinda ke hannun ta tayi.
Tace, “chatty lafiyan Ka kuwa?”

Murmushi yayi Yana kallan ta yace, “lafiyar ce ta kawo haka, da’ace bake to da bansan ya zanyi ba da tuni ta jima da Zama matar wani but…”

“Chatty enough please! Ya isa haka Ka tashi kaje Ka zuba abinci naji bansan Jin wani zance kuma”.

Binaif ne ya zo ya daga Shi Yana daga Shi shima Yana rungume Shi, zaunar Shi yayi a kusa da ita ya kamo ya kama hannun Mus’ab shima ya zaunar.

Yace, “Bari ayi muku hoto”.

Tace, “Kasa ango chatty Yana kuka ranar Auden sa zai rabu da kauwar sa”.

Dariya sukayi shi kuma ya maka harara aikuwa Binaif ya dauko su sunyi Dariya shikuma ya maka mata harara daga ana suka fara hotuna kowa da kowa har sosai sukayi hoto harda pretty tana bacci chatty ya tashe ta wai sai ta bude Ido du Shi ya rike ta akayi tayi sannan aka zauna aka fara cin abinci sun gama Kenan sai su Mariya yayun sa su Duka biyar din Banda hunaifa suka zo ko waccan su ta bada hakuri sosai Yarda suka mata uwar mijin su ta fara uzura masu da kannai Ashe Ummusalma ce ta hada wannan abun da ta bincika taga duk wayancin siblings din mijin su sunyi makarantar Daya dasu shine ta kitsa ta hada wannan abun takuwa nuna ko a jikin ta ba abinda ya faru komai ya wuce.

Mariya tace, “Saima ko san inda su Hajiya suka tafi kuwa?”

Saima tace, “wallahi bamu san Inda suke ba, wayar su bata Shiga tun sanda nayi waya da Hajiya tace min wai suna Dubai daga nan zasu wuce China bamu Kara waya da su ba”.

“Kuma kin kira su bayan nan?”

“Ai bata shiga”.

“Allah de yasa lafiya”.

“Daddy de yace zasu dawo Amma kinji shiru”.

Kowa shiru yayi sukuma suka ci gaba da rahar su Basu, basu wani jima ba suka ko gidan biki.

Da daddare aka tara su gaba dayan su aka musu nisaha mai ratsa jiki da bargo kowa sai da ya musu ba iya su kadai har su Binaif aka hada.

Daddy yace, “Mas’ud Mus’ab gidan danace Zan Baku Ashe ma wai yayan ku ya riga da ya gina muku tare Sai dai muce Allah ya bar zumunci ya kuma kare mu daga sharrin masu sharri”.

Da ameen kowa ya amsa, suna fita.

Mas’ud yace, “Finally!”

Ummusalma tace, “kayi aure saura haihuwa nan da gobe ko?”

Rufe idan sa yayi a bayan uncle.
Uncle yace, “fito nan naganka waye Kai da zaka ji kunya ai baka isa ba gaskiya ta fada”.

“Haba Dan Allah yaya kunya kuke Bani”.

Girgiza Kai kawai Mas’ud yayi ya fice ya Shiga mota haka ma uncle sune a gaba su kuma a baya Ummusalma kuwa sai yazo zasu tafi.

Mas’ud yace, “Yana ga Ka dau hanyar gidan Ka nifa ba yau nayi shirin zuwa na kwasa Kaya na ba sai nan da kamar sati haka hudu zaka ganni a gidan Ka”.

Mus’ab yace, “gaskiya ce nima haka”.

“Ai shine ni duk zumudi yabi ya cika ni Kai ma haka kaji?”

Gashi daman ba gudu yake ba sai ya Kara rage gudun Yana tafiya a hankali yau shine har da su sa waka yana tafiya.

Mus’ab yace, “hafa bb yada haka? Kayi gudu mun fa gaji muje muga Amaryar mu”.

“Dama ban shigo motar nan ba”.

Banza yayi dasu ko tanka su beyi ba sai ma tsaya wa da yayi yab fita.

Mas’ud yace, “shikenan tana can tana jira yau na ga ta Kai na”.

“Kai dai bari daman ma Uncle ne ya amsa tukin”.

“Uncle ka ansa tukin kaji ko”.

Incl yace, “tunda Ka taba gani na a kitchen ina tuka tuwo ba?”

Binaif ya dawo hannun sa rike da Leda guda hudu ya ajje musu biyu a Baya suma ya ajje musu.

Mas’ud yana turo baki yace, “ranar auren naka ma ace wai sai an bata maka rai ni da yake Allah ya zuba min hakuri da juriya bakomai nayi aure ai Nima za’a ake faran tamin rai”.

Uncle yace, “kasan har yau bata ci kazar Amarci ba kullum Mita ake min”.

Murmushi Binaif yayi yace, “Ku ai ban taba Jin irin Naku ba kafa birgeni mutumi na”.

“Ahh dawa zai zauna taab ba gashi an sallame ni ba, dafa sai na warke ras harda wani karani bed rest na sati kaji fa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button