A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya fada Yana wani lumshe ido,cire hannun sa tayi tace, “kaga asibiti fa muke zake tabani salan wasu su fara thinking otherwise”.

“And so?”

“Hmmm let’s go”.

Hannun ta ya kama suka Shiga ciki ganin su sun tare a wuri daya suna ta hira yasa suka karasa wurin gadan ya zaunar ta shikuma yaje ya tashi Mas’ud ya dauki kujera daya ya koma kusa da Shi ya zauna.

Ummusalma tace, “kunzo kun wani tare kuna damun marar lafiya haka ake zuwa dubiyar su Chatty harda tafa hannu sannu tou”.

“Ai daman ni kika Rena ga marenin wayon ki duk wurin nan ki rasa Wanda zaki Kira sunan sa sai ni, Bari de Nayi aure nan duk Wanda Baya respect dina bazai je gidan na ba”.

Binaif yace, “wai gidan nan nawa ne da Kai ne? Gidan har yanzu be kare bane ayi ta fada ayi ta fada abar Shi haka mana”.

Turo Baki yayi yace, “daman ai Ka kwace min kujera kuma kake fadar haka dole ai wallahi bakomai zaku gani ai idan anyi auren”.

“Chatty Allah ya shirya min kai”.

“Ji ‘yar renin hankali? Sai kace ita ce babba hmmm”.

Mus’ab yace, “dude rabu da su kawai let’s continue”.

Ummusalma ta kalli uncle taga wani annuri a kwance a fuskar sa Yana murmushi kawai Yana kallan su kana gani zaka san kawai yana cikin annash wa da murna.

Tace, “Yaya kana San ummu?”

Kallan sa ya dawo dashi kanta.
yace, ”me yasa kika ce haka?”

“Yaya please kana San ta?”

“Ina san ta mana she’s part of me ada nazaci kawai son Da da uba nake mata by the time nasan komai nasan ba hakan bane amma nasan ummu will not marry me because am not…”

Binaif ne ya katse Shi ta hanyar cewa, ”idan kuma itama tana san Ka fa?”

Kallan Shi ya dawo Kan Binaif, Binaif ya daga masa Kai.

yace, “yes”.

Tace, “ehh ummu loves you too,kade na kawo komai a ranka ummu na Sanka sosai kuma Ka yarda dani and kasan wani abu?”

Girgiza kan sa yayi alamar a’a.

Tace, “Yanzu fa Kai na Ummu ne Ummu taka ce”.

“Bangane ba? Me kike so ki fada ne haka?”

Binaif yace, “abinda Ka gane Kenan yau aka daura muku aure da Ummu.

Tace, “sabida tana sanka ne hakan ya faru da bata Sanka kasan Baba da Abie baza su yarda ba”.

Wani irin farin ciki yaji ya ziyarci ilarin jikin sa taso wa yayi zaiyi tashi da sauri Binaif ya daga Shi tare da Danna wani Abu na gadan a hankali gadan ya taso yayi daidai yarda yake so sannan ya tsai dashi, hannun sa yasa Wanda be iya daga wa sosai ba ya kama nata cikin dariya Dariyan tsantsanr farin ciki.

yace, ”Please Ummusalma are you serious?”

Daga masa Kai tayi sosai tsabar fari ciki kallan Binaif yayi.
yace, “Bansan me zance maku ba, nasan kune silan faruwan wannan abun nagode nagode sosai thank you so much Binaif”.

Murmushi Binaif yayi yace, “farin ciki ka shine namu”.

Sakin hannun ta yayi yace, “bata zo ba yau”.

Tace, “taya zata zo tana Jin kunyar Ka?”

Dariya yayi sosai da tunda ya farka beyi irin ta ba, sai da ya tsagai ta. yace, “yau ce ranar da Zan tuna Mata abinda tace”.

Murmushi yayi ya kalle su ganin Suma murmushin suke yace, “ca tace baza ta taba Jin kunya ta ba sai gashi yau tayi wonders”.

Hira suka Shiga yi duk wayan cin ta ta Baffa ce da Inni.

Mus’ab ya zo yace, “ake de Jin tsoron Allah ana Sawa da mutane a hira kuma nasan gulma ta ake”.

Uncle yace, “ko sannu da jiki Baka min ba kana zuwa Ka hau hira da besties dimmu”.

Rufe idan sa yayi alamar kunya, tace, “wai Naga chatty da kunya nikuwa?”

Mus’ab yace, “Baki gan Shi ba sanda yaje wurin Binaif wai Yana son a nema masa aure ke kinga yarda yake wani sunne Kai kuwa?”

Binaif yace, “ai Allah ne ya taimake Shi bata nan da tana nan ya Shiga ukun sa”.

Turo Baki yayi gaba yace, “yanzu idan mutum beyi ba ace beyi ba yanzu da yayi kuma ace wani wani waye waye”.

Uncle yace, “yi hakuri tou na Baka hakuri Naga kowa yi maka yake”.

“Yawwa bros shiyasa nake yinka over irin sosai kade gane din nan”.

Tashi tayi ta tafi ta barsu suka zaga ye Shi wannan yayi wannan yayi shidai shida Binaif iya Kar sh dariya kawai.

Tana fita tayi male ward wurin gadan su Muja Sai dai ganin mutumin da tayi a wurin gadan yasa taja ta tsaya, ita kuma Muja tana durkushe a gaban sa tana kuka tare da rokan sa, ji tayi mutumin na.

cewa, “ko kukan jini zakiyi sai kin auri wannan bawan Allah kima ji dakyau a to wannan umarni nane Bana kowa ba ko mutu ko kiyi rai ko ko uban ki ya warke ko Kar ya warke sai anyi wannan aure babu fashi”.

Karasa wa tayi ta daga Mujahid ta goge Mata hawayen idan ta ta kalli Mutumin da take tunani kila shine dan uwan baban nata Ido cikin ido tana kallan shi.

tace, ”Maryam daman Baki sanar dashi cewan ansa ranar auren ki ba?”

Yace, “ke yarinya zancen me kike haka? Wacece ma ke da?”

Murmushin gefen baki tayi tace, “bakowa bace sai ‘yar gidan wani bawan Allah Mai suna Muhimman Uthman Wanda ya rasu Shekaru ashirin da daya kenan a wurin jama’a idan Kai din mazaunin Abuja ne nasan zaka sanshi kodan kudin sa”.

Shiru yayi Yana kallan ta da mugun mamaki, wani murmushi tayi Mai kyau.
tace, “da’alama Ka sanshi kenan,hakan yayi kyau sannan kuma Dan sane yake neman auren harma ansa rana nan da wata biyar masu zuwa Insha Allah idan muna da rai da lafiya kaga kuwa babu zancen nema Kan neman sai dai idan mune muka zanje”.

Yace, “ke karki rena min hankali mana beda ‘ya’ya ko daya shima kuma ya mutu”.

“Da’alama Baka fahima ta sam a wurin jama’a nace maka Amma a wurin mu Mahaifin mu be mutu ba yana zaune a Gumel idan kana so kace Ku gana am I cleared?”

Juyowa tayi kan Muja tace, “a fuska de kamar mai wayo Ashe babu”.

Zama tayi a gefen Baban ta tace, “Abba na sannu da jiki ya karfin jiki jikin?”

Murmushi yayi Mai kyau yace, ” ‘yar ta Alhamdulilla jiki yayi dama dama dan tun safe akayi aikin kuma ko yaunzu garau nake ji zan iya ma tsera dake”.

“Anya kuwa Abba na?”

“Ehh mana ‘yata?”

Takaici ne ya ishe Abban Abuja ya sa Kai ya fice, Abban muja.
yace, “mena ji kina fada haka?”

“Abba na hakan yake yaya na ya gan ta tun ba yau ba tun a Abuja kuma Yana San ta bansani ba ko akwai Wanda take so”.

“Sabida haka kika taimaka Mata?”

“Ko kadan Abba badan haka bane tun kafin nasan ta na taimake ta ban Sani ba sai da muka je da ita zata sa min number sai da ma ta tafi sannan yake sanar min bansani ba ko bata san yaya na hakan ba zai sa taki zama kawa ta ba”.

Kallan ta yayi yace, “kinda Wanda kike so?”

Girgiza kai alamar a’a.

Yace, “to shikenan bakomai sai kun turo magaban tan naku idan Allah yasa an sallame mu daga asibiti”.

“Abba mungode sosai Bari na Kira Shi sai Ku gaisa Ka ganshi”.

Kiran shi tace ya same ta a male ward, tunda ya shigo Muja tasan shine don idan ta Akan kofar itakam tana nan kuma bata zauna ba, shikuwa bema lura da ita shida mas’ud ne suka zo, suna ganin ta suja yo wurin itama suj take gani.

Suna zuwa Mas’ud yace, “ya akayi irin wanna Kira haka?”

Banza tayi dashi kamar bata jiba ta kalli Mus’ab ta masa signing da Ido, sai anan ya lura da ita shidai kawai yaga mutum a tsaye daga can gefe besan kuma komai ba, matsawa yayi ya karasa shima mas’ud ganin haka yasa ta Karasa a kusan tare suka durkusa Shi mas’ud duk abida mus’ab yayi shima yake yi.

Mus’ab yace, “Ina wuni?”

“Lafiya qalau”.

“Ya saujin jiki?”

“Alhamdulilla”.

“Allah ya Kara sauki”

Da ameen ya amsa shima Mas’ud gaida Shi yayi tare da yi masa ya jiki. A kasan tabarma suka zauna da shidai Mus’ab kansa a kasa be Kara cewa komai ba Mas’ud kuwa bigewa yayi da cin Ayabar da Abba ya masa bismilla Shi be kawo ba shida cinye wa nan fa hira ta barke tsakanin su sosai hakan ya yiwa Abba dadi anan yasan waye sirikin nasa ita kuwa fita ma tayi ta basu waje tu kafin su lura da ita sai dai kuma Mus’ab yaganta sanda ta fita sai da ta jima da fita ganin hiran su ba karewa zaiyi ba, yasa ya dauki wayar sa ya Mata message.
Sai da kalle Shi sannan tayi yarda yace, Kiran wayar Shi tayi irin ana Kiran nan nasa yasa takalmi ya fita Yana daga wa kamar gaske.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button